Sashe 7
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yamai girma Mai shariah ayaune ranar 28 ga watan June , kotu zata saurari karar da akeyi na Fatima Zahra wadda ake zargi ta kashe Dan sarki yarima habib Kuma babban Dan siyasa,
Bayan anmikama alkali takaddun shariah ya Kara gyara gilashin da ke manne a idonshi Wanda ya fiddo da aynihin kamalar sa da dattako na shekarunshi....
"Koh lauyoyin Wanda ke Kara da wadda ake zargi suna kotu?".
A hankali Kabir ya Mike cikin kayanshi na lauyoyi wadda suka mutukar amsar fatar jikinshi ,ya gyara rigar lauyoyinshi yace cike da dakiya da jarimta
"Yamai girma Mai shariah sunanan Barr Kabir Mahmud nine lauya, Wanda zai tsayama marigayi yarima habib"yadan rankwafa alamar girmamawa
Cikin natsuwa Barr hauwa muazu ta Mike cike da kamala sannan tace" my Lord sunana Barr hauwa muazu nice lauyan Mai Kare wadda ake zargi tare Dani akwai
Barr abduljabbar "...shima ya rankwafa alamun gaisuwa sannan suka zauna ......
Yan rubuce rubuce alkali yayi sannan yace
"Koh lauyan Wanda aka kashe nada bayani"
Itadai Fatima tunda aka shigo da ita aka tsaidata a inda ake ajiye masu laifi idanuwanta a kasa suke yayinda zuciyarta keyi Mata lugude,Sai yanzun ne da alkali yayi wanan tambayar ta da'go kanta ta sauke idanuwanta akab yarima take zuciyarta tayi rauni Jin abinda yace
"Inadashi Mai Lord" cewar barrister kabir.....
" Kotu na sauraranka" .
"Inaso kotu ta bani dama domin in yima wadda ake zargi Yan tambayoyi"...
"Kotu ta baka dama Barrister"
A hankali ya taka cike da natsuwa ya Isa wurin da ake tuhumar masu laifi sannan ya kalli fatyma Zahra ....wani Abu yaji ya sokesa ga katon zuciya tamkar kibiya,da kyar ya tattaro dik wata natsuwa tasa dake neman guduwa daga jikinsa ,ganin yadda fatyma tafita hayyacinta ,cike da jarumta yace
"Kotu zataso tasan sunanki????"
Kamar bazatayi maganaba , sannu a hankali ta daga siraran lips dinta tace ,"sunana fatyma Zahra"a takaice tayi maganar
Sosai ya Kara daurewa tare da Shan kunu tamkar be taba dariya ba a rayuwarsa sannan yace,
"Iyeyenkifa?"
"Banidasu" ta fada a takaice ,
"Toh inane gidanku? "
Kallonshi tayi sannan tace" bamuda gidan da yawuce gidan marayu" ,
Gabansa ne ya cigaba da dukan uku uku ya hadiye miyau Mai kauri sanan yace
"Toh malama fatyma kina Ina ranar 20 ga watan June Dede karfe 2 na talatainin dare?
Gabantane ya yanke ya Fadi sanan ta
Runtse idon ta Tana matso wasu zafafan hawaye tace,
" Ina guess house na gidan sarki"
Nan da Nan kotu hayaniya da maganganu sama sama suka Fara tashi, aka buga table tare da umarta kowa yayi shiru.
Khausar dake gefen afnan itace ke jehowa Fatima Zahra kallon tsana tsantsa Wanda takeji da tanada iko ta Mike ta shaketa saita kaita lahira,
"Toh me ya kaiki guess house din?"
"Bakomi" tafada a takaice
"Kenan wannan na nuna kinada sa hannu a kisan da akayi ?"
"Objection my Lord, ya kamata Barrister ya gyara salon tambayarshi, yadena cusama wadda ake zargi laifi domin har yanxu baa tabbatar da ita a matsayin Mai laifiba,nagode ya maishariah"
"Barrister ka gyara salon tambayarka"
"Nagode ya Mai shariah "
"Malama fatyma kotu zataso taji adede lokacin da kike guess house din me kikeyi?ko me kikajeyi?"
"Kamar yadda nace Nina kasheshi don Allah Nima a kasheni kawai"
Hayaniyace ta kwaure a koton kowa na fadar albarkacin bakinshi ...
Sai da aka bubbuga gudamar lauyoyi sannan aka umarci kowa yayi shuru.....
"Nagode ya Mai shariah anan na kawo karshen tambayata"ya juya zuciyarsa na tsananin bugawa cike da furgici Wanda ya tattaro jarumtarsa a fili kamar baya cikin furgici ya koma wajen zamansa ya zauna.
Bayan Yan rubuce rubuce alkali ya tambaya"Koh lauyan Wanda suke Kare wadda ake Kara sunada abin cewa?"
"Inadashi ya Mai shariah ".
"Kotu na saurarenki" .
Cike da nutsuwa da jarumta ta taka har inda fatima take sannan ta gyara zaman rigar lauyanta,cikin natsuwa ta kalli fatyma tace...."malama fatima ki kwantar da hankalinki, Nan kotun adalci ce Kuma kotu bazata yanke Miki hukunciba har sai ta tabbar da ke Mai laifice, Ki nutsu kiyima kotu bayanin abinda kika sani".
Shuru tayi na wasu Yan mintuna, sannan ta share hawayenta Wanda suka Zama abokanan idonta ...
"Nima bansan komiba, Abinda kawai zance shine Nina kashe yarima"
Dafe kai🤦🏻♀Barrister hauwa tayi ganin fatima Bata Bada hadin Kai .
A hankali ta juya ta kalli alkali sannan tace" ya Mai shariah zanso kotu ta Kara bamu dama, domin nafahinci fatima Bata cikin kwanciyar hankalin. Da zata bada amsoshi,....inaso kotu ta bani dama domin Kara gabatar Mata da wasu hujjoji azama na gaba insha Allah,nagode my Lord"
Bayan Yan rubuce rubuce alkali ya gyara glass dinsa sannan yace ,"duba da wasu Yan hujjoji kotu zata da'ge wannan Zama har zuwa ranar 4 ga watan July domin ciga da sauraren wannan shariah, sannan kotu ta bada umarnin a duba kwakwalwar fatima a tabbatar da ingancinta,sannan kotu tabada dokar aci gaba da tsare fatima har zuwa Zama na Gaba"
" Courtttttttt....." Kowa ya miki sannan alkali ya fita,
Hayaniya ce kawai ke tashi yayinda dik wani mahalukin dake cikin kotun Saida yayi zufa dikda fankokin dake aiki cikin kotun,jamaa ke tururuwar fita daga kotun Saida kowa ya Gama fita lauyoyi suka fito,
Barrister Abdul da madam dinsa ne suke tafe hannunsa rike da rigar lauyoyinsa suka nufi motarsu,
Yayinda yarima ya fito a hankali yake takunsa tamkar bazai takaba zuciyarsa cunkushe da bakin ciki ya nufi jerin gwanon motocin da suka rakosu Dantafiya gida,ta gabansa mota ta wuce ta prison wadda ke dauke da Fatima a ciki ,idanuwansu suka hadu waje daya yayinda ko wanne cikinsu Saida zuciyarsa ta harba,tausayin Fatima da soyayyarta suka Kara samun gurbi a zuciyarsa,haka aka fice da ita Yana tafe Yana tunaninta,
Motar da kannensa biyu ke ciki ya shiga wanan karon,Yana rufe kofa kausar ta kallesa fuskarta cike da bakin ciki da takaici tace"Wai yaayah wacece wanan barrister din dake Kare shegiyar yarinyar Nan ?meye hadinta da ita bayan tafada cewa ita bakowa bace face tsintacciyar mage,wadda ke zaune gidan marayu?"
Kallonta kawai yayi yace "bansaniba Nima"
Tsaki kausar tayi a Karo na biyu tace"aikuwa Tana tare da kunya in Allah ya yarda Sai anyiwa shegiya kisan gilla"
Da sauri yarima ya kalli khausar ,Sai Kuma ya juyar da kansa ya basar batare da yace uffan ba,
Ita kuwa afnan dik maganar da suke batace komiba Sai daddana waya takeyi batare da tace uffan ba, har suka iso gida khausar na bambami...
*****
"Turkashi ,lallai akwai wata makarkashiya a wanan shariar,domin Babu yadda zaayi ace matsiyaciya wadda batada kowa ace ansamu wadanda suka tsaya Mata a shariah saidai idan tanada manyanta wadanda suka tsaya Mata tayi kisan shine suka samu lauyoyi suka Basu kudi suka tsaya Mata a shariah,to wallahi wallahi asirin kowa saiya tonu Kuma jinin da'n dana haifa bazai tafi a iska ba dolene mine zamuci shariar Nan"
Tunda mama ta Soma jaraba Tana maganganunta yarima bece ko kanzil ba shiru yayi Yana saurare,
Khausar dake gefe tace a hasale"Wai babu kunya babu tsoron Allah sabida yarinyar Nan shegiya wadda akayi cikin shegehta a waje tasan abinda ta taka saicewa take Wai ita ta kasheshi a kasheta kawai,ita Kuma shegiyar lauyar Sai cewa tayi Wai Bata cikin hankalinta yasa take amsa wanan maganar dayake mahaukaciya CE"
Yarima Sai a sanan yayi magana yace "basuda wata kwakkwaran hujja mama,ki kwantar da hankalinki mukeda nasara ai zamu hadu a Zama na Gaba"
Jinjina Kai mama tayi takai takawo tace "zansa a hadamun tafiya a shirya Motoci zanje guest house din zansamu securities da kaina sanan zaa kaini wajen yakubu Wanda keda alhakin kula da wajen a kunnamun computer Inga komi sanan zanbada umarni abamu komi q hannunmu don mu gabatarwa da kotu a yankewa tsinanniya hukuncin kisa,sanan kafin a kasheta ta tonawa wadanda sukasa tayi kisan asiri,sanan wadanan lauyoyin Sai sun muzanta a idon duniya"
Dammm kirjin yarima ya buga Nan da Nan ya nemi natsuwarsa ya rasa Jin kalaman da mama babba tayi....
"Sanan Suma gidan marayun zasu da'n da'na kudarsu Dan ta jefasu a bala'i Dole bincike yaje garesu Dole su Fadi gaskiya,idanma a gidan marayun take idan ma baa Nan takeba Dole asirin kowa ya tonu"
Shidai yarima zaune yake tamkar mutum mutumi,tamkar an dasashi,ya Lula duniyar tunani,meke Shirin faruwa?ya zaayi ya mallaki recording din yadda Fatima tayi kisa kafin mama tagani?Tabbas idan yaje guest house asirinsa zai tonu masarauta zata gane takunsa....
*Gyan gyan*
*Muje zuwa*
*SLIMZY🥰😍**🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*
*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*
*NA SLIMZY*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*
07
Mikewa tsaye yayi jiri na Shirin dibarsa da kyar ya tattaro natsuwarsa cikin dasasshiyar murya yace,"ki kwantar da hankalinki mama jinin da'nki Kuma da'n uwana bazai tafi a iska ba matukar inada Rai Sai naga bayan shariar Nan insha allahu kuma mune keda nasara"
Jin jina Kai mama tayi tace "Allah yayi maka albarka,kuma wanan sanyin jikin da kakeyi Ina Lura dakai ka kaudashi nasan ba wani abubane face mutuwar Dan uwanka dake tabaka ,hakuri zakayi,sanan abinda zakayi kawai ka nunawa duniya cewa kana kaunar Dan uwanka shine jajircewa a wanan shariar wadda nasara a wanan shariar me saukine duba da sanin yarinyar ko wacece ba kowa bace face matsiyaciya wadda zatayi zuwan zomo duniya tazo a guje ta koma a guje,babban burina be wuce inga an sa Mata igiya a idon duniya an kasheta kamar yadda ta kashemun gudan jinina ba,dik duniya Babu hallitar Dana tsana kamarta wallahi summa tallahi na tsaneta saboda amfani da akayi da ita wajen yiwa Dana kisan gilla to yadda ta kasheshi itama bazata zauna a duniyarba"
Kalmomin mama sun zamewa kabir tamkar wuta,dik jikinsa xafi yakeyi Masa Babu abinda ya Tsana sama da Jin wata mummunar kalma Akan fatimansa dikda abinda ta aikata babban laifine Amma yasan Fatima ba zata aikata wanan laifin Babu hujja ba,
Maganar mama CE ta dawo dashi daga tunani"Wai Ni kam kabiru ko kasan wadanan lauyoyin da suke tsayawa yarinyar a kotu?"
Da sauri ya dawo hayyacinsa ya girgiza kansa"ah ah mama"
"Zansa ayimun bincike Akan kosu wayene Dan ba haka banza suka fito Saida ransu ba akwai abinda suka taka Kuma saina tabbatar da Ganin bayansu a wanan tafiyar"