Sashe 30
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya babba dake gefe Tana murmushin Jin Dadi da cin mutuncin da hajiya babba tayiwa Fatima tace"ya kamata ta gaisheki a matsayinki na matar Dan sarki,matar uban gidanta Mana Dan tafara girmamaki tun yanzun kafin tafara aiki a karkashinki"
Murmushin kasaita deejahmah tayi batare da tace komiba ta gyara zamanta....
Kafafuwa hajiya babba ta Mike su sanan ta kalli Fatima tace "ke matsamun kafafuwana"
"Toh ranki ya dade"
Sallamar wata baiwa ce wadda ke bakin kofa ya juyo da hankalinsu duka,...zubewa tayi a kasa tace"Allah ya baki yawan Rai akwai baki dake neman iso a kofar fada..."Dan yatsina fuska hajiya babba tayi tace "wasu irin baki ne meke tafe dasu?"
"Allah ya baki yawan Rai daya dai matashiyar macece,sanan dayar Kuma Yar budurwa ce sunce mun sunzo ganin Fatima ne"
Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci Fatima lokacinda take matsawa hajiya kafa ji takeyi tamkar ta saki fitsari....tambayar kanta ta shigayi to suwaye wadan Nan?....maganar hajiya ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data fada "je ki shigo dasu"
Wani mugun kallo hajiya babba ta watsawa Fatima sanan tace "asirinki ya tonu matsiyaciya"
Tana rufe baki sukai sallama suka shigo parlorn Ablah ce da Aysha kanwarta sunsha kwalliya ta kece raini dik Wanda ya kallesu yasan cewa sunaji da kudi da aji da gayu......kallon kallo akeyi da hajiya babba da Barrister hauwa Domin Nan da Nan hajiya babba ta Gane fuskarta,dagowa tayi daga kwancen da take "sakarmun kafata "da sauri Fatima ta saki kafarta jikinta sai rawa yakeyi tamkar mazari....
Babu Wanda yace su zauna haka suke tsaye kikam mamaki da al'ajabin ganin Fatima da uniform din bayi shi ya lullube hauwa da Aysha ga yadda lokaci kankani tayi wata iriyar Rama sai farar fatar da har sheki takeyi,
Yunkurawa hajiya babba tayi ta Mike a tsaye tamkar zakanya haka take zagaye su Ablah dake tsaye kikam kamar an dasasu tafa hannu hajiya babba keyi "lallai biri yayi kamada mutum sanan shi mutum Mara kunya dik abinda akace zaiyi zai aikata,yanzun rashin kunyar ki har ta Kai ki iya takowa ki shigo gidana?bayan iyayi da jarumtar da kika Gama nunawa a kotu a matsayinki ke lawyer?yanzun shine kikazo kikara nunamin jarumtar ki a karo na biyu Babu kunya Babu tsoron Allah kika Tako har cikin masarauta kinzo ganin fatima,.....koh?me kikazoyi?"
Dariya ma maganar hajiya tabawa Ablah Dan Saida ta murmusa sanan tace "gidan sarauta inace gida ne Mai adalci da jin Kan talakawa?Babu Wanda akaiwa iko da shiga gidan sarauta matukar sarkin da magoya bayansa masu adalcine ga nakasa dasu"
Mamakin amsar da Ablah ta Bata tayi Koda yake yarinyar akwai jarumta "da kinsani da fadar sarki kika nufa sai ayi Miki iso a matsayinki na Yar talakawa wacce tazo bara gidan sarauta sai sarki yayi Miki adalci a matsayinsa na maijin Kan talakawansa"
Gyara tsayuwa Ablah tayi tace"dik wata masarauta wadda ta amsa sunanta masarauta to fa tabbas sunsan darajar Dan Adam sanan sunsan mutuncin bakonsu suna karramasa su bashi wajen Zama harma da abin motsa baki saidai Kash wanan masarautar Tasha banban da masarautun danasani wadanda sukafiku cikar mulki da izza,akwai wata masarauta danasani dik takamarsu dik nuna mulkinsu basa wulakanci ga bakinsu sukan sauraresu suji maike tafe dasu zanyi Miki misali da masarauta daya tamkar da dubu masarautar hankaka"
Zuwa wanan lokacin hajiya babba takai kololuwa a bacin Rai jikinta har rawa yakeyi idan akwai abinda ta Tsana bai wuce ace akwai masarautar da tafi tasu mulki da izzah ba dikda tasan cewa karamar sarautace barayar Zaki Bata Kai wadda ake nufiba.....
Cikin tsananin bacin Rai hajiya babba ta nunawa ablah Kofa da hannu"ficemun fice daganan tun kafin in zuciya insa dogarawa su jefaki a dakin duhu su azabtar mun dake,....kafin in bude idona ki tabbatar kin bacemun daga gani sharrin da kika kullo kika kawo Mata to asirinku ya tonu idanma kinzo ku hada bakine ta kashemu to ki sake sabon shiri".....
"Banji zafin wannan korarba dan na rigada nasan bakisan darajar Dan Adam ba saboda haka hajiya Ina Mai baki shawara da kiji tsoron Allah mulki da sarauta na Dan lokacine"
Da sauri deejahmah ta Mike zatai magana hajiya babba ta dakatar da ita ta hanyar daga Mata hannu.....
Juyawa Aysha da Ablah sukayi suka nufi hanyar fita a Nan sukai kicibis da yarima da Ahmad da Yan Mata biyu a tare dasu,
Da sauri yarima ya fadada faraarsa yace "ranki ya dade Mrs Abdul wanan ziyarar bazata haka?"
Dan yak'e Ablah tayi Masa tace "a gaggauce mukazo yanzunma banaso in Kara minti daya a gidan Nan idan kanason magana Dani zaka iya samuna a gida ranka ya dade"...Tana Gama fadin haka tayi gaba Aysha tabi bayanta....kallo ya bita dashi take ya hasaso akwai abinda ya faru...
Dik wata huduba dama yarima ya Gama yiwa Maryam da bilkisu da sharrudan daya gindaya musu dik suka amsa da zasu kiyaye....tsaidasu yayi a kofar babban parlor yace sujirashi a Nan zaisa a shigo dasu.....
Da sallamarsu suka shiga babban parlorn gidan inda hajiya babba ke kaiwa da komowa Tana nushin hannunta cikin tafin dayan hannun....Yana ganin haka saida ganansa ya fadi...
Basarwa yayi ya maida dubansa ga Fatima dake durkushe hawaye na gudu a idanuwanta....kafeta yayi da ido yayinda deejahmah tunda Suka shigo ta Dora idanuwanta akansa ta kasa cirewa saboda yadda yayi Mata wani irin kyau da kwarjini....takaicin kallon da takeyiwa Fatima yasa deejahmah a hassale tace "ke fita"....
Da sauri Fatima ta zabura ta Mike jiki na rawa ta bi hanyar fita"dakata Nan munafuka"...tsayawa tayi caka a wajen ta sunkuyar da kanta kasa kafafuwanta sai rawa sukeyi.....
Kallon yarima hajiya babba tayi "Ina fatan ka hadu da wata Mara kunya yanzun da kanwarta sun fita?...Wai zuwa sukai wajen Fatima sanan suka karemun tanadi a matsayina na matar sarki Amma sai tayi datasani"...
"Mistake akayi Amma ba wajen Fatima tazoba wajena tazo Domin abokiyar aikina ce yanzun haka akwai shariar da zan gabatar a wani gari sati Mai zuwa"
"Ka sauya kalaman ka Domin Basu shigaba na rigada na fahimci komi yanzun kabiru asirinku ya tonu tunda har ta iya takowa cikin gidan Nan ta cimun zarafi to wallahi summa tallahi wanan shine kuskuren da tayi a rayuwarta ta Sha idan ta Kara nayi Mata alkawarin nadama ka fada Mata Kar insake ganin kafarta a gidan Nan"
"Owk"
Kawai yace a takaice....shiru na Yan mintuna sanan yarima yace"na iso da wadanan bayi da nace zan kawo yanzun muka daukosu nida Ahmad"
Sai lokacin hajiya babba ta kalli Ahmad dake gefe tayi Masa murmushi suka gaisa sama sama...
"A shigo dasu"
Umarni yabawa sarkin kofa dake tsaye yace "ka shigo da wadanan bayi dake kofar shigowa"
"Angama ranka ya dade".....
Mintuna kadan aka shigo dasu bilkisu kallo daya zakayi musu kasan suna cikin tsananin wahala duba da suturar dake jikinsu da daudar dake tattare dasu.....
Fatima Dadi da farin cikine suka lullube Fatima dikda bakin cikin da ta tsinci kanta a wanan lokacin Jin shigowar Yan uwanta ta nemi bakin cikin da take ciki ta rasa...
Zubewa sukai a gaban hajiya suka kawo gaisuwa sanan sukai Shiru....
"Ko wacce ta gabatarmun da kanta"shine abinda hajiya tace fuskarta a daure tamkar Bata taba dariya ba....
"Ranki ya dade sunana bilkisu"
"Kefa"ta nuna Maryam dake tsugunne Tana Raba ido....
"Sunana Maryam"
Jinjina Kai hajiya babba tayi ta nuna bilkisu tace "ke Zaki zauna a bangarena dik abinda nake bukata ke zakiyishi da komi nawa kina dakina".....
"Ke Kuma kina bangaren hajiya karama,zansa akaiki sashenta idan ta shigo daga Dan tattakin data fita dazu"
"To ranki ya dade"suka hada baki....
"Kunfice a Nan zan nemeku anjima"
Da sauri suka Mike suka fice...
Fita yarima yayi shida Ahmad suka nufi sashinsa.....
"Hajiya Wai Kinga kallon da yarima yakeyiwa waccen munafukar yarinyar tamkar zai hadiyeta"
Kallon deejahmah hajiya babba tayi tace"ki kwantar da hankalinki wanan yarinyar azaba ce zatasa ta haka Rami ta bunne kanta da kanta kabiru nakine ke kadai ko yaki ko ya so akwai wasu Kaya da nasa ya siya Miki idan Zaki tafi zanbada asa Miki a mota".....
Murmushin Jin Dadi deejahmah tayi tace "toh ranki ya dade"....
Hajiya ta waigo ta kalli Fatima dake jingine a jikin bango tace "tace kije wajen lantana ta kaiki wajen jakadiyyar sashin sarki kice a baki Kaya irin na bayi guda biyu ki nemi wadanan sababbin zuwan ki Kai musu su canja kizomin dasu"
Durkusawa ta karayi tace "toh ranki ya dade"ta fice da sauri....
Can tasamu su bilkisu xaune sunyi jugum jugum a jikin bayi a tsattsaye Tana isowa ta sakar musu murmushi....lokaci daya wani farin ciki da Dadi ya lullubeta Wanda Saida ta zubar da kwalla...
"Kefa Fatima kinada matsala yanzun kukan me kike so kikeyi a ganemu malama cikin dare xamu hadu mu tattauna yanzun meke tafe dake"
"Kaya akace in karbo muku ku canja".....
**********
"Gaskiya abokina ka iya dabara abinda na lura wanan bilkisun shegen wayau zatayi inaga inhar suna tare da Fatima zata rinka Bata shawarwari Kuma wasu abubuwan ko anyi Mata bazata damuba Dan tanada abokanan debe kewa dikda dai ka gargadesu akan nuna sunsan juna"
Murmushi yarima yayi yace "ni inaji a jikina inda bilkisu ce Fatima akwai abubuwanda saidai a kasheta Dan yarinyar akwai karfin Hali"
"Shegen wayaune da ita kana ganin idanuwanta kuru kuru a tsaye xata gogar da Fatima,....kaikuwa inaso ka rike wuta ka koya Mata sonka sosai alhaji"
Tafawa sukai yace "ni yanzunma wallahi ganinta nakesonyi Dan jiya yadda kasan in barta ta kwana wajena Ina ganinta inayi Mata Hira...."
"Kardai ka zake mutumina"
Sarai ya fahimci abinda Ahmad ke nufi murmushi kawai yayi ya shafa kansa....ya dauki juice ya Dan kurba ya lumshe idanuwansa"
*********
Wajen magriba deejahmah ta iso gida Bata yada zango ba a ko Ina sai dakin mahaifiyarta Tana cika Tana batsewa
"Yadai deejahmah sarauniya"
"Mama wallahi bakiga wulakancin da yarima yayimunba ko kallon inda nake beyiba a matsayina na matar aurensa nunamin yakeyi tamkar besan da wata halittaba"
"Ki kwantar da hankalinki zaisan da wata halitta Nan gaba kadan Domin Ina Nan Ina Shirina na boye a kansa burina be wuce Allah ya kaimu lokacinda zaki shiga gidan ya kusanceki a matsayin matarsa".....
Yatsina fuska deejahmah tayi cikin rashin fahimta tace"banganeba"