← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 80

Sashe 24

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga inda yake ya Bata amsa da "ya rigada ya sallameni,sauri nake inje indauki Fatima Dan yamma tayi"Yana fadin haka ya saki malalacin murmushi sanan ya fice Yana murmushin mugunta idan burunsu ya cika to shima burinsa ya cika Kuma komi Daren dadewa babban burinsa zai cika su cigaba da wasan donshi haka yakeso.....

Kwafa gwaggo rahi tayi cike da takaici tace"maganinka abune Mai sauki a wajena kawai kayi kiskuren shigowa hannuna"

Lokaci kankani wani Abu ya zo kirjin deejahma ya tokare Mata makoshi tunda taji furucin da yarima yayi na cewa zai dauko Fatima ta nemi farin cikin da takeciki ta rasa tamkar ta fasa ihu Dan bakin ciki,haka Nan ta Mike ta bukaci wata kuyanga da tayi Mata rakiya zuwa fadar sarki......

********
Babu wani Bata lokaci yarima ya Isa gidan Ablah Koda ya shiga parlor wajen zamansu as usual kowa yayi jugum jugum kamar anyi mutuwa shiru kowa yayi sai TV dake aikinsa,sallamarsa ce ta dawo da kowa daga duniyar tunanin daya Lula,

Cikin sanyin jiki Ablah tace"yanzun yarima daukar Fatima zakayi ka rabani da ita?ka dage Akan saita koma gidanku?gani kakeyi mu bazamu iya riketaba koh?kadai rabani da Fatima hankalinka ya kwanta"ta karashe maganar Tana hawaye hade da dafa Kan Fatima wadda ke famar shasshekar kuka,

Murmushi yarima yayi sanan yace"haba Ablah Nima in Dana sunan,...babu Mai rabaki da Fatima sai Allah Dan a halin yanzun kece uwar Fatima ko Fatima tabar gidan Nan bazan rabakuba zan rinka kawota akai akai Tana duba ablarta kema Kuma nasan zakije ganinta Kinga ko baku rabuba ki kwantar da hankalinki har kwana zatazo yi"

Gyada masa Kai kawai tayi Tana kallon Fatima Tana sharar hawaye,

Aysha dake gefe ta hada fuskarta ta zunguro baki gaba saboda takaici,yarima ya kalleta shi dariya ma ta bashi saida yadanyi dariya sanan yace"haba Ashmah bakya kyau da kunci kisaki ranki kinji ban rabaki da kawarki Fatima ba Kuna Nan tare har kawota zanyi ta rinka Miki kwanaki,sanan makaranta ma nakeso in nema Mata Kila makarantarku zan kawota ko ai Kinga Kuna tare wannan bakin da aka turomin a maida"

Harararsa aysha tayi ta Mike tabar parlorn dukansu suka bita da kallo,

Kallon Ablah yarima yayi yace "magriba tayi banaso a Kira sallah Ina Nan Naga abokina bayanan Kuma naso mu hadu wallahi Amma bakomi zan dawo zamu tafi saboda tare da Mai martaba muke sallar magriba "

"Badamuwa shima fitar ta gaggawace ta kamashi an kirashi daga gidansu shine ya tafi zan fada Masa,"....kallon Fatima tayi hade da mikewa tace"kindaiji maganganun Danayi Miki ko Fatima karki kuskura ki ketare shawarwarin Dana baki kinji Allah ya baku zaman lafiya"

"Ameen"....

Mikewa Fatima tai ta rungume Ablah ta fashe da kuka a haka suke tafiya har waje,yayinda Aysha ta biyota da Dan akwatin kayanta Wanda Ablah ta sissiya Mata da Wanda itama ta Bata har wajen mota suka rakasu dakyar Fatima ta saki Ablah ta shiga mota Aysha tasa akwatinta a bayan mota yarima ya shiga yaja suka wuce,

*********
Deejahmah ce tsugunne a gaban Mai martaba fuskarta a lullube yake sanar da ita shawarar da suka yanke na hadata da yarima aure,

Tambayarta yayi kamar haka "khadijatu kin amince da bukatarmu Koko kina ganin kinfiso kisamu wani miji can daban kiyi aure?"

Shiru tayi na kimanin minti uku,kanta a Duke take motsa bakinta"babu bukatar amincewar yaro Akan shawarar iyayensa matukar sunga dacewar hakan aikin yarone yayi biyayya ga iyayensa Akan ko wace bukata,na amince ranka ya dade"

Murmushi hajiya babba keyi dake gefenta don ita kanta Tana kaunar yarinyar haka kawai deejahmah ke burgeta cike da gamsuwa da maganarta sarki yace "Allah yayi Miki albarka"

Kara rankwafawa tayi tace"ameen ranka ya dade Allah ya Kara maka lafiya da nisan kwana"

"Ameen"

Hajiya babba na murmushi ta bude baki zatayi magana sallamar yarima ta katseta ta juyo da sauri.....Mai martaba ne ya karba musu sallamar yayi musu umarni da shigowa.....

Gefen deejahmah Fatima ta raba ta durkusa kanta a kasa yayinda yarima ya koma gefen hajiya babba ya zauna dikda hararar datake watso Masa besan tanayiba,

Durkusawa yarima yayi yace"Allah ya taimaki Mai martaba na kawo Fatima fada in gabatar da ita gaareka "

Zuciyar deejahmah ce ta shiga bugawa sauri da sauri babu dama ta dago Kai ta duba wadda aka Kira da Fatima gata a gaban sarki,

Jinjina Kai sarki yayi cikin nishadi ya kalli Fatima da kanta ke sunkuye a kasa yace"barka da zuwa yata"....

Nauyinsa Fatima taji tai murmushi ta Kara durkusawa cikin zazzakar muryata Mai dadin gaske tace"Allah ya karawa sarki lafiya,hakika banida isassun kalmomin da zanyi amfani wajen godiya gareka ,hakika Kai adalin sarki ne Mai kaunar talakawansa Wanda bayaso yaga wani nakasa dashi a cikin mawuyacin Hali nagode da amincewarka na shigowata wanan masarauta"

Murmushi kawai Mai martaba yakeyi hakikanin gaskiya ko wani sarki yanaso a kodasa haka yadda Fatima tayi yaji dadin kalamanta da tayisu cikin natsuwa.....

Shiko yarima mamakine da al'ajabin kalaman Fatima suka daskarar dashi a wajen,don be taba tunanin ta iya tsara magana hakaba dikda yasan cewa mafi yawancin kalaman yarinyar masu hukima ne.....

Hajiya babba kuwa dake gefe jinjina Kai kawai takeyi a ranta Tana fadin yarinya kinyi kuskuren shigowa wanan gida harda wani iyayi takewa sarki bayan bada sarki Zaki zaunaba wata dabara ce ta fadowa hajiya babba da sauri tayi yak'e Wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo tace"sannunki Fatima barka da zuwa masarautar barayar Zaki"

Darammm kirjin Fatima ya bada baki na rawa Fatima ta amsada "yauwa hajiya....nagode da karamci Allah ya saka muku da alheri"

Yak'e baki hajiya babba ta karayi tace"ameeen".....dan rankwafawa tayi alamar girmamawa ta kwantar da murya ga Mai martaba tace"ranka ya dade zanso ace rukon Fatima ni zan kasance uwar goyonta a wanan masarauta Mai albarka da nayi matukar farin ciki da hakan"

"Da Fatima da Kabir duka mallakinki ne uwar gidan sarki saboda haka ki rike Fatima har muddin Rai"...

Mutuwar zaune yarima yayi lallai hajiya babba ta shammacesa,.....zuciyarsa ce kawai ke harbawa maganar Mai martaba ce ta dawo dashi daga sumar wucin gadin da yayi "kabiru nayi magana da Khadija matarka itama ta amince da shawararmu,Kuma nayi matukar farin ciki da kuka kasance ya'ya masu biyayya ka riketa Amana tamkar dama Kaine ka nemi auren nata haka Allah ya kaddara Allah yayi Muku albarka"

Cikin dasasshiyar murya yarima yace"ameen"......

Fatima kuwa kalaman hajiya babba na jiya a gareta suke yawo a kwakwalwarta lokacin da taji kalaman da take yiwa Mai martaba....shikenan tafaru takare Mata...

Sallamarsu sarki yayi saboda Kiran sallah da akeyi dukkansu suka Mike tsaye suka fito.....

Kuyangar data rako deejahma itace ke biye dasu itada hajiya babba da Fatima wadda ke bin bayansu kamar kwai ya fashe Mata a ciki batare da sanin inda zata dosaba a gidan saboda yarima sarki ya tsaidasa suje masallaci fada....

Binsu takeyi har cikin gidan inda suka tarar da gwaggo rahi zaune Tana karkada kafa da sauri ta dago Kai Jin shigowarsu,afnan dake gefen kawar deejahma baby da sukai ido hudu da Fatima.....saida ta firgita Dan daga ita har mahaifiyarsu basusan wainar da ake toyawa ba....

Gefen bango Fatima ta rabe a tsugunne ta tasa Dan akwatinta a gaba ta sunkuyar da Kai....

Kallon Tsana deejahmah ke watsawa Fatima yayinda ta tako cike da Isa da kasaita har gaban Fatima ta tsaya Tana Kare Mata kallo har zuciyarta tasan babu karya Fatima kyakkyawar yarinya ce ajin farko babu mahalukin da zai kalleta ko a kuskurene be juyo ya Kara kallontaba,..wata hassada ce ta tasowa deejahmah tace"kinyi kuskuren shigowa gidan sarauta Fatima kina tare da danasani Domin kin kawo kanki Ramin kura inda take zaune da yayanta fita daga ciki sai kin shirya,kin kawo kanki makabarta inda dakanki Zaki ginawa kanki kabari ki rufe kanki da ranki batare da kin mutuba wallahi summa tallahi saina shayar dake azaba tunda dake aka hada Kai wajen kashemun tsohon mijina,sanan yanzun sabon mijina kike bibiyarsa ke marainiya ko?shine ubanki to kinyi babban kuskure".....

Murmushi hajiya babba tayi ganin irin kallon tsanar da deejahmah ke watsawa Fatima wadda ke tsugunne jikinta na karkarwa,zufa ce ke tsattsafowa a jikinta tamkar an watsa Mata ruwa....

Takowa hajiya babba tayi tazo ta dafa kafadar deejahmah tace"ki kwantar da hankalinki daukar fansa ba naki bane ke kadai ta shigo hannun da bazata taba fitaba,idan anyi mak'isa a kotu an hada baki an wanketa Nan gidan babu Wanda zai wanketa saboda haka ki kwantar da hankalinki"

A fusace deejahmah tace "wallahi mama ni ban yarda wannan yarinyar marainiya bace dubeta fa wallahi muna furci ne"

Gwaggo rahi zatayi magana kenan yarima ya shigo parlorn Dan Allah Allah yakeyi su idar da sallah ya baro fadar dikda yasan sarki be barinsa sai anyi ishai Amma karya yayi Masa da yanaso ya watsa ruwa baijin dadin jikinsa....

Koda ya karaso parlorn suna tsattsaye akanta kamar wasu sojoji suna ganinsa dukkansu suka watsa Masa wani irin kallo Wanda shi baima San sunayi ba,.....ita dama afnan tunda taga shigowarsu ta ruga tayi bangaren mahaifiyarsu Dan sananr Mata abinda ke faruwa,

Karasowa yayi ya sa hannu ya dago Fatima yace"haba bintu ya zakizo Nan ki tsugunna umm?saikace ba Yar gidaba?muje in nuna Miki dakinsu khausar Nan xaki zauna tare dasu"

Murmushi Fatima tayi Masa ta dago daradaran idanuwanta ta saukesu Akan fuskarsa tace"kasan bakunta ya Zama Dole ai Amma zan Saba yaayaah kaji"ta kafesa da ido jinjina Kai yayi Yana murmushi tabi bayansa,

Dukkansu galala sukai suna kallonsu,deejahmah wadda ta Gama fassara irin kallon da Fatima keyiwa yarima irin kallon masoya ji tayi kamar ta shaketa a haukace ta juyo tace da mamanta"mama kina kallo fa wallahi tallahi shegiyar yarinyar Nan budurwarsa ce ki duba irin kallon da tayi Masa fa"

"Ki kwantar da hankalinki yarima mijinki ne ita kuwa saidai ta tsaya a iya kallon Dan wallahi mallakar Kare da hantar kura....harabada bazata cuwu masaba Kinga ko harabada saidai ta ganshi"

Nannauyar ajiyar zuciya hajiya babba tayi tace"kuje abinku kubarmun komi a hannuna"....

********
Hawayen bakin ciki kawai mama karama keyi yayinda afnan ke famar kwantar Mata da hankali Dan bakaramim tashin hankali take cikiba....
Chapter 24 · 0% Book details