← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 80

Sashe 1

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[8/25, 2:38 PM] Meenatah: *🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*

*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA SLIMZY*

*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*

           01

      2pm

Cikin tsananin furgici da kidimewa take kallonsa  kwance warwas cikin jini batare da ko yatsansa Yana motsawa ba,maida dubanta tayi ga rigar jikinta data kasance doguwa pink yadda ta jike sharkaf da jini tamkar an yanka saniya...."innalillahi wa Inna ilaihi rajiun "shine abinda bakinta kawai ya iya furtawa a furgice ta yarda wukar dake hannunta tayi kofar fita gabanta na tsananin faduwa ta  Murda handle din kofar dakin, cikin saa taji kofar a bude take, bata tsaya wata wata ba ta runtuma a guje tun daga third floor take gudu Tana tsallakar matakala kasantuwar ko Ina tsittt, duba da yadda dare ya tsala ko Ina shiru Sai wadatar hasken lantarki a ko ina,harta sakko kasa babu Wanda taci Karo dashi ya ganta, Nan da Nan tayi azama ta fice daga main entrance din shiga guesst house din, tayi kofar gate....

  Tana fitowa daga gate din guest house din titi ta tadda Nan da Nan ta shiga waige waige  na neman hanyar da zatabi Dan tsira da rayuwarta,hannun dama ta bi Tana gudu sosai ba kakkautawa har tayi tafiya Mai Dan Nisa ba tare da gajiya ba,batare da ta hadu da kowa ba,  hangen  hasken touch light da tayi ne  gabanta ya Yanke ya Fadi,tsayawa ta danyi sanan ta juya da niyyar chanja hanya,kamar daga sama sautin murya ance "ke dakata a inda kike"cikin kakkausar muryar da Saida ko Ina ya amsa kasantuwar darene.

  Bugun zuciyarta ne ya karu,firgicinta ya karu akan Wanda take ciki ji tayi tamkar ta saki fitsari a inda take tsaye, har suka karaso inda take ta kasa kwakkwaran motsi saboda tsabar tsoro da firgicin da take ciki, inhar ba mafarki takeyi ba to tabbas masu tahowa gareta jami'an tsaro ne.....sandarewa tayi a tsaye a inda take, har suka karaso wajen, dukkansu Kara haska ta sukeyi daga sama har kasa ,daya daga cikinsu ne cikin kakkausar murya ya jeho Mata tambaya "ke daga Ina kike cikin Daren Nan?"

  Kallonsa kawai ta tsaya yi tamkar wata kurma Sai kyarma da jikinta yakeyi kamar mejin sanyi,shiru tayi batare da ta CE komiba har minti biyu suka shude....Ganin Bata da niyyar amsa Masa tambayarsa, ya Kara jeho Mata  wata tambayar a Karo na biyu "wanan menene a jikinki kamar jini?na  menene shi?"

  Kallon jikinta tayi sanan ta dago idanuwanta ta sauke a kansa a Karo na biyu batare da tace uffan ba Sai zufa dake karyowa daga jikinta tamkar Ana watsa Mata ruwa.

Dan sandan dake tambayarta Shi ya juyo ya kalli daya daga cikin ukun dake tsaye suna kallon ikon Allah yace "Sargent"

"Yes sir"

"Arrest her,kasata a mota mu wuce da ita office"

  "Ok sir"yace sanan ya juya da sauri cikin minti biyu Sai gashi dauke da hand cuff ya nufeta Dan sanya Mata...

Dakatar dashi Dan sandan yayi "kada ka sanya Mata don bamuda tabbacin ita Mai laifice kawai dai sata a gaba kasata a mota muje....

*******
Zaune yake a tangamemen parlornsa Wanda ya Sha kayan alatu na more rayuwar duniya,tsayawa fadar irin dukiyar dake cikin parlorn kansa Bata lokacine,tunda aka kawo Masa jarida ya kifa kansa da ita misalin karfe biyu na Rana ya kasa Koda motsi a inda yake kishingide a kujerarsa 3seater ya runtse idanuwansa ya Lula cikin duniyar tunani....

  Ya rasa dalilin da yasa yarinyar ta shiga ransa lokaci daya,yarinyar data kasance batada gata ta taso cikin gidan marayu,yarinyar da besan asalinta ba Amma ta shiga zuciyarta tayi Kane Kane,Wanda har ya kasance babu ranan da zatazo ta wuce batare da yaje ya ganta ba dikda ba samu yakeyi tayi Hira dashi ba,Amma  a  iya fahimtarsa  yarinyace marason hayaniya....

  Karfe shida na yamma jiya yaje gidan marayu don ya ganta Amma hakan be yuwuba tunda ya shiga akace Masa Bata Nan ya tsaya jiranta har goma na dare,amma Bata dawoba to Ina taje?Ina FATIMA ZAHRA ta shiga?...haka kawai ya tsunci kansa cikin faduwar gaba wanda besan dalilinsa ba,fatansa Allah yasa dai ba guduwa tayi daga gidan marayu ba, don Koda ta gudu babu inda zataje Dan batada kowa batada gata Sai Allah...

  Ajiyar zuciya ya sauke tare da busar da iska Mai zafi daga cikin bakinsa,idanuwansa ya bude wadanda suka kada sukayi jajir ya saukesu kan jaridar da aka kawo mishi ita Awa daya data wuce jujjuyata yakeyi a hannunsa sanan ya bude shafin farko na jaridar Yana budewa idanuwansa suka sauka akan rubutun da akayi da manyan bakake kamar haka *AN TSINCI GAWAR YARIMA HABIB A WANI GUST HOUSE  DAKE CIKIN GARI, WANDA AKAYI AMFANI DA WUKA WAJEN CAKA MASA A KAHON ZUCIYA,... Bugun zuciyarsa ne ya tsananta ya cigaba da karantawa hannunsa na rawa kamar ansa Masa shoking,  NA'URAR CCTV DAKE MAKALE A CIKIN DAKIN TA NUNA FUSKAR YARINYAR DAKE DA ALHAKIN KISAN DUMUDUMU  HANNUNTA DAUKE DA WUKAR DA TAYI AMFANI DA ITA WAJEN  CAKA MASA A KAHON ZUCIYA,WADDA BAZATA WUCE KIMANIN SHEKARU GOMA SHA TARA BA*....zumbur ya Mike tsaye kasantuwar hoton yarinyar dayake kallo a gefen rubutun yayi dishi dishi Amma hakan bazai hanashi gane fuskarta ba a ko wani yanayi, " Fatima Zahra" ya ambata q fili,dik AC dake aiki cikin parlorn be hana zufa keto Masa ta ko Ina ba....idan ba gizo idanuwansa keyi ba to tabbas wanan gawar Dan uwansa ne YARIMA HABIB...

  Jifa yayi da jaridar ya furta a fili"No Fatima Zahra bazata taba kisa ba",kisar ma Dan uwansa na jini ta kashe..."Anya habib ne kuwa yayansa?idan haka ne meyasa baa nemesa an sanar Masa ba?

  Wayarsa ya janyo kirar iphone7+ ya Danna makunin hasken wayar Sai yaga a kashe take Ashe,kunna wayar yayi ko kafin ya Gama lalubo number da yake nema Tex ya shigo kamar haka Assalamualaikum yarima,Mai martaba sarki Yana nemanka a fada da gaggawa idan har sakon Nan ya iso gareka tun cikin dare ake neman wayarka a kashe.

  Zuciyarsa CE ta tsananta harbawa Yana gama karantawa ya kwashe komi nasa ya fice daga parlorn yabar gidan....

*******
Fada ta cika tayi dankam bakajin komi Sai sautin koke koke dake tashi daga bangaren da Mata ke tsattsaye  jigum jigum.. sallamarsa a fadar CE tasanya kowa juyawa da kallonsa gareshi babu Wanda ya amsa mishi haka yake takowa a hankali har ya karaso tsakiyar tangamemen falon da suke Kira fada...tsugunnawa yayi gaban gangar jikin da ya gani a lullube da zani ya sanya hannu ya janye mayafin take yayi tozali da fuskar Dan uwansa habib...."innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"shine abinda ya furta a fili...take zuciyarsa ta hasko Masa rubutun jaridar daya karanta dazu da fuskar yarinyar da ya gani....lullube gawar yayi ya Mike jiki a sanyaye yayi hanyar inda mahaifiyarsa ke tsaye Tana sanye da lafaya ta yane jikinta idanuwanta sunyi jajir alamar taci kuka harta gaji...kallonta yakeyi Yana neman Karin bayani daga bakinta,itama kallon nasa takeyi sanan ta bude baki a hankali tace"yadda ka ganshi haka muka ganshi,jiya daddare aka kasheshi Sai da asuba muka samu labari sanan aka kawo Mana gawarsa....runtse idanuwansa yayi take yaji wata juwa na dibarsa da kyar ya saisaita natsuwarsa ya kafe mahaifiyarsa da Ido batare da yace komiba.

*******
  Yana zaune a office dinsa masinjansa ya shigo da takarda hade da jarida ya tsugunna har kasa ya Mika Masa yasanya hannu ya karba sanan masinjan ya CE "ranka ya Dade wanan takkadar statement CE da aka rubuta game da kisan Dan sarkin  masarautar Barayar Zaki da akayi jiya daddare,wanan jaridar Tana dauke da baya Nan komi"

   "Ok"kawai yace Masa ya juya ya fice....ya rufo kofar.

  Glass dinsa ya gyara bayan ya Gama karanta statement din sanan ya bude jaridar ya karanta bayanin tsintar gawar da akayi a guest house,kasa Kuma wani hoto ya gani Wanda be fito sosaiba itace yarinyar da ake zargi da kisan...eye glass dinsa ya cire tare da Kara kallon hoton da kyau...tabbas wanan hoton yayi Kama da yarinyar da suka dauko a yawon patrol da suka fita jiya daddare....Kara kallon hoton yayi sanan ya Kara tabbatar da hasashensa.

  Wayar salula ya dakko ya Danna lambobi bugu daya cikin na biyu aka dauka Saida yayi gyaran murya sanan ya Soma magana "ranka ya Dade inspector barka da Rana"

  "Barka dai ASP Aminu me ake cikine?"

  "Ranka ya Dade takadda aka kawomin office yanzun wadda ke dauke da statement Akan kisan da akayiwa yarima habib na masarautar Barayar Zaki,hade da takaddar akwai jarida wadda aka buga da hoton gawarsa da Kuma hoton yarinyar da naura Mai kwakwalwa ta nuna Dumu Dumu da alhakin kisan,ranka ya Dade akwai wata yarinya da muka dauko jiya daga patrol din dare da muka fita Ina kyautata zaton itace yarinyar da ake zargi da kisan YARIMA HABIB"

  "Ka tabbatar da abinda kake fada kuwa ASP Aminu?"

  "Na tabbatar ranka ya Dade"

  "To alhamdulillahi tunda hakane yanzun akara tabbatar da tsaro Akan yarinyar,yanzun zankira masarautar in sanar musu da cewar anga yarinya"...

   "To shikenan ranka ya Dade"

*******
"Na rantse da Allah inhar yarinyar Nan ta shigo hannu wadda ta kashemun gudan jinina Sai na wulakanta rayuwarta itama Sai anyi Mata kisan wulakanci,bazan taba yafewa wannan yarinyar ba"

  Wayarta CE ta shiga ringing lokaci daya takai hannunta gefen kilishin da take kishingide akai Tana famar rizgar kuka Tana sambatu kala kala,kallon screen din wayar tayi taga bakuwar number ce,dauka ta Danna sanan ta Kara wayar a kunnenta,daga can bangaren aka Soma magana "ranki ya Dade ASP Aminu ke magana daga headquarter na Yan sanda"

  "Ina jinka"tace a dakile cike da Isa da mulki.

"Yarinyar da ake zargi da kisan YARIMA habib yanzun haka Tana hannun hukuma"

  Mikewa tayi zaune daga kishingidar da tayi,cikin daga murya tace"kana nufin anga yarinyar data kashemun da'na habibu?"

   "Ehh ranki ya Dade"bata bashi amsa ba ta kashe wayar ta Mike tsaye gaba daya Ido ya koma kanta da jin kalmarta ta kashe na ganin yarinyar da tayi kisan Kai kowa jiran Karin bayani yakeyi....

  Mutuwar zaune yayi a inda yake Jin abinda mama babba tace....zuciyarsa ta shiga yi Masa lugude tamkar zata Huda kirjinsa ta fito"Allah yasa dai ba ke kikayi kisan Kai ba Fatima Zahra!!!

[8/25, 2:38 PM] Meenatah: *🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*

*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA SLIMZY*

*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*

02
Chapter 1 · 0% Book details