← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 80

Sashe 38

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

********
"Ranki ya dade na zagaye gidan Nan kaff ciki da kewaye Banga Fatima ba Domin har taimakon saade na nema Akan ta tayani nemanta bangantaba Babu ita Babu labarinta har inda take aiki mukaje bamu gantaba"

Wani kallon wulakanci da tuhuma take watsawa Rahane wadda ke tsaye jikinta na faman rawa tamkar mazari.....

"Rahane kina wasa da rayuwarki kina wasa da aikinki,idan har baki nemomin Fatima ba to hukuncin da zan Yanke Mata ke zan yakewa shi Domin Babu yadda zaayi kice ki karade gidan Nan kaff baki gantaba wanan maganar ruwan kwando ce"

Zubewa Rahane tayi a kasa hade da fashewa da matsanancin kuka Tana fadin "kiyimin Rai ranki ya dade wallahi tallahi bansan inda Fatima takeba na rantse da Allah Babu inda ban dubaba a gidan Nan ban gantaba har cikin tsohuwar rijiyar tarihi nasa aka rakani mukaje muka Duba Babu ita"..

Wata uwar tsawa deejahmah ta dakawa Rahane hade da nuna Mata kofa "bacemun daga gani munafuka idan ma hada baki kukayi kika fada Mata saina shayar dake azaba"

Jiki na rawa Rahane ta fice Tana sharar hawaye,kirjinta na dukan uku uku....

Kaiwa da komowa deejahmah keyi hannunta rike da aska Tana jujjuyawa,

Girgiza kafa kawai hajiya babba keyi dakyar ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta bakin ciki "ki kwantar da hankalinki diyata kila ta gudune azaba tasa tabar gidan,idan kuwa haka ne murna ya kamata kiyi ba bakin cikiba"

"Banajin a jikina wanan bakar dagar xatabar gidan Nan saidai idan gudu tayi ta boye a wani waje saboda azaba dik inda ta boye ma zata fito"

Murmushin keta hajiya babba tayi ta nisa tace "dik inda ta shiga tunda na hadata da isyaku magana ta Kare nasan cikin duhun dare zai shiga nemanta Kuma zai aiwatar da abinda nasashi"

Sai yanzun gwaggo rahi tasa baki cikin maganar"bayan ya aiwatar da wanan kudirin ni Kuma akwai wani kuduri nawa na zuciyata Wanda sai hakan ya faru zan sanar daku"....

Shigowa bilkisu tayi hannunta dauke da flask na abinci da aka Gama Allah Allah takeyi ta shigo Taji tattaunawarsu Amma lokacinda ta shigo ta tarar Dasu shiru tamkar ruwa ya cisu....

********
"Innalillahi Ina Fatima ta shiga ne?me yarinyar Nan take nufi?badai ta gudu ba"...shi kadai yake tafe yana sambatunsa Yana zancen zuci....

Dik yau be gantaba ya rasa inda zai tsoma ransa yaji dadi,zuciyarsa Kara azalzalarsa takeyi da tsananin kaunarta Mai zafi.....daya zauna sai ya Mike ya fito tamkar wani sabon mahaukaci haka yaketa kaiwa da komowa har magaruba ta rufa be gantaba....

Haka ya hakura ya shige dakinsa ya rufe kansa ya shiga rera kuka Mai ban tausayi "shikenan Fatima kin tafi kinbarni da ciwon sonki cikin zuciyata Wanda nasan shine zai halakani,Ina tsananin kaunarki meyasa zakiyimun haka?"...dafe kansa yayi a bakin gado idanuwansa na fidda hawaye masu zafi.....

Ciwon Kai ne Mai tsananin gaske ya rufesa Wanda ko masallaci sallahr magriba kasa zuwa yayi.....

*********

Duhu ya rufa sosai bilkisu ta kasa zaune ta kasa tsaye,....ta rasa inda zatasa rayuwarta hakanan ta Mike ta fito daga wajen kwanciyarsu ta nufi dakin da Fatima ke ciki,Wanda ya gauraye da tsananin duhu sai Dan Haske kadan ta saman karamar window din dake ciki shima hasken farin wata ne,

Motsi Fatima taji Wanda ya furgitata Saida ta saki fitsari a inda take zaune hantar cikinta ta kada,hade da yin suman gaske....

Cikin murya Mai kamada Rada kasa kasa bilkisu ta Soma magana"Fatima nice bilki kina Ina?nakasa sukuni nakasa kwanciya inbarki cikin wanan halin yasa na fito nazo Dan in tayaki Zama da asuba sai inkoma"

Wasu hawayen farin ciki suka shiga gudu a idanuwan Fatima tasa hannu ta share hade da sauke ajiyar zuciya,Tana bayan wani buhun Kaya a boye ta fito a hankali take lalube harta hango inuwar bilkisu inda take tsaye Tana faman waige waige,

Kafadarta ta dafa bilkisu ta juyo suka rungume juna suna kuka Mai ban tausayi,hannun juna suka rike suka koma can gefe suka zauna shiru Babu Mai cewa wani uffan,

Suna Nan zaune suka hangi inuwar mutum biyu maza,suna Haske Haske da tar touch light wadda batada wadataccen Haske,

Magana sukeji kasa kasa"kasha kuruminka hajiya ce tasani wannan aikin shiyasa na gayyatoka Dan Kai ma ka Dana"

"Kamar kasan cewa Ina kwadayin wanan yarinyar tun ranan Dana fara ganinta komai yaji fa"

Zabura bilkisu da Fatima sukayi jikinsu na matukar rawa ko wacce hanyar buya take nema,

Cikin Kaya bilkisu ta shige hade da toshe bakinta saboda tsananin tsoro,

Fatima lungun kofa ta shige ta baya ta tsugunna Tana hangensu suka shigo suna Haske Haske,

Tana Nan tsugunne Tana Raba Ido cikin duhu taji wani mugun cizo gefen kafarta Wanda Saida ya ratsa har tsakiyar kwanyar kanta,take network din jikinta ya dauke......azaba da zugi da radadi suka dirar Mata lokaci daya.....zufa ce ke tsattsafowa a jikinta ta ko Ina cikin mintuna da Basu wuce uku ba jikinta ya shiga rawa,

Haske Haske sukeyi da Yar touching daidai kasa ya haska touch light a karo na biyu Karaf Fatima idonta yakai Kan wani Abu Wanda ko baafadaba kunama ce ta harbeta tunda gashi ta daga k'arinta a karo na biyu.....

*Muje zuwa*.....

*Kuyi maneji da wanan sanan Ina rokon dik wani masoyina Mai karatun littafin Nan da yamun addua ta Allah ya kawomin farin ciki cikin rayuwata ya duba al'amarina🙏🏼*

*SLIMZY😍✍🏼**🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

_Ina daukacin_ _jama'ar_ *KUNDIN* *HASKE?..* _wanan shafin kyautace ga dik wata member ta group din kundin_ _Haske,ku rarraba_ _Banda wawa😹_ 😹😹.....

28

Zaro ido Fatima tayi waje hade da sakin wani fitsari Mai zafi a tsugunne jikinta na faman karkarwa,a wanan yanayin da take ciki har gara Harbin kunama da balain dake Shirin samunsu,

Zagaye dakin kawai sukeyi suna Haske Haske Amma basuga kowaba,kusan minti arbain basuji motsiba tsaki isyaku yayi "Kai Amma yarinyar Nan Bata kyautamunba dik na Gama Shirina dazun Dana fita har jiko Nasha yadda zansamu karfin cin uban shegiya Yar taadda Mai kisan Kai sai gashi ta gudu,komi Daren dadewa tunda hajiya tabani go a head saina aiwatar da nufina"

Tsaki abokin yayi hade da kashe yar touch light dinsa yace "muje mu kwanta dare nayi dik Kai kasamun Rai wallahi"....Yana karasa fadin haka yayi gaba abinsa,

Jiki a mace isyaku yabi bayansa yanata jera uban tsaki haka suka fita suna waigen dakin....

Jin takun fitarsu da kamar minti goma Fatima ta saki sassanyar ajiyar zuciya hade da fashewa da kuka ,rike da kafarta take fadin "na shiga uku shikenan ajalina yazo".....

A guje bilkisu ta fito daga mabuyarta jikinta jike sharkaf tayo hanyar kofa Tana lalube,waigawa takeyi gefen hagu da dama "kina ina Fatima meyasameki?meya faru?"

Kuka Fatima ta Kara rushewa dashi hade da janyo jiki ta fito daga bayan kofar ta zube a kasa "ganinan bilkisu kunama ce ta harbeni"

Dafe kirji bilkisu tayi hade da zaro ido cikin duhu "kunama fa kikace,munshiga uku a Ina ta harbeki"

Cikin shasshekar kuka Fatima ta Bata amsa "a kafana"

Ai bilkisu batayi wata wataba ta daga kasan rigarta tasa hakori ta yago dogon kyalle tayo Kan Fatima Tana lalube da hannu kasantuwar akwai duhu sosai,....Kama hannunta Fatima tayi hade da fadin "gani nan"

Da sauri bilkisu ke zare Dara daran idanuwan Nan nata ta shiga nada Mata kyallen a kafar tanayi Tana daurewa tamau,yayinda azaba da radadi ke Dada ratsa sassan jikin Fatima ga karkarwa da jikinta keyi Nan da Nan zazzabi Mai tsanani ya rufeta....

Kallon bilkisu takeyi da rashin fahimtar wanan dauri da taiwa kafarta tamau "bilki kin dauremun kafa Tana karamun zugi da azaba Mai hakan ke nufi"

"Kiyi hakuri Fatima hakan shine mafita kafin safiya Domin k'arinta bazai rinka Miki yawo a jikiba kinji ki daure zuwa safiya musan abunyi"

Murmushi Fatima tayi hade da Jan majinar hancinta "abunyi kawai mu gudu na gaji da wanan azabar nagaji da wanan masifar"hawaye na Dada gangarowa a idanuwanta....

Cikin tausayawa bilkisu wadda itama zuwa yanzun ta karaya da wanan lamari Wanda tun kafin aje ko Ina masifa ta ishesu tace"ki kwantar da hankalinki Fatima wuya Bata kisa sai kwana ya Kare"

"Idan wuyar Bata kasheni ba ai ta wahalar Dani ko bilki,gaskiya nagaji bazan iya jure wannan masifar ba tun Ina kubuta watarana zaayimun abinda zai nakastamun rayuwa"

Hawayen da bilkisu ke boyewa su suka zubo Mata tasa hannu ta share "kece fa kike fadamana cewa bawa baya taba wuce kaddararsa,sanan bawa baya taba samun cigaba a rayuwa sai ya hadu da kalubale kala kala.....haba fati karki karaya Allah daya haliccemu Yana sane dake Wanda dik wuyar da kikasha kina jarinta zuwa yanzun ya rayaki kika girma da ranki da lafiyarki shi zai duba lamarinki"...

Kuka Fatima takeyi Babu kakkautawa ga rawar sanyi da takeyi jikinta yayi zafi rau tamkar an hura wuta.....bilkisu ta nemi jikin bango ta jingina hade da lumshe idanuwanta wasu hawaye masu zafi suna gangarowa.....

Kiran sallahr farko na asuba karfe hudu da rabi ya farkar da bilkisu wadda ke jingine tana baccin karfin hali....a firgice ta farka hasken farin wata ya wadata dakin,mikewa tsaye tayi Tana kakkabar kayan jikinta....

A gaggauce tazo daidai kunnen fatyma ta Rada Mata "Bari inje Kar a Gane baa daki na kwanaba idan na tabbatar kowa ya farka zan wayance zan dawo kinji?"

Gyada Mata Kai kawai Fatima tayi Banda zugi da azaba Babu abinda kafarta keyi,bazata iya furta ko kalma dayaba sabodda yadda jikinta ya zuge da zazzabi....

*********

Tafe take Tana adduar Allah yasa Babu Wanda ya ganta,...kicibis sukayi da yarima ya fito daga bangarensa zaije masallaci ya rage lokaci saboda bacci daya gagaresa,

Idan ba idonsa keyi Masa gizo ba to tabbas waccen yarinyar dake tahowa bilkisu ce daga wancan mugun dakin na tsohuwar ajiya,tafe yake Yana sake sake ita ko sai waige waige takeyi har suka hadu,

Saida gabanta ya fadi ganin mutum da farar jallabiya a gabanta Dan batasan da dahowarsaba,....zubewa tayi a gabansa "barka da tashi ranka ya dade"....

Kallon tuhuma yake binta da idanuwansa da suka canja kala zuwa launin ja saboda kukan da yaci a Daren jiya Yana rokon Allah...

"Me ya fito dake daga can daki?me kikajeyi?"
Chapter 38 · 0% Book details