Sashe 62
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gaskiya na tayaki murna kasancewar Zaki dandana niimar dana da'ndaneta na rage....ba haka Rai yaso ba kanin miji yafi miji kyau"ta saki wani malalacin murmushi tai wucewarta side dinsa zuciyarta fesss cike da nishadi haka ta fito hannunta rike da kayansa har Zata wuce deejahmah ta dakatar da ita da fadin "idan kin shiga kicewa mijina inada bukatar ganinsa"
Murmushi Fatima ta sauke "karki damu zan fada Masa Amma saidai bazaki samu ganinsa yanzun ba Domin wanka yakeyi sai ya shirya matarsa Zata sanar Masada amaryarta nason ganin Mai gida"....
"Karya kikeyi baki isaba wallahi a dik lokacinda naso ganin mijina zan ganshi ba sai kinbasa umarni ba"
Dage kafadarta Fatima tayi hade dayi Mata gwalo tayi sama a guje Tana dariya.....
Ta tura kofar a hankali bakinta dauke da sallama Yana tsaye Yana goge jikinsa "mekika tsaya yi?naji kamrr hayaniya a kasa"
Farrr tayi da idanuwanta sanan tace "wayyoo Ina magana da su zaituna ne Akan bazamu samu damar yin breakfast ba sai mun dawo"...
"Ok"kawai yace ya cigaba da shiryawa ita ta taimaka Masa ya shirya tsaf....
Ta zura alkyabbarta ta Kara feshe jekinta da turaruka masu sanyin kamshi....
Sanan suka fito a tare daka kallesu Dole ka Kara kallonsu saboda tsabar kyawu da daukan hankali da sukayi...
Kallo deejahmah ta bisu dashi baki galala....dakyar ta hadiye miyon bakin ciki tace "barka da tashi ranka ya dade"
"Barkanki da tashi deejah,Yaya kika kwana?"
"Lafiya"kawai tace a takaice ta juyar da Kai....
"Naga yau kin tashi da wuri"
"Umm"shine abinda tace still Tana kallon tv ....
Rahane da zaituna suna zaune a kasan carpet fatima tai gyaran murya "ammm zaituna kije sama ki gyaramin dakuna na inada bukatar a caccajamin zannuwan gado sanan ki shiga kitchen ki fada musu burabusko da miyar kwai sa farfesun kifi danye mukeda bukata idan mun dawo dan fita zamuyi"
"Angama ranki ya dade"....Jin abinda Fatima tace yasa deejahmah saurin juyowa Tana binsu da kallo cikin karfin Hali ta bude baki tace"matarka Bata fada maka inason ganinka bane naji zaka fita"
"Laaa kaga habeeb na mance amarya ta murda kambunta nason ganin mijinta"tai maganar Tana dariya
Dariya yarima yayi "to deejah ya akayi kinada bukatar wani Abu ne?"
Ganin Fatima ta kalli agogo yasa deejahmah mikewa cike da yanga da Isa Tana Taku dai dai "inason ganawa da mijina Amma a dakina"
Tai gaba abinta,...ya dauki seconds kafin ya dubi Fatima a gaggauce yace "ina zuwa"....ta kaicine ya lullube Fatima ganin lokaci na tafiya sai batace komiba ta gyada Masa Kai....
*******
A gefen gado ya sameta zaune Yana shigowa cikin gaggawa yace "gani mekikeda bukata?mekikeso kice"
Kawai sai deejahmah ta shiga rera kukan kissa hawaye na gudu a idanuwanta ta shiga fadin "ni yanzun banida yancin da zantashi bacci mijina ya shigo dakina yaji ko inada damuwa?banida yancin da kwanciya bacci mijina zai shigo yayimin sallama Saida safe?banida yancin da darana mijina zai zauna a dakina yabani lokacinsa ya kula Dani Koda na minti talatin ne?dik banidashi yayah?saboda ni din ba matar so bace?Koko bakasona ne aka daura makani Dole zaka kula Dani ka duba lamarina....niba kanwarka bace?ko wani yayimun haka a gidan mijina nadauka Kai Mai zuwa ka amsarmin yancina ne sai gashi da kanka kakemun haka?...yanzun banida hakkin da zaa fadamin zaa fita saidai kawai inganku?ko ka manta inada hakki akanka ne?"....ta karashe maganar da rushewa say kuka Mai karfi....
Sandarewa yarima yayi a tsaye saboda yadda maganganunta Suma shiga jikinsa....tabbas maganganunta dik gaskiya ce Babu karya tabbas be kyauta Mata ba,
Dakyar ya motsa jikinsa ya karaso gabanta ya dagota zuwa jikinsa ya rungumeta tsammm....shafa Mata jiki kawai yakeyi zuwa gashin kanta Wanda hakan ya Bata damar manna Masa albarkatun kirjinta Wanda take yaji wani Abu nayi Masa yawo a jiki Jamar Ta'na....ya shiga rada Mata a kunne "kiyi hakuri kinji nadaina insha Allahu zan rinka kulawa dake Kuma Ina sonki kema kinji"..
Ta dago kanta Tana manne a jikinsa yasa hannu ya shiga share Mata hawaye "ya Isa kinji?nabari banason kukanki"
Dora kanta tayi a kafadarsa "Amma kasan nice keda Kai koh?ta shagwabe murya,
"Yi hakuri nasani ai zamu dawo da wuri yau Ina tare dake ko"...yadda yaji Tana sakin ajiyar zuciya tausayinta ya Kara kamashi ya dagata cakkk Yana juyata a daki kawai saigata Tana dariya sanan ya direta kasa ya ja hancinta "zamuje saimun dawo ko?"
"Ka kukamin da kanka"tace idonta kirrr Akan nasa fuskarta dauke da murmushi,shima murmushin ya mayar Mata sanan ya fita a gaggauce ta bishi a baya,
Fatima na tsaye babu abinda zuciyarta keyi sai tafarfasa bakin ciki ya lullubeta tamkar ta fasa ihu ta sani sarai deejahmah tayi hakan ne don ta tozarta ta ta Bata Mata Rai ta Kuma Bata tayi nasara saidai ta tsokalowa kanta tsuliyar dodi inhar wanan wasan ne Bismillah....
Shigowarsu parlon ya Bata damar kirkiro faraa ta Dora a saman fuskarta "har Kun Gama?amarya saida lallashi dama muje koh?"
Kallo yabi Fatima dashi Dan ya hango tsantsar kishi da bacin Rai a fuskarta dauriyace kawai da jarumta irin Tata...
Tsabar mugunta yasa deejahmah sakin Yar dariya kasa kasa ta Haye kujera ta Dora kafarta daya Kan daya.
Ficewa sukayi ko kafin su fita dama Fatima ta aika a shirts motoci haka kuwa akayi da Yan rakiyarsu dasu kansu motoci uku suka dauka....
Tunda suka shiga motar yake kokarin aika mata da sakwannin soyayya Amma ko kallon inda yake batayiba savida takaicinsa daya lullubeta data kalleshi sai Taji haushinsa ya kamata ya gamo soyayya da lallashi da rungume wata yazo zai Mata barazana...ta kauda kanta gefe ganin haka ya sashi tabe bakinsa ya maida nasa Kan gefe batare da yace komiba......
Tafiyar minti arbain ta daukesu zuwa gidan marayu,....karya kwanar da zata sadasu da gate din shiga gidan driver yayi take Fatima hankalinta yayi mummunan tashi tunda tai tozali da wanan gate din,abubuwa da dama suka shiga dawo Mata da yawo a cikin kwakwakwar kanta.....
Koda suka shiga ciki runtse idanuwanta tayi ganin yadda yara ke famar fitowa daga wajen karbar abincin safe dayawa daga cikinsu kafafuwansu Babu takalmi wasu suturar jikinsu dik a yage wasu Kuma tsabar dattin da sukayi ko miyau bazaka iya hadiyewa ba idan ka kallesu....
Ganin motoci sunyi parking yayi matukar daukar hankalin yaran inda dayawansu Sukai wajen motocin wasu Kuma suka tsaitsaya suna kallonsu,
Bangarenta diriver ya bude Mata mota ta sako kafafuwanta ta Dade ciki kafin ta fito gabaki daya wata Yar karamar yarinya ce da bazata wuce shekara biyar ba ta shiga ihu tana murna Tana fadin "yeeehhh ankawo taimako yau zamuci shinkafa".....sai duka yaran wajen suka dauki ihu da sowa na murna
Tsaye tayi Tana kallonsu yadda suke murna suna farin ciki Wanda ita ma a lokacin baya Bata wuce yin hakan ba Domin da zarar aka zo dubasu ji suke tamkar ansasu a aljannah....
Kwallace ta taro a cikin idanuwanta ta mikawa wannan yarinyar hannu alamar tazo Aiko a guje tayo wajenta Tana fadin "Kun kawo Mana abinci ne?harda shinkafa?....tuwo aketayi Mana kullum kullum"...Yar ta canja fuska tamkar zatayi kuka,
Fatima ta share hawayen daya gangaro Mata batare da yarinyar tagani ba,ta shafa kanta "insha allahu yau zamuci shinkafa kinji?"
Sai kawai ta saki hannun Fatima tai cikin yara tana murna duka yaran suka shiga murna suna shigewa bangarensu a guje,
Ta dau Yan mintuna Tana sharar hawaye abubuwa da dama na dawo Mata na Baya....tabbas rashin iyaye da gata babban gibi ne a rayuwa dik ranan daka rasa iyayenka idan kanada damaryin kuka kayi Domin dik maraya Yana tare da wani ciwo a cikin zuciyarsa Wanda me iyaye bazai taba fahintar wanan ciwon ba....😭(ya ilahi Allah ka jikan iyayenmu)....
Kallonta yarima yake hannuwansa rungume a kirjinsa,shi kansa ganin yanayinta ya sashi karajin tausayin nata Domin dik Wanda ya kalli fuskar Fatima a wanan lokacin sai ya zubda hawaye...
Tana tsaye tamkar an dasata,batasan yazo bayanta ba sai Jin sautin raunanniyar muryarsa tayi "haba ranki ya dade yanzun kin tashi daga marainiya fa kin koma uwar marayu,be Dace uwar marayu ta tsaya gaban yatanta Tana zubar da hawaye ba"
Hannu tasa ta share kwallar data zubo Mata Tana kallonsa lokaci daya "Ina tayasu jimamin abinda sukeji ne Domin dagajin kalaman yarinyar Nan kasan cewa basa samun cikakkiyar kulawa daga wajen gwamnati sai lokacinda Allah yasa suka tuna dasu sanan su kawo musu dauki,...bana manta lokacinda mukai yunwa a makarantar Nan harta da ruwan Sha bamu dashi abincin da zamuci babu Saida mukai kwana uku Babu ci Babu Sha Wanda sanadiyyar hakan dayawa daga cikinmu sukaita ciwo suna rasa rayukansu saboda yunwa da kishin ruwa.....masu kudi suna mancewa da taimakon marayu ko fidda dukiyarsu sukayi saidai su nemi me karfi su Kara mishi karfi ga inda ya kamata su kawo dauki su ciyar da maraya Domin su samu babban rabo ranan gobe kiyama Amma sun manta da hakan"
Shi kansa yarima Saida yaji hawaye na Shirin zubo Masa ganin yadda Fatima ta rikice,Amma gudun Kar ya Kara karya Mata zuciya yasashi ruko hannunta batare da yace komiba suka nufi record office na gidan...
*******
Bincike sosai akeyi a cikin record office baaga file din Fatima ba,Wanda ya Kara sata cikin mummunan tashin hankali dik ta fada damuwa ta furgice,
Sai manager na wajen ya shiga cikin store din wajen inda tsofaffin files suke da wadanda suka gudu baagansuba Nan ya shiga ya Soma duddubawa,ya dauki lokaci kafin ya fito wajen zufa dik ta Gama wanke Masa fuska ga kura da jikinsa yayi,
Kakkabe file din yayi sanan ya Ciro medical glass dinsa dake makale a aljihun gaban rigarsa ya Sanya ya bude ciki ya shiga karantawa Yana girgiza Kai....ya dau lokaci kafin ya dago kansa ya maida hankalinsa garesu,
"Toh a bisa alamu da bincike da abinda file dinki ke kunshe dashi na record dinki Wanda ya kawoki gidan Nan namijine Kuma babban mutum Domin ko a lokacin shekararsa hamsin da takwas ke kuma an kawoki gidan Nan ne a shekara hudu da watanni"
Kallon juna sukai da yarima a tare ko wanne gabansa na tsananin faduwa,
A hargitse Fatima tace"shekara hudu da Yan Kai?....Kuma namiji ne ya kawoni gidan Nan?"
Jijiina Mata Kai maaikacin yayi
"Kenan hakan na nufin tsuntata yayi kenan?"