← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 80

Sashe 42

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gira daya yarima ya daga "yason ranka dolema gobe inyi shigar burtu in burkice kamar baniba inje musha soyayya da deejahmah"ya karashe maganar da Dan murmushin mugunta...

"Wallahi wanan yarinyar sonka takeyi,ta rigada takamu Domin dik haukar da takeyi Akan fati fa kishi ne bawai Dan kaddarar da ta aukawa faty bane kadai"

Canje fuska yarima yayi "zata Soni nikuma zanyi amfani da wanan damar wajen ramawa Fatima takaicin da suke kunsa Mata na tanadar Mata manyan bokatai da zata cikasu da hawayen takaci a cikin gidana"

Dariya Ahmad keyi Yana nuna yarima da yatsa "friend wallahi masarauta zata rikice"

Dage kafadarsa yarima yayi batare da yace komiba ya janyo kofin da ya ajiye na ruwa ya kwalkwale sanan ya kalli Ahmad ta gefe "muje incigaba da jinyar amaryata"....

********
Kuka Fatima keyi Tana rike da kafarta yayinda bilkisu ke tsugunne gabanta Tana Danna Mata kafar da ruwan zafi Wanda ta dibo a kitchen batare da kowa ya gani ba...

Cije labe takeyi Tana janye kafar bilkisu ta dago Kai a fusace "malama so kikeyi ki gurgunce kenan akaiwa yarima ke da kafa daya,ki tsaya a gasa Abu kina iskanci Aida gashin soyayya ne da bakiyi kuka ba"...ta watsa Mata harara...

Cikin kuka Fatima ta dago Kai "ki sakarmun kafar Mana kibari yazo ya gasamun tunda dama ai aikinsa ne jinyar matarsa"

Murmushi bilkisu tayi bayan ta tsomo tsumma ya Nadi ruwan zafi batayi wata wataba ta dorawa kafar....wani mugun duka Fatima takai Mata a baya "muguwa ki kyaleni wallahi kina sane kikemun wanan mugunta kibarni haka yazo ya gasamun"....takarashe maganar cike da shagwaba..

Harararta bilkisu tayi sanan ta kwashe da dariya"dama ai soyayya kece Kan Gama lailah da majnun"....ta saki tsumman a kasa "to Bari yazo yayi Miki"....ta juya tai tafiyarta,kallo Fatima ta bita dashi harta kule Bata ganinta sanan ta runtse idonta zuciyarta na bugawa sauri da sauri Babu Wanda take bukatar gani sama da yarima yayi Mata wanan lallashin da yakeyi mata.....murmushi ta sauke hade da dafe kirjinta Tana sauraren yadda zuciyarta ke harbawa....

*********
Zaune deejahmah take a gefen gadonta tana sanye da kayan bacci milki colour da bakar hula a kanta ta tura gashinta ciki,...hannuwanta duka biyu suna tallabe da habarta ta fada duniyar tunani,har mahaifiyarta da kanwarta suka shigo dakin batasaniba Saida uwar ta dafa kafadarta Tana kallonta sanan tayi waigo a furgice ta bisu da kallo..

"Deejahmah na fada Miki wanan Abu bamai yuwuwa bane ki kwantar da hankalinki wallahi tallahi Nina shiryawa wanna yaki...saboda haka karki damu kanki ki Hana kanki sukuni kisawa zuciyarki damuwa"

Kallo tabi mamanta dashi fuskarta dauke da damuwa "kishi da baiwa kuyanga?,mama Dole hankalina ya tashi ki duba kigani fa yadda kawayena keyimun kamar xasu lashi tafin kafanta tunda na sanar musuda kabir zan aura ake girmamani sai Kuma a kawomin ziyara watarana aga wanan kucakar itace kishiyata wallahi na tsaneta"...ta karashe maganar hawaye na bin idanuwanta....

Gefenta uwar ta zauna ta janyota jikinta Tana shafa kanta "nayi matukar bakin cikin ganin hawaye a fuskar jarumar yata Khadija Wanda bantaba tunanin hakanba,Wai kin manta auren huce takaici xakiyi?kin manta da kudurinki Akan shi kansa yariman ne?kin manta da fansar jinin habibu da zakiyi akansa?Koko kinfara sonsa ne?"....."ba sonshi nakeyi ba bazan taba sonsa ba harabada Kuma bazan taba janye kudurina akansaba harabada,da zarar bukatata ta biya zan aiwatar da kudirina akansa".....

*Nagaji🤨....*

*SLIMZY🥰✍🏼*🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

_nagode da kauna_ @ *ZAHRA MAI GARI*.... _son so_ _fisabilillahi_

30

********
A gurguje bayan kwanaki uku da faruwar haka kusan tunda Mai martaba ya yanke wanan hukunci Fatima ke cikin azaba dik ta rame tayi bakin Kirin, kwana uku kenan batasa yareemah a idanuwanta ba ta shiga matsananciyar damuwa wadda tunda take Bata taba shiga irintaba....

A bangaren yarima shima hakan ce ta kasance Domin kusan kullum cikin fakon Ido yakeyi ko zai ganta,saboda zamanta a gidan yasa ya mance da gidansa da yake bayan gari Wanda a al'asarsa ma can ne wajen zamansa zuciyarsa yauma sake sake kawai takeyi mishi Yana zaune ya rafka uban tagumi ya kurawa TV dake manne a bangon dakinsa Ido a zahirin gaskiya ba kallo yakeba ya fada duniyar tunanine...

Yau kwana uku Fatima be gantaba ita Kuma Bata nemeshi ba me hakan ke nufi?yarinyar Nan kenan ba sonsa takeyiba dik abubuwan da takeyi mishi Tana yi Masa shine kawai bawai Tana sonsa bane ya shiga rigingimu kala kala daban daban akanta Amma ta juya Masa baya,bazai taba nemanta ba inhar Bata nemeshi ba tunda abin nata haka ne....

Mikewa yayi ya suri makullan motarsa da wayoyinsa ya zura a aljihunsa ya fice daga bangarensa har ya Miko hanyar parking space ya juya yabi side din da akeyi Masa gini...

Sauri sauri ya keyi ya tsaya daga Dan nesa kadan abin ba karamin mamaki yabasa ba ganin yadda cikin kwana uku ansa foundation gini ya Mika,zuciyarsa cunkushe da takaici haka ya juya ya nufi motor park

Sauri sauri bilkisu ke bin bayansa bai San da itaba ya shige motarsa yaja a guje ya bade wajen da kura....itama kallo ta bishi dashi haka ta juya jiki a sanyaye ta nufi cikin gida....

A daki ta tarar da Fatima kwance sai rawar sanyi takeyi dik jikinta Babu inda baya rawa a kwance take saman tiles Babu arzkin abinda zata shimfida ta kwanta ,gefenta bilkisu ta zauna fuskarta dauke da damuwa ta sa hannu ta taba wuyan Fatima Wanda yayi zafi rau

"Fati nabi bayan Yaya besan Ina binsa ba ya shiga motarsa ya wuce dama tunda ya fito daga bangarensa Ina fakonsa inga inda zaije in sanar Masa da halin da kike ciki sai Naga yabi bangaren can da ake gini ya dade wajen tsaye sanan ya Mike wajen motoci Ina kiransa beji ba haka ya wuce"

Runtse idanuwa Fatima tayi hawaye na gangarowa ta gefen hancinta masu zafi "ban taba tunanin yareemah zaimun haka ba,Saida ya samun soyayyarsa da kaunarsa sanan yake neman juyamin baya idan ko haka ne na shiga babban bala'i"

Cikeda alhini bilkisu ta matso kusa da ita sosai ta kamo hannunta "kiyi hakuri ki kyautata zato akansa kila abubuwa ne suka Sha Masa Kai saboda aurensa Nanda sati biyu da Yan kwanaki ne Kinga kila akwai hidimomin da yakeyi kuma a kwanakin Nan Ina lura be shigowa sai dare kiyi hakuri"

Kuka Fatima takeyi harda shassheka "tun kafin yayi aure kenan ya Soma canjamin inaga yayi aure ni danasani ma da ban jefa kaina cikin matsala ba Dan tabbas soyayya matsala ce bilki"

Rufe Mata baki bilkisu tayi da hannunta "karki Kara cewa haka wallahi Yana sonki kidai kwantar da hankalinki kila yanada uzuri ne karki zargeshi kinji Yar uwata?....yanzun Bari inje Kar hajiya ta nemeni"

Daga Mata Kai kawai Fatima tayi daga kwance yayinda bilkisu ta Mike ta fice a dakin Fatima ta bita da kallo har ta bace....

********
Hajiya babba ce zaune a parlor gefenta lemon Zaki ne da ayaba Wanda bilkisu ke bare Mata Tana Mika Mata daya bangaren Kuma Mami ce kuyangarta Tana durkushe....

Kallon gefen da Mami take hajiya babba tayi "ke jeki kiramun Fatima tazo inji dalilin da yasa abinda nasata tamun batayimun shi ba "

"Allah ya baki yawan Rai ai Fatima yau wuni tayi kwance a daki Tana jijjiga Wai sanyi takeji batada lafiya Kuma ninasan karya takeyi zannuwan gadon da kikasata wankewa ne Bata gada ma ba"

A fusace hajiya ta dago Kai "yi sauri kiyimun kiranta"

Da hanzari Mami ta Mike ta fice,....batafi minti biyar da fitaba sai gata ta shigo Fatima na biye da ita a baya dakyar take motsa idanuwanta saboda yadda sukai Mata nauyi....jikinta Babu kuzari kwata kwata ga yunwar dake kwakularta haka ta Tattaro dik wani karfinta tasa a kafarta Dan idan batayi wasaba zata iya zubewa a wajen "barka da hutawa ranki ya dade gani'

Sarai hajiya babba ta lura da yadda jikin Fatima ke rawa ga uban Rama da tayi daga ganinta ko baa fada ba ansan akwai abinda yake damunta Amma saita Sha murr hade da Kara tamke fuskarta "Ina aikin da nasaki kiyimun?banace ki tattaramun zanuwan gado harda barguna ki wanke munba?sarkin gida kemun wanki Amma tunda gaki na hutar dashi maza ki Mike kije kiyi abinda nasaki cikin awannin da Basu wuce uku ba idan ba hakaba sai Nasa an lallasamun ke"

Kwalla ce ta taro a idanuwan Fatima haka ta cije lebe hade da boyesu ta Dan rusuna"to ranki ya dade"

Hanyar Kofa hajiya ta nuna da yatsa cikin tsawa ta ce "bacemun daga gani kinyi da shegun idanuwa kamar na tsofaffin mayu"

Da kyar Fatima ta iya saisaita tsayuwarta ta fice da sauri saboda yadda jiri ke dibarta tamkar zata Fadi....

********
Kwance yake rigingine a Kan doguwar kujerar parlorn ahmad ya kife fuskarsa da jarida Idanuwansa a rufe zuciyarsa keyi Masa tsananin suya tamkar an zuba Masa rushin wuta,

Ahmad dake gefensa ya zuba Masa Ido tun shigowarsa ya Gama fadansa bece Masa komiba sai nazarin maganganun yarima yakeyi....

"Niko a ganina friend ka binciki yarinyar Nan kaji meyafaru da har baka gantaba tsawon wadanan kwanakin yadda takeyi maka shagwaba da soyayya ko baa fada ba Tana sonka"

Dagowa yarima yayi daga kwanciyar hade da jefar da jaridar gefe ya saukewa Ahmad idanuwansa da suka canja kala suka kankance "Ahmad nasan Fatima Tana Sona Amma meyasa zatayimun wasa da so?meyasa zatayi mun wasa da zuciya?me hakan ke nufi guduna fa takeyi tunda har yau bankarasata cikin idona ba tun bayan haduwar da mukayi last a fadar sarki muke wasan buya da ita"

Murmushi Ahmad yayi "kaga ne Mana friend kasani sanin kanka cewa Fatima batada yancin kanta a gidanku tazone a matsayin kuyanga baiwa kaga ko Dole ta bautawa iyayen gijinta da baka da masaniya Akan abinda takeyi da har ka kasa sata a Ido cikin wadanan kwanakin"

Shiru yarima yayi Yana nazarin maganar Ahmad din Wanda wata zuciyar ta aminta da hakan yayinda wata ke ayyana Masa wani Abu daban.....

Kusan minti talatin batare da yace komiba kamar Wanda aka tsikara ya Mike "Bari inje inaso inje wajen Khadija inji abinda suke bukata Dan ni daga yau tabar sake ganina"
Chapter 42 · 0% Book details