Sashe 13
Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru nayi a tsaye Ina sauraron me hajiya zata Kara cewa,....kaiwa da komowa ta shigayi Rai a bace tacemun "Fatima ta yaro kyau take Bata karko saboda haka kije idan kinsan wata ai Baki San wata ba"......
Da'go kaina nayi da sauri na dubeta ta dakamun tsawa"nace ki fice Koh?"
Sumi Sumi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki nake tafiya na fice a wajen Ina sharar hawaye.....
Ina tafe Ina kuka,babban abinda ya tadamun da hankali shine kalmarta ta karshe "idan kinsan wata ai Baki San wata ba"....sunayen Allah kawai nake Kira Ina kuka har na karasa inda na hango Yaya yarima tare da su bilkisu.....
*******
Kwanci tashi babu wuya wajen Allah,tun daga wanna lokacin hajiya Bata Kara tunkarata da maganar fita Dani yawon iskanci ba yayinda likafa kullum Kara gaba takeyi na fita da Yan Mata,
Wajen fita da Yan Matan ne firdausi tasamu ciki a wanan lokacin munga tashin hankali Wanda bamu taba ganiba tun hajiya suna boye boye har aka gano firdausi rashin lafiyar da takeyi,Wanda hajiya da kanta ta kawo Mata magunguna Tasha jini ya balle Mata tamkar zata mutu haka Tasha wahala dakyar ta samu lafiya,hakan besa hajiya daina wannan aika aikar ba,
Kwatsam muna zaune akazo da takadda Akan muda muka Gama makaranta tun shekarar data wuce cewa gwamnati zata dauki nauyin karatunmu zaa kaimu domin cika form na jarabawar share fagen karatun jamia,bakaramin murna mukayiba cikin wadanda aka kawo subayensu harda sunana saidai Babu na Yan uwana banji dadin hakanba su kuwa suntayani farin ciki sosai....
Saura kwana biyu mutafi hajiya ta shigo har dakin da muke kwana daddare takiramu takawo sababbin Kaya ta Raba Mana inda Ni aka bani wannan rigar dake jikina pink colour tace insa tagani....
Ina saka rigar ta amshi jikina sosai na da'go Kai Ina kallon hajiya Tana murmushi Wanda bansan dalilinta na hakan ba nikuwa kunyace ta lullubeni na sunkuyar da kaina Ina tsaye....
Hajiya tace "to wadda ta kawo kunya duniya,ko itan ma zakice bazaki iya sawa bane?sarkin musulunci?wadda ta yankewa ustazanci cibiya?Ina abun ustazanci anan anyi cikinki a titi an wurgar dake gwamnati ta taimaka Miki har wata kafafa zakiyi?keda Zaki karar da rayuwarki a gidan marayu batare da ko Kare ya shinshine yace zai aurekiba?saboda Babu Wanda zai dauki tsintacciyar mage Dan Bata mage"
Hawayene suka wankemun idanuwa Jin irin cin zarafin da hajiya kemun take na tuna da kalmar Yaya yarima da yacemun a lokacin "insha allahu Ni Zan Zama sanadiyyar farin cikinki Fatima bazaki dawwama a gidan marayu ba inhar Ina Raye"....wani sanyin dadine ya ratsani Dana tunada wanna kalmar saita wankemun cin zarafin da hajiya tayimun....na tube rigar na Mika mata tace"ki ajiyeta a wajenki domin ita zakisa Dan akwai inda nakeson biyawa daku idan kuntashi jarabawar,gabana ne ya shiga faduwa zuciyata ta shiga bugawa sauri da sauri,ilahirin jikina Babu inda baya rawa.....
Murmushi hajiya tayi tace "yaro yaro ne"....ta juya abinta ta wuce Ni kuwa na bita da kallo jiki a sanyaye....
*******
Yau ta kasance Ana gobe zamuje jarabawar,tunda na tashi nake Dan Jin zazzabi gabaki daya hankalina baa kwance yakeba tunani nakeyi kala kala yayinda nake tsintar kaina cikin faduwar gaba Wanda bansan dalilinsaba,
Ina zaune a Kan benci Yan uwana suka zagayeni na rafka uban tagumi,
Hannu bilkisu tasa ta ciremun tagumin tace"Fatima banason kinasawa ranki damuwa nafada Miki hajiya tabar wanan maganar tunda dadewa ki kwantar da hankalinki ki cire damuwa a zuciyarta"
Wasu zafafan hawayene suka shiga saukadaga idanuwana Babu kakkautawa juyowa nayi da dubana Ina kallon bilkisu da wani irin kallo Wanda bansan irinsaba nikaina ,kallonta nake Babu kakkautawa,
Huramun iska tayi a idon tace"Fatima yadai kikemun wannan kallon Kuma kina hawaye ?saikace wadda idan ta tafi bazata dawoba?"
Runtse idanuwana nayi nace"haka nakeji a jikina bilkisu,ji nakeyi tamkar kallon karshe nakeyi Miki tamkar bazan sake rayuwa a cikinkuba,inajin wani bakon lamari a jikina tamkar wani Abu na Shirin faruwa Dani"
Bude idanuwana nayi na saukesu Akan bilkisu Naga itama hawayen takeyi....rungume juna mukayi muna kukan da bamusan dalilinsaba......
*Muje zuwa shafi na gaba Kuma karshe Akan labarin Fatima....ya abin zai kasance?*
*SLIMZY🥰✍🏻**🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*
*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*
*NA SLIMZY*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*
11
Kuka sosai mukeyi nida Yar uwata bilkisu Babu me lallashin wan hakikanin gaskiya tausayin kanmu nakeji a wanan lokacin saboda rayuwar da mukeyi ta rashin gata,uwa uba rashin gata yasa ake dibarmu Ana lalata Mana rayuwa,inda a gaban iyayenmu muke hakan bazata faru ba....
Kwana nayi Ina zubda hawaye wanda bansan dalilinsaba haka kawai na tsinci kaina a matsananciyar damuwar da bansan dalilinta ba.....
********
Washe gari da sassafe aka kawo mota yayinda dukanmu muka shirya tsaf damu muka karya da kunu da kosai ,misalin karfe bakwai da rabi mukaita shiga mota....sauran yara Yan uwanmu Sai fatan alheri da samun nasara sukeyi Mana,
Har na shiga mota na fito na rungume bilkisu Yar uwata hade da bubbuga bayanta nace "ki kula da kanki Sai Allah ya Kara hadamu"
Kwallar da nake boyewa CE to sulalo a idanuwana,ban Bari taganiba nasanya hannuna na goge na kauda fuskata na shige motar aka jamu,Sai daga musu hannu mukeyi.....
Tsagaitawa Fatima tayi da labarin ta kalli barrister hauwa wadda ke kuka harda majinu Tana kallon Fatima cike da tsantsar tausayawa ,girgiza Kai Fatima tayi itama Tana hawayen ta cigaba da cewa....
Makarantar da zaa kaimu yin jarabawa Nan aka nufa damu,Sai kallonmu sauran yara sukeyi da jamaar wajen mussaman da akace yaran gidan marayu ne wasu na tausaya Mana wasu najin kyamar mu,nidai ko a jikina tunda nasan cewa baninayi kainaba Allah ne yayini,a haka aka shigar damu ajin jarabawa inda mukabar hajiya da haruna zaune jikin mota suna jiranmu.
Nice farkon fitowa da aka Gama babu inda na nufa Sai wajen motar mu,a Nan na tararda su hajiya halima,tun daga nesa sukemun faraa itada haruna Sai jikina be bani ba Amma Sai na kauda zargi a zuciyata Dan babu kyau....
Dan durkusawa nayi nace "sannu da hutawa hajiya"na sunkuyar da kaina,
Washe Baki hajiya tayi tace "Fatima kune zaayiwa sannu kuda kukasha Zama a ciki,Allah dai ya bada saa Fatima"
"Ameeen hajiya"
Na koma jikin mota na jingina,
Malam haruna ne ya juyo ya miko min lemon gora guda daya da fanke yacemun ga nawa sauran ma zaa Basu nasu,
Hannuna na rawa na amsa nayi Masa godiya,na tako na karasa Kan wani benci wajen Mai Saida abinci na zauna Ina ci Ina kurban lemon Nan saboda yunwar da nakeji,minti minti Ina da'go Kai in kalli wajen dasu hajiya ke zaune tare da haruna saboda kada Yan uwana su fito a tafi a barni ,Sai Inga Basu fitoba hajiya CE ke shewarta itada haruna a wajen.
Biyu na Raba lemon da fanken na ajiyewa bilkisu Yar uwata Wanda Zan Kai Mata a matsayin tsaraba idan na koma,Ina Nan zaune shiru shiru nafara gyangyadi wani irin bacci Mai nauyin gaske yake dibata Ina wartsake idona,tun Ina controlling kaina har na kasa,na kifa kaina a cinyata na Soma bacci......
Zuwa wannan lokacin kukan Fatima ya tsananta,barrister hauwa ta dafa kafadarta tace"daure ki karasamun labarin Nan Fatima Kinga ankusa zuwa tafiya dake ga yamma tayi"
Share hawaye Fatima tayi ta cigaba da magana....
Wanan baccin da nayi shine Wanda ban farkaba Sai cikin dare Wanda Ina bude idanuwana na ganni Akan babban gado Wanda tunda nazo duniya ban taba Hawa irinsa ba,
Zumbur na Mike nafara waige waige,Ganin irin dukiyar dake cikin dakin tamkar dakin wani sarki ko shugaban kasa,kici kicin sakkowa nafarayi Sai naji motsin bude kofa da sauri na waiga,
Muna hada Ido dashi na zaro idanuwana waje tamkar zasu fito hade da Dafe kirjina,Nan da Nan jikina ya dauki rawa tamkar mazari dik sanyin AC dake dakin da fanka be hanani sharbewa da gumiba cikin seconds da Basu wuce talatin ba,
Kafeni yayi da idanuwansa Yana sanye da jallabiya Fara yace "babe har kintashi?yanzun nake cewa wanan baccin idan ba na mutuwa bane ya kamata kitashi,niyyata idan Baki tashiba in daukeki inyi Miki wanka Kila kitashi"
Bakina na rawa nace "wanka Kuma bawan Allah ?"
Mai makon ya amsamun Sai ya daga mun gira daya kawai ya nemi kujera ya zauna ya janyo karamin table Wanda ke dauke da apple da wuka akai ya Fara yankawa yanaci Yana kallon tangamemen tv dake faman aiki a dakin,..
Munsamu kimanin minti biyu Babu abinda ke Kara Sai tv sainan ya juyo da dubansa gareni yace "kitashi kiyi wanka ki gargasa jikinki Dan bazan hada jiki dake kina danko na dauda ba"
Wani irin bugu kirjina keyi tamkar zuciyata zata fito a Raina nace "hada jiki?"....waya kawoni Nan?...take su hajiya suka fadomin ,gabana ya Yanke ya Fadi Dana tuna da kalmarta ta "ta yaro kyau take Bata karko,idan kinsan wata bakisan wataba"
Dago kaina nayi da sauri na dubesa beko kalli inda nake zaune ba apple dinsa kawai yake yanka yanaci tamkar Mai yanga haka yake motsa bakinsa,...tsura Masa idanuwa nayi inaso in tuno a inda nasanshi,....take na tuna shine Dan sarki Wanda sukazo kawo Mana tallafi kwanakin baya masu yawa da suka wuce,sanan shine Dan takarar sanata na wanan jaha tamu....."innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"....dama abinda sukeyi kenan su fake da guzuma su harbi karsana?....jikina ya jike da zufa tabbas wanan zaluncine,shin kowa ne yake haka ko kuwa wadansu ne ke Bata wasu cikin masu kudin?
Ina cikin wanan tunanin maganarsa ta dawo Dani hayyacina "Fatima sunanki ko?"
Da sauri na gyada Masa kaina alamar ehh "nace ki tashi kiyi wanka kinki dare nayi gashi inaso in huta dake,saboda hajiyarku ta tabbatar mun dake cikakkiyar budurwa CE"
Nan da Nan naji marata ta kulle inajin fitsari,idan nayi kwakkwaran motsi Zan iya sakin fitsari,zuciyata ke harbawa sauri da sauri....
Bakina na rawa nace "Dan Allah kayi hakuri kada ka lalatamun rayuwa"
Wani mayaudarin murmushi yayi ta gefe daya ya waigo ya dubeni yace "dama ku yaran talakawa kunada wata ingantacciyar rayuwa ne?ko kuwa ku da iyayenku suka wofintar daku a titi aka tsunceku aka rufa muku asiri aka killa ceku?"
Kallonsa nakeyi Ina hawaye,bakaramin ciwo maganarsa tayimunba,dama suna amfani da damar bamuda gata suke Bata Mana rayuwa?"