← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 80

Sashe 64

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Surukata surukar arziki ce wadda tasan yakamata tasan darajar Dan Adam sanan ta daukaka addininta ta tsaida sallah sanan take nunawa na kasa da ita kauna Bata fifita kantaba Akan Wanda ke kasanta shiyasa Koda nace Mata banzo gaishekiba tabani umarnin Nan da Nan inzo ingaisheki shiyasa na shigo sanan inyi Miki godiya Akan bawa danki maganin karfin shaawa Wanda hakan ya bashi damar barje amarcinsa a wajen matar so ba matar da aka lika Masa doleba,....naso ace ita ya saukewa gajiyarsa kamar yadda kukaso sai reshe ya juye da mujiya"

A gigice hajiya babba ta Mike zaune jikinta har rawa yakeyi Tana kokarin saukewa Fatima tafi a fuskarta da sauri Fatima ta guce "ai wata fuskar tafi gaban Mari,hajiya kayya fuskar sarauniya tafi karfin Mari a wajenki yanzun ,a da datake baiwarki kin mareta kin duketa yanzun lokaci ne na maida martani....."

"Kinyi kadan kice zakizo in rinka hada numfashi dake yarinya,ban hada numfashi da manyan mutaneba cikakkun Yan asali saikece kadangaruwar bariki zan tsaya musayar miyau dake?yarinya kinyi ganganci Amma ki tabbatar Nan gaba kadan zaki rasa hankalin da zakizo kice zakimun rashin kunya "..

"Da Allah na dogara hajiya ban dogara da boka ko malam ba nazo inyi Miki bangajiya ne Akan Wasafa yayi kyau sosai yanzun aka fara bugashi,Ina fatan kin Kira diyar Taki kinji halin da take ciki?"ta kashewa hajiya babba idanuwa wadda gabaki daya take kallon komi tamkar a film ganin komi takeyi tamkar a mafarki....

Girgiza kafa takeyi Tana girgiza kai idanuwanta sun kankance cike da tsananin bacin Rai...ta bude baki zatayi magana yarima yayi sallama,

"Barka da zuwa ranka ya dade,kajini shiru ko?hajiya ce ta rikeni da Hira wallahi"

Kallon rashin yarda yake binta dashi take ta kashe Masa Ido daya sai kawai yayi murmushi ya gurfana a gaban hajiya babba "barka da yamma ranki ya dade"...

Kallon kallo sukeyi da Fatima sanan ta kauda kanta kadan "barkadai"....murmushi dauke a fuskarsa yace "inbarki Nan ko?"

"Dau matarka kutafi Domin ko ganinta banasonyi"....

Bece kokiba ya Mike jiki a sanyaye cike da rashin Jin dadin abinda hajiya babba tace,

Itakuwa Fatima ko a jikinta Koda yayi gaba tsayawa tayi kadan ta dubi hajiya yadda bakin ciki da tsananin takaici ya bayyana karara a fuskarta "hajiya bakida yadda zakiyi Dani Domin yanzun kika fara ganina yanzun kikafara rayuwa Dani Domin Ina Nan daram a cikin gidan Nan....rashin ganina yanada nasabane da ranan da dik kika wayi gari kikaga kin makance shine kawai Zaki daina ganina'...ta karashe maganar cike da tsiwa ta juya abinta Tana girgiza tai tafiyarta wani kululun bakin ciki da takaicine suka taru suka cunkushewa hajiya babba a zuciyarta....

**********
Babu yadda deejahmah batayiba da zaituna Akan ta bude Mata dakin Fatima ta shiga Amma fafir zaituna Taki yarda ta watsawa idanuwanta toka tace ita baa bar Mata makulliba,..

Takaicine ya lullubesu dukkansu suka shiga jibgar zaituna tamkar an aikosu deejahmah Tana haki take fadin "yau zakibar aiki a gidan Nan tunda kin nunamin cewa shegiya tafini mutunci da daraja a idanuwanki Bari Mai gidan ya dawo"

Fauziyya ce tace "ko a harabar dakin shegiya mu watsa yadda da ya nufo dakinta zaiji takaici da bakin cikin da zai hanashi shiga"

"Kin kawo shawara"cewar khausar,

"Muna fuka bacemun daga gani"...Sumi Sumi zaituna ta juya zuciyarta cike da tausayin Fatima da alhinin abinda ake Shirin yi Mata....

********
Ana kiraye kirayen sallahr magriba Fatima ta shigo a gajiye,ta baro yarima cikin mota daganan zai wuce masallaci,

Da sallamarta ta shigo Amma deejahmah dake zaune dasu fauziyya Babu Wanda ya tanka mata,ganin faizah a tare dasu yasa Fatima cin birki Tana bin fauziyya wadda takewa faizah kallo,

"Danki ya dade faizah abun naki ma yau Babu magana Yar shariya ce?"

Yatsina fuska fauziyya tayi cike da takaici "kedai kikasani tun yaushe nazo kin fita da miji ance tun safe kuka fita Kuma ba girkinki bane"

Mamakine ya lullube Fatima sai Bata kawo komiba tace"wayyoo ai girkin be fita a hannuna ba sai daddare tukunna zan shirya angon nawa yaje wajen amaryarsa fatana dai Kar yaje dakin amarya Yana baccin gajiya"ta kashewa deejahmah Ido wadda suka hada Ido lokaci daya hade da dariyar mugunta,

"Faizah kisameni a sama zan rage kayan jikina"Tana fadin haka ta Haye benenta,

Kallon juna sukayi dukkansu dake falon khausar ce wadda takaici ya Gama kasheta "tashi kije dama tasamu da zarar shegiyar ta shiga alwala kiyi yadda yadda Dace,idan yaso kice Mata haushi kikaji na jiranta da kikayi Bata dawoba yasa kikai Mata bakar magana"

Rage murya fauziyya tayi cike da munafurci "Allah koh"..

"Sauri sauri"

Fatima a daki kuwa zaituna ta tutsiye Tana famar zazzaga Mata masifa "saboda kin rainani yasa nace ki canjamin zannuwan gado nadawo na tadda dakina yadda yake ko"

Girgiza Kai zaituna tayi gabanta na tsananin faduwa tsoro da fargaba suka cikata lokaci daya taji Tana son Fatima tun ranan da aka ce tana daga cikin bayinta savoda haka Mai martaba a manar Fatima ya Basu bazataciba...

Bakina rawa tace"ranki ya dade ba laifina bane nayi hakan ne Domin Kare lafiyarki da igiyar aurenki"

Cikin Rashin fahimta Fatima ta watso Mata tambaya "banganeba"

Nan zaituna ta kwashe komi abinda ya faru cike da tsoro ta fadawa Fatima,wadda tun kafin ta karasa tai mutuwar tsaye saidai ya zaayi ta gasgata zancen zaituna?Bata kai karshen tunaninta ba ta tsunkayi muryar zaituna Tana fadin

"Ranki ya dade akwai abinda na fahinta guda daya shine Wanda shima ya kamata in fargar dake"

"Umhmm Ina sauraronki"

"Faizah da fauziyya Yan biyu ne yaran wazirine suna son suyi Miki Wasa da hankali,wanan wasan abinda na fahinta shine faizah itace me kirki ita kikasani yayinda fauziyya ke amfani da wanan damar tanaso ta cutar dake"

"Zaituna kema nafarajin tsoronki banason Mina furci karki hadani da mutane"

"Ba munafurci bane ranki ya dade gaskiya ce Bari kiji abinda naji".....Nan ta kwashe labarin da Taji fauziyya Tana fadawa deejahmah na har turaren jaba ta kawowa Fatima a boye.....Jin haka yasa Fatima gasgata zaituna tunda Babu Wanda yasan anbata turare Kuma turaren na Nan cikin Jakarta idan haka ne kuwa tasan maganinta,

Zufa ta share,jiki Babu kwari ta zauna gefen gado ta rafka uban tagumi Tana fuskantar zaituna,...buga kofar dakin akayi Wanda shine ya tabbatar Mata da kila fauziyya ce,sai kawai ta sallami zaituna tace "bude kofar,kije abunki idan nagama zan nemeki"

"Toh Allah ya taimakeki"....zaituna ce ta bude kofar ta ratsa ta gefen fauziyya tai tafiyarta,

Shigowa fauziyya tayi, fuskarta dauke da faraa "ranki ya dade guda dakinki a hargitse"

Wani irin kallo Fatima Kebin fauziyya dashi Wanda yasata tsarguwa ita kanta fauziyya dakyar ta zauna a gefen gadonta tana waige waige,

"Lafiya Naga kina waige waige?Koda yake shi Mara gaskiya haka lamarinsa yake"

"Bangane Mara gaskiya ba Fatima mekike nufi?"

"Wayyoo bansan bakida fahinta ba yasa na Fadi hakan Amma Nan gaba kadan kwakwalwarki zata bude ranan da kika nemi manemanki kika rasa kin Soma warin jaba saboda rashin wayau irin naki"

Kan fauziyya ba karamin daurewa yayiba Nan da Nan jikinta ya Soma rawa "mekike nufine"..

Fatima ta janyo Jakarta dake rataye a jikin abun rataye jaka "Bari inbaki babbar kyauta"...hannunta na cikin Jakarta ta bude turaren ta fito dashi batai wata wataba ta watsawa fauziyya dik turaren a jallabiyarta"idan kinje gida kifadawa babarki naji dadin turaren gashi kema na tsan Miki Wanda kika kawomin ne ranan kamun bikin mijina"

Turo kofar yarima yayi ganin fauziyya yasashi sauke faraa a dik tunaninsa faizah ce yasashi cewa "faizah Yar innah "

"Ba faizah bace fauziyya ce wallahi muke wani game Nan a wayarta Wanda ya burgeni na mage da bera Dan Allah habeeby ka siyamun waya"ta shagwabe fuska,

NA bada order wayarki gobe zaa kawo,

Jikin fauziyya sai rawa yakeyi tanabin Fatima da kallon ikon Allah da al'ajabi dama yarinyar Nan haka take?Ashe ba kyalle bace turmin zani ce?"

"Fauziyya Ashe kema kuna shiri da Fatima kenan"

Jinjina Masa Kai tayi "umm Yaya zan wuce"....

Fatima ce ta Mike muje inyi Miki rakiya koh?"ta bi bayan fauziyya suka saukko bene a tare,dik deejagmah ta dokanta,ganinsu dare yabata tabbacin komi ya auko....ta sauke wani malalacin murmushi,

Tsayawa tayi a tsakiyar parlorn ta rike kugu kanta babu dankwalin sai fanka dake kada gashin kanta "Wasa yayi kyau saidai an Kara rashin saa Domin tsintacciyar dai a dik inda take da saaarta take da kuma Allah na tare da ita,saimu Tara a Wasa na gaba ko fauziyya?Kya basu labari"....ta juya abinya har takai wajen matakala ta tsaya ta juyo "ranki ya dade ki shirya dakyau Domin angonki xaiyi Shirin zuwa dakin matarsa"ta Haye sama abinta,

Inda ta barshi na ta taddashi Tana shiga ya rungumeta Yana shinshinar wuyanta ta Shiga shafa sumar kansa zuwa kunnuwansa,a hankali ta rada Masa a kunne "ba aikina bane aikin amarya ne yau zaka dandana zumarta itama"

Jiki Babu kwari ya saketa daga rukon da yayi Mata ya juya ya fice daga dakin kawai....

Kallo ta bishi dashi Tana sauke numfashi a hankali,ga gabanta da ya tsananta faduwa na tunawa da tayi yau ce Rana ta farko da zasu raba wajen kwanciya itada masoyinta,tsaki tayi kadan ta zauna jagwab Akan gado ta dafe kanta zuciyarta nayi Mata zugi da tsananin radadi,...ta Dade zaune Tana tunani dakyar ta Mike tsaye ta rage kayan jikinta ta fada toilet a can toilet din ma kuka ta zauna tanayi wiwi saboda tsananin kishi da yake taso Mata,dakyar tasamu tayi wankan ta fito ta shafa Mai sama sama ta feshe jikinta da turare saban ta bude drawer dinta ta Ciro Yar doguwar Riga Mai siririn hannu yellow har kasa take ta zura sanan ta daura zani tasa hijabi ta tada sallah,

Tana zaune Tana adduointa Akan dadduma Tana rokon Allah Akan Allah ya cigaba da kareta da mijinta Akan dik sharrin da zasu nufeta dashi Allah kuma ya rage mata wanna mummunan kishin dake dawainiya da ita,

Tana Nan zaune da hisnul Muslim a hannunta zaituna tayi knocking,...kallon kofar tayi sanan tace"umhmm,waye"

"Nice zaituna ranki ya dade"

"Shigo"

Ta bude kofar ta shigo ta zube a gaban Fatima "ranki ya dade yarima ne yake kiranki a parlorn kasa"

"Meyafaru?"

"Nima bansaniba"tace a takaice ta sunkuyar da kanta kasa,

"Jekice Ina zuwa"

Zaituna ta Mike Sumi Sumi ta fice,
Chapter 64 · 0% Book details