← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 80

Sashe 11

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke bilki kirufawa kanki asiri da jita jita a Ina kika jiyo?"

"A bakin uwaliya da ke kitchen naji dazun lokacin da naje kankaro Mana kanzon Nan?to a Nan naji,...umm Ni barci nakeji "Nan bilkisu ta gyara kwanciya ta kwanta abinta tabarni Nan zaune a cikin duhu Amma hankalina baa kwance yake ba,

Koda na kwanta idona biyu juyi kawai nakeyi Ina tunanin Ina hajiya ta dibi su firdausi ta kaisu domin Ni bawani gasgata magabar bilkisu nayiba dik dauka nake shirmenta ne don Babu abinda masu kudi zasuyi da kazaman yara kamarmu marasa galihu,

Kwana nayi ina tunanin maganar hajiya halima,wadda kemun yawo a kunne,juyi kawai nakeyi har gabanin asuba naji karar bude kofar shigowa dogon dakin namu,na dauka anzo tashinmu sallahr asuba ne Nan da Nan nayi zumbur na Mike aikuwa karaf hajiya halima ta hangoni sai ji nayi tace "wace munafukar CE ta mike zaune don iskanci a wanan tsakiyar Daren?uban me kikeyi?"

A hankali na sulale na kwanta batare da nayi ko kwakkwaran motsi ba nasan ba karamin aikinta bane ta rufeni da duka a wanan Daren,

Idona biyu suka wuce Tana biye dasu firdausi har wajen kwanciyarsu, gefe ta zauna ta daga hannunta tace "nasan bazaku rasa samo kyautar kudi ba Banda Wanda aka bani,to inji dumus Dan vazakuje kuci kaji kusha AC a banza ba anbar kwanan sauro ,kuce baa Dan Baku wani abuba"

Cikin rawar jiki suka shiga fitowa da abubuwan da suka samu suna dire Mata Saida ta amshe Yan kudaden tsaf Kuma suka Raba abinda sukazo dashi na ciye ciye suka zube Mata nata,sanan ta umarci ko wacce ta Ciro kayan jikinta tabata,

Babu musu Suma shiga cire kayansu suna Bata ta tattara tasasu a jakar ledarta ta fice.....

Niko dake gefe tausayin kanmu ne ya lullubeni take naji wani hawaye da bansan daga ina yake ba Yana sauka a kuncina,lallai rashin iyaye babban rashin jigone a rayuwa,inda munada iyaye dik lalacewarsu bazasu yi Mana wanan wulakancinba,

Hannu nasa na share hawayen daya wankemun fuska lokaci daya, Jin sanyin iskar asuba na kadani yasa nakara kudundunewa cikin tsumman zanina ina shasshekar kuka....

*******
Da safe bayan anbamu kunu da kosai kwaya uku uku kununma tamkar besan da wata suga ba sunan ansa gashi tsululu yayi ruwa haka ake zuba Mana ludayi biyu biyu a Kofi mun kafa layi muna amsa,bayan mun karya ne hajiya tazo tare da mukarrabanta haruna da sauran maaikatan da sukejin tsoronta ta taramu tafara jawabi cikin daga murya"dik wata yarinya dake bangaren Mata a gidan marayun Nan to ta tabbatar ta bada gudun mawa wajen aikin gayya da zamuyi yanzun Nan domin munada manyan Baki daga gwamnati maana,Dan sarkin garin Nan Kuma Mai takarar sanata ya sanar Mana da zai kawowa marayu ziyara hade da mukarrabansa da ahalin gidan sarki Baki daya,to ina Mai sheda muku ku tabbatar da ko Ina yayi fess Babu datti don zaiyi zagaye"

Tana Gama fadin haka aka shiga watso Mana tsintsiyoyin kwakwa wasu da manjagara haka muka kwasa muka shiga aikin Nan Sai wajen karfe daya muka Gama don dama munsani idan zaa kawo Mana ziyara mafi yawan lokuta da yamma ake zuwa...

*******
Misalin karfe hudu da rabi muna zaune a daki nida bilki a daki nasamu munyi wanka da kyar Shima kitchen mukaje bilkisu ta dibo Mana batare da kowa ya ganiba mukayi wanka,rabonmu da wanka kwana hudu kenan,

Wata kodaddiyar atamfata nasaka ringa da zani Wanda matar Mai girma gwamna ta kawo Mana tallafi ,sanan nakawo farin hijabina Wanda dauda da rashin tsafta yasa ta koma Mai ruwan kasa nasa abuna na shirya tsab,na bude Baki zanyi magana kenan,Maryam ta shigo a guje Tana haki Tana fadin "ku fito ga tawagar gidan sarki Nan da mukarrabansu ku firfito"

Sauran tsurarun Yan Matan dake dakin suka shiga ficewa a guje wadanda dik wadda zaka kalla a gidan Nan Babu kayan arziki a jikinta saboda karancin kayan sawa da muke dashi,

Bilkisu ta kalleni ta gefe taga banida alamar tashi tace"malama mikewa zakiyi mutafi don kada ayi babumu dan inaga kila ayi Mana rabon kayan sawa"

Haka kawai gabana ya yanke ya Fadi na Mike jiki a sanyaye Ina tafiya tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki,su kuwa bilkisu da Maryam sun kusan kaiwa inda muke hango dandazon jamaa, Dan tsayawa sukayi suna jirana a hasale Maryam tace "Fatima Naga take takenki idan bazakiyi sauriba mu wuce"

Sauri na kamayi Ina hardewa da zanina,yayinda suke tsaye suna jirana nadan tsaya in gyara zanina daya nannade ta kasa bilkisu ta Gama kuluwa ta da'go murya tace"Sai kintaho Allah yasa kada kisamu kayan Nan da zaa raba,Sai shegen yangar tsiya bayan kinfi kowa fatarar Kaya "

Sukai tafiyarsu,Niko na tako a hankali na kusa isowa wajen jamaar na hangi mutum a jikin wata bakar mota Yana facing Dina da alama waya yakeyi,

Kallonsa na tsayayi tamkar wawuya don tunda Allah ya halicceni ban taba Ganin halitta irin wanan ba fari Tass dashi Yana sanye da bakar shadda dakakkiya wadda Tasha aikin hannu ta matukar karbar farar fatar jikinsa,Nan na shagala Ina kallonsa naji an fincikoni "Fatima meye haka?kinsan me kikeyi kuwa?to Dan sarkine Allah yasa ma yasa a zaneki"

Murmushi ya sakar Mana daga inda yake hannunsa sakale da wayar da yake amsawa ya nufomu,aikuwa muka runtuma a guje kamar munga aljani mukayi cikin mutane dukanmu muka rarrabu....

*Muje zuwa ku biyoni a shafi na gaba,kuyi hakuri jina shiru da kukayi kwana biyu hkn ya farune sakamakon rashin lafiya da nayi nagode*

*SLIMZY✍🏻😍* 🥰*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*

*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA SLIMZY*

_Wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*

10

Kallonmu yakeyi Yana murmushi,ganin yadda muka runtuma a guje yasa ya tsaya daga inda yake takowa zuwa garemu,

Mukuwa rarrabuwa mukayi duka mu ukun kowa ya nemi wajen buya,Sai haki nakeyi a jikin wani karfe Ina maida numfarfashi Ina Dan leko da kaina ko Zan hangoshi Amma ban ganshiba,ajiyar zuwa na sauke na dafe kirjina da yake bugawa fatt fatt saboda gudun da mukayi.....

Taro sosai ake gudanarwa a wanan ranan domin harda kayan sawa aka kawo Mana tallafi gidan marayu da buhun Hunan abinci,yayinda Yan jarida keta daukar hoto.....shiru Banga Yan uwana ba na fito Ina takawa a hankali tamkar mejin tsoron wani Abu inayi Ina waige waige Sai ji nayi ance cikin wata murya Mai dadin sauraro"har yanzun tsoron be sakeki ba kenan?"cakkk na tsaya wani irin tsoro da furgici suka shigeni lokaci daya nakasa ko kwakkwaran motsi,

Takowa ya karasayi ya tsaya a gabana shine dai na dazun Wanda muka gani Yana waya yanzun hakan ma wayarce a kunnensa yakeyi, karkarwa kawai jikina yakeyi, domin har ga Allah na firgita sosai da wanan bawan Allah Sai ji nayi yace "yanzun haka Yan uwanku ake rabawa kayan sawa ke kuwa kina Nan kina buya,to boyon me kikeyi?"

Bakina na rawa nace "Dan Allah kada ka saceni kaji?kayi hakuri wallahi bazan sake ba"

Cikin mamaki yake kallona yace "Babu abinda kikamun Yan mata,sanan Ni Kuma bame satar mutane bane Koda Kika ganni a Nan ba a cikin mutaneba akwai dalili, dalilin kuwa shine bana son hayaniya shiyasa nadawo gefe inata waya abuna"

Jin jina Kai kawai nayi na juya nafara tafiya Ina hardewa har na danyi nesa dashi naji yace "Amma ya sunanki?"

Sarai nasan Dani yake na cigaba da tafiya,Sai ya Dan daga murya yace "idan har Baki fadamunba to Zan saceki in gudu dake"

Ai da sauri na juyo nace cikin daga murya "Fatima"Ina fada Masa na Ruga a guje ko Ganin gabana banayi saboda tsoron kada ya saceni,

Daidai tawagar Mai girma sanata sun taho domin zagayen gidan marayu lokacin na rugu a guje Zan gifta ta gabansu aikuwa hajiya ta kwalamun Kira "ke Fatima meye haka saikace wata akuya kin taho a guje kamar ba mace ba"

Da sauri na zube a wajen Ina Bata hakuri "hajiya Dan Allah kiyi hakuri wallahi tsoro naji shiyasa"....da'go idanuwana nayi don kallon yanayin hajiya kawai Sai muka hada Ido da wani kyakkyawan mutum fari Tass tamkar na dazun saidai wanan Shi yanada Dan jiki Kuma be Kai na dazun tsawo ba,

Da sauri na sunkuyar da kaina na Mike na wuce tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki,su kuwa wucewa sukayi domin zagaye.....

Cikin Yan uwana yara na shiga dik Wanda na kalli fuskarsa a wanan ranan cike yake da farin ciki saboda murnar an kawo Mana tallafin kayan sawa da kayan abinci, ...neman su bilkisu na shigayi cikin mutane Amma ban gansuba,Nima kawai Sai na juya na nufi dakin kwanciyar mu ko can sukaje,

Haka kuwa akayi,Ina shiga suka tuntsiremun da dariya dukansu dariya suke Babu kakkautawa,cikin dariyar bilkisu ke nunani da yatsa "faty Wai me yace Miki Dana hangoku ya kamaki?"ta Kara tuntsirewa da dariya,haushi ne ya kamani batare da nace komiba na karaso na nemi waje na zauna hade da daure fuskata,domin idan akwai abinda na tsana be wuce a kalleni a rinka yimun dariya ba ,su kuwa Yan uwana dabiarsu kenan musamman bilkisu,

**********
Bayan kwana biyu,

Muna zazzane a ta bayan kitchen nida su Maryam da Kuma tsurarun yara a wajen Sai mukaji hajiya halima ta rangad'a guda a cikin kitchen,dik Sai muka juya da sauri muna kallon windown kitchen din Wanda hayaki ne kawai ke fitowa,

Zumbur muka Mike muka Ruga a guje ta bayan kitchen din muka tsaitsaya muna lekenta,a tsaye take Tana kirga kudi masu yawan gaske fuskarta dauke da faraa take kallon haruna Wanda ke gefenta ya rike kugu Sai washe Baki yakeyi tace "tabdijan babban goro Sai magogin karfe malam haruna"

Kara washe baki haruna yayi hade da cewa "hajjin bana damu zaayi hajiya,harka da masu dala ai tayi ki dubi wadanan makudan kudin da aka Aiko dasu na shigar ciniki ne kafin mu Saida Kaya"

Kyalkyalewa da dariya hajiya tayi tace"ai Kaya sun siyu,idan cewa yayi a bar Masa ita ta zauna dashi har illah mashaa nibabu abinda ya dameni aika shegiya zanyi,wayasani ko ta sanadin hakan akasamu cikinta?"

Dariya sosai haruna yayi sanan yace "hajiya Akan kudi Zaki iya kashe mutum,yanzun menene abunyi hajiya?"

"Kabar komi a hannuna haruna nasan abunyi"
Chapter 11 · 0% Book details