← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 80

Sashe 78

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin faduwar gaba ta tsinci kanta ciki,...Fatima Kuma?yanzun saboda Fatima yake fushi?wato soyayyar da yakeyi Mata ta tsananta da har in sun samu matsala zai tsinci kansa cikin tsananin damuwa,dikda kishin da ya taso Mata be hanata numfasawa ba ta nisa tace,

"Kayi hakuri yaayah ai kasan Fatima yarinya ce sanan Kuma kaga halin da take ciki na rashin lafiya Dole ne ayi Mata uzuri koh?bedace ka rinka fushi da bintu ba"

Mamaki da al'ajabin maganarta ne ya lullubesa Dan be taba tunanin deejahmah zatayi wanan comment din Akan Fatima ba Domin dik sainsar da sukeyi yasani ,wani lokaci kyalesu yakeyi saboda Fatima ta tsinci kanta....shin me kalaman deejahmah yake nufi,ta Soma sonta ne?Koko ta daina rigima da itane....shin waye ya sanarwa da deejahmah Fatima na cikin wani Hali kenan tasan tanada ciki....tsoronsa Kar suyi Mata abinda zaisa cikin Nan ya lalace....

Hannunsa yasa ya dago fuskarta Yana karantar yanayinta,yadda take kallonsa hawaye kwance a fuskarta yasashi karaya yasa yatsansa Yana goge Mata,

"Kukan na menene?"

"Ina kuka ne saboda nasan bana cikin zuciyar mijina ko kadan saboda abubuwan da nayi a baya...koba haka bama zuciyarka gabaki daya Tana wajen Fatima"

Girgiza Mata Kai yayi "Ina sonki Deejahmah,ko Babu komi kedin fa Yar uwata ce,Sanan itama Fatima haka Kinga Baku da banbanci a wajena"

Hawayen da take boyewa ne suka sulalo Mata "naso ace nice a zuciyarka kamar yadda Fatima take,saidai hakan bazai yuwuba Domin zuciya so daya ne Kuma Fatima kakeyiwa shi,bazan ga laifinka ba Dan ka sota Domin ta cancanta ne....Nima yanzun burina be wuce mijina ya Soni Koda kwatankwacinta ba dikda yanzun Fatima tayimun nisa......koba komi yanzun dauke take da cikinka a jikinta kaga matsayinta da martabarta ta Karu a idanuwanka"

Tausayinta ne ya lullubesa saidai ya kasa gasgata kalamansa Domin zuciyarsa nayi Masa waswasi akanta,ya kasa yarda da itadin ya yada makaman yaki xaman lafiya take nema....

"Fatima Yar uwata ce....Ina sonta yanzun haka banida wani kudiri a zuciyata dangane da ita Wanda ya wuce alheri"....

Zuwa yanzun kalamanta sun Gama Shiga jikinsa dik jikinsa yayi sanyi dikda bawai ya gasgatata bane Amma ta bashi tausayi Amma zaisata on trial...

Rungumeta sosai yayi ya sumbaci goshinta ya cigaba da shafa bayanta Yana lallashinta.....

Zuwa dare yarima ya saki jiki ya mance da wani bacin Rai na Fatima dikda gangan jikinsa ne ke gidan Amman zuciyarsa da ruhinsa sunaga farin cikin rayuwarsa bintu....

*********
Kuka sosai Fatima keyi na Rashin yarima a kusa da ita daddare,....gabaki daya hankalinta ya tashi saboda yadda ya fita daga gidan ummu a fusace ya nuna alamar yayi fushi da ita....

Shin meye laifinta Dan tayi kishinsa?kishin miji halak ne ga ko wace matar aure....yarima bazai taba fahintar yadda takeji ba ko deejahmah ce ta amshi girki ya kwana a dakinta ji takeyi tamkar ta kashe kanta saboda tsananin bakin ciki da takaici....

Kifa kanta tayi a pillow Tana kuka harda shassheka,dakyar ta motsa hannunta ta janyo wayarta tayi dialing numbersa....

Ta Dade wayar na ringing be daukaba Jin hakan yasa wani sabon zazzabi ya Kara rufeta...

Texx ta tura mishi kamar haka...

_Habeeby bazan iya bacci ba,bacci ya kauracewa idanuwana....banida farin ciki Wanda ya wuce inganka yanzun a gefena kaimun mayafi da faffadan kirjinka....Ina sonka mijina...._

Yana sama tare da deejahmah ya sauko kasa daukar wayarsa da ya manta a kujera yasa hannu ya dauka ya taba yaga Miss calls dayawa ya duba ciki harda na Fatima...be Gama dubawa ba Tex dinta ya shigo wayar,

Tex dinta ya karya Masa zuciya...girgiza Kai kawai yayi ya kashe wayar ya juya ya Haye sama wajen deejahmah....

******""

Tare suka shirya da safe da deejahmah suka nufi gidan Mai martaba...

Bayan driver yayi parking hannunsa na cikin na deejahmah ya dubeta "Zaki Shiga cikin wajen hajiya ne?"

"Umm umm inaso inje induba Fatima"....yadda tayi maganar ba karamin mamaki ta bashiba sai kawai ya sauke ajiyar zuciya ya ruko hannunta suka fito...maimakon su Shiga sashen su hajiya sai suka nufi sashen ummu,

Tana zaune a parlor saboda zazzabi da takeji Tana sanye da katuwar rigar sanyi da safa,hannunta dauke da tea da takesha kadan kadan sukai sallama...

Kallo tabisu dashi cike da mamaki,

Gefe ya zauna dik yadda yaso ya kauda kansa daga gareta kasawa yayi besan lokacinda ya kafeta da idanuwansa ba tamkar ranan ya Soma ganinta,

Deejahmah dake gefe kishi na neman taso Mata ganin Fatima da yayi lokaci daya ya manta da ita a wajen sai kawai ta daure tayi gyaran murya Wanda hakan ne yasashi saurin wayancewa ya sa hannu a aljihun rigarsa ya Ciro wayarsa ya maida kansa ga wayar tasa,

"Ya jiki Fatima?"

Tambayar ce tazowa Fatima a banbarakwai don Bata taba tunanin haka ba,

Dakyar ta motsa lanbanta ta amsa da "da sauki"a takaice tayi maganar,

Murmushi deejahmah tayi "to Allah ya Kara lafiya ya rabaku lafiya"Tai maganar hade da kauda kanta gefe,

Ummu ce ta fito daga dakinta Tana fadin "waye ne yazo yakesa patient Dina magana" ..turus ta tsaya tanabin deejahmah da kallon mamaki,ta daure fuskarta tamau ta karasa shigowa parlorn ta nemi kujera ta zauna Tana bin deejahmah da kallo,

Ganin irin kallon da ummu keyi Mata yasata sunkuyar da kanta kasa "barka da tashi ummu"

"Kema barkanki,Ashe kinsan hanyar gida na"

"Kiyi hakuri ummu wallahi....

"Wallahi me?yau ma mijinki ne nasan ya tilastaki kikazo sashin nawa saboda ki gaida kishiyarki Amma da badan haka ba banida wanan arzikin a wajenki,yanzun ma tashi zakiyi kibarmun gida Dan ban yarda dake ba"

Da sauri yarima ya amshe zancen "Haba ummu ya zakice haka?"

"Da katamun kabiru karka kawomin iskanci kanajina koh?idan Kai ta kanainayeka da kissa ni Bata isaba Dan Nima macece sanan wani rawan jiki yasa ka fada Mata halin da Fatima ke ciki?to kasani idan wani Abu yasami cikin Nan bazan yardaba"

Kunyar deejahmah hade da tausayinta ya lullube yarima yadda Tai tsumu a zaune ummu na zazzaga Mata cin fuska ba karamin tausayi ta bashiba dikda shima bawai ya Gama yarda da ita bane,

Kwalla ce ta jika idanuwanta a hankali tasa hannunta ta cire hade da mikewa jiki a sanyaye tabi ta gaban Fatima ta gifta,kamshin turaren jikin deejahmah ne ya daki hancin Fatima Wanda tajishi a hancinta sakkk na yarima aikuwa take amai ya taso Mata ta Mike a guje tayi cikin daki ko kafin ta Kai ta amaye jikinta....cakkkk deejahmah ta tsaya hade da juyowa zata Shiga dakin,

"Dakatamun deejahmah wuce kawai zan gyara yata Dan bansan wani mugun Abu kikazo dashi ba Wanda ta Shaka ta Soma amai tunda tafara ciwo batayi amai ba ko sau daya sai yau da zuwanki....bansan mugun nufin ki ba"

Zuwa yanzun ranta ya Gama baci haka ta taka kafarta ta fice jiki Babu kwari...Tana tafe Tana sharar hawaye zuciyarta na Raya Mata Allah ubangiji yasa itama tasamu ciki kodan wanna abun da ummu tayi mata itama a kula da ita kamar yadda Fatima take ganin gata.....gashi Allah ya jarabceta da son ciki...

********
Saida Fatima ta numfasa sanan yarima ya dubeta kadan ya kauda kansa,

"Naga bakida lafiya gashi inaso muje wata Yar unguwa bansaniba ko Zaki iyayin karfi da jikinki daganan sai mu biya asibiti a Kara dubaki"...

Shiru tayi kamar bazata ce komiba sai can tace"zan iya Nima inaso infitan kodan Inga gari tunda na kwana biyu ban leka wajeba"

"Shiga ki shirya"

Mikewa tayi ta Shiga bedroom inda nan ne wajen zamanta ta bude karamin akwatinta ta Ciro bakar doguwar Riga Mai stones jajaye Mai shegen kyau ta cire kayan jikinta ta zurata kawai ta shafa Hoda a fuskarta da man baki sanan tasa Jan gyale tayi rolling tayi masifar kyau dikda ramarta data fito da wani irin fari da ta Kara Tai mugun kyau...

Ko alkyabbar batasakaba ta cire Jakarta ta rataya side bag red da flat shoes jajaye masu Dan flowers a sama ta fito,

Kallonsa tayi kamar bazatace komiba ta sunkuyar da kanta kasa "na fito"

"Ok"kawai yace ya Mike yayi gaba a abunsa tabishi a baya,

Tasha mamakin ganin shine zaiyi driving dinsu Dan haka kawai saita Shiga gabam motar ta bude Jakarta ta Ciro wayarta ta Shiga buga game suka dau hanya Babu mecewa wani uffan...

******

Tankakemem gidan sama Wanda ya tsaru taga sun nufa yarima ya Shiga horn da gudu Mai gadi ya bude Masa kofa hade da fadin "barka da zuwa ranka ya dade" hannu kawai ya daga Masa ya nufi parking space yayi parking motarsa....

Kashe motar yayi ya dubeta "muje koh?"

Turo bakinta tayi gaba "Ina ne Nan Kuma?"

"Idan muka Shiga zakiga ko inane na kawoki wajen sabuwar budurwata ne Inna wuro"...

Tabe baki tayi ta bude mota ta zuro kafarta kasa take Taji wani irin faduwar gaba ya ziyarcewata Wanda hakan ya haifar Mata da rawar jiki...

Har yayi gaba yaga Tana takowa a hankali ya Mika Mata hannu sai kawai ta Mika mishi ya rike Mata hannu Yana lura da yanayin yadda jikinta ke rawa bece Mata komiba haka suka nufi cikin gida....

Suna zazzaune a parlor har malam liman lokacinda yarima yayi sallama,

"Assalamu alaikum"...shine abinda yace hade da Shiga fuskarsa dauke da faraa,

Dukkansu faraa dauke da fuskarsu suka amsa harda xahrau dake gefe a zaune ta sunkuyar da kanta,

A sanyaye Fatima ta shigo parlorn hade da sallama dauke da bakinta kanta a kasa,

A tare suka Mike malam liman zuhra da Inna wuro suka hada baki "Allahu akhbar"sukace a tare fuskokinsu dauke da tsananin farin ciki,

Fatima na dago Kai suka hada Ido da zuhra Yar mamanta Taji jikinta ya Kama rawa ganin yadda hawaye ke sauka a idanuwanta...kirrrr tayi da Ido Tana kallon zuhra,

Inna wuro ce ta zare farin glashin fuskarta tasa hannu ta cire kwallar data cika a idanuwanta.....

Xahrau wadda ke zaune kwalla na sauka a jikinta yadda ta sunkuyar da Kai ko motsi ta kasa....a hankali Fatima ta taka gaban zuhra bakinta na tasbihi saboda tsananin kamar da ta gani da hotonta Dana mamanta Tana karama....

A gaban zuhra ta tsaya idanuwanta ko kiftasu batayi sai kawai zuhra ta bude Mata hannuwanta alamar ta taho Bata tsaya wata wataba ta fada jikinta ta fashe da kuka dukkansu kuka sukeyi sosai Tana kissing din gefen fuskar Fatima...
Chapter 78 · 0% Book details