← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 80

Sashe 70

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganina yasa ta furgita ta Mike tsaye na shiga girgiza Mata Kai "banazo Dan in cutar dake bane zahrau nazo ne in nemi gafararki Akan abubuwan da mukayi Miki kiyafemun nidai na cire hannuna"..

Kuka sosai takeyi Tana fadin "na yafe Miki mama karama har duniya ta nade na yafe Miki Dan Allah ki taimakeni kubarni in haifi abinda ke cikina"Tana kuka take fadin hakan,..

Saboda tsananin tausayinta bansan lokacinda hawaye ya Soma zuba a idanuwana ba Nan da Nan da kaina na gyara bangarenta nasa Mata turaren wuta na rufo Mata kofar na tafi sashena cike da zullumi da tunanin halin da Yar mutane ke ciki....

Tun daga ranan kullum nakan leka inganta yayinda Koda yaushe Ina turaka ka dubata Kaine abokin hiranta lokacin Nima inada cikin afnan wata uku a jikina,

Shirye shirye sosai Mai martaba yakeyi da kaninsa na haihuwar zahrau inda ya shirya zahrau a saudiyya zata haihu lokacin cikin nata nada wata takwas ranan da safiya Taji wanan labarin batayi bacci ba Dan dik a tunaninta zahrau ta haifi abinda ke cikinta matacce tunda bataji wata duriya daga gareta ba uwaliya ke kawo Mata rahoton karya cewa zahrau batada ciki.

Ranan safiya ta tasa rahina da wani tsohon maaikacin gidan Nan zubairu suka shiga sashin zahrau suka firgitata a gabanta safiya tabawa zubairu umarni da yazo sashen cikin dare ya farde cikinta ya Ciro abinda ke cikin nata ya kashe batare da kowa ya saniba saboda ranan Mai martaba da kaninsa sunje ran gadi wata masarauta kusa damu....

Tsagaitawa mama karama tayi tana kuka harda shassheka ta maida dubanta ga Fatima wadda ta kifa Kai Tana kuka tamkar ranta zai fita,shi kansa yarima kuka yakeyi saboda tsananin tausayi...

"Tun bayan barinsu sashin zahrau suka nufo sashen mu zahrau ta shiga furgici da tsananin tashin hankali Nan ta nemi taimakon uwaliya Akan tanaso ta gudu ta taimaka Mata uwaliya batai musuba ganin gwalagwalan da zahrau ta mallaka Mata dik Dan savida ta taimaketa aikuwa ta taimaketa ,Dan uwaliya itace Tai Mata hanyar data gudu cikin dare batare da kowa ya saniba....

Washe gari muka tashi da mummunan tashin hankali na batan matar sarkin masarautar barayar Zaki...Nan da Nan aka baza a ko Ina Akan an save matar sarki fadin mummunan tashin hankalin da abdallah ya shiga Bata baki ne a sanadiyyar hakan ne ya kamu da tsananin cutar barin jiki saboda faduwar da yayi lokacin da labarin batan matarsa ya ruskesa,

Hankula da yawa sun tashi a wanan lokacin ko Ina labarin abinda ya faru a masarauta ake ciki ko harda ciwon sarki abdallah....

Safiya da rahina kuwa dik alhinin da akeyi be damesuba Dan su farin ciki ma sukeyi na batan nata Dan rahina dama bayan ta haifi deejah ta dawo gida saboda aiki da galadima ya samu a Egypt ,

Kusan kwana arbain da faruwar lamarin mugun labari ya riskemu daga zubairu cewa ai matar sarki data bace yaji labarin mota ta bigeta ta rasu da ciki motar data bigeta ne Suka dauki gawar suka tafi da ita baasan inda suka kaitaba,...Nan sabon tashin hankali ya samemu Dan Babu Wanda be firgitaba da Jin wanan labarin jikin sarki abdallah ya Kara rikicewa gashi yaki yarda akaisa asibiti ayi Masa magani na bature yafison na gargajiya,Nan aka tattara shi aka maidashi garin iyayen su Dan ayi Masa magani,...

Koda labarin rasuwar xahrau ya riski Yan uwanta sunyi matukar bakin ciki da rasuwar Yar uwar tasu yayinda wasu Basu yarda da cewa ta rasunba,

Bayan shudewar lokuta abubuwan sun faru ciki kuwa harda nadin sarautar da akayiwa mahaifinku a matsayin sabon sarki lokacin na haifi afnan babu dadewa Dan dama khausar ita kusan saanni suke da deejahmah....

Kuka sosai Fatima takeyi lokacin da ta dago fuskarta a rikice tace "yanzu a Ina mahaifina yake?"shine tambayar data jefo Wanda ya Kara razana hajiya karama,

Take yarima ya ruko hannunta Yan girgiza Kai hawaye na gudu a fuskarsa,..

"Fatima mahaifinki Allah yayi Masa rasuwa kwanakin baya Dan lokacin da abun ya faru ma kina gidan Nan"

Mikewa Fatima tayi tsaye cike da tashin hankali Tana fadin "innalillahi wa Inna ilahi rajiun"

Rukota ummu tayi ta fada jikin ummu ta rungumeta Tana kuka "Ina saudiyya dik wadanan abubuwan suka faru lokacin Dana dawo sarki yayi Yar tafiya lokacin mahaifinki ya rasu yaje can garin....abinda yasa baa sanarba kuwa shine saboda tun da dadewa jamaa sukai tunanin ya mutu Dan haka shiyasa akai shiru da maganar"..

Rungumeta sosai Fatima tayi tana kuka harda shassheka,..

Sallamar hajiya rahina ce ta shigo gidan direct sashin hajiya karama ta nufa hajiya babba da tajiyo muryarta itama ta fito tare da deejahmah suka shigo,..

"Wani sabon labari ne ya riskeni yanzu yanzun Nan na karyar da naji Ana Shirin shiryawa"..

A zabure Fatima ta Mike daga jikin ummu jikinta har rawa yake tasa hannu ta share hawayenta "ba karya bane ba Kuma sharri akai muku ba abinda kuka binne cikin duhu shekaru ashirin da suka wuce yau *ANYI WALK'IYA* asirinku ya tonu.....Kunyi sanadiyyar korar uwata daga garin gabaki daya saboda karta haifi abinda ke cikinta ya gaji sarauta sai Allah yasa da hannunku kuka reni abinda ke cikin nata tunda gashi na dawo cikinku na dawo cikin dangina......shegiya tsintacciyar mage Ashe yar Sunnah ce cikakkiyar Yar dangi uwa uba Yar saarkice dakanta Dan haka ku shirya daukar fansa da zanyi akanku daya bayan daya"

Mamakine ya lullube kowa dake wajen na furucin Fatima da takeyi tamkar wata babba Babu alamar tsoro ko fargaba take fadan magana kanta tsaye...

"Karya kikeyi Fatima baki Isa kice kindauki fansa akanmu ba saboda labarin karya da aka zauna aka shirya Miki shine Zaki Mike kina fuffukar banza?idan kikace Zaki shiga shirginmu wallahi saina halakaki"..

"Idan kin halaka uwata kinci riba ni bazan halaku Miki ba Domin ni din Nan kainuwa ce dasheb Allah badai mutum ba kwayoyi da dacin madaciya Basu kasheniba sai tuggunki Wanda gabaki dayanku a tafin hannuna kuke?"

Yarima ne ya Mike tsaye ya ruko Fatima ta fada jikinsa ya rungumeta matarsa ya fice a dakin ya barsu suna faman jaraba da kumfar baki....

********

Cikin tsananinn tashin hankali hajiya babba ke magana "lallai na tafka babban kuskure tunda na kashe macijine bansare kansa ba,barin xahrau gidanmu shine babban tashin hankalin da yanzun yake Shirin tunkaroni....hanya Mafi sauki itace yadda zaayi in kauda Fatima daga wannan masarautar idan ba hakaba yarinyar Nan sai ta kaskantar Dani ta wulakantani a idon duniya"..

Gauron numfashi rahina ta sauke dik a firgice take "wallahi hajiya tun ranan Dana fara ganin shegiyar yarinyar Nan fuskarta keyimun Kama da uwarta Dan Babu inda tabar mahaifiyarta sakkk Abu daya ya banbantasu mahaifiyarta tanada Dan fadin fuska kadan ita Kuma doguwar fuska gareta,ni a ganina hajiya musawa yarinyar Nan Ido tayi dik haukar da zatayi"...

"Bazansa Mata Ido ta wulakantani ba cikin wanan masarautar inda nake abinda nakeso nake juya Wanda na gadama"...

A gadarance Fatima ta shigo sashin ta tsaya a kansu duka ta rike kwankwasonta hade da kauda kanta gefe "naji Dadi da yakasance diyar da ake Kira shegiya itace Yar asalin sarauta ba wadda take ikirari da ita din Yar asali bace,.... deejahmah kenan ya kikaga abinda ya faru?Ashe Aron mulki kikayi ba naki bane tunda ubanki be gaji mulki ko sarauta ba,uwarki itace Yar sarki tayi karfa karfar da Saida aka mallakawq ubanki galadiman garin Nan to ki tabbatar indai inada Rai sai nayi sanadiyyar da aka sauke galadima"

Mikewa Deejahmah tayi tana Shirin. Wankawa Fatima Mari ta rike hannunta Tana sakin murmushi "fuskar sarauniya tafi karfin Mari a yanzun....idan kikayi gigin Marina wallahi tallahi saina shayar dake mamakin da baki taba tunani ba....albishir nazo muku dashi na sarki yaji labarin *ANYI WALK'IYA* a masarautar sa sirrin dake boye cikin duhu hasken walkiya ya bayyanashi a Fili....zaku iya zuwa ku amsa Kiran Mai martaba"....Tana gama fadin hakan ta juya abinta suka bita da kallo,

Kukan takaici deejahmah ta rushe dashi "nashiga uku na lalace meke Shirin faruwa Dani?meyasa wadanan mugayen abubuwan suke samuna ta ko wani bangare?yanzun Ashe dama Fatima kanwatace nake kishi da ita?"

Dafata rahina tayi wadda take cike da furgicin halin da suke ciki da irin tunanin hukuncin da Mai martaba zai yanke musu....

Dakyar hajiya babba ta yunkura ta Mike ta janyo gyalen ta ta yafa "muje fadar sarki"

Idanuwan rahina ne kawai suke yawo ta ko Ina a cikin fadar lokacin da suka shigo ta tararda fuskoki dayawa cikin fadar ciki kuwa harda mijinta galadima....waziri da iyalensa kaff sun hallara...dik wani Mai ruwa da tsaki a wanan masarautar ya hallara saboda yadda Kiran sarki yake yawo a ko Ina na masu ruwa da tsaki a sarautar...

Dakyar rahina ke taka kafafuwanta wadanda suka kasa daukarta saboda furgici ta nemi gefen hajiya babba ta zauna.....

.

*Muje zuwa*

*SLIMZY😍*
[8/31, 19:38] 🥰slimzy🥰: 🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

*NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

_Sakon gaisuwa da fatan alheri a gareku_ *FARIDA KAKANGI,ASMAU IBRAHIM* *BELLO(MA'U),AISHA USMAN(DADA),FAEEZAH* *ISYAKU(FA'EEH)...* __son so fisabilillahi_💙💜
_
46

Gyaran murya Mai martaba yayi hannunsa rike da hoton da yarima ya gabatar Masa ya dago kansa ya dubi kowa dake cikin fadar Sanan ya maida dubansa ga hoton dake hannunsa lokaci daya ya sauke ajiyar zuciya Sanan ya fara magana a nutse,

"Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wataala da ya bayyanar Mana da wani bakon al"amari Wanda bamusan dashi ba tun bayan shekaru da suka gabata,watakila ma mun cire Rai da cewa wata Rana wani bakon al'amari zai faru,hakika kabiru ya gabatarmun da wani hoto dazun dazun da wasu bayanai dangane da hoton da Kuma wani rubutu a bayan hoton dikda bamu da tabbas Akan hakan"

Murmushi hajiya babba tayi tana kada kai,

"Saidai dik wani Mai hankali Wanda yasan marigayi abdallah yasan zahrau to tabbas wanan yarinya batada banbaci da iyayenta ko wajen kamanni,...na Dade Ina zargin wani Abu dangane da Fatima tun ranan da Allah ya jehota gidan Nan nagasa samun natsuwata narasa hankalina saboda tsananin Kama da itakeyi da ubanta ta wani bangare Kuma jini Yana nuna kamaninta da uwarta Dan haka yanzun da kabiru ya gabatar mun da abinda ya faru ban tsaya wani waswasiba na yanke shawara Akan Fatima diyar abdallah ce marigayi"
Chapter 70 · 0% Book details