← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 80

Sashe 35

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta kalli yarima zuwa wanan lokacin idanuwanta sun Gama rufewa wani masifar kishi ne ya taso Mata Domin tasan wadda yake nufi ba wata bace face shegiyar yarinyar Nan Mai kamada mayu ,takaicine ya lullubeta Amma saita dake "ya Zama wajibi a gareta da ta koyi sallama kodan kasancewarta kuyanga baiwa kaskantacciya sanan tsintacciya,matukar Bata koyi sallama ba to tabbas tasan zaayi Mata horo Mai tsanani so saboda haka inaso in fada maka da kadaina hadani da ita da take baiwa a wajenka da ni da nake a matsayin matarka"

Ba karamin batawa yarima Rai kalaman deejahmah sukayiba Domin a duniyarsa Babu abinda ya Tsana ji fiye da Kiran Fatima kaskantacciya tsintacciya hakan na Sosa Masa Rai Domin shi kallonta yakeyi kamar kowa,idanuwansa sun canja kala zuwa launin ja Domin tunda yake Babu yarinyar da ya taba zuwa wajenta da sunan zance balle ta rainasa ta fada Masa maganganu,haushi da takaicin kansa ya kamasa meye ma dalilinsa na amsa zuwa wajenta ?danne zuciyarsa dake tafarfasa yayi yace "matukar Ina numfashi bazan taba daina hadaki da Fatima ba Domin keda Fatima matsayinku daya a wajena"......

A fusace deejahmah ta Mike tsaye ta rike kunta kadan ta juya Masa baya "kadaina mafarkin cewa matsayinmu guda da ita Domin ni matarka ce ita Kuma baiwarka ce wadda Nan gaba kadan zata Zama baiwata"

"Yadda kike tunanin ke matatace to itama Fatima haka nakeyi Mata burin ta kasance daya daga cikin matana,idan baki sani ba kisani yau din Nan nakai maganar neman auren Fatima gaban Mai martaba"

Da sauri deejahmah ta juyo ta kafesa da ido,

Shima kallonta yakeyi Ido cikin ido take ya hango tsananin bacin Rai da tashin hankali hade da kishi cikin idanuwanta,murmushin mugunta yayi Mata Dan ya rigada ya Rama rashin kunyar da tayi Masa,

Gira daya ya daga Mata da Dan murmushi dauke a fuskarsa yace "ki kwantar da hankalinki kece zakije a uwar gida ita Kuma amarya sanan saiki shirya yadda Zaki zauna Dani a matsayin mijinki yadda Zaki kwatarwa kanki yanci a wajena ki koyi ladabi da biyayya da iya kalamai masu dadi uwa uba tarbiyya"

Hawayen bakin cikine suka fara sulalowa a idanuwan deejahmah wadda ke tsaye idonta cikin nasa tamkar an dasata,tsananin takaici yasa ta zubar hawayen da Bata shiryaba,Rabon da tayi kukan bakin ciki tun mutuwar habib yau gashi yarima yazo har gida ya ci Mata zarafi ya wulakantata,Babu wani namijin daya taba yi Mata wanan tozarcin sai shi,

Murmushi yayi hade da takowa har gabanta Yana Kare Mata kallo fuskarsa har yanzun dauke da murmushin mugunta,....hannu yasa a aljihunsa ya Ciro farin kyalle Mai kamshi ya Mika Mata "amshi ki goge hawayenki sarauniya"ya kashe Mata ido ,

Juyar da kanta gefe tayi batare da ta kallesaba ta fara takawa a hankali ta nufi kofar fita,har ta Kai kofa ta tsinkayo muryarsa Yana fadin "ga kudin zancenan na ajiye miki da Wanda Zaki siya kyallen da Zaki share hawayen da nasaki,Ina Mai gargadinki Nan gaba sai kisan irin kalaman da Zaki furtamun Domin idan baki yasan abinda zai fada baisan amsar da aka tanadar masaba sai ki koyi kalami masu dadi,ki mikamun gaisuwa ga uwata"....

Tsaye tayi a wajen a daskare Tana sauraron maganganun da yake jifanta dasu a tsanake cike da kasaita da gadara yake jifanta dasu da muryarsa Mai matukar dadin saurare.....

Juyawa yayi ya ficewarsa ta kofar da ya shigo karar sautin futarsa taji ta waigo da sauri ta kalli kofar,durkushewa tayi a wajen Tana kukan bakin ciki ta dau kimanin minti talatin sanan ta Mike ta fice a guje ta nufi dakin mahaifiyarta.....

Kuka takeyi harda shassheka a jikin mamanta,a kidime take tambayarta da "lafiya?me akayi Miki?waya tabaki?meyafaru?"....lokaci daya take jero Mata wadanan tambayoyin hannunta daysma rungume da deejahmah dake rizgar kuka,...cikin kuka take fadin "wallahi bazan yardaba bazan taba amincewa da maganganun da Yaya yarima ya fadamun na cewa Wai bayan ya aureni zai auri Fatima a matsayin Mata ta biyu"....da sauri gwaggo rahi ta ture deejahmah a Kan gado ta Mike tsaye "mekike fada?kinada hankali kuwa?kodai mafarki kikeyi?"

Mikewa deejahmah tayi zaune Tana hawaye ta kwashe dik yadda sukayi da yareema daga farko har karshe da cin zarafin da yayi Mata ta fadawa mahaifiyarta"

"Karya yakeyi wallahi,karyane be isaba wallahi yayi kadan yace zai hadaki kishi da kuyangarki baiwarki sanan shegiya Mara uba a matsayinki na sarauniya wadda aka haifeki a mulki kika tashi a mulki Yar asali Yar dangi wanan maganar shirmece,bazan taba yardaba idan kuwa haka ne to ya daukowa yarinyar balai ya jefata cikin masifa Dan saina tabbatar da na halakata ko insa a batar da ita"

Cikin kuka deejahmah ke fadin "mama ki taimakeni yarima yanaso ya kaskantar Dani a wanan masarautar yanaso inzama abin kwatance a sauran masaratu wadda ke kishi da kuyanga baiwa"ta rushe da kuka....

Zama gwaggo rahi tayi hade da janyo deejahma jikinta ta rungume Tana bubbuga bayanta"ki kwantar da hankalinki lokaci yayi da zaayi yakin da baa tabayinsa ba a wanan masarautar Babu Wanda ya Isa yasamun gudan jinina kuka da hawaye a matsayinki na Yar gata gaba da baya gobe zanje gidan zan samu Mai martaba da maganar "

Kara shigewa jikin mahaifiyarta tayi Tana ajiyar zuciya.....

**********
Hankalinsa kwance ya shigo cikin gidan direct babban parkor ya shiga a Nan ya tarar da Fatima durkushe a gaban hajiya babba idanuwanta sunyi jajir fuskarta ta kumbura da alama Tasha mari....hawayene kawai yake gudu a idanuwanta kanta a kasa....

Jikinsa har rawa yakeyi ya karaso wajen ya kalleta ya kalli hajiya ya rasa inda zaisa kansa har ya karasa takowa wajen,

Ganinsa yasa hajiya sa kafa ta hambare Fatima da sauri ya Mike zai riketa "idan ka taba ta sainayi mummunan Bata maka Rai kabiru maciya Amana wallahi munsa kafar Wando daya daku ku duka Kai banida hurumin da zan azabtar dakai Amma ita inada shi Domin baiwata ce sai yadda nayi da ita kayi kuskure daka bayyana asirinku da wuri ka gasgata zarginku da nakeyi sanan nakara gasgata labaran da nake samu game daku wannan dukan da nayi Mata somin tabi kenan azaba ita zatasa tabar gidan Nan da kafafuwanta kafin insa a hallakata....

Bilkisu dake rabe a gefe minti minti take kauda fuskarta ta share kwallar dake zubowa a idanuwanta na tausayin Yar uwarta Tana gani tun dawowar hajiya babba daga fada ake azabtar da ita kala Kala duka dai ta Shashi kamar jaka hajiya babba ta bugeta tasa an bugeta dik Dan yarima ya fadi zai aureta,...haushi yasa bilkisu furtawa a cikin ranta "insha Allahu sai ya auri Fatima saidai ku mutu".....

Takaicine yasa yarima barin wajen ya nufi sasansa cike da bacin Rai Yana zuwa ya cire kayan jikinsa ya zura jallabiya ,bayan minti talatin ya fito sashin hajiya babba ya shiga babu kowa a parlornta sai bilkisu da alama hajiya ta shiga bedroom don dare yayi hannu yasa ya yafito bilkisu yayi Mata alama da tazo ya juya abinsa ,

Gudun bacin Rai yasa bilkisu kwankwasa kofar hajiya,daga ciki ta amsa Mata da "lafiya?menene?"

"Nice bilki ranki ya dade yarima ne ya nemi da in Kai Masa abinci bangaren sa ingyara masa shine nace Bari infadawa uwargijiyata"

Murmushi hajiya babba tayi daga kwancen da take tanajin dadin girmamawar da bilkisu keyi Mata tace"Zaki iya zuwa ki rufomin kofa"

"Nagode ranki ya dade".. daga waje ta watsawa kofar harara ta rufo kofar parlorn dama neman hanyar fita takeyi,

******
Sasan yarima ta buga daga ciki ya amsa Mata ya Bata umarnin shigowa ,Yana zaune a kujera ya Dora kafarsa daya Akan centre table din dakin idanuwansa a lumshe,...zubewa tayi akasa tace'gani ranka ya dade"

"Jeki tahomin da Fatima"

Dan jimm kadan tayi sanan ta bashi amsada "hajiya tasata aiki yanzun hakan Tana can kofar baya"

Dakawa bilkisu tsawa yayi cikin bacin Rai "nace ki kiramun ita ko?aikin hajiya yafi kirana ne?"

A tsorace ta girgiza Kai "ah ah ranka ya dade tuba nakeyi"

Ficewa tayi hade da rufo kofar.....

Can tasamu Fatima Tana famar aikin dibar Kaya masu uban nauyi Tana shigar dasu store na cikin gidan kayanda dogarawa ke shigar dasu karfafa Amma yau da kanta take Diba Tana shigarwa dasu Tana numfarfashi hawaye dik ya bushe a idanuwanta....bilkisu ta Dade a bayanta tsaye Tana kallonta cike da tausayawa dakyar ta bude baki tace"Fatima kizo bangaren yarima yanason magana dake"

"Kije kice bazanzoba"

"A dalilin me?"

"Saboda shine silar jefani cikin wanan masifar na fada masa kada ya fadawa sarki zai aureni ya kafe sai ya fada ga balain daya jamun Nan idan suka kasheni ya huta"

"Karkice haka Fatima ko yarima be fadawa sarki ba haka Allah ya rubuto zai faru dake banaso azabarsu tasa ki canja Masa ko kice Zaki tsanesa Dan shi ya janyo Miki aisu haka sukeso ni Kuma banaso ki sakar musu wanan wasan ya zamana kin rike wuta kina kyautata Masa Kuna soyayyarku hakan shi zai Kara bakanta ran makiyanki,Dan Allah kizo muje karkice bazakiba"

Murmushi kawai Fatima tayi Wanda a iya fuskarta ya tsaya tabi bayan bilkisu har bangarensa,da sallamarsu suka shiga dukkansu suka durkusa,

Kallon bilkisu yayi "bamu guri"...da sauri ta Mike ta rufo musu kofa....

Ruwa da towel din dake gabansa ya janyo ya Dora Akan centre table ya kalli inda Fatima ke durkushe a rabe ya girgiza Kai sanan yadan sassauta murya "taho Nan"

Ko motsawa batayiba balle yasa ran zatazo,Kara shegewa jikin kujerar tayi ,

Tasowa yayi da kansa ya dagata cak ya dauketa yayi Jan kujerar dayake zaune dazun ya zauna ya dorata Kan cinyarsa ya rike hannunwanta biyu da hannunsa daya sanan yasa dayan Yana juko towel din Yana matsewa Yana shafa Mata a fuska Yana gargasa ida ya kumbura da ida jini ya kwanta a fuskarta,...haushi ne ya cikata batace masa komiba sai faman tura Baki takeyi Tana yatsina fuska Dan tanajin zafi,har ya Gama ya janye robar gefe hannunsa na rike da ita Akan cinyarsa,

"Dan Allah kabari nidai kasakeni sai an samemu a haka ka Kara jamun ko?"idanuwanta suka kawo ruwa..

Kara rungumeta yayi zuciyarsa na bugawa sauri da sauri ita kanta zuciyarta bugawa takeyi Amma saita Samu kanta da kwantar da kanta a kafadarsa Tana hawaye,
Chapter 35 · 0% Book details