← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 80

Sashe 23

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Fatima ta dafe kirji ta zaro idanuwa waje Tana girgiza Kai take fadin"Aysha kiyi shiru kada kiyi zunubi Domin wanan maganar da kike fada saidai a mafarki Dan abune da bazai taba yuwuwa ba ki dubani fa kiga koni wacece sanan ki tunada yadda yarima yake ni tunda mukema bai taba furtamun kalmar so ba nadaisan Yana tsananin tausayina"

Hmmmm"Fatima kenan wallahi Yaya sonki yakeyi,koya fada miki Kobe fada mikiba sanan yayi hakan ne don yasamu damar aurenki"

Jijjiga Kai Fatima keyi zuciyarta nayi mata zafi tace"Aysha ko giyar wake yarima yasha bazai taba aurenaba iyayensa da danginsa bazasu bariba sanan yarima yafi karfina ni wacece?waye gareni a duniyar Nan sai Allah mahaliccina"

"Kuma Allah da kike dashi Fatima shike azurta bawansa a dik lokacin daya gadama saboda haka banaso kicire Rai daga rahmar Allah"

"Mubar maganar Nan Aysha"....

Dik maganar da sukeyi Ablah Tana tsaye a jikin kofa ta harde hannayenta a kirjinta Tana kallonsu musamman Fatima dake magana cikin karayar zuciya....gyaran murya Ablah tayi musu dukkansu suka juyo da sauri suka dubeta,...lallausan murmushi ta sauke sanan tace"hirar ta Isa azo muje a shiga kitchen muyi abincin Rana yanzun haka har azahar tayi"

"Toh Ablah"dukansu suka hada baki suka Mike a tare ita tayi gaba suka bita a baya don shiga kitchen...

*******
Bayan sallahr laasar tawagar gidansu gwaggo rahi data gidan waziri suka shigo gidan sarki Domin yiwa sarki barka da dawowa daga Yar tafiyar da yayi,....

Gida cike yake makil da jamaa ko Ina yarane samari da Yan Mata na masarautar wasu na Hira wasu na ciye ciye bayan ko wannensu ya je ya kaiwa sarki gaisuwa....

Dik suka dawo babban parlor na gidan suna zaune suna Hira sama sama ko wacce da abokiyar hirarta yayinda deejahmah ta koma gefe can ta kishingida da kilisa Tana daddana waya bakinta na taunar chewing gum a yangance fuskar Nan ta dau kwalliya....

Yarima ne ya fito daga bangarensa wanan karon yayi wanka ya canja Kaya zuwa wasu Riga da wandon na jamfa masu kwalliya kakarsu daban jajaye ,kansa sanye da hula baka tayi Masa kyau sosai fuskarnan babu walwala sosai ya fito ya bullo ta kofar baya wadda zata sadashi da main parlor na gidan ,kamshin turarensa shi ya fara karade parloyn gidan dukkann Yan matan dake parlorn saida suka waiga don ganin Wanda zai shigo Banda deejahma dake taunar chewing gum bakinta Yana kass kass a hankali....sallama yayi musu a ciki ya shigo parlorn dukkansu suka hada baki wajen gaisheshi hannu kawai ya daga musu har ya wuce ya dawo ya daura fuskarsa yace"Ina fatan dukkanku kunyi sallahr laasar"...mikewa suka shigayi daidai da daidai suna ficewa ,deejahmah ko dake kishingide zuciyarta nayi Mata bugu sauri da sauri tunda yarima ya shigo ta tsinci kanta a wanan yanayin Amma hakan besa ta daga Kai ta kallesaba,dago idonta tayi ta saci kallonsa sai ta ganshi a tsaye da sauri ta sauke kanta kasa Tana daddana wayarta,

Dan waigowa yayi ya kalli inda take ya kauda Kai cikin wata iriyar murya yace"kefa bakiji abinda nafadawa sauranba kenan"

Yatsuna fuska tayi ta dago daradaran idanuwanta ta saukesu akansa tace"banayi Ina hutu"....

Dan taking ya saki sanan ya fice a dakin tabi bayansa da kallo hade da tabe baki....

**********

Gwaggo rahi ce durkushe a gaban Mai martaba suna Kara gaisawa yayinda hajiya babba data kasance itace da girki a wanan Rana Tana gefen Mai martaba,bayan sun Dan taba Hira da Mai martaba gwaggo rahi tayi Masa sallama ta fice a fadar ya rage daga hajiya babba sai Mai martaba,

Shirune ya biyo baya na minti goma sanan hajiya babba tadan durkusar dakai kasa tace"Allah yaja da ran Mai martaba akwai maganar da nakeso mutattauna"

Jinjina Kai sarki yayi yace"Ina sauraronki"

"Nagode ranka ya dade,....dama wata maganace nakeso mu tattauna Kuma shawarace nake ganin ta Dace"

"Ina sauraronki"

"Dama a game da yaran Nan ne kabir da Khadija Yar wajen rahina wadda akayiwa marigayi habibu baiko da ita shine a ganina tunda haka takasance Kuma yarinyar batada manema dikta sallami kowa shine nace zan shawarceka Mai zai Hana kabiru ya maye gurbin Dan uwansa hakan shi zai cirewa yarinyar radadin rashin tsohon mijin nata"

Shiru sarki yayi na wani lokaci Yana jinjina lamarin sanan yayi gyaran murya yace"wanan shawarar taking tayi"...washe baki hajiya babba tayi,sarki ya cigaba da magana"amma kina ganin hakan baa shiga hakkin ita yarinyar ba?"

Kara durkusawa tayi cike da ladabi tace"ranka ya dade Khadija batada wani zabi daya wuce zabinmu kafin in zanta dakai saida nafara tuntubar yarinyar batare da kowa yasaniba Kuma ta amince da hakan"

"To alhamdulillah naji dadin wanan shawarar Kuma tayi sanan shi kabirun zaizo ya sameni zan sanar Masa da hukuncin da muka yanke"

Wani dadine ya lullube hajiya babba tamkar ta Mike ta taka rawa kudurinta ya cika saura na biyu na Hana Fatima zaman gidan sarauta....

"Assalamu alaikum"yarima yayi sallama cikin fadar shine ya katse hajiya babba daga tunanin data fada.....

Takowa yayi cike da ladabi ya karaso Kan babbar daddumar dake cikin fadar ya nemi gefe ya zauna ya sunkuyar dakai hade da Mika gaisuwa wajen Mai martaba da hajiya babba,....cike da kulawa Mai martaba ya amsawa Dan nasa Banda hajiya babba dake gefe Tana jifansa da mugun kallo na tsantsar tsana da kiyayya....

Sarkine yayi gyaran murya yace"Dan halak yanzun muke maganarka da mamanka sai gaka ka shigo"...dammmm gaba yarima ya yanke ya fadi Nan da Nan zuciyarsa ta shiga yi Masa bugu Amma sai ya daure yayi murmushi kawai....

Sarki ya cigaba da magana cike da Kamala "mamanka ta gabatarmunda wata shawara data yanke gameda maida neman auran Dan uwanka akanka Wanda dama ko aurenta yayi ya mutu kanada damar da zaka kula da iyalinsa da yaransa balle Allah be kaddaro hakanba saboda haka mamanka ta kawomin shawarar hakan ni Kuma Naga dacewar hakan me magani"

Jikin yarima rawa kawai yakeyi yayinda ilahirin network din jikinsa gaba daya ya dauke zuface kawai ke tsattsafowa a goshinsa dakyar ya iya motsa bakinsa yace"banida wani iko da zanja dashi Akan hukuncin iyayena dik hukuncin da suka yanke akaina daidaine,yanzun haka tafe nake da tawa bukatar zuwa gareka mahaifina"

"Alhamdulillah Allah yayi maka albarka ka cika Dan halak wanan ya nuna lallai kaidin kaunar da kakewa Dan uwan naka ta hakikace,mecece taka bukatar Dana Fadi ko meye inhar inada halinta to zan biya maka ita"

Gyara Zama yarima yayi yace"Ina neman agajin sarki Akan ya duba lamarin wanan marainiyar Allah wadda kaddarar kisan Dan uwana ya fado a hannunta bada niyyartaba inaso sarki Mai adalci Akan talakawansa ya duba lamarin yarinyar Nan rukonta ya dawo hannun wanan masarauta Mai cike da adalci"

Wani mugun kallo hajiya babba ta wurgawa yareema sanan tace"ka canja bukatarka yarima Dan sarki wanan bukatar bame yuwuwa bace Dan bakada kwakkwaran dalili sanan babu yadda zaayi yarinya tayiwa Dan sarki kisan gilla a daukota a kawota masarauta a ajiyeta ni mahaifiyar marigayin Ina gani baayimun adalciba"

Gyaran murya sarki yayi hajiya babba tayi shiru,

"Yarima meye hujjarka da dalilinka nason rukon yarinya yadawo hannun masarauta?"

Gyara Zama yarima yayi yakara gurfanawa dakyau a gaban sarki yace"yin hakan zai kauda zargin mutane Akan labarin da sukaji na Dan sarki na neman yin lalata da yarda batada galihu,sanan yin hakan zai karawa masarautarmu kima da mutunci da daraja a idon duniya Kuma yin hakan zai daukaka masarautarmu Akan ko wace masarauta,duniya zataga munyiwa yarinyar adalci da muka daukota muka kawota cikinmu Don muyi Mata rukon gaskiya da Amana ranka ya dade"

Jinjina Kai kawai sarki keyi cike da gamsuwa da kalaman yarima "tabbas kabiru wanan tunanine Mai kyau kayi Kuma na karbi bukatarka na yarda na amince kaje ka dauko wanan marainiyar Allah ka kawota cikinmu mu riketa har muddin rayuwar mu......

Murmushi kawai yarima keyi na tsantsar farin ciki lokaci daya ya mance da din wani bakin ciki daya tsinci kansa Yan dakiku da suka gabata....

Durkusawa yakarayi yace"nagode ranka ya dade Allah ya Kara lafiya da nisan kwana, nagode ranka ya dade zan iya tafiya?"

Daga Masa Kai yayi sanan ya Mike har ya Kai kofa Mai martaba ya tsaidashi ta hanyar cewa "ka kirawo Khadija "...Dan durkusawa yayi yace"to ranka ya dade".....

Hajiya babba kuwa Tana zaune tamkar gunki babu yadda zatayi tai bori a gaban sarki tasan hakinsa tasan yadda yakeson Kabir yakejin maganarsa tun kafin habib ya rasu a cewarsa yafi kowa hankali....lallai Kabir ya dauko ruwan dafa kansa da kansa ya dibi rushin wuta ya zuba a bakinsa saiyayi danasanin zuwansa duniya....

Yarima jikinsa har tsuma yake Yana fita yayi dialing number barrister Abdul....ringing biyu ya dauka yace"ranka ya dade"

Murmushi yarima yayi yace"tare da naka kana gida ne?"

"Ehh ganinan da iyalaina inbawa Fatima wayar ne?"

"Ehh"....

Barrister Abdul ya mikawa Fatima waya hannu na rawa ta karba ta Kara a kunne tace"assalamu alaikum"....

"Waalaikumussalam ki shirya ganinan zuwa indaukoki sarki yace inzo intafi dake"

Batasan lokacinda ta sumbular da wayarba a carpet ta Mike a guje tayi cikin daki Tana sakin kuka Mai karfi.....a guje Ablah tabi bayanta...

*Muje zuwa*.... *Nima sauri nakeyi muna shirye shiryen birthday party na beloved mommah (Billy Galadanci)a can masarautar hankaka zaayi celebrating inda takawa yadau nauyin komi da* *komi shida meenal😍lol...(Happy birthday onece again *)**...... *Allah* *yasadai madam season seven tayi* *Mana cake kada TAFARU TAKARE MANA😆*

*SLIMZY😍✍🏼*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

19

Lokacinda yarima ya Isa babban parlor inda dik Yan matan suke,ya tararda gwaggon sa rahi tsaye Tana magana da su deejahma Akan suyi haramar tafiya gida motocin daukarsu dunzo,

Sallama yayi ganin kanwar mahaifiyarsa ya tsugunna har kasa ya gaisheta,a dakile ta amsa ta kauda Kai gefe sanan ya Mike tsaye ya kalli inda deejahmah ke ciccin magani yace"kije Mai martaba na kiranki"...

Da sauri dukkansu suka juyo suna kallonsa cike da mamaki hada girar sama da kasa yayi ya juya zai wuce gwaggo rahi ta dakatar dashi da cewa"ai saika jirata kujera tare koh"
Chapter 23 · 0% Book details