← Book details Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 80

Sashe 31

Anyi Walkiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaki Gane Nan gaba kadan....Dan bakaramin shiri nakeyiba akanki matukar yarima ya aureki to shida wata mace saidai kallo"

Dadine ya cikata tace"da zarar nasamu ciki na haihu ,zan cika borina akansa"

Murmushin mugunta gwaggo rahi tayi tace "hakan nada kyau....mahaifinki nake jira ya dawo ya samu sarki Akan a matso da bikinki Nanda wata daya"

"Yauwa mama Dan na kagara in shiga gidan in baza makaman yakina"

Murmushi gwaggo rahi tayi tace"hakan nada kyau"....

*********
"Faizah ni bana yaki saina shirya sanan ta karkashin kasa nake cizona Domin ni macijin kaikayi ce"

Faizah da fauziyya suka jinjina Kai suna kallon innarsu dake wanna maganar wadda ita kadai tasan maanarta Dan Basu fahimceta ba....

"Bokana ya fadamun cewa Babu makawa sai yarima ya auri Fatima.....komi Daren dadewa"

Da sauri fauziyya ta dafe kirji "wace fatimar tsintacciyar mage"

Gyada Mata Kai matar waziri tayi tace "ita fa sanan dik Shirin da rahina keyi insane dashi Domin karkuzu ya sanarmun da komi,....Nima nayi nawa Shirin Dani dasu zamu zuba mugani...".....

*******
Kasa bacci Fatima tayi cikin dare sai juyi takeyi dago kanta tayi ta kalli sauran kuyangin dake kwakkwace suna sharbar baccinsu hankali kwance,....data rufe ido Babu Wanda take gani sai yarima tunaninsa ya dabaibayeta zuciyarta na harbawa dik lokacinda ta tuna dashi wani irin so da kaunarsa ke ratsa sassan jikinta,...runtse idanuwanta tayi ta budesu hawaye ya shiga gangarowa daga idanuwanta wanan wani irin balai ne zuciyarta ke Shirin jefata ciki?tabbas son yarima takeyi Amma tasan harabada kasancewa dashi saidai a cikin mafarki......kuka ta fashe dashi Mai ban tausayi Tana juyi a kasa ga sanyi Yana kadata ta ko Ina.....bacci ya gagareta kanta ne ya shigayi Sara Mata tamkar zai rabe biyu....

Bangaren yareemah shima hakan ne kaiwa da komowa kawai yakeyi daga parlornsa zuwa bedroom bacci ya gagaresa Fatima kawai yake bukatar gani Fatima kawai yake bukatar kasancewa da ita.....idanuwansa sun kankance bacci ya kaurace musu hannu yasa ya dafe kansa ya jingine da jikin bango hade da runtse idanuwansa,....kamar daga sama yaji Ana buga Masa kofa Dan bude idonsa yayi ya Kara saurare bugun kofane,daga kansa yayi ya kalli agogo Sha biyu na dare....to waye ke buga Masa kofa?...

*Muje zuwa*

*Zanje hutu da typing din nan☹*

*SLIMZY😍✍🏼*🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

23

Da sauri ya bude kofar shiru sai hasken pitilu da hasken farin wata,....mamakine da al'ajabi ya rufesa tabbas yaji bugun kofar daki Amma ya fito bega kowa ba to waye?.....kodai tunanin da yakeyi ne zuciyarsa keyi Masa gizo Akan bugun kofa?ajiyar zuciya ya sauke ya koma ciki maimakon ya kwanta sai ya dauro alwala ya fara sallah.....

Biyu saura na dare bilkisu ta Mike ta shiga waige waige ganin dik bayin dake cikin gidan wadanda ke kwana daki daya sunyi bacci ita sai juye juye takeyi tanaso su kebe suyi maganar sirri da Fatima,....saye ta Mike cikin sand'a ta lallaba ta fice shiru cikin gidan ta zagayo ta kofar dakin da su Fatima ke kwana,tura kofar tayi cikin saa ta tarar da ita a bude,

Zaune ta tarar da Fatima ta runtse idanuwanta kanta jingine da bango,Jin motsin shigowa yasa Fatima bude ido da sauri sukai Ido hudu da bilkisu wadda ke zare Ido cikin duhu...

Hannu tasa ta ya fitota suka fita a tare ba tare da kowa ya gansuba ko tsoron duhun dare basayi wani kebabben waje suka samu Mai wadatar Haske suka zauna,

Tagumi Fatima ta rafka idanuwanta sun kada sunyi jajir,....shirune ya biyo baya sanan bilkisu ta dafe kafadarta cikin kasa kasa da murya ta Soma magana,

"Wai nikam Fatima meya hanaki bacci na tarar dake a zaune?"

Harararta Fatima tayi ta gefe "ke meya hanaki bacci?"

"Malama so nakeyi muyi magana don nasan ba lallai bane da Rana musamu halin kebewa mu zanta shiyasa nakeso inyi Miki wasu tambayoyi game da gidan Nan"

"Umhmm Ina sauraronki"

"Wai shin wani irin Zama kikeyi a cikin gidan Nan faty?Wai Kinga yadda kika rame kika lalace kuwa?ko mu da muke zaman ukubar gidan marayu munfiki kyan gani sanan abun mamaki ma Wai aka daukoki aka kawonan gidan a matsayin kuyanga Fatima banji dadin wanan lamariba"

Hawayen da Fatima ke boyewa su suka sulalo Mata a kumatunta tasa bayan hannu ta share "bilkisu to kina tsammanin dama ki ganni cikin gata ne?bayan kin manta ni babbar Mai laifice a wajen wadanan mutanen?sanan kin manta da matsayina na rashin gata da galihu banida wani gatan daya wuce Allah da manzonsa sai yarima, ..Mai martaba ma ya nunamin kulawa ranan da aka kawoni,...wanan Hali da kikaga na shiga bai wuce mahaifiyar wadda na kashewa da ba itace ke azabtar Dani dik wata hanya wadda zata muzantani ta wulakantani shi takeyi saboda na fado a marainiya kallon shegiya kowa yakemun"....zuwa wanan lokacin kuka yaci karfin ta,

"Kiyi shiru da wanan kukan yanzun ya kuke ciki keda yarima?kindaisan yareema sonki yakeyi ko?dikda kinfadamun a baya bai taba furta Miki kalmar so ba sai tausayi"

"Bilkisu yareema Yana Sona yanzun abubuwan da yakemun ya wuce tunaninki ma ni tsoro nakeji ranan da zaa kamani nasan shi tashi Mai saukice nice ke cikin bala'i Domin na lahira sai ya fini Jin Dadi,...ai jiya Kinga matar da zai aura"

Tabe baki bilkisu tayi ta harari Fatima "ni matsalata dake rashin jarumta wallahi,yo Dan zai auri waccen sai me?bayan kinsan yadda yake sonki mu shaidane?to Bari kiji sakin jiki zakiyi ku rinka soyayya Dan bazaa barki a baya ba"

Zaro ido Fatima tayi hade da dafa kirji"Kinga bilki bazaki sani a masifa ba na tabbatar da yanzun sai kunfini mutunci a idon mutanen gidan Nan nida nake kamar mujiya"

"Munafuka kinaso kina kaiwa kasuwa yanzun ubanme ya hanaki bacci?kike zaune kina runtse runtsen Ido?inba tunaninshiba ki zauna sonsa ya kasheki"

Kamo hannun bilkisu Fatima tayi muryarta na rawa "wallahi bilkisu Ina Jin wani yanayi game dashi Amma abinda nake tsoro wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa,ni ba Saar auren yarima bace idan zamuyi sara mu rinka duba bakin gatari,Wai kin manta da matsayina ne?ba gidan sarautabana Babu Wanda zaiso ya hada zuri'a da tsintacce Wanda baa San asalinsa ba"

Tureta bilkisu tayi ta Mike tsaye "dalla malama tunda bazakibi shawarata ba ki tsaya dari dari tun Yana sonki Yana kulawa dake ya juya Miki baya sai ciwon so da na zuciya ya kasheki,wallahi keda halinmu daya da bakiyi wani abunba matsoraciya kawai Kinga tafiyata kafin a kamamu a ci ubanmu da safe"

Fuuuuuu bilkisu ta wuce Fatima tabi bayanta da kallo Tana girgiza Kai,bilkisu sarkin fushi da fada abu kadan ke Bata Mata Rai sanan batason rainin wayau ko kadan Dan ko a gidan marayu ma rashin mutunci takeyiwa su hajiya halima dikda ubanta da sukeci.....

Jiki a sanyaye Fatima ta Mike ta juya hanyar dakinsu,tafe take Tana tunani abubuwa dayawa sun taru sun cunkushe Mata a zuciya,....a hankali ta tura kofar dakinsu ta shiga,....tsulum saade wadda tun fitar Fatima ta Mike Tana kallonta Amma tsoron duhu ya hanata bin bayanta taga me tajeyi....kallon kallo akeyi da Fatima da saade wadda ke faman wurgawa Fatima harara "munafuka Ina kikaje?"

Da sauri Fatima tace "fitsari najeyi"

"Karya kike munafukar Allah fitsarin ne kika tafi kusan Awa nawa ai na leka ba hanyar bayi kikaje ba hanyar fita sasan Nan kikayi gobe zakiyiwa hajiya bayani wayasan ubanda kikaje kika shuka shiyasa nifa tun ranan da aka kawoki nakejin tsoronki saboda Jin labarin ke kika kashe yarima habibu"

Kwanciya Fatima tayi batare da tacewa saade uffan ba dik balai da take zazzaga Mata Dan ta Dade da lura da yanayin saade tun ranan da suka fara haduwa ta tsaneta....

Juyi kawai Fatima keyi har asuba Bata runtsa ba Kiran sallar farko ta Mike ta fice a dakin ban daki taje tayi tsarki ta dauro alwala,...Yar barandar data Saba zuwa tayi ibadah yauma can taje ta shimfida dankwalinta ta fara nafilfili sanan ta zauna kafin a Kira sallar asuba tanata Yan adduointa.....

*********

Kaiwa da komowa yakeyi tun safe besa Fatima a idonsa ba dik hankalinsa a tashe yake,

Dik inda yasan zai sameta ya bi ta wajen bai gantaba har ya wuce ta kofar kitchen yaji alamar motsi dawowa yayi ya Dan leka,itace tsaye Tana faman aikin abincin Rana da sauran maaikatan kitchen din.....juyowa lantana tayi sukai Ido hudu dashi zubewa tayi a kasa "barka da warhaka ranka ya dade kanada bukatar wani Abu ne?"

Basarwa yayi har ya juya ya dawo "ke"

Da sauri dukkansu suka juyo Suka zube har Fatima,...."Fatima ki dafomin ruwan zafi ki kawomin bangarena".....bai jira komiba ya juya yayi bangarensa,...jikinta ne ya hau rawa ganin Mami ta bita da wani irin kallo na tuhuma yayinda lantana ta cigaba da ayyukanta,

Ruwan zafi ta dafa ta zuba a flask ta dauko cups da spoons ta Dora Akan farantin Tana sanye da Dan karamin hijabi da take dorawa Akan uniform din nata fari ta fito dik jikinta Babu kuzari har ga Allah bataso haduwa dashi ba Dan haka yau wuni tayi cikin kitchen ko su bilkisu Bata hadu dasu ba,haka Nan ta nufi bangarensa,

Ta Dade tsaye a kofar shiga sashinsa zuciyarta na harbawa sauri da sauri ta rasa dalilin da yasa ta tsinci kanta cikin wannan yanayin kusan minti uku Tana tsaye wajen dik jikinta rawa yakeyi dakyar ta bude baki tayi Masa sallama "assalamu alaikum".....

"Shigo"...kawai ya bada amsa a takaice tasa hannu ta Murda handle din kofar a hankali ta shiga kofar ta rufe Yana zaune Kan kujera ya rafka ta gumi hannu biyu biyu ta shigo hannunta sai rawa yakeyi dakyar ta iya durkusawa ta Dora farantin Akan centre table ta Mike da sauri zata fita,...."da kika ajiyemun waye zai serving Dina?"...mshine tambayar daya jefo Mata....cakk ta tsaya kusan second talatin sanan ta juye ta durkusa ta zuba Masa ruwan zafin ta hada Masa da Yar sugar kadan ta dauko kofin ta dago Kai tace"gashi"

Hannunsa yakai zai amsa ya hade da hannunta Gam,....yakai cup din bakinsa a haka idonsa na kanta,...Dan kurba yayi ya lumshe idanuwansa ya ajiye cup din idanuwansa akanta....."Ina kika shiga dik yau bangankiba hankalina dik ya tashi Fatima?umm?so kikeyi in zauce ko?...idanuwansa akanta yake maganar
Chapter 31 · 0% Book details