Sashe 98
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/14, 19:12] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 86*
Sake kallonta tayi sanda ta miqa mata awarwaraye da suka dace da kayan jikinta. Ta zubawa birra din idanu,haka kawai takejin yau bata yarda da birra ba,haka kawai takejin wani baqon yanayi a tattare da ita.
"Maidasu basai na saka ba"
"Nannie tana dakin hutu tana jiranki" Birra tayi saurin fadi ganin akhnan din ta juya a hankali tana nufar sashen da aka ware mata cikin tafkeken dakin da wasu qawatattun kujeru biyu da mulmulallen table saboda daura tarkacen system dinta da sauransu akai.
Cak ta tsaya ta waiwaya tana duban birra,still taqi bari su hada idanu.
"Tun yaushe kika barta tana jirana?" Ta fadi Kai tsaye. Sosai take ganin girma da kimar Nannie,don soyayyar da Nannie din take nuna mata a bayyane take. Uwa uba daga sultane har mammina tana ganin irin yadda suke girmamata.
Dan sosa kai kadan birra tayi tana kaucewa hada idanu da ita.
"Kafin ki shiga wanka ne......kuma itace tace kije kiyi wankan ai". Idanunta ta maida ta lumshe. Ta manta sai yanzun da birra ke sake gaya mata. Amma haka nan takejin wani faduwar gaba da bata saba da ita ba,ta taka anutse da wannan qasaitartata,ta isa inda takalman da birra ta ajiye mata suke,ta zura dogayen qafafunta da suke subul kamar bata taba taka qasa ba tunda aka haifeta.
Da dan mamaki kadan a ranta sanda take ratsa falukanta ganin hadimanta kusan dukka suna nan. Kamar tun dazun basuyi ayyukansu bane sai yanzun. Kadan kadan take amsa gaisuwarsu,murya can qasa cike da wannan izzar. Tayi wani iri kyau,fuskarta tayi fayau saboda damuwar data shiga kwana biyu. Material din ya karbeta,ya kuma fidda qirarta da kyau. Bata yada mayafin da birra ta miqa mata ba,ganin bawai wani guri zata fita ba,tayi gaba ne tabar birra da mayafin a hannu tana binta dashi.
Tayi wani irin kyau wanda va zaka gaza ganinsa ba koda daga ness ka hangeta. Wani irin sassanyan kyau take dashi,wanda yake iya fusgar hankalin d'iya mace ta maimaita kallonta akan akhnan din ballanta namiji. Qirarta ta fita sosai kamar wadda sam sam.bata cin abinci a rayuwarta. A haka take takawa a nutse zuwa kebantaccen falon nata wanda takeson xama sosai a cikinsa saboda ba abinda ya rabashi da cikin mini garden din datasa aka mata a gefan parlor din sai wata glass door me murfi biyu. Idan tanaso tana budeta,iska me kyau tana shigo mata,sai yanayin yake sake qawata zamanta a gurin.
*_WHEN THE CALL CHANGED HER LIFE_*
Da siririyar sallama a saman siraran labbanta da suke qyalli da hasken lip gloss ta tura qofar falon. Daidai sanda Nannie dake zaune gaban system din da aka aza saman side table din da aka jawoshi gaban three sitter din da take zaune ta zube idanunta akan akhnan dake shigowa.
Wani irin kyau.....wani irin haske da qyalli taga akhnan din tayi mata. Sai take ganin kamar ba akhnan din data gani bace jiya.....kamar wani abu ya sauya tattare da ita. Fuskarta ta nuna GIRMA irin girman dake hawa kan kowacce mace a sa'o'in da aka kammala daura aurenta......gashi yanzu tana ganinsu muraran a fuskar akhnan din,duk da ana kan daura auren ne ba tare da an kammala ba.
Mamaki ne ya darsu akan fuskar akhnan din,ya kuma bayyana kansa da kansa ganin aisa da shehnaz harda falaak a gurin. Gefe daya ga Nannie data dasa system a gabanta abinda bata taba gani ba tattare da Nannie din. Don ita ko waya bata dameta ba,idan kaga waya ta dameta to tabbas dan uwanta sultane ne ya kirata ko ita take nemansa. Daga gefanta kuma yakumbo ce. Yakumbon da take jimawa bata ganta ba saboda shekaru da suka fara ja,saidai kuma dattijuwar a nutse take tsafff.....akwai tarin nutsuwa tattare da ita....hangen nasa da hikima gami da tarin ilimi me yawa a tattare da rayuwarta.
"Yakinan.....qaraso" Yakumbon ta fada tana yafitarta da hannu.
Haka kawai taji gaba daya gwiwoyinta sunyi wani irin sanyi......yadda suka zuba mata idanu a yau sai takejin kamar idanunsu sun mata kwarjini da yawa. Mamakinta ma yadda aisa din tazo amma bata nemeta ba,yaushe ma aisa din tazo?,yaushe ta bar agadez harta dawo ba tare da ita tasan zata shigo ba?. Kodai festival d l'Aïr dinne ya kawota tun yau?.
A hankali take takawa tana maida dubanta ga yakumbo,kafin ta qaraso Nannie tuni ta miqe,ta kuma kamo hannunta har zuwa gaban kujerar da suke kai,har kuma gaban system din da ta zaunar da ita a tsakiyarsu ita da yakumbo.
Sai a sannan idanunta suka sauka kan screen din,fuskar sultane ya bayyana tarwai cikin masallacin madeenar daya bada background me kyau da haske,kaman yadda kowa ya saba ganinsa.
Idanunsa ba screen din yake kalla ba,idanunsa suna gaba da screen dinne,amma zamanta a gurin ya sanya sultane din saka qwayar idanunsa a kanta a nutse,abinda ya sanya taji wani abu ya tsarga mata tun daga saman kanta har qafafunta,kafin ta sakeji ko fuskantar komai ya karkatar da fuskar tablet din zuwa ga inda idanunsa suke.
Daya bayan daya takebin mutanen dake zaune saman lausasan carpet din masallacin da kallo. Daidaiku ta gane,kaman imam dinsu da wazeer. Kanta ya kulle da yanayin data gansu a zaune sunyi da'ira. Zaman kaman na masu daukan karatu,idan kuma ta lura da kyau ma kaman wata tattaunawa sukeyi a tsakaninsu,kafin kuma taga an ajjiye daurin kudi CFA dinsu me yawa da daurin goro da wasu kwalaye data fahimci alawa ce a ciki.
"Me sukeyi ne haka?,me sultane yake nunamin?" Ta tambayi kanta da kanta ba tare data iya fidda tambayar sarari ba saboda yadda taji tana neman shiga rudani.
"Daurin aure ne" Taji zuciyartata tana bata amsa saboda tunawa data tabayi. Cikin wani film data taba gani shehnaz na kalla ta taba ganin irin wannan zaman,don itadin ba ma'abociyar kalle kallen finafinansu na gargajiya bace. Fina finanta dukka basa wuce na fada da gwagwarmayar rayuwa,saina soyayya da takan kalla a sace gudun kada su aisa su sanyata a gaba.
"Ni sarki abubakar al'assad.........na bawa sheikh muhammad haisam ibraheem auren d'iyata khadeeja muhammad hammud.......bisa sadaki na sisin gold dubu d'ari da hamsin,lakadan ba ajalan ba,bisa sharadin ciyarwa tufatarwa da Matsugunni......bisa kuma sunnar annabi muhammad S A W". Yayi maganar cikin girmamawa yana duban bobbo muhammad dawud dake sanye cikin manyan kaya da suka sake kwarxantashi.
"A matsayina na waliyyin muhammad haisam.....na karba masa auren 'yar abokinmu khadeeja,bisa sunnar ma'aiki S A W da kuma yarda da duka sharuddan da addinin musulunci ya tanadar mana".
"Kun amince?" Me martaba sarki abubakar al'assad ya fadi har sau uku,bobbo muhammad dawud yana fadin
"Mun amince mun karba" . Sai sarki abubakar al'assad ya juya zuwa ga sauran dake zaune a guri dama hausawa da mutanen niger da suka marmatso wadanda jin auren diyar sarkin agadez ake daurawa a gurin wanda wasu daga cikin su tuni suka fara nad'ar recording na video don su samu abun dorawa da bada labari.....sai ya dan daga sauti kadan daidai da yadda kowa zaiji yace.
"Jama'a kun shaida?" Har sau uku nan ma kowa yana amsawa da
"Mun shaida"
"Ma sha Allah,salati goma ga annabi". Sarki abubakar al'assad ya furta yana hada hannuwansa guri guda ya fara karanto sigar daurin aure.
*HAISAM*
Baya ya koma a hankali yana jingina bayansa da sofa din da yake kai. Bai taba yarda da gaske aure wani abu ne me girma da nauyi ba sai a yanzu daya tabbatar kammaluwar bayarwa da karbar sadakin da baisanma wanda ya biyashi ba ya gama maida akhnan din sunan MATARSA HALAK MALAK ba sai yanzu. Abinda yakeji a dukka jikinsa dama kansa bai dauka zaiji wani abu me nauyi kwatankwacin wannan ba. Aikin na nasaeeb ne,yana Riyadh gurin wani aiki da aka turashi gurin aikinsu,ya katse dukkan abinda yakeyi yayi tattaki har zuwa madeena,yayi umra kuma yayi joining wadanda suka zauna don shaida daurin auren,takanas kuma ya kirasu sanda yake tare dasu omar.
Su sunsan da kiran.....shine kawai abun yazo masa a bazata.
"Congratulations captain" Ya tsinci muryoyinsu a sanda bai taba zata ba.
Da hanzari ya buden idanunsa,sai suka sauka akan khadeem......mutallab da Amjad. Idanu ya zuba musu,kaman yadda suka zuba masa idanu. Wani murmushi na fita a fuskarsu,wanda a hankali tasa fuskar ta soma washewa da murmushi. Miqewa yayi da wani irin kuzari da zafin naman daya rasa a dazu ya qarasa gaban khadeem yakai masa wani naushi da hannu,sai khadeem din ya tare yana dariya,sai kuma suka cakume juna suna huggin din juna.
"Komai Nisan inda kake obbo....komai nisan tazarar dake tsakaninmu hakan bazain hanamu zuwa a lokaci me muhimmanci irin wannan a rayuwarka ba. Koda ma yaya ne kayi auren nan congratulations.....congratulations once again Capt sheikh" Amjad ya fada yana suna sakin juna shida haisam gami da sake bawa junansu hannu sukayi musabaha me zurfi da kyau.
Yasan wannan aikinsu maleek ne.....yasan sunsan da komai,sun kuma shiryawa komai,gaya masa ne kawai basuyi ba. Zuwan ya masa dadi,bai kuma San yayi kewarsu haka ba saida suka wanzu a gurin,sai kawai ya yanke su wuce zuwa personal home dinsa. Ya waiwaya ya dubi abdii da ya fahimci walwalarsa kawai yakeyi,da gaske farinciki yakeyi da auren ta kowacce fuska.
"Idan ka kammala ka samemu a gida"
"Tom in sha Allah" Ya fada yana hada kayayyakin da haisam din ya sanyashi hadawa.
"Awa biyu ta ishemu,don dole mu dawo muyi sallar juma'a cikin gida" Haisam din ya fadi yana jin wani sassauci cikin ransa.
*AKHNAN*
Yadda dakin yayi shuru haka akhnan ta tsinci wani irin shuru cikin kanta. Shurun data jishi ne kawai bawai don ta gama fahimtar ahinda ma yake shirin faruwa da ita ba. Abu daya ne kawai ya tsorata tunaninta,yake kuma yi mata kai kawo.