← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 101

Sashe 2

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bakka kana bane eenyuuf hin hayyaminaa........Sanduuqa sana irraa fagaachuu hin dagatinaa........Sun lubbuu kee balaaf saaxiluu dagachuu.....Ajaja Mammina ti" Wata irin jarumta yayi gurin riqe kansa,y kuma kame hankalinsa da nutsuwarsa da barin waiwayawa zuwa ga inda maganar take fitowa.

Dukkan wani reaction da zaiyi zai nuna cewa eh yaji yaren oromo......yaji kuma wani abu da yaja hankalinsa,wanda baya fatan hakan ya faru.

Yarensa sirrinsa ne......reaction dinsa akan komai makaminsa ne. Yaren oromo cikakke yakeji......da wasu nauyayan saqo daga bakin bayin nan guda biyu. Dayan ya fahimci fuskarsa TAMIM na farko daya fara gani maqale jikin window din sultane......saidai bai samu nasarar ganin fuskar mutum na biyu ba,don ya bada baya yana kuma bada umarni da zafi zafi da alaman bacin rai akan bude gurin daya fahimci wani store dinne.

"Kada kabar kowa ya sake bude gurinnan......kada ka manta,kayi qoqarin nesanta kanka da akwatinnan.......manta hakan yana daidai da sanya rayuwarka cikin hatsari......umarnin mammina ne wannan" Ya maimaita maganganun cikin kansa yana kuma sake tisasu yadda zasu zauna a gurbin da yake buqatar su zauna din,har yanzu kuma idanunsa suna kallon qasa,saidai idanun hankali dana zuciyarsa suna tare dasu sanda ya sanya hannu yana rufe gurin suka kuma taka suna barin gurin da sautin magana qasa qasa da baya iya jin abinda suke fadi.

Lallai bai shakka gidan sarautar agadez itace TA DAYA da zarginsu zai fada a kai......kuma itace ta farko daya kamata hankalinsu ya koma kai. A yau yaji yaren oromo gaba daya da irin karin harshen da yake tabbatar masa OROMIA ne koma waye yayi wannan maganan,dashi din dame sauraronsa.

Cikin mamaki ta damqe hannuwanta da taji yatsunta sun fara rawa kamar wadanda aka kama ake sarqesu cikin na juna,tadan sunkuyar da kanta tana duban yadda yatsun nata sukaci gaba da motsawa da hanzari hanzari. Mamaki ya kamata tana jin yadda idanunta suka soma mata nauyi,kamar sunkuyar da kan nata data yine bai musu daidai ba suke yunqurin fadowa daga gurbinsu zuwa qasa,wannan ya sanya daga kanta da sauri,a wannan karon kuma ba inda idanun nata suka sauka sai a kanshi.

Bibbiyu bibbiyu idanunta suke gani kafin su fara nuna mata blurry (dishi dishi). Amma duk da hakan idanunta basu gaza sauka sosai kuma fes cikin fuskarsa ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 04*
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Zagayen idanunsa take ta qoqarin tsaida idanunta tare da kwatantasu da wadannan idanuwan.....wannan idanun da suka zame mata barazana a hippodrome......wadannan idanun da suka zama barazana ga zaman lafiyar baccinta.......wadannan idanun da babu wani dare da zai mamaye sararin subhana......ta kwanta da zummar bacci ba tare da sun farmaki baccin nata ba.

Wannan qamshin.......wannan turaren shine abu na biyu daya dinga tasowa tun daga tazarar dake tsakaninsu yana yin kyakkyawar ajiya cikin hancinta. Kaman zata shide saboda yadda takejin qofofin iskarta suna rufewa suna raguwa daya bayan daya,amma hakan bai hanata shaqo qamshin da kyau ba,abinda ya sake dawo mata da hoton hippodrome cikin idanuwanta kenan fes.

Nutsuwarsa dake bayyane muraran saman fuskarsa,da takunsa dake cike da wata ajiyayyar qasaita ne taji yana qona zuciyarta dake wani irin matsewa a qirjinta,kamar ana saka hannu ana barazanar takureta guri daya. A yau gangar jikinta dama zuciyarta gaba daya suna sake bata tabbacin shine.......daidai sanda yake ci gaba da takowa cikin kame ganinsa da kuma shagala da al'amuran da suka shafeshi kadai,da zare kai daga cikin al'amuran da basu kasance damuwarsa bane. Wani irin sanyi taji yana ratsa kowanne sashe na jikinta,amma taqi baiwa hakan hankalinta,tafi tattara hankalinta a kansa. Har yanzu bai dago idanunsa ko sau daya ba ballantana ya kalleta,har yanxu bai dubi sashen da take ba ballanta ta samu nasarar aika masa da saqon data binne cikin idanunta.

Wani irin ninkuwa gudun zuciyarta yayi,abinda ya fara barazanar daukewar numfashinta sanda haisam din yake dab da ita,abinda ya bata daman sake kallon qwayoyin idanunsa......irin kallon da ake kira na tsaf da tsaf......kallon daya tabbatar mata SHINE ABOKIN KARAWARTA NA WANCAN RANA.

KAMANCECENIYAR nada yawa.......hujjojin data tara a kansa sunyi yawan da za'a iya kauce musu,ta lumshe idanunta sanda numfashinta yake yunqurin toshe hanyar da zata samu iskar da zata kaiwa hunhunta.......taji kaman iska ta dauketa tana shirin cilli da ita wani guri na daban,abinda ya tilastata dauke idanunta daga kanshi tana riqe wuyanta da daya hannun,daya hannun kuma ta miqashi da zummar dafa bango,saidai ko kusa da bango batakai ba bare ta samu tallafinsa,sai tayi baya kaman fefan takarda tana shirin zubewa warwas a qasa.

Duk da cewa numfashinta kadan ya ragewa qirjinta amma hakan bai hanata ganin bayyanarsa a gabanta. Kamar walqiyar data gifta cikin sararin samaniya da wani irin hanzari da yanayin gushewar hankalin da take ciki bai hanata fahimtarsa ba ya sanya hannunsa ya tare bayanta,abinda ya hanata kaiwa qasa kenan.

Numfashi ta sake zuqa da wani irin qarfin daya sabbabawa qirjinta dagawa. Fata take ta samu koda qarin mintuna ne da zata tabbatarwa kanta shine yake tallafe da ita......shine yake riqe da ita,kamar dai a wancan lokacin.....
.a wannan filin.......a wannan yanayin da thunder yaso kayar da ita,tana ganin gurin yana ninka duhu a idanunta da ainihin duhun data sanshi dashi,amma still fuskar nan......idanuwan nan masu wani irin kaifi sun juye mata......ranar da lokacin duka a yanzu suna dawo mata kamar yanzu abun ya faru. Hancinta na sheqar qamshinsa fiye da ko yaushe,fiye da yadda ta saba jinsa......da wani irin kusanci,da wani irin taushi,kamar dukka duniya ta tattaru a iya gurinne.

Bakinta da zuciyarta na dauke da maganganu......na dauke da abubuwa da yawan gaske da zataso fada.......zataso tayi abubuwa da yawa a gurin,amma tana jin kamar duniyarta tana qarewa,kamar numfashinta na qarshe take zuqa. Qirjinta na qara matsewa da yadda ta tabbatar cikin hannuwansa take a yanxu haka,kuma batajin zata iyayin komai akan hakan

"Toi encore toi?......pourqoui toujours toi? (Kai?.....kaine kuma dai......me yasa ko yaushe sai kai?" Ta motsa labbanta tana maganan a hankali muryarta tana kakkaryewa....ganinta na qoqarin dusashewa amma tana qoqarin tsaidashi.

Janye idanun nasa yayi da sauri daga kan labbanta yana lumshesu gami da furta

"Hasbunallahu wani'imal wakeel" Saboda sosai wani irin abu yayi tasiri cikin jikinsa......tsigar jikinsa yayi mummunar zubawar da banda namijin qoqarin da yayi ba abinda zai hanashi saketa a gurin. Mamakin qarfin halinta yakeyi,yasan akan me take magana,tunda already shi din ya riga yasan wacece........amma a wannan yanayin da take......a abinda yake iya hasashe?.

Sake maida dubansa kanta yayi karo na biyu,dabara tana qwace masa na abinda ya kamata yayi. Idanunsa ya sake sauka saman lips dinta,saidai abinda ya gani a karo na biyu ya dakeshi sosai.

A dazu a kuma dukka ganinta da yayi a rayuwarshi idan bai manta ba pink lips ne da ita......amma a yanzun lips din canzawa suke suna komawa wani color na daban.

Wannana abun daya gani ya sanyashi matsawa da fuskarsa dab da tata zuciyarsa na bugawa a hankali saboda irin kusancin da suka samu me yawan gaske. Idanunta ta lumshe abubuwa biyu suna kutsawa cikin rayuwarta da takejin kamar tana kan gargara,na farko gaurayar numfashinsu guri guda da suka fara musayarsa wanda duk numfashin da take zuqarsa da qyar dinnan yana cakuda da wannan qamshin dai natacce......na biyu kuma wani abune taji ya taso a qirjinta zuwa maqogoronta ya kuma ga mafitar numfashinta na qarshe.

"Subhanal malikul quddus" Ya fadi da hanzari saboda kai hancinsa da yayi daidai lips dinta.

"Qaseera" Sunan ya doka a tsakiyar kanshi farat daya. Baya manta komai......kaman yadda baya manta dukkan wani training daya samu a yayin horon aikinsa. Dukka wani training nasa yazo ne cakude da personal baiwan da Allah ya bashi.

Qwayar idanunta ya sake kalla,a hankali suna sauya launi zuwa kalar yellow daya sake tabbatar masa qaseera tasha.

"How comes?" Ya tambayi kansa da kansa idanunsa still a kanta yana jin wani irin yanayi yana ratsashi. Laluben sunanta ya soma yi cikin kansa,don ya zame dole yayi keeping maimaita sunanta don ya samu yadan riqeta conscious.

"Akhnaaan" Ya furta sunan da wani irin sauti da zai gaya maka akwai banbancin yare a tsakaninsu. Idanunta da suka lumshe,ruwan hawaye kuma na azaba ya soma jiqa zara zaran eyelashes dinta ta bude a hankali,ya kalli tsakiyar idanunta yana ganin yadda blue pupil dinta ya nutse cikin sclera(farin dake cikin idanu) wanda suka canza zuwa yellow din.

Har tsakiyar kanta taji kiran,duk da yadda take kokawa da numfashinta. Da hanzari ya dagata cak wani abu yana dukan qirjinta ya soma takawa da ita ganin dafara kadan saman labbanta da suka koma purple shar.

★"Alhamdulillah". Morsa safiyya ta furta sanda motocinta sukayi parking a muhallin adana motoci na sassanta. Tana shirin daga idanunta taji an bude mata bangaren da take zaune,koda ta daga idanu sai taga Armelle ce wadda ta sadda kanta qasa ta kuma ja da baya riqe da murfin motar.

"Armelle......ina kyautata zaton ke kika koyawa falaak shegen son kada nayi nisa.....duka duka fa ko awa daya banyi ba,ba'a kammala karbar lefen bama na taho......" Ga mamakinta gyada kai kawai armelle tayi,sai ta zubawa armelle idanu.......tana hangen wani baqon yanayi a tattare da ita,amma batayi gaggawar tambaya ba,har zuwa sanda ta sako qafafunta waje.

A mamakance take bin dukka fuskokinsu da kallo,kusan kowa ta kalla a cikinsu sai taga ba wani sauran kuzari ko fara'a a tattare dashi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Chapter 2 · 0% Book details