Sashe 55
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maleek ne na kusan qarshe da sukayi musabaha din,sai ya riqe hannun haisam din kadan yana tambayarsa da idanu jin yadda dumin jikinsa ya qaru. Dukkaninsu magana da kuma bada umarni da ido bai zame musu baqon abu ba,saboda fita daga tsatson sarauta,tsatson izza da mulki,don haka suke da saurin karantar body language,da idanu ya yiwa Hakeem sign din baya jin dadi ne,sai ya zame hannun yana maida hankalinsa ga wazeer.
Qasa qasa yake masa maganan waliyyan almaz su matso kusa,don sosai yakejin raunin yana ratsashi,yana kuma jin kamar bazai iya qara mintuna goma cikin masallacin ba.
Wani babban hadimi ne ya miqe yana shelar neman waliyyan almaz din,wanda cikin qasa da mintuna uku kacal suka soma tasowa daga muhallan da sukayi sallah suna matsowa.
A nutse ya daga kyawawan idanunsa yana karantar kowanne mutum dake matsowa gurin. Can qasan ransa yana wassafa abun,ba yau ne karon farko daya fara daura aure ba,daga manyan gidajen alfarmar na yankinsu,mutanen motii da yawanci suke damqa daurin aurensu cikin babban masallacinsu,wanda duk sanda ya kasance haisam din yana nan shi motii ke wakiltawa ya daura auren. Da yawan lokuta waliyyan angon yakan gansu a sahun gaba cikin sallah,wadannan sai gasu a warwatse guri daban daban suke tasowa suna isowa gurin da aka tanada don qulla auren,a haka suka kammala a gaban haisam din.
Still dai a nutse yake kallonsu,can qasan ranshi yana jin wani abu yana motsuwa. Yana jin kamar ya sallamesu ya kuma hana qulla auren,akwai abubuwan da haka kawai yakejin bai masa daidai da tsarinsa ba,akwai abubuwa da yawa da yake ganin kamar basu zauna a muhallansu ba,saidai kuma ta yaya?.
Ta yaya zai watsa taron wadannan mutanen da sukayi tattaki daga unguwannu da garuruwansu yace ya fasa bada auren akhnan din?.....a matsayinsa na wa?......wacce hujjar yake da ita wadda zai gamsar da sultane da dukkan me tuhuma akai?. Baya ga haka ma me yayi ruwansa da shiga sha'anin mara kunyar yarinyar da sam GIRMA baya cikin dabu'unta? Sai dukka ya kauda wannan,ya kuma lumshe idanunsa ya soma bada sigar daurin auren.
Daidai sanda ya kammala bada auren,dukkanin shaidu suka shaida da AKHNAN din a yau ta zama mata ga ALMAZ IDRISSOU daidai lokacin ya miqe tsam yana bada uzuri sannan ya fara ratsa mutanen a hankali don ficewa daga masallacin yana bi ta qofar baya gami da barin wazeer dasu. Tsam maleek ya miqe ganin yadda ya wuce,sai yabi bayansa shima a nutse ta hanyar daya fita din.
*_MUKAN BUDE WASU QOFOFIN QADDARA DA HANNUWANMU........YAYIN DA WASU QOFOFIN QADDARAR SUKAN BUDE KANSU DA KANSU KODA BAMU SHIRYAWA HAKAN BA_*
*_NACE BA🙋🏽♀️,karkuyi qasa a gwiwa.....kuma kada ku sare.....ku biyoni muje_*
*_Akwai QOFOFIN da suka bude kansu da kansu.....akwai wanda sheikh muhammad haisam ya budesu a wannan ranar......a wannan lokacin.....a wannan gurin ba tare daya sani ba_*
Ya manta da maleek sam cikin masallacin,har sai da yaji ya taba kafadarsa,a nutse ya juya yana duban maleek gami da zura hannunsa sosai cikin na maleek din.
"Gidan nan yayimin hayaniya da yawa maleek,mu qarasa gurin motoci,ka kira salana ya matso da mota kusa,zan dan fita gida kadan na huta,kaina sosai yake ciwo" Haisam yayi maganar yana dan riqe kan nasa da yatsunsa.
"Yakai kwana biyar baka a daidai haisam......qin maganinka ne kawai yasa kake pretending you're okay" Maleek ya fadi yana riqe hannun haisam din sosai cikin nasa,don da gaske ya lura jikinsa yana qara zama weak ne,daya hannun kuma ya fiddo wayarsa yana qoqarin kiran omar,don yana ganin kamar zaifi salana saurin zuwa,don su din kam basa wasa da damuwar d'ayansu.
Ido ya runtse sosai sanda sanarwar ta shiga kunnenta. A hankali kuma sai ta budesu,tana jan wani qaramin tsaki gami da gyara kwanciyarta sosai. Bata dauki almaz a matsayin miji ba bars ya zama takurarta,don me zata aza damuwa a kanshi?,saidai abu daya data gaza kankarewa kanta da kuma kankareshi daga zuciyarta shine TSINTACCIYAR MAGE YA ZAMA MADAURIN AURENTA? ta tambayi kanta da kanta tana jin haushin abun yana tsumata sosai,saita sake jan tsaki,fuskar sa ta jiya cikin majigin tana gilmawa a idanunta,cikin tsaiwar na tasa ta lafiyayye kuma ingarman namiji.
Yatsunta ta sake azawa saman fuskarta.kamar tana gargadin idanunta da kwanyarta akan tuna komai daya shafeshi,saita girgiza kai tana hade rai kamar d wani take magana.
Cike da girmamawa duka hadiman dake kai kawo suke kai masa gaisuwa sanda yake tattaki shi da maleek din da ficewa daga gidan. A hankali idanunsa suka kai kan wasu gungun motoci dake tsaye a gurin,inda maroqa da masu busa irin na sarauta suka baibaye gurin. Sosai kuma a fakaice ya saka hankalinsa a gurin yana karantar yanayin mutanen dake gurin.
Daidai lokacin da wani yaketa faman rabon kudi tsakanin maroqan,yayin da idanunsa suka sauka a hankali akan fuskar almaz da tamim ke cusashi a mota.
Sosai wani irin abu me kaifi da haske ya gilma ta cikin kwanya da idanun haisam,ya qanqance idanunsa a hankali yana sake kaifafa ganinsa ta guraren ko zai sake nasarar ganin fuskar almaz din,saidai bai samu nasara ba don tuni tamim ya rufe qofar motar,alamu kuma suna nuna barin gurin zasuyi.
"Salaaana ya qaraso?" Haisam ya tambayi maleek dake duban wayarsa.
"Ya qaraso mu yake jira"
"Oya hurry up" Ya fadi yana qara daga qafa cikin wani irin zafin nama da kuzari,abinda ya sake motsa bugawar da kansa yayi har sai daya runtse idonsa.
Suna shiga motar motocinsu almaz suna wucewa suka wucesu da wani irin gudu. Da zafin nama haisam ya shiga yana bawa salaana umarni da yaren oromo wanda har ya manta rabon da ya yishi cikin agadez
"Ka bisu da sauri" Cikin cika umarni salaana ya tayar da motar ya kuma bi bayansu cikin qwarewa da hikimar iya tuqi gami da bin diddigi.
Idanunsa kan motocin da suke bi a hankali,yana nazartar lambar kowacce mota yanayinta da kuma tsadar da take dashi.
A tsakanin mararrabar titunan motoci biyu suka bi wani titi daban,dayar data rage kuma gangara wata hanya.
"Wacce zamubi a ciki?" Salaana ya tambaya a hanzarce gudun kada su bace musu. Shuru yayi na second biyar sannan yace
"Hannun dama" Wato mota daya data gangara kenan.
A hankali suke bin titin har zuwa sanda suka fada wannan layin. Wannan layin dai daya sanya tsaro da sanya idanu a kansa,wannan layin daya dasa zarginsa a kanshi. Daga nesa ya sanya salaana ya kashe motar,ya bude murfin yana nufin sauka tare da cewa salaana din.
"Ka janye motar zuwa street din dake bayan wannan.......zan qaraso da qafa idan na kammala". Har ya sanya qafa maleek ya riqe hannunsa,ya waiwayo yana duban maleek din.
"Amma kasan baka da lafiya ko?" Kai ya jinjinawa maleek har yanzu yana jin yadda kansa yake sarawa da gasken gaske kaman zai fadi.
"Na sani maleek.......amma akwai wani nauyi da ya hau kaina yanzu yanzunnan daya zama dole na bincika akai.....banason Allah ya tuhumeni bani da bayanin bashi ranar qiyama"
"Amma bai kamata ka tafi kai kadai ba"
"Ni kadai ya kamata na tafi maleek.....kada ka damu zan dawo in sha Allah" Yana kaiwa qarshe ya sanya qafafunsa cikin zafin nama ya fita.
Da zafin naman kuma cikin takatsantsan yake sake kutsawa cikin layin,yanajin qarar tashin motarsu salaana a bayansa,yaci gaba da aza hankalinsa akan wannan gidan da tun ranar basu sake samun komai akai ba sai a yanxun.
Qofar gidan motar ta tsaya,sannan cikin qasa da second talatin murfin ya bude. Tamim ne na farko daya fara fitowa, sannan fuskar da yake sake son gani ta sake bayyana a fili. Almaz ne,da wani irin yanayi na rashin qwarin jiki da ya riga ya zame masa al'ada saboda yawan kasancewa cikin shan kayan maye koda ba mayen yake ciki ba.
Zuciyarsa ta wani motsa da qarfin gaske sanda almaz ke juyawa yana shiga cikin gidan tamim yana biye dashi.
"Me ya hada tamim da angon?" Tambayar farko da taxo kansa kenan sanda yake sake laluben kwanyarsa kan neman inda yasan almaz din.
"Takardun zaituna" Amsar tambayar ta haska cikin kansa. Wani mugun bugawa ya sakeji kansa yayi,har sai daya sanya tafin hannunsa ya riqe goshinsa sannan ya zare hannun nasa a hankali,zuciyarsa da kwanyarsa tana son ganar dashi tarin sarqaqiya da abubuwa masu yawa da yanzu suka harba cikin kansa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kai yake girgizawa a hankali,ba'a iya takardar kawai ya soma ganin fuskarsa ba. A nutse sunan gidan marayun ya dawo kansa,ya soma maimaitashi a jere har sai da yaji kansa kamar zai buga.......sai kuma hoton komai ya sake haska masa......gani sau daya daya taba yi masa cikin gida marayun na YATAAMA......a bangaren wadanda ake bawa horo da tarbiyya. Da kansa yaji zuciyarsa tana kokwanton shine ko ba shi bane......sai yaji gaba daya tunaninsa yana rikicewa da wani irin yanayi daya tilasta masa juyawa yana barin gurin,saboda yana jin yadda jikinsa yayi zafi sosai da wani irin zazzabi,sai ya aikewa beeno saqo kawai,ya tabbatar zaizo yaji da komai a gurin.
Ga mamakinsa maleek ya soma hangowa tsaye jikin wata motar daban bata dazu ba. Maleek din ya sauke hannayensa ya fara takowa zuwa inda haisam ke kusantoshi shima.
"Kasan bazam iya tafiya na barka ba.....hankalina bai kwanta ba sam" Ya fadi yana miqawa haisam hannunsa. Zafin da yaji jikinsa ya qarayi ya sanya ya kalleshi.
"Mu tafi gida" Ya fadi a hankali yana takawa,abinda ya alamtawa maleek shuru kawai haisam din yake da buqata ba tarin tambayoyi ba.
Tafiyar mintuna qalilan suka qarasa gidan,dukkan wani guard da security na gidan suka soma kawo gaisuwa,don ya kusa sati biyu rabonsu dasu ganshi. Kowa yayi kewarsa a cikinsu,bawai don wasa da dariyarsa ba,aah,sai don kyautatawarsa a garesu.
Maleek bai tsaya ba har sai daya taka masa har zuwa master bedroom dinsa. Yalwataccen bedroom dake nuna zallar izzar sarauta da kuma tarin dukiya dake kwance muraran a cikinsa dama tsarin ginin gaba daya.
"Kana buqatar magani captain....."