← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 101

Sashe 56

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"......ba yanzu ba maleek" Ya dakatar da maleek din yana qarasawa saman wata irin sofa kewayayya dake da wani dan madaidaicin table wanda ke dauke da qananun na'urori. Idanu maleek ya zuba masa,yana mamakin qarfin halin haisam. Sam shi bata lafiyarsa yakeyi ba,ta aikinsa yakeyi,duk da yasan halinsa dama,ko a baya wani irin mutum ne da sai ya gama ciwonsa baisha maganin komai ba. Sau tari sanda suna secondary school sai sun hada da kiran nanay,ita zatayi tsaye cikin waya kafin ya maida hankali yasha din. Ja masa qofa kawai maleek yayi ya koma da baya,bawai don ya qyaleshi bane gaba daya,aah yayi hakanne kawai don bashi space saboda ganin yana hada system da na'urar daya samu a dakin. Cikin ransa kuma yana ganin tsananin jarumtar dake tattare da haisam din,risk da rashin sakewa dake cikin aikinsu gaba daya,lallai aikin ya dace da sunan INTELLIGENT SECURITY. Aiki ne tabbas da bai cancanci kowa ba,aiki ne kuma da ba kowa ne zai iya yinsa ba da gaske,sai jajirtacce irin haisam din,wanda kwanyarsa ke gudu yadda ya kamata..

Idanu ya zubawa system din yana jiran ta qarasa kunnuwa,cikin jikinsa yana jin yadda zazzabin ke nuqurqusar qashinsa,kansa yake sake masa nauyi har yana dan lumshesu kadan kadan saboda yadda yakejin zafin zazzabin yana shiga da kuma yadda yakejin ciwon kamar yana sauka masa a idanun ne.

Yana jin ciwon sosai a jikinsa,amma baisan me yasa yakejin wani takura da qunci cikin zuciyarsa ba sama da abinda yakeji a gabbansa. Hannu ya sake miqawa da hanzari yana bude saqon da noorah tace ta aike masa,wanda ta aika ne ta email kuma system din a nan gidan ya barta,don haka koda ta gaya masa dama ya ajiye sai yau ko gobe zai ware awanni yazo ya duba hotunan.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/30, 19:53] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 50*

Fes suka fita hotunan,don dama yana cikin dabi'un noorah din daukan hoto. Tana da son dauke dauken hotuna,don har shi da kansa ya siya mata tarin cameras da sauran tarkacen daukan hotuna,wannan ya sanya ta cika dakinta da hotunan tsuntsayenta da take kiwo masu tsananin tsada da daukan hankali,wanda takanas tayi order dinsu daga nigeria ta hannun HALY JASHERU VENTURES
07046665338,ta samu sauqin isowar saqon saboda akwai wani company a nan Ethiopia din da suke order man kitso daga gurinsu suna kaiwa nigeria.
(Suna kawo original kayan islamic chemist masu kyau,original body suit na jarirai,harda na manya ma,track suit da sauransu,masu neman nau'in aku,dawisu,irin tattabarun nan masu tsananin kyau farare qal da nau'ikan kaji masu tsada,har na million daya qwaya daya hajiya akwaisu😂,ki sana'a ki samu riba me yawa,ko kuma idan SARAUTA takai irinsu haisam maleek da akhnan,kawai sai a siya a ajjiyesu saboda su qawata farfajiyar gida ko garden idan kina da 07046665338).

Zooming na hoton yayi sosai,abinda ya sanya gabansa wani irin faduwa har sai daya motsa labbansa yana furta.

"Subhanallah" Kamanni yake gani sosai,duk kuwa da cewa asalin wadda ya sani da kamannin bai taba mata kallon daya wuce na minti guda ba kacal......amma yaga kamanceceniya me yawa a gurin,hatta da dimples din dake kumatunta a duk sanda qaramin bakin nan nata na rashin kunya ya motsa itama wannan tana da,banbancin wannan nata qwaya daya ne ta hannun dama.

Ipad dinsa ya matso da ita,ya kunnata ya dorata a saiti,sannan ya miqe a hankali yana jin kamar jiri zai kayar dashi ya shiga toilet. Alwala ya daura ko hakan zai rage masa tururin da yakeji tun daga gangar jikinsa har zuwa zuwa zuciyarsa,bayaso kuma nanay ta fuskanci komai tattare dashi,nutsuwarta da labarin data jima tana basu shi a tsintstsinke yake nema ya jishi a yau full.

Qaramin towel ya sanya ya goge damshin daya jiqa gargasar hannunsa,sannan yaja kujera ya zauna yana kunna camera din ipad din sannan ya kira nanay. Wasu bayanai ta tafa da sauri,kai tsaye kuma ya aika wa bobbo muhammad dawud yayi highlight na YATAAMAH ORPHANAGE. Bayanai yake buqata akan gidan gaba daya,da duk wani yaro da ya taba bata ko ya fita a gidan,da saninsu ko bada saninsu ba,na shekaru talatin baya. Yasan aikine babba daya bayar,amma yana buqatar gano bakin zaren komai a tsakanin nan.

Ya jima yana lalubenta kafin a daga,fuskar Anaani ta fita saman screen din.

"Captain obbo......barka da warhaka" Kai ya gyada mata a hankali muryarsa can qasa ya amsa mata,sai tasha jinin jikinta,zuciyarta kuma ta fara raya mata 'yan miskilancinne tabbas a kusa,don haka bata tsaya wahala ba tace

"Bari na miqawa nanay" Baice komai ba har zuwa sanda wayar ta isa hannun Nanay din,Anaani ta saita mata wayar sosai sannan ta kauce ta basu guri tun kafin a qwaqulo mata laifin da zataci qaniyarta a gurin Captain din.

Sassanyan murmushin nan nata daya sanya yaji wani nauyi na raguwa a zuciyarsa ta sakar masa.

"Assalamu alaikum warahmatullah" Tayi cikakkiyar sallama. Zai iya cewa sallama tarbiyyarta ce,a gurinta suka fara sanin muhimmancinta da kuma tarin ladan dake cikin sallama da alfanun dake cikin yawaita yada sallama tsakanin musulmai. Murmushin ya maidata mata,murmushin da ita daya ke samunsa duk duniya,koda su anani hussam noorah da Aarif ba zasuce ga kalarshi ba,harma gwara noorah saboda ta hannun damansa ce ita din.

"Nanay na biyo labarina" Ya fada cikin tausasa murya da kwantar da kai daya saba,saboda duk sanda yake gabanta yana jinsa ne kamar wani jariri,saidai yau din hakan ya hade masa da ciwon kan dake sara masa,da yadda jikinsa ke qara daukan dumi. Murmushi ta saki wanda ke qara mata wata irin kamala.

"Shi alqawari abun tambaya ne,zan cikashi yanzu in sha Allah" Ta fadi tana gyara zamanta a nutse.

*KHADEEJA YUNNUS JALLATA(NANAY)*

"Kamar yadda ka sani,nice d'iya ta biyu da mahaifina ya haifa,bayan babban yayana Aliyyu yunnus jallata,sarki alimayu na yanzu da ya zama d'a na farko a gurin mahaifiyata data kasance mace ta biyu a gurinsa,mata ta farko a gurin mahaifina itace FALMATA,wadda sam ba 'yar qasarmu bace,kuma har yanzun mu kasa fadin ainihin sunan qasarsu,abinda ya zama silar matsala da kukan da nakeyi kenan har yanzu. Mummu falmata haka muke kiranta dashi,ta samu jinkirin haihuwa abinda yayi sanadin auren mahaifinmu ga mahaifiyarmu. Mahaifina shine sarkin gumma kaman yadda ka sani daya daga cikin yankunan da qabilarmu na oromo suke rayuwa. Samun magaji namaji abune me girma a gurin basarake,wannan shine silar auren mahaifiyata BELKIS.

Gidan mahaifina wani irin zama ne da sam basusan KISHI BA,wani irin zama ake na yaya da qanwa tsakanin falmata da belkis,zaman dake bawa kowa mamaki da sha'awa. Ba wanda yayi zaton a gidan sarauta irin wannan za'ayi irin wannan zaman,wani irin xama me matuqar daukan hankali tamkar 'yan uwan da suke uwa daya uba daya.

Bayan mamana ta haifi alimayu ne da shekaru biyar mummu falmata ta dauko d'iyar qanwarta da suke uwa daya uba daya data rasu,wadda tare sukazo Ethiopia gumma,kuma itama anan aka aurar da ita,don haka bayan rasuwarta mummu falmata itace UWA a gareta,kuma dole ta daukota don duka duka watan yarinyar me suna SAFEENA biyu a duniya.

Ba jimawa da dauko safeena din mamana ta samu cikina,cikin wani ikon Allah sai mummu falmata ta fara ciwo,daga qarshe ya tabbata itama ta samu juna biyu ne,don haka ko da aka tashi haifarmu ni da SAFIYYA sai ya zamana tazarar kwana bakwai ne akwai a tsakanin mu,wannan ya sanya ake kiranmu da TAGWAYE.

Mun tashi dukkaninmu tamkar 'yan uku,ni safeena da safiyya,har baka iya banbance uwar kowa daban,mun zama tamkar taurari da samun wata iri cikakkiyar kulawa da tarbiyya daga gurin motii yunnus. Iyamu daya samu yana jin ya toshe masa duk wata damuwa ta rashin samun haihuwa.

Munyi wata irin shaquwa taban mamaki,irin shaquwar da idan ka kallemu zaka dauka mahaifa daya muka kwanta,ko bacci baya iya rabamu,komai namu daya,hatta da abinci cikin kwano daya mukeci. Daidai da dan kunne idan wannan ta canza sai wannan ta canza nata,wata iri shaquwa taban mamaki da ba zaka taba ganin d'aya bakaga daya ba,komai tsanani komai runtsi. A haka muka taso da wata mugun qaunar juna,ko ciwo daya keyi to hankalin sauran ya tashu,tare ake ciwon nan,dame ciwon dame lafiyar gaba daya...." Sai nanay ta sauke numfashi tana sakin wani murmushi me sanyi,wanda ya tabbatarwa haisam ta tuna da quruciya ne.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"A haka muka girma,muka zama yammata sosai.....abun burgewar kowanne namiji,kowa kuma qoqarin mallakarmu yakeyi,saidai wani ikon Allah nice naketa samun manema a sannan,amma naqi yarda da kowa,saboda alqawari muka yiwa junanmu babu wadda zatayi aure tabar 'yar uwarta. To amma da yake shirin Allah daban yake dana mutum,ba zato Allah ya kawo sarkin jimma kakanka kenan,ya kuma ganni,ya yiwa d'ansa yarima me jiran gado kamu,take mahaifina ya bashi ni,ban ganshi ba,bai ganni ba,amma saina samu kaina da qin musawa umarnin motii" Ta sake kai gabar maganar tana murmushi,murmushin da ya tabbatar ya boye abubuwa masu yawa data tuna. Samun kansa yayi shima da murmusawa kadan,kwanyarsa tana dauko masa banbamcin tarbiyyar yaran yanzu da na daa......tunaninsa yana kawo masa dauki ba dadin da aka dinga yi watanni kadan tsakanin akhnan da mahaifinta,sai ya zame tunanin ya watsar yana maida hankalinsa ga nanay.

"Na haifi yayanka bai jima ba ya rasu,ina da cikinka kuma rigima ta barke tsakanin mummu falmata da mahaifin SAFEENA ta" Ta dakata kadan tana shan numfashi,dakatawar daya tabbatar akwai wani abu cikin qirjinta da take hadiya da bai wuce mata ba har yau.
Chapter 56 · 0% Book details