Sashe 53
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Window din qarshe ya rufe na dakin,yasa hannu ya zuge curtain din dakin wai yana sanya rai ko hakan zai rage dauko masa hayaniyar dake cikin gidan zuwa dakin nasa. Hayaniyar da tunda aka fara shagulgulan yake jinta a tsakiyar kansa tana shiga masa dukka kunnuwansa. Ya sani mutum ne da bame son hayaniya da yawa ba,amma wannan yawaitar hayaniyar batayi qarfin da zata dinga damunsa har haka ba,baisan me yasa yake jinta a kurkusa da kunnuwansa ba.
Har a ransa yakejin banda amanar masarauta da sultane yabar masa da gidansa zai koma,kamar hakan zaifi sama masa nutsuwa.
A hankali yake takawa zuwa gaban dressing mirror dinsa wanda a gabansa dressing table ne dake dauke da kayan shafawa na maza designers. Omar yasha tsokanarsa da cewa social sheikh,don idan kazo gurin zaka raina gayunka ne da ganin wasu irin designers perfume designers cream and oils,roll-on body mist da hair mist da baka taba ganin irinsu ba. Idan turare ake magana KAMFANIN ne shi da kansa dama,bayan personal wannan mayen turaren nasa,akwai turaruka daban daban da suke masa,kaman turaren gashi,dana underwear dinsa daya zama unique,nashi ne kawai a matsayinsa na mamallakin kamfanin. Kaman turarensa na jikin kaya,haka sanyayan body perfume dinsa da suka kama fatarsa da duk wani gashi na jikinsa babu inda zakaje kaf kasuwannin turare na duniya ka samesu. Maleek na dason turare,wannan ya sake sanya shaquwa tsakaninsu sosai,shima kuma daban ake masa nasa turaren,duk da baikai na CEO ba.
A hankali maleek yake binsa da kallo har zuwa sanda ya zauna saman stool,jikinsa sanye da wata tattausar milk color din bathrobe.
"Haisam" Ya kira sunansa kai tsaye,abinda ya janye hankalin haisam din kenan zuwa ga maleek.
"Kana lafiya?" Ya tambayeshi yana dubansa sosai. Manyan fararen idanunsa ya lumshe sannan ya jinjina kai a hankali ya furta.
"Alhamdulillah" Idanu maleek yadan kafeshi dashi,sai ya jinjina kai shima yana furta.
"Ma sha Allah" Saidai cikin jikinsa yana jin ba hakan bane abinda haisam ya fadi. Maida kansa ga cream dinsa haisam din yayi,bashi da tabbacin me yakeji a jikinsa ko kuma me yake damunsa,amma yasan ba lafiya komai yake tafiya daga gangar jikinsa zuwa zuciyarsa ba.
Mintuna arba'in ya kwashe aqalla kafin ya fito tsaf cikin shigar kurta pyjamas fari qal,kamar yadda tun daga half shoe din qafarsa da wani irin modern amam daya zagaye kansa dashi kaman na Indonesia ko Malaysia shima ya kasance fari din.
"Ma sha Allah" Hakeem ya fadi yana duban haisam da murmushi.
"Nayi burin su khadeem suna kusa.....zamana a nan sai nakejin kamar wani yawon bude ido nazo da ban taba zuwa irinsa ba" Murmushi kadan haisam ya saki,duk da yadda yakejin kansa kaman yana sara masa kadan kadan. Yasan me maleek keson fadi,ya saba da jin maganganunsu irin wannan a duk sanda yayi ado,don shi din dama ma'abocin ado ne koda ba inda zaya fita.
"Ba lecture bace takai tsaye ba......muna gurinmu suna gurin su" Ya furta yana daukan turarensa ya fesa kadan saman kayansa ya ajiye. Agogonsa dake ajiye a gefe Rolex brand yana daurawa a lafiyayyar fatar hannunsa dake da wani irin kwantaccen gargasa.
Murmushi maleek ya saki,haka tsarin haisam din yake,duk sanda lecture irin haka ya tashi indai ta mata ce saidai su ganshi jikin screen makeke da zaa saka musu a hall din,wannan shine abinda ya hanashi zama malamin university duk da yana da burin hakan don alfanun da ilimantarwa take dashi,ya tattara hankalinsa dukka akan kamfanonin sarrafa turarukansa da yanzu yake shirye shiryen bude branch a hadaddiyar daular larabawa wato UAE.
Takawa kawai yakeyi amma bayajin wani sauran karsashi a tare dashi,ya tsammaci ganin omari a qasa yana jira amma koda suka sauko baya nan,sai ya sanya hannunsa a aljihu ya ciro wayarsa ya fara neman omar din.
Bayajin zai iya tsaiwa gabatar da lecture din,don haka ya yanke kiran omar tun dazu ya jagorancin abun. Wani irin rauni yakeji a jikinsa da wani ciwon kai qasa qasa,yanayin kuma ya fara masa ne kusan kwanaki biyar baya,tun ranar da suka fara bukukuwansu na al'ada cikin gidan,a sannan yana zaune a balcony dinsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
*AKHNAN*
"Ma sha Allah,tabarakarrahman" Hairaan ta fadi tana duban akhnan din. A yau take sake gamsuwa da baiwar kyan da Allah yayi mata dari bisa dari,duk da ko a baya bata inkari,don momma safeena dama tafi kowa kyau cikin dakinsu morsa safiyya.
"Wanne irin turare ne wannan biftu?" Hairaan ta dauke idonta daga kan kwalbar turaren tana duban akhnan. Nata idanun ta janye daga kan kwalbar turaren ta dubi hairaan din. Batasan yadda zata misaltawa hairaan din yadda take mutuwar son kamfanin turaren ba......bata da wani zabi a turare a duniya yanzu sama da turaren tun wata shekara data taba zuwa dubai ta siya product din ganin yadda ya mamaye shops dinsu a can da supermarket dinsu. Tana maitar son turaren kamfanin,tasha attempting halartar taron da sukeyi na product dinsu yearly a dubai amma bata samun dama,saboda yawanci yana zuwa ne a sanda sahel couture ke lissafin ribarsu na shekara da wasu gyare gyare a kamfanin.
"Bansan yadda zance miki ba,amma ki gwada amfani da kayan kamfanin" Ta amsawa hairaan a taqaice. Tun daga kansa bata sakejin turaren da yayi mata ba,sai wanda birra ke turara mata kayanta dashi na kamfanin INCENSE BY KABODAUGHTER +2348032119803. Tarin Gift na turarukan da falaak ta kawo mata batayi niyyar budasu ba bare amfani dasu,amma bayan fitarta qamshin yaja hankalinta,koda ta duba dai taga kamfani daya ne da wanda birra ke mata using dashi,cikin karramawa ta sanya birra ta kwashesu ta musu gurin ajiya na musamman. Qamshin yana bata wani irin nutsuwa,yadda kuma yake dada kama kayanta da jikinta abun yana bata mamaki. Dama turaruka na gargajiya irin wannan suna da qamshi me tasiri har haka da kama jiki?.
Suna shirin fita falaak na shigowa
"Subhanallah" Ta fadi tana murmushi,kyan da akhnan din tayi yana ratsata,saita miqa hannu ta kama hannun akhnan din suka tako tare,hairaan a damanta falaak a hagunta,abinda ya kusa sanya qwalla fitowa daga idanun morsa safiyya kenan sannan suka fito ga farfajiyar dake a tsare da hadimai sahu sahu suna jiran isar akhnan din kebantaccen gurin da zaa gudanar da taron.
Sam a zuciyarta batason auren,bata gamsu dashi ba,bata kuma nutsu dashi ba,amma batasan meye Allah ya boye ba daya dauke mata wannan quncin zuciyar,ya sanyaya mata rai akan auren. Ko iya yadda taga 'ya'yan nata data mallaka duk duniya jere da juna,abinda bata taba ganin irinsa ba shi kadai ya isheta farincikin da har ta mutu wannan hoton bazai matsa daga idanunta ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/29, 21:31] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 48*
Dab da zasu shiga sassan da zai kaisu parlor din dake manne da dakin gabatar da taron,wanda a nan ne zai zauna da cameras din da zasu dauke video dinsa sukutum da guda sukai qawataccen dakin taron dake kama da parlor na alfarma me girman gaske,daidai lokacin da suke fitowa sannu a hankali bisa takewar bayan hadimai masu yawan gaske.
A kanta ita daya idanunsa ya fara sauka,sai ya zaresu a hankali sanda suke basu baya kan hanyar isarsu ga hall din,ya maida dubansa a hankali kan maleek,amma sai mamaki ya darsar masa sanda ya dubi idanun maleek din kafe a kansu. A nutse ya dauke kansa daga maleek yana maidawa gabansu don saita gurin da maleek keta kalla haka,kai tsaye idanunsa suka sauka akan falaak wadda ke gefan akhnan din kaman yadda suka fito a daxu.
A mamakance ya maida dubansa kan maleek,still wannan basaraken murmushin yakeyi,sai ya motsa bakinsa a hankali,muryarsa can qasa ya furta.
"Ina kyautata zaton samun matar aure ne ya karkato da hankalina agadez......wani rabonne yaketa kirana,shi yasa na kasa nutsuwa sai dana zo gurinka" Ya qarasa maganan yana dauke dubansa daga kansu saboda sun bacewa ganinsa ya dawo da kallonsa kan haisam.
Shima haisam din shi yake kalla,yana mamakin yadda lokaci daya maleek din ya iya bayyana abinda ke ransa kai tsaye. Shi da maleek suna cikin mutum biyu a team dinsu dake da farinjini sama dana kowa kuma ake shakkar tunkararsu ace ana sonsu,amma har gwara maleek a kansa. Don maleek yakan tsaya ya saurari wadda yake ganin ta cancanci hakan na wasu kwanaki kafin ya gama karantarki,idan yaga tafiyar ba zata yuwu ba sai ya sallameki.
"Da gaske nake" Maleek ya furta cikin nutsuwa yana son jin abinda haisam zai fadi. Kasa cewa komai haisam din yayi,don da gaske yakejin kanshi yana sara masa,sai ya janye idanunsa daga cikin na maleek yana cewa.
"Booda haasofna(zamuyi magana wani lokaci)" Jinjina kai maleek yayi a nutse,bai sake takura masa da magana ba ya qyaleshi,don yanayinsa ya tabbatar masa da gaske baya jin dadin.
*AKHNAN*
Wani yanayi takeji na daban tattare da ita,wani sanyin jiki dama mutuwar jiki gaba daya,har zuwa sanda ta zauna muhallin da aka tanada wanda mammina ta shirya yi mata kamu bayan an gama lecture din.
Shuru ne gaba daya ya dauka a gurin lokacin da babban allon screen din da yaci bango guda na gurin ya fitar da hotonsa. Tsaye cikin tsaiwar dake nuna zallar kamalarsa da nutsuwarsa.
Murmushi me dan qaramin sautin wanda akhnan tana iya jinsa shine ya kubucewa falaak sanda idanunta suka sauka a kansa. A yau zata kalleshi son ranta,irin kallon da bata taba yi masa irinsa ba,Koda ya kasance ta cikin screen ne bawai ganin ido da ido ba.......yana da wani irin kwarjini da cika ido,tana jin ya mata wani girman da takejin nauyinsa har cikin jininta.