← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 101

Sashe 10

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dare daya tal ya kwashe yana bincika tarihi yanayi da al'adun kowacce qabila dake cikin qasar da yankin na nijer,a wannan daren guda daya bacci bai ziyarci idanunsa ba ko sau daya. Yasha coffee har baisan iyaka ba,amma kuma bai damu da rashin baccinsa ba,don ya tattara dukkan abinda yakeso,ya kuma san duk abinda yakeso ya sani,wannan ya sanya daga wannan kallon yaji cewa tabbas akwai wani abu daba daidai ba.

Bata ankara dashi ba,har sai da tazarar data rage tsakaninsu ta kasance bame yawa bace. Yalwa ce ambaci sunanta a hankali,yanayin kiran kadai ya gaya mata akwai wani abu,don haka kai tsaye gabanta ta kalla bawai sashen yalwa ba.

Wata irin bugawa zuciyarta tayi,amma sai tayi gaggawar zuqar iska sosai tana daidaita kanta,kafin a hankali ta sauke numfashin tana gayawa kanta da kanta wani abu.

Sarrafa kansa yake qoqarin yi don yanayinsa ya dace da yadda zaiyi magana da ita. A yanayin kallonta ya tabbatar akwai abubuwa da yawa game da ita. Yadda take kallon kowa da yadda take hada nutsuwarta a duk sanda taga wani baqon abu da bata saba gani ko mu'amalanta ba. Wani yanayi da yake bayyana a tattare da wasu mutane da suke dauke da baqin abubuwa a cikin halayyarsu da dabi'arsu.

"Barka wannan lokaci" Ya furta a nutse yana qoqarin daidaita matsayinsa da yanayinsa da yadda ya fahimci tana mu'amala da hadimanta.

Murmushi ta kawo ta aza saman fuskarta,ta kawo wata irin sakewa ta sake shimfidawa a sama sannan ta amsa masa.

"Barka kade sheikh muhammad........ina fatan ba wani matsala bace ta fito dakai cikin irin wannan lokacin?". Kai ya jinjina yana daukar wasu abubuwa cikin kalamanta yana turasu wani sashe na zuciyarsa tare da shirya amsar da zaya bata duka cikin qasa da second biyar.

"Ba wata matsala.......ina buqatar iska me kyau ne kawai" Ya amsa mata a taqaice ba tare daya kalli idanunta ba. Kai ta jinjina a hankali,burinta da muradinta shine ya kalleta,tana son karanto wasu abubuwa cikin idanunsa.

"Amma ai da kasanar......yanzun kai din kamar d'a kake a wajenmu.......sai a hadaka da wanda zai maka jagora gudun shiga shiyyar da bai dace da girmanka da matsayinka ba". Murmushin qasan zuciya y saki wanda ko labbansa bai motsa ba bare ka gani,ya sake aikewa da kalamanta wani sashe na zuciyarsa,sannan ya motsa kadan alamun yana nufin wucewa.

"Bazai zama damuwa ba.......ba wani zurfi ko nisa tattakin zaiyi ba......duka duka na awa daya ne......a fito lafiya" Ya fada da salon girmamawa yana ci gaba da wucewa a hankali.

Bin bayansa tayi da kallo komai na tunaninta yana warwarewa lokaci guda.

"Tabdijan" Ta furta a sanda yake bacewa ganinsu tana aza idanunta akan fuskar yalwa.

"Ya wuce a sanda bani na bashi umarnin hakan ba,bai kuma nemi izinin wucewa ba.....bai kuma dakata da tafiyarsa ba a sanda ya ganni.....hakanan ba wani alamun kwarjini da nakewa kowa a cikin muryarsa.......yana bani amsa ne da wani irin qwarin gwiwa da tsaiwa a muryarsa.........lallai akwai wani abu.......akwai wani abu daban cikin JININSA.....ko ya kasance irin abinda ke cikin jinin SARAUTA ko kuma halittarsa zuciyarsa da ruhinsa masu tsananin qwari ne......yalwa" Ta kira sunanta tana ci gaba da takawa a nutse.

"Allah ya baki nasara" Ta amsa da girmamawa.

"Kinga dukkan abinda na fada?"

"Qwarai da gaske......abu daya ne kawai dana gani,baya kallon mutane"

"Yana da addini da kuma sanin addini.....maza irinsa suna da wannna dabi'ar.......bawai tsananin girmamawa bace a gareni.........inason insan wayeshi?......idan har sakamakon yazomin mutum ne yadda muke zatonsa ordinary kaman kowa.......to lallai ina buqatar sa cikin tafiyata........ina buqatarsa a gefe na.......".

"Sheikh haisam din?" Yalwa ta tambaya cike da tantama. Qaramar dariya ce ta kubcewa mammina.......tana jin wani nishadi yana ratsata.

"Da kamar wuya ko?......abune me sauqi yalwa.......KUDI ba sune masu maida abinda bazai yiwuwa ba ya yiwu......kudi sune masu juya kowanne mutum zuwa yanayi da siffar da kake buqatar ganinsa a kanta. Idan kana buqatar mallakar wani abu......ko wani mutum idan ka gutsira masa IKO cikin ikon da kake dashi komai ma zai sallama maka......malamai a wannan lokacin sunfi kowa son zuciya da mutuwar zuciya......mallakar wannan malamin shine abu mafi sauqi da nake hange zanyi......inaso daga yau dukkanin motsinsa ya zama abun bibiya......inason daga wannan lokacin duk inda zai saka qafarsa.....duk inda zai sauketa ya zamana abun kiyayewa......bacci ne kadai idan zai kwanta na yarda ma rataye da aikin yaje ya huta a sannan.....na bawa tamim wannan aikin......amma inaso wannan ya sake zama wani aikin na daban ba tare da kowa ya sani ba".

Yatsansa yakai kunnensa ya taba a hankali,wani tattausan murmushi ya subuce wanda ya tsaya saman labbansa.

"Tamim" Ya maimaita sunan a hankali yana motsa labbansa. Ya fahimci akwai tarin abubuwa tattare da mutum biyun nan da suke sharing suna GUDA DAYA,sai ya jinjina kansa cikin wata irin nutsuwa

"Kwanciyata bacci?.....shine zai zama lokacin faduwarki.........lokutan kwanciyata bacci.....sune zasu zama lokutan kwanciyar dukka wata sa'arki......zanyita bacci kala daban daban,daga nan har zuwa kwanakin dana fahimci WACE KE?. INA KIKA SAKA GABA?....kin shiga cikin lissafi na...." Ya fada qasan zuciyarsa da wata irin nutsuwa. Bai taba tunanin na'urar daya wurgar a gurin zata kawo masa amfani da wani bayanai daya shafeshi shi karan kansa ba......bai taba tunanin na'aurar zata zama me amfani me girma har haka ba. Hanyar dake gefan hagunsa ya kalla,yaji kuma a cikin ransa itace hanyar data dace ya shiga ba tare daya damu da komawa daukan na'urar ba. Bata da wani girma da wani zai gane meye,tafi kama da ba'awon gyada sak da sak,yasan ba jimawa wani zai taketa shikenan amfaninta ya qare a wajensa. Har qasan ransa yakejin matar tamkar tana da alaqa da duk wani bahagon al'amari da masarautar ta taba fuskanta,duk da bai sani ba.......amma motsinta na baya dana yanzu yana gaya mata tana daya daga cikin QALUBALEN SULTANE.....tana daya daga cikin MATSALOLINSA TABBAS!.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Yanaso yana mugun sha'awar ayyukansa subi takan mutane irinta......sa'arsa daya bai shigo agadez don ceto masarautar agadez ba......bai shigo agadez don bawa sultane ko iyalinsa ko mulkinsa kariya ba......ya shigo agadez ne kawai saboda QASARSA.....ya shigo agadez ne don ya kare rayuwar MAHAIFINSA.....hakanan ya shigo agadez ne don ya zaqulo boyayyen mai laifin nan ya damqawa qasarsu shi!. Iya wannan kawai zai iya sanyata ta tsira muddin bata zama cikin wadanda yake tuhuma ba......daga sanda ta sadashi da abinda yake muradin farauta ta fita daga AGENDA dinsa.

Tunda buhaina ta gaya mata an shiga tattaunawa tsakanin sultane mammina da nannie ta kasa cikakken sukuni. Kowanne irin zama ne ta tabbatar yana da alaqa da ita.....koda ba don ita aka zauna ba ta sani issue dinta yana abu na gaba gaba da za'a tattauna akai.

Yau da kanta ta shirya shirin baccinta,don bata dade da sallamar birra ba,wadda suka jima yarinyar na mata kuka da rantsuwar bata xuba mata komai cikin tea dinta ba.

Bata da wani kokwanto akan birra ko kadan,yadda ta yarda da ita haka ta yarda da kanta,to amma tana ji a jikinta tabbas akwai wani abu,akwai abinda ya faru......bai kamata kuma tabar komai yaci gaba da tafiya a haka ba.

Tafi karkata dukkan amincinta akan tamim......to amma a yanzun tamim din yana kan wa'adin ragowar kwanaki biyu na aikin data bashi,tana jin zata jirashi don sake bashi wani aiki na bincika mata me ya farun,wannan ya sanya ta hana a taba duk wani ruwa da kwanuka na bangarenta,har zuwa sanda tamim din zai dawo.

Sanda birra data dawo take shaida mata mammina ta shigo tana buqatar ganawa da ita. Bata kammala jin abinda birra ke fadi ba ta soma yunqurin sauka daga gadon. Net din dake zagaye da gadon ma wanda take controlling nashi da remote gani tayi yau baya saurin zugewa don ya bata hanya,saita sanya hannu ta yayeshi gefe tana saukowa. Bata ko tsaya neman flip-flops dinta ba ta soma taka tattausan tafin qafanta kan carpet din tana qoqarin cusa gashinta me tsaho da sulbi cikin bonnet da take mahadin kayan jikinta.

Yadda take saukowa daga stairs din a gaggauce ya sake sanya mammina cilla plan dinta da qara masa wani adadi.

Ido ta lumshe tana sake budesu akan akhnan din,wani irin kishi yana ci mata zuciya. Har tana jin kamar wani ciwo ciwo na dunqulewar da zuciyarta tayi guri daya.

Wani irin sassanyan kyau yarinyar ke dashi,kyan data tabbata banda wasu dalilai ba abinda zai sanya akhnan ta rufa shekaru goma ba tare da an aureta ba zuwa ga ahali mafi daraja da sukafi na mahaifinta. Ita kanta akhnan tana mata kyau,saidai kyan yana tsaye mata a rai da wani irin ciwo saboda tuna daga inda ta samo ASALIN KYAN nata. Daga gurin safeena ne......wannan kyan nata da tayi imani yana daya daga cikin abinda ya sanya ta rasa wannan martabar.......ta rasa wannan darajar.......ta kuma rasa wannan MATSAYIN da TAMBARIN na MATAR FARI a gurin sultane.

Bayan kyan ya mata wannan sanadin......wannan KYAN HALIN da a wajenta ba komai bane face zallar kissa da kisisina ya sake zame mata silar qara rasashi a KARO NA BIYU,ya sake cillata can nesa da matsayin zamowa MATA TA BIYU ga sultane din.

Ware idanunta tayi akan akhnan sanda take kusa isowa da inda take. Tuna baya kadan da tayi ya sake rura wata sabuwar wutar a zuciyarta. Ta zubawa akhnan idanu,tana tuna fuskar safeena da wani lokaci zaka ganta shimfide akan fuskar akhnan din.

Sau da dama tana mamakin kanta na yadda ta tsaya bin akhnan ta wannan doguwar hanyar. Tana ganin imaninta da yawa idan ta tuna shekarun data dauka kawai tana dakon ta dauki FANSA akan abinda tana iya aiwatar dashi cikin kwana uku kacal. To amma zuciyarta tasha gaya mata cewa.
Chapter 10 · 0% Book details