← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 101

Sashe 65

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/2, 22:22] +234 903 768 6798: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 57*

"Haka ake girmama......miji.....ki shigo ki sameni amma.....ba zaki....ddurd.....durqusa ki gaidanai ba?" Yayi maganar jimlar tana tsintsinkewa yana hadata da qyar.

Wani zallar mamaki ne yaso kasheta daga zaunen. Mamakin farki na batun gaisuwar da yakeyi,dubansa takeyi da kyau tana son gasgata kunnenta ko kuma qaryatashi. Ita akhnan yakema batun ta durqusa ta gaidashi?. Bayan sultane ba wata halitta guda daya data samu wanna girma martaba da mutuncin.

"Kana da hankali kuwa?" Ta tambayeshi fushinta yana motsawa a hankali. Idanunsa ya fidda sosai a kanta.

"Ni kikeso ki kira da mahaukaci kai tsaye?...ina matsayin mijinki?" Ya fadi yana nuna qirjinsa da alama maganan ya masa zafi sosai data fadi din.

"Bana daukan raini fa......ina zaman zamana bazan dauki iskanci ba......ahhhht...m.toooo,auren banza auren wofi" Ya qarasa fada yana watsa hannayensa.
Mamakinta sake ninkuwa yayi,ta sake zuba masa idanu tana qare masa kallo da gasken gaske. Wanne irin mutum ne mammina ta zaba mata?,akwai hankali cikin maganganunsa da nutsuwarsa kuwa?. Idan har idanunta sun gane mata da kyau ma kamar cikin yanayin maye yake maganar,idanunsa sun nuna mata haka,hakanan dukkan wani acting nasa da yakeyi. Fidda idanunsa sosai yayi waje yana son ganinta da kyau,don ta fara yi masa dishi dishi,so yake ya nuna mata da gaske shine sama da ita. So yake ta gane shine gaba da ita,bazai yarda da yadda take wulaqata kowa ba,yana jin haka a jikinsa cewar shi din ba wulaqantacce bane.

"Ni bana daukarrrrrr......raini kome za'a bani......zan iya babbbbbballlaki ko kece sarkin" Sosai zuciyarta tazo mata iya wuya,wannan narkakken bacin ran da ya dade cikin qirjinta da zuciyarta ta yunqoro mata.

Tsawa ta sakar masa tana bude dukka blue eyes dinta waje,ta miqe tsam tana dubansa sanda yake miqewa tsaye shima yana dafa daya daga cikin hadiman da mammina ta bashi fa suke koya masa abubuwan da zai saje da gidan sarauta sosai,tun zuwansu kuma yana tsaye daga gefan nasa saboda nuna girmamawa.

"Kabi a sannu,ka iya bakinka....koda kai din waye idan kayi kuskuren fadin wani abu mara kyau akan mahaifina zan sanya a batar dakai ne cikin agadez,za'a kuma shafe babinka,ba za'a sake jin labarinka ba" Tayi furucin tana nunashi da yatsa.

Wata dariya ya saki idanunsa suna jujjuyawa gami da shanyewa,girmansu yana raguwa sosai.

"Gimbiya ko?...." Ya fadi yana shammatarta,bata ankara ba ta tsinceshi dab da ita. Wani irin ja baya tayi da zafin naman da ita kanta batasan tana dashi ba. Ya sake zuba mata ido na wasu mintuna kafin ya saki wata irin dariya.

"Tsammani kike zan miki wani abu?,tab.....wannan ai ba matar aure bace...ni dama can ba damuna kukayi ba" Sai ya daga hannu yana nunata da yatsa gami da fara tafiya da baya da baya yana tangal tangal kamar zai zube a gurin

"Mara kunyar banza kawai....kije na sakeki.....na sakeki......na sakeki.....na sakeki....." Ya yita maimaitawa kaman wanda aka baiwa aikin ibada wata qaramar dariya kuma tana kubce masa.

Bai gaji da maimaitawa ba yana kuma yunqurin fita a gurin,yana jin kamar qasar tana juyawa dashi saboda wani irin mahaukacin nauyi da yaji kansa ya masa.

*HAISAM*

Kebantaccen dakinsa ya wuce kai tsaye yabar omar da maleek a sitting room din farko,idanunsa saman duka na'urorinsa,ya qarasa a hankali cikin qwarewa ya fara hadasu. Wasu irin qananun device ne da idan ka kallesu ba zaka dauka suna da wani alfanu ba,dauka zakayi abun wasan yara ne kawai idan ka dauke system qwaya daya dake gurin.

A nutse ya hada komai,connection ne tsakanin mutanensu dake aiki cikin gidan,location hudu,bakin babbar qofar shigowa gidan dame binta,sassan bangaren mammina,sai kuma babban kitchen na dafe dafe na gidan.

Green din haske ya kama,abinda yake alamta masa kowa yana kusa. Kujera yana yana shirin zama,wayarsa tayi blinking haske kadan,ya dakata kadan yana dubawa,sai yaga nanay ce,sai ya zauna saman kujerara nutse yana furta.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Dukka sassan hudu ya aikewa hold on sign,sannan ya katse kiran nanay yabi kiran nanay din. Bugu daya ta daga,abinda ke tabbatar masa tana bakin wayar tana jiransa,tana kuma qagauce ta gaya masa koma mene

"Muhammad" Ta kirashi da wani irin yanayi muryarta tana rawa,abinda ya sanya duk wani jijiyar jikinsa tayi relax. Da husky and deep voice dinnan mash ya kira sunanta.

"Nanay.....Tasgabbaa'i .(calm down).......of gadhiisuu(relax)nanay........ki fadamin a hankali" Ya furta da wani irin coolness,don tuni jikinsa da zuciyarsa sun gama gaya mishi sakamakon.

"tole(okay)" Nanay ta fada da wannan nutsuwartata me cike da dattijantaka da harshensa da ya riga ya narke cikin yaren oromo.

Idanunsa a lumshe,zuciyarsa na wani irin gudu yayin da zuciyarsa ke sauraron sautin muryar nanay dinsa. Yadda take masa bayani daki daki,muryarta na karyewa gami da yin rawa a gurare masu yawa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Muhammad.......Nama tokko natti fakkaata,inaji a jikina mutum daya ce......zeenatun ajani itace zeenatun lamaan dina....aikin mutum daya ne muhammad wannan tabbas.....inajin shi yasanya na kasa daina mafarkin safiyyah ta.....shi yasa na kasa daina ganinta tsahon lokaci cikin mafarkaina.....safeena ina hangenta acan nesa dani,wani irin nesa da yake ban tsoro......ko ina da rabon sake ganinsu?" Nanay ta furta dukka dauriyarta tana yankewa,wani irin qauna irin na 'yan uwantaka yana ratsata.

"Nanay" Ya kirata da tausasawa

"Na'am muhammad" Ta kirashi da wani rauni sosai da me saurare ke iyaji cikin muryarta.

"Na miki alqawari,koda ban kawo miki safeena ba,koda ban hadaki da safeena ba,zan hadaki da safiyya" Wuta ta daukewa nanay,tunaninta yana yin nauyi.

"Muhammad......ta yaya?"

"Nanay karki tambaya,karki tambayi yaushe,karki tambayi ta yaya,amma wannan din alqawari ne na miki,koda shine abu na qarshe daya ragemin da zanyi cikin rayuwata" Yayi furucin yanajin abinda ya fada da gasken gaske har cikin zuciyarsa.

"Allah yayi maka albarka......addu'ata tana tare daku muddin numfashina"

"Ameen nanay" Ya amsa yana jin wani qwarin gwiwa yana ratsashi,sannan ya yanke kiran.

Dukkanin hankalinsa ya maida ya kuma tattara akan kiran da ya yiwa kowanne,ya danna madannin daya dawo da connection din daya hada da farko.

"Ina buqatar tashin gobara cikin darennan daga madafa......sannan tayi kaman zata taba sasssannin matan gidan nan......amma bana buqatar ayi asarar rai ko daya.....kafin sannan,abeer....." Ya kira sunansa yana duban signal din abeer din.

"Yes obbo"

"Ina buqatar analysis na dukkan abinda ya halaka cikin gobarar bayan komai ya kammala,ina buqatar kuma a siya komai a maidashi muhallinsa kamar komai bai faru ba,koda tsintsiya banaso wani yayi asara"

"An gama obbo" Abeer ya amsa cikin matuqar girmamawa. Kai haisam din ya jinjina yana duban lafiyayyen agogon Rolex me tsadar gaske dake daure a tsintsiyar hannunsa

"Ina buqatar ta fara qarfr biyu na dare,banaso kuma ta haura awa biyu ayi a gamata" Ya qarasa fada yana sauke agogon daga fuskarsa gami da janye manyan idanun nan nasa da suka rusuna sosai.

"Vous pouvez reprendre votre travail(zaku iya komawa bakin aikinku)" Ya fadi cikin harshen faransanci daya sanya kowa ya koya qarfi da yaji cikin qanqanin lokaci.

Window din da iska ke kada curtains dinsa a hankali yake kalla,yanajin wani yaqini da qarfin gwiwa a tattare dashi,yana jin a yau abinda zai shiga tsakaninsa da shiga dakin ajiyar mammina shine fitar numfashi daga gangar jikinsa.

*MAMMINA*

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/3, 20:17] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 58*

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Dukkanin wanda yake a muhallin.....kunnuwansa kuma suna iya dauko masa jirkitaccen sautin dake fita daga bakin almaz sai daya rasa numfashinsa na wadansu daqiqu. Da yawansu da qyar suka iya controlling iskar da suke shaqa cikin hunhunsu wadda take iya sarrafa komai na jikinsu yake aiki daidai.

Ba akhnan ba da jinta da ganinta ya dakata na wucin gadi ba......hatta da birra ji tayi a lokacin kamar idan aka tsaga jikinta ba za'a samu jini ba.

Da wani irin kallo da batasan wanne iri bane.....da wani irin yanayi da take jin kamar gangar jikinta bata tare da ita.....da wani irin yanayi data gaza bambance wanne iri ne take duban hanyar da almaz yabi ya wuce,hadimansa na biye dashi ba tare da kowa a cikinsu ya iya cewa komai dashi ko da ita ba.

A hankali ta daga hannunta tana shafa fuskarta zuwa kafadarta,tanason taji idan idanunta biyu ne,tanason taji idan da gaske ne.....itace akhnan,idanu biyu take tsaye da qafafunta ba cikin bacci ba,ba kuma cikin mafarki ba.

Itace hamshaqiyar GIMBIYAR QASAR AGADEZ itace d'a namiji a yau ya tsaya gabanta kansa tsaye yake furta ya saketa. Ya saketa a gaban BAYI ya saketa a gaban HADIMAN da suke bauta a garesu. Ya saketa ba tare da damuwa ba,ya saketa yana me juyawa ya kuma fice abinsa hankali kwance.

Idanunta ta daga a hankali tana saukewa saman fuskar kowanne hadimi. Kowa yana tsaye a muhallinsa ba tare da qwaqwaqwaran motsi ba. Ba wanda yake iya daga koda yatsarsa guda daya a cikinsu. Saidai hakan tasan bawai yana nufin basuji komai ba.....hakan bawai yana nufin komai bai faru ba,hakan kuma bawai yana nufin komai zai canza daga muhallinsa zuwa inda yake ba.
Chapter 65 · 0% Book details