← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 101

Sashe 72

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu irin bayanai da yayi imanin bacewar basira ce ta sanya ta binne komai a guri guda a muhalli guda ba tare data rarraba gurin ajiyar bayanan ba.

Katin daurin auren dake tsakiyar takardun yakai hannunsa yana budeshi a hankali. Sunanta ne da manyan rubutun da akayishi da yaren gumma......da kuma manyan sunayen AHMADE AJANI daga sama.

Wani irin iska me zafi ya fessr,zuciyarsa ta fara wani irin kumbura. Ashe dukkanin hasashensa ba wani da yayishi ba daidai ba?......

"Zeenatu.....ZAITUNA" Ya maimaita sunan a fili,sannan ya miqa hannunsa yana zaro wani file gami da komawa gefe ya zauna tamkar ya manta lokacinsa qayyadadde ne.

Dairy ne.....diary din mamminan data zauna ta rubutashi da hannunta cikin cikakken yaren oromo da babu algus ko kadan a cikinsa.

∞∞★ Cikin wani irin zafin jiki dana zuciya yake kaiwa da kawowa cikin bedroom din nasa.

Komai ya lafa,gobarar ta dakata kamar yadda yaso,bata kuma ci wani abu me yawa ba sai tarin hayaqin data turnuqe masarautar dashi. Sunyi aiki me kyau dukkaninsu cikin tarin qwarewa da gogewar da suka samu qarqashin *obbo muhammad haisam,code name dinshi na gurin aiki AL-SAAMIT(THE SILENT ONE)* Tinjimin aiki cikin yanayi na nutsuw kamewa da yin shuru,saidai yakan fidda sakamakon da yake qarawa NISS daraja martaba da daukaka a duk sanda ya kammala wani operation nasa,wannan ya sanya ya fita da wannan sunan cikin code name da ake bawa kowa a hukumar.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Yasan komai ya tafi daidai,tunda a nutse ya kammala bincika dukkan abinda zai bincika din,sannan ya maida komai a muhallinsa kamar ba'a taba komai din ba,saidai kuma ya gaza maida wannan dairy din cikin tarin tarkacen takardun. Tarin lifidi lifidin wasu documents dake dauke da sunan sultane muhammad hammud da kuma sa hannunsa,wasu a ciki kuma suna dauke da suna da signature na khadeeja muhammad hammud qarara a cikinsu,wanda tarin abubuwan da ya gani a rubuce cikin diary din mammina din ya janye hankalinsa daga duba ko zurfafa nazarinsa akam documents documents din.

Yana tattaki ne da wani irin sassarfa daya sake bayyana tsaho fadi da cikar halittarsa ta GIANT MAN,daga bango zuwa bango na dakin. Ko sau daya ya gaza ajiye wayar hannunsa da yaketa maimaita kirawa bobbo muhamamd dawud,ko sau daya kuma ya gagara ajiye diary din mammina dake hannunsa yana sake bin shafi bayan shafi yana karantawa.

Mamakin tarin qarfin halinta ke sake mamaye zuciyarsa da wani irin bacin rai masa misali. Har rashin imani rashin mutunci da zallar izgilancin dan adam yakai ya zauna ya rubuta tarin rashin imanin da ya aikata a rayuwarsa?. Har yakai ya zauna ya rubuta tarin alwashinsa akan rayayyu da matattu?. Iya littafin kawai yana jin ya isheshi hujja......ya isa dalilin da zai kama mammina a safiyar gobe cikin masarautar ya kuma bayyanawa duniya samun nasarar kama me laifin da suka kwshe shekaru masu yawa suna nema.

Bama iya laifin da suke hasashe bane kawai........ta dauki rayukan wasu mutane daban da bincike ma bai taba biyowa ta kansu ba. Kawai don ta kashe bakin munanan ayyukanta,kawai don ta rayu yadda takeso,kawai don taci gaba da wanzar da umarni da kuma mulkar kowa cikin wani irin SHURU da ma'abota zurfafa tunani da bincike ne kawai zasu fahimci hakan.

Iska ya kaiwa naushi a sanda kiran daya yiwa bobbo muhamamd dawud ya sake katsewa,wannan kiran shine kira na ashirin da takwas da yayi masa. Yanajin kamar zuciyarsa zata fashe ne,yana jin kamar ana jan jininsa ne,so yake kawai ya samu bobbo,so yake kawai yayi accepting ya bashi daman cafke mammina. Yanajin ma kamar safiya tayi masa nisa.......yana jin kamar yayi nisa ya jirayi safiya. Ta cutar da kowa.......ciki harda nanay dinsa. Ashe itace sila na barin nanay dinsa cikin wani irin yanayi......yanayin da a kullum ta tashi a cikinsa su kansu wunin ranar baya musu dadi. Ta kife sultane ta binneshi yadda ya kamata,bama sultane kawai ba......duk wani dake rayuwa cikin masarautar a binne yake,duk wanda yake rayuwa cikin masarautar yana qarqashin sarrafawarta ne,hakanan duk wanda yake rayuwa cikin masarautar rayuwarsa cikin barazana take.

SHURU da masarautar take ciki da ake masa kallon aminci......ba aminci bane......HADARI NE......wannan shurun ba ZAMAN LAFIYA BANE annoba ce......wata kwantacciyar annoba da ba wanda ya farga da wanzuwarta.

Cilli yayi da wayar yana cusa yatsunsa cikin gashin kansa,ya furzar da wata zazzafar iska daga bakinsa yana sauke idanunsa akan tarin document din da yayi snapping a wayarsa ya kuma dawo dakin ya fiddasu zuwa hardcopy ta wata mini printer ta masu aikin tsaro irin nasu.

Kafin yayi kowanne tunani akai kira ya shigo wayar,taku uku yayi cikin zafin naman nan na ingarman namiji ya isa ga wayar,ya miqa hannu ya dauka yana danna gurin amsa kiran da gaggawa ganin bobbo ne.

"Ina ka shiga bobbo?" Ya samu kansa da furtawa abu na farko. Mamaki kadan ya kama muhammad dawud,don ya sani,komai tsanani sallama itace abu na farko da haisam yake fara yi kafin komai bayan daga wayarshi.

"Muhammad mun shiga masallaci ne nida sultane......sai yanzu muka fito"

"Mission accomplished sir!" Ya furta da wani irin yaqini a muryarsa,zafin rai da kuma qwarin gwiwa dari bisa dari.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/5, 20:38] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 64*

"Alhamdulillah" Bobbo ya fadi,yana jin wani abu me sanyi yana ratsa zuciyarsa. Wannan wahalar......wannan aikin na shekara da shekaru yau an kawo qarshensa.

"Izini kawai nake buqata daga gurinka obbo muyi arresting nata,zuwa safiyar gobe ko kuma daren yau".

" Zakayi hakan Muhammad da hannunka,zaka huce wahalarka gaba daya......but,inason wani yanki kadan daga hujjojin da ka samu zan duba kafin na sake maka dama".

"Done" Ya fadi yana katse kiran,sannan yayi snapping wasu daga cikin takardun ya tura masa.

Tsaye yayi harde da hannunsa a qirji,ba abinda yake imagination irin yadda zai shaidawa nanay dinsa ya kama azzalumar data raba soyayya da qaunarsu da 'yan uwanta na jini......ba abinda a duniya a yanzun yake buri irin Allah ya ara masa numfashi na wadannan awannin da zai kama mammina ya kuma damqata a hannun hukumar tsaro na Ethiopia. Ko a iya haka idan ya tsaya ya tabbatar yaci ribar aiki da security service. Wani irin zugi zuciyarsa take masa idan ya tuna jerin lissafin mutanen data batar wanda ta zauna da kanta cikin alfahari ta rubuta da hannunta. Ashe qeqashewar zuciyar dan adam takai ya iya zama yana tsara zunubinsa da kansa?.

Kiran bobbo ne ya katseshi ya maida dubansa kan wayar da hanzari yana daga kiran.

"Kama matar nan bazai yuwu ba muhammad..... Kamata zai zama abu mafi girma cikin dagulewar case dinnan" Ya tsinci muryar muhammad dawud tana sanar masa da wani mafi munin saqo.

Wani irin abu yaji da bazai tantance mene ba......sam kamar kwanyarsa ta daina fahimtar komai.

"Bobbo......me kake fada ne?"

"Bazaiyuwu ka kamata ba muhammad" Ya sake maimaitawa haisam da karyayyar muryarsa wadda ba irin ta dazu ba kafin suyi magana. Amsar da bobbo din ya bashi sai yaji kamar ya samu wuqa ya karta saman zuciyarsa ne

"Me kake fada ne haka bobbo!......na samu dukkanin hujjoji fa!" Ya fadi da fada da zafin zuciya.

"Muhammad,Tasgabbaa'i (calm down),akwai abubuwan daya kamata ka tattara hankalinka ka fahimcesu".

"Hankalina a tattare yake guri daya bobbo.....na gama fahimtar komai,na kuma gama hada dukkan wata hujja a kanta,ba abinda ya ragemin banda na kamata!,ba abinda ya ragemin banda na kawo qarshen zaluncinta!,.......zan kamata bobbo kamar yadda doka ta tanada,zan kamata wannan ya zama dole!!!" Yayi maganar da zafin dashi kansa baisan a haka yakewa bobbo din magana ba yana me dukan table din dake gabansa,take ya amsa ya kuma tsage daga tsakiyar glass din,Allah ya taqaita bai fashe gaba daya ba da tabbas ba qaramin mummunan ciwo zaiji ba.

Kiran kawai ya katse,don a yanzu baya buqatar duk wani abu da zai dakatar dashi daga kama mammina.......a zafafe ya soma hada connection dasu beeno,yanaso a daren kowa a cikinsu ya zama cikin shiri,da asubar yau din da awanni uku kadai suka rage tayi yakeso mammina ta zama a hannunsu,a gobe warhaka kuma ya tabbatar mammina din tana hannun hukumomi a Ethiopia. Qasar data shuka manya manya laifuka ta kuma binnesu a ciki,ta dawo wani sashe daban na duniya ta samarwa kanta amintacciyar mafaka. Hakan kuma bai mata ba ta sake fesarwa sa baza gubar dake qumshe a bakinta zuwa ga duk wanda rayuwa ta kawoshi kusa da ita.

Da sauri da sauri yake qoqarin hada komai,saidai gefe kansa daya da yaji ya sara,ya sara ne tare da zabge kaso tamanin na karsashinsa gami da gilmawar sunan KHADEEJATU baro baro cikin idanunsa. Sunan daya gani rubuce a documents masu yawa dake gabansa yanzu haka.

A hankali ya saki wayar ya koma gefan sofa bed ya zauna akai. Sai yakejin kamar akwai wani gibi.....kamar akwai wani abu daya kamata yayi baiyi ba,a jikinsa yakejin kamar akwai wani gurbin wani abu.

*MUHAMMAD DAWUD*

Wani irin shuru yayi yana rungume da wayar a qirjinsa. Wani irin tsoron haisam ne yake shigarsa a karon farko. Karo na farkon daya soma ganin tsananin fushi a tare dashi,irin wanda bai taba ganin makamancinsa ba.

Akwai hadari me yawan gaske game da kama matar a yanzu. Idanunsa ya sauke a hankali akan sultane da yake amsa waya,amsa wayar da tayi tsaho,kuma yake ganin wani irin yanayi na tsoro da tashin hankali yana mamaye fuskarsa. A iya saninsa matarsa ce ta kirashi,a cikin matan nasa bai tantance ko wace ba......amma yanayinsa kawai yana gaya masa kiran yana dauke ne da wani saqo na mummunan tashin hankali.
Chapter 72 · 0% Book details