← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 101

Sashe 81

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban sani ba sai dana tashi......ita ta zauna bata da ko guda daya......a ranar naji inama nasan inda ruhina yake na fusgoshi na qarawa safeena......ina riqe da hannunta cikin nawa......tana kuka ina kuka 'me yasa kikayimin haka safeena.....me yasa zakiyimin haka?,na rasa khadeeja ban shirya rasaki ba'. Budar bakinta cemin tayi "kinfini buqatar rayuwa safiyya......zaki iya abubuwa da yawan da ni bazan iyasu ba.....inata baki wahala safiyya kinata wahala dani.....rayuwarki tafi tawa muhimmanci......na baki amanar KHADEEJA don a yanxu ita kadai ta ragemin......ita kadai ce nake da tabbas akanta......ahmad da dan uwanshi bansan ya rayuwarsu zata kasance ba.......amma indai kin samu labari ko alamun suna raye.....muddin ci gaba da haquri.......muddin ci gaba da shuru akan lamarinsu ne zai basu daman ci gaba da rayuwa,don Allah safiyya na roqeki KICI GABA DA SHURU......don Allah ki barsu su rayu ta dalilin SHURUNKI"

Wannan roqon......wannan magiyar.......wannan muryar.....wannan sautin da wannan sadaukarwar sune suke riqe dani har yanzu.....sune suke takamin burki akan abubuwa da dama da nake gani nakeji. Safeena ta rayu akan wankin jini na kusan kullum saboda rashin qodojin dake tare da ita,muna rayuwa cike da fata tare da ita......amma ita sam ba wani fata tattare da ita saina mutuwa. Ba yadda sultane baiyi ta bari ya fita da ita a mata dashe ba,amma sai tayi murmushi.

"Ko an dasa bazan sake rayuwa me tsaho ba,iya kwanakin da aka debarmin nayi a duniya sun cika" Wata irin azababbiyar rayuwa tayi......ga ciwon rashin qoda......ga kuma wannan ciwon haukan da yake tayar mata lokaci lokaci babu qaqqautawa. Sam akhnan batasan dadin uwa ko duminta ba,sai a lokutan da safeena ke hayyacinta. Idan tana hayyacinta wuni take a hannunta,idan tana hayyacinta bata yarda kowa ya dauke mata ita,zata wuni ta kwana tana mata wasa,tana kallonta,tana mata addu'a ita da sauran 'yan uwanta,takance.

"Allah nayi imani dakai,nayi imani da dukka qaddarar daka aza a kaina.....na yarda komai ka tsarawa bawanka adalci ne.... Alla idan suna raye komai dadewar zamani ka hademin kansu guri guda.....Allah ka sanyasu qarqashin wani adali......wani adalar inuwa.....wani adalin shugabanci da zai amintar da rayuwarsu......wani ruhi da zai zame musu garkuwa ya basu amincin da ni na gaza basu,Allah ka albarkaci rayuwarsu,ka aminta dasu duniya da lahira". Bansan iya adadin sau nawa take maimaita wannan addu'ar ba a rana. Ranar da aka karbe akhnan daga hannunta aka daina barinta da ita,tana tsaka da riqonta ciwonta ya tashi,haka ta dagata ta saketa daqyar numfashinta ya dawo,koda safeena ta dawo daidai aka gaya mata abinda ya faru,abinta ta tambaya kawai shine BAN MATA ILLA BA KO? Ana amsa mata da EH ta saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa,saita maida kanta ta kwantar tana fadin

"Allah yasa haka ne yafi zama alkhairi a gareta"

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Bazan Manta maganar qarshe da mukayi da ita ba,ana jibi zata rasu,ta kira sunana na amsa mata,sai ta saki murmushi tana kallon bangon gabas na dakin,wanda na lura tafi sati tana kallon gurin,a duk sanda take kalla kuma murmushin takeyi

"Nifa na kusa tafiya gida na,gidan daba qunci ba wahala,ba zalunci sai zallar adalci da rahama,na kusa tafiya inda zan huta....." Saita dakata murmushinta yana sake qaruwa. A sannan kowacce gaba ta jikina tayi matuqar sanyi,ina murna ne ganin kwanakin ciwonta ya rage tashi,ko wankin jininma da ake mata wanda take fita hayyacinta kafin ayi a yanzu ba wannan abun sam,ta sake wani kyau abinta,har ranar da zeenatu ta shigo dubata ta kasa shuru sai data magantu. Amma kuma a lokacin tazo da wani kalan magana daya zaremin dukka lakar jikina.

"Kina da gidan da yafi wannan ne safeena?" Na fada cikin tsoro,daga kai tayi da murmushi akan fuskarta ta kalleni.

"Wannan gidan?......akwai birnannun abubuwa,abubuwan da wadanda zasuzo gaba sai sunfi wanda muke ciki yanxu.....kiyi haquri safiyya.....kiyi haquri.....kiyi haquri. Karkiyi fushi da akhnan kome zaya faru.....kada ki juya mata baya don Allah,ki tsaya a tare da ita. Ni na sani komawarta hannun zeenatu ba alkhairi bane,amma na roqi Allah na ya kareta kuma nasan ya amsa min,na roqeshi ya sanyata a mafificin hannu......ya sanya kulawarta a hannun bayinsa masu tsoronsa.....ya kuma bata mafificin miji ma'abocin saninsa da tsoronsa wanda zai ja hannunta zuwa aljanna ba wuta ba......amma akwai abubuwa masu yawan gaske da zasu dinga faruwa a gidan nan,ba lallai yanzu ba safiyya....Allah ne masanin lokaci,don Allah kada ki qara bari zeenatu ta shigo gurina.....banason ganinta da gaske,wani irin baqin duhu nake gani a tattare da ita.....ta cutar dani amma na barwa Allah hukuncinsa" Ta qarasa fada wani hawaye da tunda ta shiga wadannan jarrabawar ban taba ganin ta zubdasu ba a ranar sai gasu suna fita daga idanunta. Komawa tayi ta kwanta tana murmushi sannna tace.

"Kin tambayeni ina da gidan da yafu wannan ne?,ina dashi safiyya.....gidan da koda wasa wannan gidan bai isa ya hada kansa dashi ba.....tazara ce me mugun yawa,inama zaki iya vaji da na nuna miki" Ta fada still tana kallon wannan bangon,wannan bangon da har yanzu idan na shiga ta gurin saina tuna komai kamar yau ya faru.

Safeenata ta rasu a tsakanin cinyoyina,a kanta na fara sanin yanayin fitar rai a jikin dan adam.....wani yanayi me wahalar gaske.....wani irin yanayi me nauyi da kai kanka da mutum yake jikinka sai kasan babban aiki ne a gabanka ba qarami ba.......magananta ta qarshe bada amanar akhnan a hannuna.....amanar akhnan a hannun sultane dake tsugunne gefe yana riqe da ita kamar zai hana a zare ranta,daga wannan sai kalmar shahadar data yota maimaitawa har sanda tabi wani abu da kallo idanunta sukayi sama,wanda nake da tabbacin ruhinta tabi da kallo......".

Katsewa maganar morsa safiyya tayi,ta lullube fuskarta da hannuwanta tana sakin wani itrin kuka maras sauti me d'acin gaske. Tana tuna komai,tana jin kamar a sannan komai yake faruwa.

A nutse ya zare idanunsa daga kanta,yanajin qirjinsa ya masa nauyi,wani iri zafi yakeji daga cikin qirjinsa. Ya jima baiji labarin daya taba masa zuciya tsakanin dan uwa da danuwansa ba irin wannan. Bazaice ga adadin ajiyar zuciyar daya dinga saukewa a boye ba kamar yadda ya saba a duk sanda ranshi ya dugunzuma. Ya tabbatar nanay dinsa ba zata iya jurar jin wannan labarin ba......idan nanay ce yayi imanin zata kamu da ciwon zuciya ne kawai. Labarin rayuwar safeena dinta da rasuwarta bayan rabuwarsu bame dadi bane sam. Ya miqa hannu a hankali ya jawo ruwa cikin tarin kayan ciye ciyen da aka ajjiye masa,ya dauki cup daya ya tsiyaya ruwan sannan ya miqawa morsa safiyya da batasan ma ya zuba ba. Da manyan idanunsan nan da suka rusuna yake duban yadda ta qudundune fuskarta tana boye masa hawayenta.

"Kiyi kuka don yana ragewa zuciya radadi.....amma ki karbi wanna kisha tukunna". A hankali ta sauke hannuwanta daga fuskarta tana kallonsa da fuskarta da tayi jajur......wani nutsuwa taji me yawan gaske a kalamansa,saita miqa hannu ta karbi ruwan kaman yadda ya buqata.

Tas ta shanyeshi,ta kuma ajiye cup din tana jin yadda zuciyarta ke samun sassauci daga radadin da take mata. Shuru ya ratsa gurin ba tare da kowa ya sake cewa komai tsakaninsu ba.

Sai daya bata mintunan daya tabbatar gudun da zuciyarta keyi ya daidaita sannan ya fara magana a nutse.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 72*

"Ba wani abinda yake tabbata sai ikon Allah......haramtaccen abune zalunci koda akan ubangiji daya haliccemu,ya haramtawa kansa zalunci,ya kuma sanyashi abun haramtawa a tsakaninmu,Allah yayi rantsuwa da kan kansa cewa saiya taimaki wanda aka zalunta koda bayan wani lokaci ne". Kai take gyadawa a hankali,tana jin wata nutsuwa na sake mamayarta. Tana jin wani qwarin gwiwa sosai a tare da ita.....tana jin qarfin gwiwa na gaya masa buqatarta kai tsaye......mafarkanta da safeena a satittikan suna dawo mata kanta,tana jin kamar safeena na tare dasu.

"Rayuwar safeena ta riga ta wuce muhammad......rayuwar akhnan ce kadai yanzu ta ragemin......ita kadai ce abinda zan iya daukan mataki ko bada kariya akai........mammina ta shirya lalata rayuwarta fiye da yadda take a yanxu.....ni na sani....ba iya haka taso taga biftu ba.......amma ban taba bacci ba tun daga wancan shekarun har yanxu,ina mantawa da hairaan da falaak saboda na shagala da addu'a wa akhnan.....wannan sautin MIJI NA GARI da safeena taketa roqawa akhnan a qarshen rayuwarta yanata maimaituwa akaina daga sanda yarinyar ta zama budurwa.....tana da wata irin izza....na sani,tana da taurin kai na sani.....tana da wahalar sha'ani na sani......amma an qara koya mata da wasu dabi'u da ba a cikin ainihin halittarta suke ba. Na tsorata da yadda take gudun aure.....na zurfafa addu'a.....bazan boye maka ba daga qarshe na fahimci bawai wani abu bane daban......halinta ne yazo a haka koda an hada da wani abun ma daban.......muhammad" Morsa safiyya ta kirashi a wannan karon tana duba zuwa cikin idanunsa kai tsaye. Shima ita yake kalla,sai yake ganin nanay dinsa cikin idanunta.

"Ba wanda ya cancanci ya auri khadeeja a wannan lokaci IDAN BAKAI BA!!!" ta furta da wani irin confidence daya bawa haisam din mamaki. Idanu ya zuba mata sosai,yana son karantar ko gano wani abu tattare da ita,saidai itama morsa safiyya din kamar kowa,kwarjinin idanunsa ya hanata ci gaba da kallonsa,saita dauke idanunta gefe,a sanyaye ta dora.

"Ina me roqarka muhammad........ka auri akhnan ko bazaka zauna da ita na HAR ABADA BA......ina roqonka kayi mata ALFARMA ka zauna da ita koda na wasu shekaru ne....zuwa sanda dukkan wani buri da aka ci a kanta zai wargaje.....zuwa sanda idanu sukaja baya a kanta.....ka bata GARKUWA muhammad ta hanyar aurenka......KA TAIMAKI RUHIN SAFEENA yaci gaba da kwanciya lafiya.....wallahi nayi imanin cewa,mutuwar auren akhnan a yanzu zai buda wasu sababbin qofofi ne da Allah kadai yasan adadinsu da kuma iyakarsu.....KAYI MATA ALFARMA ka ceci rayuwarta" Takai qarshen maganar tana dawo da dubanta kansa.
Chapter 81 · 0% Book details