← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 101

Sashe 45

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin wata fusata da ba zata barta ta fara magana da mammina ba......tanajin ya mata nisa ta tsaya shawara da mammina. Shi ya aikata,shi ya kamata ya fara ganin fushinta. Ya dace zuwa yanzu yasan iya matsayinsa.......ya kamata ya fahimci ya zurfafa da yawa,ya kamata ta farkar dashi idan ya soma shaqar iskar 'yanci da yawa harta bugar dashi ya manta matsayinsa......ya kamata old version na AKHNAN BIFTU ya motsa.

Cikin jikinta da jininta gaba daya takejin kunya.....kunya me lullube da wani irin tarin baqinciki na yadda ya zartar mata da hukunci cikin rayuwarta,bayan shi din ba kowan kowa bane a rayuwarta,shi din bai darajar da hannayensa ma zasu taba sadakinta ba.....amma dukka sultane ya tattara wannan damar.....wannan kimar.....wannan martabar ya damqa masa.

Shigowar birra ya sanyata daukan siririn band ta tattare gashinta me tsaho da sulbi ta daureshi,birra ta matso cikin girmamawa da zummar mata shiri na musamman,ga zatonta baqi gareta masu muhimmanci cikin daren,ko wata muhimmiyar fita.

"Kaya kawai zaki bani na canza,cikin gida zan shiga" Ta fada tana qoqarin karbar kayan da tuni birra ta cika umarninta ta ciro mata su.

"Ki tabbatar da lafiyar hanya,sannan a dubamin kowanne sashe na gidannan a gayamin inda wancan malamin yake a yanzu haka". Tayi maganan tana fara zame hannayen rigar baccinta da har tayi shirin kwanciya labarin sadakin daya fara yawo cikin gidan ya hanata kwanciyar. Dan damm kadan birra tayi,tana tuna sabuwar dokar hana zirga zirga daga wannan sassan zuwa wancan sashen da lokacinta yake dan da fara aiki kamar kowanne dare daya zama zartaccen hukunci cikin masarautar. Tana kyautata zaton jwar dakin nata ta manta?,duk da bata da tabbacin tana da masaniyar fara aikin dokar. Dole ta shaida mata,don gudun karya dokar kamar yadda akayi gargadi me zafi akan kowa.

"Allah ya taya miki sirrin farincikin sultane......akwai doka da aka sanya na hana zirga zirga daga goma na dare a masarauta gaba daya". Cak ta daga fararen idanunta dake dauke da blue din qwayar idanu daga tsakiya tana zube dubanta akan birra,kallon dayayiwa birra nauyi,kwarjinta daya cakude da tsananin bacin rai yana tasowa.

"Doka?......waye gwanin sanya doka a sanda sultane baya nan?,sa'annan har yake da qarfin ikon tilasta kowa yin biyayya ciki harda ku da kuke qarqashin umarni da kulawarmu?" Sake yin qasa da kanta birra tayi sosai sannan a ladabce tace.

"Sheikh haisam" Ta fadi a hankali. Tunani kwanyarta ta cilla,amma bata wahal da ita da dogon nema ba ta canko mata wanda birra din ke nufi,saboda shi kadaine yake amfani da laqabin sheikh a jikin sunansa.

Wani sabon bacin rai taji yana sauko mata,ta ware idanunta sosai tana duban birra da kyau.

"Birra......hala kin manta a gaban wa kike da kike iya sanar mata akwai wata doka bata sultane ba da zata bi?" Tayi maganar da maqurar bacin rai da kuma mamakin yadda komai yake sarrafuwa ta hannunsa.

"Tuba nake ranki ya dade,kiyimin rai" Idanunta kawai ta maida ta lumshe tana jin yadda adadin farashin tsanarsa ke ninkuwa a ranta,kafin daga bisani taja iska me nauyi

"Kada na bude ido na ganki a nan,ki kuma aiwatar da umarni na......doka koda ta sultane ce a yau nasa qafa na taketa,ballanta ta tsintacciyar mage". Sosai kalaman suka yiwa birra girma,bata kuma sake tsaiwa cewa komai ba ta fice da sassarfa,don ya zame mata dole cika umarnin uwargijiyarta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/26, 19:09] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 41*

Sassauqar rigar buba ce data zauna mata das a jiki,duk da bada fadi ta gefe da gefe amma ta tsakiya ta zauna daidai fadin qirjinta da kuma shafaffen cikin ta. Wani irin yadine me taushi daya kasance daya daga cikin suturun da asalin buzaye kan sanya a jikinsu,sai mayafin da baida cikakken kauri data dora saman kanta da zummar suturce sumarta,ta zurawa sambala sambalan qafafunta takalmin tana jan wani irin tsaki kamar zata cire harshenta.

Da wani irin qasaita take saukowa daga stairs din,kowanne motsinta kowacce gaba ta jikinta tana fidda lallausan qamshin incense by kabodaughter,duk cewa bata qara wani turaen ba a yanzu,amma yadda qamshin ya kama suturarta haka ma jikinta ya sanya ko yaya ta motsa ko ta gifta sai wani irin sassanyan qamshin ya fitini hancinka.

Birra buhaina da bushira dukkaninsu suna tsugunne suna dakon fitowarta,don haka sai kowacce ta miqe suna saita kansu gami da fara take mata baya cikin girmamawa da bada kariya ta musamman ga amanar sultane dake hannunsu.

★Shirunne yaci gaba da gudana a gurin da wani irin yanayi na kadawar iska dake nuni da tasowar hadari da kuma yiwuwar zubar ruwa daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Tun yammacin ranar hadarin yake qugi yake kuma hada kansa,so a yanzun ba abun mamaki bane don ya soma zubda ni'imar daya qunso a cikinsa.

"Me ka fahimta game da yanayin nanay akan wannan abun hannun?" Haisam ya tambayi omari kai tsaye,don yanason gwada nasa kaifin hasashen ba tare daya buda masa bayanan daya samu daga gurin nanay ba. Bayanan da suka tunzurashi kuma ya saka wani sabon binciken bin qwaqwaq afi da diddigin yadda akayi ZEENATU amaryar ajani tayi baton dabo. Rana ta qarshe da aka ganta a Ethiopian da gurin da aka ganta na qarshe. Tare da matsawa da kunna kowanne abu da zai tayar da qurar lullubin tsohon aiki tsohon bayani,tayar da duk wani ma'aikaci daya ajiye aiki a wancan shekarun,duk wani ma'aikaci na shige da fice daya ajiye aiki shekaru goma baya da suka wuce har zuwa yanzun.

A jikinsa yakeji da gasken gaske komai yana kan turbar bayyana da warware kansa. Zarginsa yana sake tabbatuwa da qarfafa akan mammina da kowanne irin wucewa second. Bayanai yana iya samunsu yanzu na abinda ke gudana cikin gidan,saidai ya sake tabbatarwa TSANANIN WAYO gareta,wanda hakan yake sake sanyashi damqe tasa damarar da kyau. Ta canza duk wani takunta,saidai a wannan sauyin akwai wasu qofofin data bari a bude da suke iya kai ganinsa ga wani sabon babin zargin. Sake jaddada tsaro da tsari dama qofofin dakin ajiyarta dake cikin gidan,wanda ba wani daki da aka tasamma wannan aikin sai nata. Yaga zallar rashin wayonta a nan,hakan kuma ya zama NUNA KAI da motsi dake tabbatar da tsarguwa da rashin yarda,motsinta ya haifar mata da kuskure,KUSKUREN da ya qara jan hankalin haisam zuwa ga isa ga ma'ajiyar. Ya tabbatar akwai tarin SIRRIKA ajiye a ciki,girman sirrikanne kuma ya sanya hankali da nutsuwar mammina suka kasa samun sukuni da tunanin abubuwan dake binne a ciki.

"Ina tunani gani da hasashen nanay tasan komai akan abun hannun,don reaction dinta ya nuna hakan" Omari ya fada yana tattara hankalinsa akan haisam. Shuru ya sakeyi yana jinjina kansa a hankali,sai ya ajiye nannauyan ajiyar zuciya. A hankali ya motsa bakinsa cike da tarin nutsuwar nan data zame masa jiki.

"Jikina yana gayamin......akwai wata alaqa tsakanin zaituna da zeenatu,qaqqarfar alaqa" Ya fadi can qasan yana qanqance idanunsa saboda sabon gilmawar wani motsi me qarfi da yaji,motsin daya tabbatar omar baikai ga jinsa ba,bayaso kuma yaji din don a yau yana son sake aikewa da mammina ne wani babban GARGAD'I da yakeso ya ganshi baro baro saman fuskarta da ayyukanta.

Kai omari ya gyada shima yana gamsuwa da zancan.

"Idan hakan ta kasance fa?". Shuru yayi sannan wani irin lallausar murmushi ya kubce masa lokacin da idanunsa suka sake dauko masa inuwar bulama dake qoqarin kusanto inda suke.....saidai kar yake hangen inuwar bulama da irga kowanne motsi nasa.

" Zan shayar da kowa mamaki" Ya bada amsar don isar da saqo ga bulama da motsinsa,da kuma isar da saqon amsa ga omari.

Tun daga nesa kadan dasu ta sauke idanunta a kan mutum biyun dake tsaye gaban qarfen,tana tsammanin kasa tantance malamin tsakanin mutum biyun,saidai a sanda idanunta suka sauka kan mutum na biyu daga qasan zuciyarta taji tana gaya mata SHINE.

Idanunta ta qanqance tana ci gaba da duban bayansa tana jin kamar tayi taku guda ta isa gabansa maimakon taku kusan goma sha biyar da suka rage tazarar dake tsakaninsu

"Kafi gaban bada mamaki.....saidai kace al'ajabi,ina tsoronka sometimes" Omari ya fadi yana kurbe coffee dinsa. Maganan ya sanya haisam murmushi kawai,ya maida dubansa ga gabansa sosai yana hangen yadda iska ke wasa da ganyen bishiyoyin daketa rangaji a gabansu tare da ci gaba da karantar sauyawar kowanne motsi na bulama da yake iya qiddigeshi cikin kansa da yanayin lissafin ma'abota kakkaifar qwaqwalwa dake aiki da intelligence na security. Baiyi niyyar sake cewa komai ba......sai kuma sabon takun da yaji a bayansa ya sake waftar wani kaso na hankalinsa,saidai hakan bai iya janye nazarinsa akan bulama ba dake sake kusantosu cikin irin hikimar da yake zaton yana da ita,kamar yadda takun bai sanyashi ya juya bayansa ba kamar yadda omari yayi.

"Subhanal malikul quddus" Omari ya furta qasa qasa yana tabo haisam,still idanunsa suna kan akhnan da nata duban yake tsaye akan haisam kawai,haisam din da bai ko motsa ba bare ya waiwayo gareta.

"Haisam......princess din agadez ce da kanta" Omari ya furta a karon farko daya soma ganinta ido da ido kuma kai tsaye haka. Wani irin mamaki ke saukowa yana lullube omari,da gaske ne yadda ake radi radin kyawunta,yadda ake wassafata har bai kai yadda take a fili ba,ganinta a fili ya zarta yadda ake maganarta,tabbacin da gaske ba kowa bane ya taba tozali da ita.

"Idan har tazo nan ne saboda ni.....ka barta ta qaraso,banaso kaci gaba da damuwa da isowartata" Abinda yace da omari kenan still na abinda ya sauya daga tsaiwarsa a gurin hankalinsa na rarrabuwa gida uku yana kuma qoqarin kula da kowanne sashe.
Chapter 45 · 0% Book details