← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 101

Sashe 95

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Irin wannan kallon kamar ranar da muka fara haduwa?" Ya fadi yana kashe mata ido daya. Qaramar dariya ta saki,tana jin kunyarsa kadan tana saukar mata. Duk tsahon shekaru da kuma haife haifen da tayi ba abinda ya sauya tsakaninta da IBRAHIM. Har yanzu wannan kallon qauna rahama da soyayyar yana nan a inda yake,takan kalli haisam a yawancin lokuta,tana kuma rayawa a ranta tana yiwa diyar duk data sameshi a matsayin miji murna,musamman idan ya dauki halayen mahaifinsa. Wannan dalilinne ya sanya take tsananin yiwa saamee sha'awarsa,ko don maraicinta,ko don kuma nata nutsuwar da kuma hankalin.

"Allah yasa ba wani laifi nayi ba ake tuhumata da idanu.....abu daya dana karanci a gurinki muhammad haisam ya gado" Sake sunne kanta tayi a nutse tana murmushi.

"Ko daya Allah ya baka yawan rai,....ina na isa na tuhumi mijina haka?" Murmushin ya maida mata shima yana dan jan hannunta.

"Magana nakeso muyi Allah yasa aban aron hankali duka da tunanin a nan"

"Ba aro za'a baka ba,domin kuwa hankalin tunanin da wadda ta mallakesu dukka naka ne"

"Na sani,na gode da aka sake tabbatarmin" Ya furta yana murmushi.

"Khadeeja....." Ya kirata da sunanta na asali.

"Sanin kanki ne komai muqaddari ne daga Allah,sannan sanin kanki ne muna rayuwa ne akan rubutacciyar qaddararmu......sannan sau da dama akwai abinda muke hanga ga yadda zai kasance sai Allah ya canzashi ya kasance daban da yadda muke tunani.....duk Allah yana yine don zaba mana maslaha da kuma abinda xai dace damu....wasu suna shiga rayuwarmu a sanda bamu zacesu ba,wasu kuma suna fita a sanda bamu tsammacesu ba.....haka rayuwa take. Ka marabci dukkan wanda Allah ya kutso dashi rayuwarka don bakasan dalili ko manufar haka ba....kada ka koreshi kada ka qyamci kalar qaddararsa.....hakanan duk wanda ya zabi fita daga rayuwarka kada ka tsaidashi,.......bakasan manufar Allah na koreshi daga cikin rayuwarka ba,wataqila bai cancanci zama da kai ba......wataqila wanzuwarsa a rayuwarka matsala ce" Kai ta jinjina a nutse tana jin jikinta yana sanyaya,hankalinta kuma yana gamewa guri daya.

"Kin tuna sultane hammud na yankin sahel?" Ya tambayeta yana duban idanunta. Nazari kadan tayi sannna ta girgiza kai da sauri tana murmushi.

"Wanda yazo barkar haisam?.....yace in sha Allah shi din babban malami ne da ba'a taba irinsa ba?.....ga sarauta ga ilimi.......dan gatan malami.....isa takai isa kenan malamin dake da sarauta" Sosai murmushi ya qwacewa motii,ya sani zai wahala nanay ta manta sultane ko don saboda wadannan kalaman. UWA bata manta wanda yayi KYAKKYAWAN FATA ga yaronta.....kamar yadda bata manta wanda yayi mummunan fata a gareshi. Lokaci lokaci takan tambayeshi ina hammud na sahel?,saidai shi kansa bayace ba,don baisan ainihin sunan qasar ba har suka rabu,sadarwa ta yankewa kowa a cikinsu,tun a Egypt.

"Yana ina kuwa?,har yanzu ba wani labarinsa?"

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Ya dawo khadeeja......ya dawo rayuwarmu ta hanyar bawa haisam auren diyarsa me sunanki khadeeja......auren da zaa daurashi nan da kwana biyu ko uku a madeena". Wani iri taji xancan,kwata kwata saita gagara fahimta,ta zubawa motii idanu tana neman qarin bayani.

Murmushi ya saki,ya miqa hannu yana lakace mata hanci.

"Dauke idanuwannan ma'abota kwarjini.....irin idanun sheikh muhammad haisam sak" Tare murmushi ya qwace musu,tana kallonsa ne bawai don bata aminta dashi ba,ta yarda da mijin nata dari bisa dari,da wata irin yarda da d'a yakewa iyayensa.

"Bani labari motii" Ta fada cikin son jin yadda wannan bahagon al'amarin ya kaya. Nutsuwa yayi sosai yana sake riqe hannunta cikin nasa.

"Gidan sultane haisam ya sauka,acan kuma yame gudanar da bincikensa,saidai cikin binciken ya samu gidan sultane a hargitse......ya samu komai baya tafiya daidai dalilin hatsabibiyar matarsa......akwa tarin abubuwan da suke a rufe da sultane bai sani ba bai kuma fahimta ba har yanxu......akwai abubuwan da suke tafiya akan hadari da ba daidai ba......ciki kuwa harda d'iyarsa da aka yiwa saki uku kwana uku kacal da daura auren da ko tarewa batakai gayi ba.......MARAINIYA ce data rasa uwa......marainiyar data rasa UBA ba kuma don baya raye ba......sai don kawai yadda aka kifar da tunanin mahaifin da nata tunanin dukka,bara gane daidai daba daidai ba cikin rayuwarta,an amintar da ita duk wani kuskure da za'a yiwa rayuwarta daidai ne.....duk wata halaka da za'a jefata daidai ce...... Bamu sani ba addu'a ce?,Allah masani,sultane ya yanke bawa haisam diyarsa wanda haisam din ya dade da zama cikakken d'a a gidan.....ya kuma dade da zama amintacce ga sultane din ba tare da yasan daga inda ya fito ba......sun sake haduwa da bobbo.....yasa bobbo ya nema masa izini,ni kuma na yarje......haisan ya yarje shima saboda ceto......duk da banda tabbaci d'ari bisa d'ari akan dalilin da ya sanya ya amince haka da wurwuri shi din.....wannan shine abinda ya faru". Yayi mata bayanin a dunqule ba tare daya buda mata dukkanin abinda ya shafi aikinsu haisam ko hukumar tsaro ta sirri ta farin kaya ba.

Shuru tayi tana rasa abuncewa,wani bahagon al'amari ne daya kamata ya zame mata me nauyin gaske,auren d'anta a wata qasar,a sanda ba'a shiryawa komai ba. D'anta mafi soyuwa a gurinta,d'anta na fari.....to amma kuma komai tasan tsarin Allah ne kamar yadda motii ya gaya mata a yanzu. Uwa uba kuma MARAICIN yarinyar da rayuwarta a baragurbin hannu shine abinda yafi tsaya mata. Tana tausayin maraya sosai,tun sanda ta fada nata maraicin. Batun shiri akan aure ko biki dukka tasan wasu abubuwa ne da za'a iya yinsu daga baya......wasu abubuwa ne da za'a iya maye gurbinsu a wani lokaci na daban,bata da haufi ko matsala a kansu.

"Shi kuma muhammad tasa qaddarar ta auren marayun mata ce....Allah ya qara cika zuciyarsa da tausayinsu da kyautatawa" Ta furta a sanyaye. Furucin yaja hankalin motii a kanta.

"Marayun mata?" Ya sake tambayarta. Murmushi ta saki tana dubansa.

"Eh.......ina da burin ya auri saamee Allah ya taimakeka......saidai hakan baya nufin na tursasashi.......zan bashi dama har sanda zaiji ya gamsu,zan bawa saamee dama itama idan tana jin zata iya riqe soyayyar ita kadai.....kada kace komai don bazan tilasta daya daga cikinsu ba,duk yadda nakai gason wanzuwar abun" Idanu ya zuba mata sosai,yana jin kamar ya hadiyeta. Komai nata akwai sauqin kai a ciki,komai nata akwai hankali nazari da kuma fahimta,bata da zafafawa akan komai,mu'amalarta sassauqa ce,iya wannan yana qara yawan sonta a zuciyarsa,yana jin bazai samu wata mace kamarta ba.

(Yake me karanta wannan littafi.....muddin kina biyayya ga mijinki da kuma qoqarin kyautatawa tuquru,soyayya da zama bisa amana,ina roqa miki Allah ya kadaitaki a gidan mijinki......ya kadaitaki a zuciyarsa dama rayuwarsa gaba daya ki zama KE DAYA CE TAK!).

"Zan aika jama'ata in sha Allah zuwa nan da gobe ko jibi zuwa madeena,zan yiwa sarkin Gibe da sarkin kaffa. Ki sanar da me martaba sarkin gumma don ya zama wakilin mahaifiya da d'an yar uwarsa" Murmushi ya qwacewa nanay......yadda motii ke girma ahalin yunnus jallata na dada burgeta,har yau har gobe ba abinda ya sauya. Yayanta sarkin gumma motii yana kallonsa ne a matsayin mahaifinta,duk da kuwa kusan sa'anni suke da junansu. Murmushi ya saki,ga jawota kadan yana rungumeta cikin jikinsa

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/13, 21:28] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 84*

"Ya kamata a samu yawaitar shaidu......kowa yasan ibrahim aba jifar ya aurar da sheikhun malamin d'an nashi,duk da mun boyewa sultane har yanzu baisan nine asalin mahaifinsa ba.....har yanzu kuma baisan daga wanne DANGI daga wanne AHALI haisam ya fito ba......duk wani hidima da shirye shirye zasu biyo baya......ba abinda xan hanaku aiwatarwa khadeeja......haisam na musammanne,kuma na dabanne a raina" Kanta ta ajiye a qirjinsa tana sauke ajiyar zuciya,gurin da kullum idan ta sanya kanta a gurin sai taji wata tarin nutsuwa da kasancewa cikin aminci a zuciyarta da jikinta.

"Allah yayi mana zabi mafi alkhairi,ya shige mana gaba"

"Ameen......a ranar ina da tafiya duba mutancan da asara ta samesu na qauyencan,inaso a duba yadda za'a biyasu diyya su rage radadin asarar da sukayi" Hannunsa ta matse cikin nata tana sake alfahari da kasancewarsa mijinta uban 'ya'yanta. Ba shakka da yawa daga cikin halayen nagartar haisam daga gurinsa ya gado.

"Allah ya qara maka suttura arziqi da rufin asiri"

"Ameen ya rahman ya raheem" Ya amsa mata yana jin wani farinciki yana ratsashi.

*WHEN FATE SPOKE IN MASJID ANNABAWI*

_(MADEENA ALMUNAWWARA)_

Tun asubahin ranar juma'a ya fita kamar yadda ya saba duk lokaci irin wannan don samun sallar juma'a a masallacin ma'aiki a guri na gaba daura da liman. Duk kuwa kasancewar yana cikin jerin sahun manyan mutanen daka iya tsaiwa dab da liman a kowacce sallah,amma yafi zabar sammako don dacewa da dukkan falalar da ranar ke dashi.

A yau din juma'ar ta zame masa ta daban,juma'ar ta zame masa ta musamman,juma'ar da yakejin kamar itace juma'a ta farko a gurinsa.

Da qyar a jiya bobbo ya tilastashi kan ya koma masauki yayi bacci koda na awa uku ne kafin asubahi tayi. Baisan iya adadin addu'ar da yayi akan auren ba a kwanaki ukun kacal,baisan iya adadin rahamar Allah daya nema ya sauka akan auren ba,kariya da albarka. Baisan kalar addu'ar samun shaquwa da qauna me zurfi da yayi ma ma'auratan ba. Tunda ya sani.....wani aure ne da dukkaninsu zaizo musu da wani bahagon yani bahagon al'amari. Yasan haisam me sauqi ne,kamala dattako da sanin ya kamata,ya san muddin maganan sauke haqqi na iyali da kulawa ake magana akai bazai bashi da haufin khadeeja dinsa ta gama samun dukkan wadannan,saidai bayan wannan din......yanaso ta samu SOYAYYA soyayyar ma irin ta haisam daya tabbatar muddin ta sameta ta gama samun cikakkiyar kamala dacewa da jin dadin duniya harda na lahiran ma yana sanya mata rai.
Chapter 95 · 0% Book details