← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 101

Sashe 26

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata kujera ya jawo ya zauna sasai akai,ya jawo personal system dinsa ya jona device din ya kunnata yayi connecting.

Kai tsaye ya wuce fannin tura hotuna,yayi clicking duka hotunan uku da beeno ya tura masa ya soma nazarinsu.

Nazari ne irin na qwaqwaqwafi da qwararrun jami'ai na binciken sirri ke yi a kan kowanne abu daya fado hannunsu da sunan bincike.

Dukkaninsu ba wadda ya samu nasarar ganin fuskarta kaman yadda beeno ya gaya masa,saidai kaya dai kaman wancan ranar.....kamar wancan lokaci. Tufafi ne na masu muqami sosai cikin masarautar agadez din.....manyan muqamai da sun kusa mata hamsin daga manyan sassan gidan uku. Iska ya furzar,yana jin lokaci yayi da zai sanya idanu yasan bayanan kowacce mace dake ta'ammali da uniform din,matsayinta da kuma iyakacin hurumin da take dashi a gidan.

Yana shirin rufe hotunan sai ya fasa,ya koma hoto na biyu yayi zooming nasa sosai. Hoton tafisu ne a farko,don haka shi ya fara zuqowa. Hannunta ya fito sanda take gyara itama lullubin kanta don sirranta fuskarta. Akwai wani abun hannu na duwatsu da suka zama ado wa tsintsiyar hannunta. Iya gurin kawai ya yanke ya fiddashi hoto me zaman kansa.

Dukka hotunan yayi marking sannan yayi forwarding nasu zuwa ga wani sabon adreshin,da rubutu taqaitacce da yaren Oromo a qasa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Ina buqatar bayanan tsaho da hasashen qiba na kowacce mata.......wannan hannun inason bayanai da binciken qwaqwafin me shi.......a fidda asalin halittar da me shi zata iya kasancewa dashi. Yana kammalawa ya tura,sai ya maida bayansa ya jinginar da makarin kujerar yayi relaxing sosai yana jin yadda a yau gajiya take bin sassan jikinsa.

Maher yayi kadan,yana buqatar kota yaya ya zuba ma'aikatansa Shima cikin gidan.......yana aqalla kowacce qofa ya zamana akwai mutuminsu koda mutum daya daya ne......tabbas zaiga sultane a gobe duk da bai shiryawa hakan ba,zaisan kuma yadda zai shigo da tsarin cikin sauqi.

Hannun rigarsa ya nannade ya kuma wuce zuwa toilet ya daura alwala,ya dawo ya shimfida lallausan abun sallarsa ya tayar da sallah a nutse. Sallar dare wani makaminsa ne ne qarfi da girman gaske tsakaninsa da ubangijinsa.......wani qarfinsa ne walwalar matsalarsa sannan kuma jagoransa a duk sanda ya sanya wani al'amari a gaba dama rayuwarsa ta yau da gobe.

Koda ya idar ya jima saman abun sallar yana karanta wasu addu'o'i,tsantsar dangantaka me qarfin gaske yake ji tsakaninsa da ubangijinsa a irin wannan lokacin. Gari yayi shuru,ko ina yayi duhu ciki harda dakinsa da yake zaune a yanzu haka,don yana jin dadin kebancewar da zaiyi da ubangijinsa ta zamana cikin sassauqan haske da ba can can zaka gane abinda ke dan nesa da kai ba.

Shafa addu'arsa sai ya zamana kamar maqullin budewar duk wata dabara tasa. Qaramin murmushi ya subuce masa yana sake imani da yaqinin cewa,tabbas idan ka roqi Allah kana da nufi me kyau,to tabbas ne zaya amsa maka addu'arka a kusa ko a nesa,sai ya miqe tsam yana kunna bedside lamp da yakeji haskenta kadai ya isheshi. Komai ya bude sosai cikin kansa........kai tsaye ya jawo wayarsa da har ya riga ta kasheta ya soma da kiran maher.

Bugu biyu kawai maher din ya daga,muryarsa da sanyi sosai da alama bacci nason fara daukarsa.

"Ka matsa daga qofa na?"

"Aah......lokaci baqai qarasa ba"

"Akwai buqatar koda lokaci yayi kada ka matsa din.......akwai qaramin hari da zai faru yanzu cikin gidan,kada ka aiwatar da komai banda abu biyu,basu hanyar shiga da basu hanyar fita cikin mintuna goma kadai.......ba wanda za'a cutar ba wanda za'a illata......kawai akwai hankulan da nakeso a tabasu da shiyyar da nakeso a bawa qarfi....."

"Done obbo" Ya fada cikin tsananin girmamawa da biyayya.

"A bayan ka basu qofa sun fice ina buqatar basajar da zata bayyana cewa kaika fatattakesu daga shiyyar zaituna da suka nufaci zuwa......koda qaramin rauni ne ka samar dashi a jikinka......zan kula da wannan".

"An gama obbo"

"Ka fahimta?" Ya tambayeshi don gudun samun sabani. Kai ya jinjina

"Sama da yadda kakeso na fahimta" Ya amsa masa da qarfin gwiwa.

"Ka fara shiryawa,amma na'urarka ta kunne ta zama active to keep in touch"

"Yes obbo" Sai duka suka gintse kiran,sannan ya maida akalar kiran ga omari.

"A cire beeno a ciki......he done the best a wannin da suka wuce,a bashi relaxation hours" Ya bayar da umarni wa omari.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/13, 22:33] +234 903 768 6798: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 24*
________________________
*Assalamu alaikum warahmatullah*

*_Ina me farincikin sanar daku in sha Allah gobe zan saki hotunan tsala tsalan takalmanmu da suka iso kai tsaye daga qasar sin wato CHINA_*

*_Takalman yara maza da wasu nau'ikan unisex DAKI BARI_*

*_MUNA MUKU ALQAWARIN AMINCI DA QUALITY IN SHA ALLAH_*

*_ZAKU IYA JOINING GROUP DINMU TA WANNAN LINK DIN_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

*KO MAGANA DANI KAI TSAYE TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER WAYAR*

08187255862

*SIYAN NA GARI....MAIDA KUDI GIDA*🙌🏽🙌🏽🙌🏽🙌🏽
____________________________

*_WASHEGARI_*

Cikin wani kyakkyawan kurta pyjamas yake da akayi da sassauqan yadi navy blue a idanu,sadai asalin zare da audugar da aka saqa kayan masu tsadar gaske ne. Simple dinki akayi mata wanda ya fidda kyansa da kuma haibarsa,kamar yadda color din kayan ya fidda moderate hasken da fatarsa ke dashi me ban sha'awa.

Da alama cikin shirin fita yake,saboda gefansa agogo ne da farin rawanin da ya nadu ya zauna sosai saman gewayayyar hular da yakan sanya me wani irin yanayi me daukan hankali,rawanin da yawan mutane ko ince malaman Indonesia Malaysia ke amfani dashi.

Tsaye yake riqe da takardun guda biyu a hannunsa,tsaiwar data fidda siffa da zubinsa na GIANT GUY dake sa wani irin cikakkiyar suffa da kamala me janye hankali da idanu.

Takardar farko dake dauke da gwajin komai dangane da hoton matan jiya bata dauki hankalinsa ba kamar wannan ta biyu,wadda ke dauke da qerarren abun hannun daya gani daga hannun mammina......da kuma bayanan da bincike ya bayar akan abun hannun.

Abun hannu ne me dad'ad'd'en tarihi tabbas,wanda a yanzu ba kowanne gida ake samunsa ba cikin oromian region,sai gidajen sarakuna da manyan attajirai,wanda Shima yasan da hakan,amma abinda yafi janye hankalinsa shine an samu tabbacin akwai me irin abun hannun cikin iyalin gidan AJANI da ita daya ta taba mallakar irinsa,saidai kuma an samu bacewar abun hannun ba'a san kuma inda za'a ganshi ba bare a zurfafa bincike a kansa. Danyan gwal ne aka dunqule aka sarafashi a haka,wanda gidan mahmud ajani shine gida na farko da aka taba ganinsu da irinsa,wannan ya sanya nasu ya banbanta da irin na kowa.

Takardar ya maida ya ajiye kafin Shima ya zauna a gefanta yana fidda siririyar iska daga bakinsa. Yana jin wani qarfin gwiwa da yaqinij qarfafa zarginsa akan mammina. Meye hadinta da qasar Ethiopia?........meye hadinta da abun hannun daya kasance shaida ce kuma alama ce ta attajiran qasarsa?......ya akayi ta samu abinda ya kasance yana da alaqa me qarfi da zuri'ar AJANI AHAMED?.

Yatsunsa ya cusa cikin gashin kansa,ko yaushe abubuwa sake gabatowa suke gabansa da zafinsu,ta kowanne bangare ta kowanne sashe da qulli da dabaibayi komai yake zuwa masa.......amma zuwa yanzu ya samu cikakken hujjar da zai sanya idanu......cikakken hujjar da zai fara bibiyar al'amuranta da tsananin qarfi.

Faruwar komai a jiya kawai yasan wani babban mabudi ya samu,wata babbar hanya da komai zaizo masa da sauqi.....dole ya dauko asalin abun hannun daga can cikin dakinta zuwa hannunsa don ya aike dashi a sake duba masa tabbacin SHI DINNE?.

System dinsa ya jawo,yayi wasu rubuce rubuce sannan yayi saving ya maidata ya ajiye,ya miqe a nutse yana daukan Amama dinsa ya qarasa gaban madubi. Yaji dadin nemansa da sultane yayi a yau din,don dama yasan dole hakan tana iya faruwa......zaya nemeshin ko don abinda ya faru a jiya cikin wasu sassa na gidan. Wannan kjma shine target dinsa,zai ganshi ne a sanda shi sultane din da kansa ya nema zuwa gurinsa,ya kwana jiya yana addu'a samun sassauqar hanyar shigar da buqatarsa,ya kuma samu dukkan wani dama,komai ya tafi daidai,komai kuma ya tafi har fiye da yadda ya tsara.

Ya dora amaama din saman kansa,jelar da kanyi reto daga gefan kafadar damansa ya zagaye habarsa har zuwa saman hancinsa da ita yadda ya saba yi a yawancin lokuta,wannan ya santa dogon hancinnan da kyawawan labbansan masu daukan hankali.

A nutse yake saukowa zuwa qasa,inda ya samu cook dinsa ya kammala breakfast tsaf cikin tsafta da tsari. Yau din shi daya ya kwana cikin sassan,don abdii ma cikin plan din jiya bai kwana cikin gidan ba.

Cikin matuqar girmamawa ya rusuna yana gaidashi gami da yi masa barka da fitowa. Kai ya gyada masa,sannan a nutse ya shaida masa a kwashe komai,zaiga sultane ne,baisan kuma ko qarfe nawa zai shigo ba.

A nutse yake karantar yanayin sauyawar masarautar daga jiyan zuwa yau,yanayi ne da zai tabbatar maka akwai wani alhini daya faru. Gefan sassan mammina da morsa safiyya akwai qarin adadin masu bada tsaro Sosai fiye da ko yaushe......saidai na gefan mammina din har yaso ya dara na morsa safiyya.

Idanunsa ya janye yana lumshesu,wani qaramin murmushi dake boye qasan mayafin amaama dinsa ya qwace masa. Haka mutane ire irenta suke,basa qaunar mutuwa ko wani abu da zai kawo barazana ga rayuwarsu......iya wannan motsin nata kawai ya sake dasa zargi me qarfi game da ita a ransa.
Chapter 26 · 0% Book details