← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 101

Sashe 64

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yayanmu ya qaraso.....zan iya shiga sahun 'yan rakiya?" Ta tambaya tana dage dukka girarta sama.

"Yayanmu?" Ta maimaita sunan cikin kanta,saita ware idanunta akan falaak

"Me yasa kike da rawar kai har haka falaak?,yaushe ya zama yayanki?" Tayi maganar haka kawai tana jin furucin falaak din yana tabata. Bata wani damu ba,zuwa yanzu halayen akhnan din duka ba baqinta bane,sannan uwa uba tana sanya ran lokaci yayi da akhnan din zata sake janta a jiki,don zata tafi gidan aurenta ne,zata fara wata rayuwa ta daban ba wadda sukeyi ba a yanzu,dole komai zai canza.

"Tunda kina nuna min careless,na sani koshi zai daukeni a matsayin qanwarsa ta gaske,irin abinda na rasa a tare da ke" Sosai maganan ya ratsata,amma duk da haka saita dauke idanunta daga kan falaak din taci gaba da sanya takalmanta a hankali,kafin ta soma nufar qofa,birra buhaina bushira barratu bara'atu dama falaak suna biye da ita.

*HAISAM*

Yau din tun daga nesan nesa da gidan ya sanya salaana ya ajiyesu. Akwai nazari da yakeso ya sakeyi na unguwar duka dama anihin ginin katangun masarautar. Tare da maleek suke takawa,wanda dukkaninsu suna maqale ne da Bluetooth suna hira a tsakaninsu ta conference call din da suka hada da mutallab....khadeem....amjad.....naseeb. Duk da maganarsa qalilanne cikin hirar tasu,amma hakan bai hana masa jin dadin hirar ba,wadda ta gauraya da yanayin garin daya bada lullumi na hadari. Jikinsa har yanzu bayajin qwarinsa sam,amma kuma hakan dai bai kauda wannan jarumtar qarfin halin da qarfin zuciya da qawazucin dake tattare dashi ba.

Surutu ko dogon magana ba dabi'ar maleek bane,suna dan kamanceceniya ta wannan fannin,duk da wani lokaci maleek idan da zurfin sabo tsakaninku yana dogon hira,kamar dai a cikinsu su bakwai din,to amma yau tunda suka taho yake basu labarin agadez.

"Nan kusa zakuzo guys....don nikam har nayi farin kamu" Maganan yaja hankalin haisam,amma sai baice komai ba da wannan salon basarwar tasa,yayi kaman baiji ba,yaci gaba da takawa abinsa yana nazarin ginin katangar masarautar da suka fara cimmata.

Yanajin ihun khadeem,dan rud'u ne na gasken da kusan yafi kowa rudu a cikinsu,wannan ya sanya yafi kowa tara 'yammata.

"Me nakeji kana fadi maleek?,yau kuma an biyo ta kanka?" Idanu maleek ya lumshe yana shafa qirjinsa murmushi yana qwace masa.

"Wata princess tayi wuf da zuciyata daga shigowata......kuma bazan tsaya kallon ruwa ba kwado yayimin qafa.....zan zauna,zan jira mahaifinta ya dawo na nema aurenta da kaina Allah khadeem" Still haisam yaji maganan ta masa ba zata,duk da cewa yayi hasashen haka dama tun wancan ranar,amma kuma issues din da suka sakoshi a gaba ya sanya bai maida hankali ba akai.

"Amma mutumina.....ya akayi ka riga dan gari yin farinjini?" Naseeb ya fadi da alamun yana danne dariya qasan ranshi.

Sarai maleek yasan da waye yake,saiya saci kallon haisam sannan ya janye idanun nasa da sauri kafin ya masa wannan kallon nasa yana dariya qasa qasa.

"Ya qaryata zuciyarsa ne kawai.....ina kuma masa fatan kada nan gaba kadan na sake kiranku kuzo kuyi jinyar me ci......" Qit! Haisam ya yanke kiran gaba daya,kowannensu take wayarsa tayi disconnecting,abinda ya sanya kowa dariya a cikinsu daga shiyyar da yake. Sunsan halinsa,sunsan aikinsa ne,kuma shi daya yake iya musu wannan yankar qaunar idan hira batayi masa ba,don shi kadai ne a cikinsu ya karanci sanin ilimin sanin na'ura ciki da bai dinta.

Harara yadan watsawa maleek sannan yace

"Ashe dama ba don Allah ko zumunci kace zaka zauna ba?....."

"Ba haka bane captain......"

"Haka ne.....kuma zanga waye zai baka auren....badai falaak ba?" Hannu maleek ya dora saman qirjinsa yana marairaicewa haisam.

"Tsaf zaa maidawa motii ni unconscious.....a haka ma nayi kara ne ban tareta ba,inaso nabi komai bisa tsarin addini.....mahaifanta kafin ita" Kai haisam yake jinjinawa,ya sani dukkaninsu har yanzu ba wanda ya sauka daga kan tarbiyya mutunci kima da martabarsa,saidai isowarsu bakin babban qofar shiga masarautar ya sanya suka aje zancan a nan.

Duk wani hadimi dake bakin kowacce qofa da zai wuce zuwa hanyar ciki rusunamasa yakeyi cikin GIRMAMAWA. Irin girman da sultane ne kawai ya cancanceshi,abun har ya fara bawa maleek mamaki.

Su kansu wani jin dadin dawowarsa sukeyi,hakanan sukejin rashin karsashi na gabatar da aikinsu,da wani irin salam da gidan yayi musu a tafiyar da akace musu yayi na kwanakin.

Daidai sanda suka iso farfajiya ta biyu data hada sassa da dama na gidan,daidai lokacin da falaak ke takawa gefan akhnan tana mata magana qasa qasa.

"Kinyi kyau yaa biftu,kayan sun miki kyan da duk wanda ya kalleki yasan amarya ce". Wani abu taji ya sauka a qirjinta,taji kamar falaak ta qara sauke mata nauyi saman zuciyarta,abinda ya sanyata daga idanunta kenan ta saukewa falaak harara. Kan fuskarta idanunshi suka sauka,fararen idanunta dake dauke da blue din qwayar idanu da haskensu ya fita tsakiyar blue din sosai. SAK amarya saboda yanayin gown din dake jikinta wadda birra ke dage mata ita daga baya.

Wani harbawa zuciyarsa dake cikin qirjinsa yaji tayi,a hankali ya janye qwayar idanunsa daga kanta yana jin yadda zuciyarsa taci gaba da bugawa kadan kadan.

A lissafinsa yanzun ba lokaci bane a al'adarsu na kai amarya ba,baya kuma zaton hakan,don inda hakanne zai kasance tabbas sai an sanar dashi. Tunaninsa ya sake dawowa jikinsa.......WAYE ALMAZ bayan kasancewarsa wanda aka dauko daga gidan marayu na YATAAMA.....shin ya cancanci ya bari sultane da damqa gudan jininsa a hannun da yayi imani SHIRYAYYEN SHIRI ne da manufa da akeson cimmawa?.

"Zanji da wannan tabbas" Ya samu kansa da bawa kansa da kansa yaqini.

Damqo hannun maleek yayi sosai yana tsareshi da idanu.

"Ina zaka?"

"Ko sau daya ne ka bari nayi magana da ita mana" Maleek din ya fada cikin bawa haisam tabbaci akan abinda yake fadi. Idanunsa ya tsaurara akan fuskar maleek dim sannan ya girgiza kai.

"Ba inda zakaje yanzu maleek.....tana tare da matar mutane ne,matar aure ce a gefanta,ta yaya zakaga adon daba naka ba?". Sosai maleek ya tsare haisam da kallo,sai ya zame hannunsa daga cikin na haisam din,wata irin dariya tana qwace masa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Meye naka na kishin matar wani?" Cak yaji maganar ta tsaya masa a rai,sannu a hankali ya dauke dubansa daga kan maleek,yaci gaba da takawa zuwa ciki kafin yace

"Saika dawo"

"Ba inda zani,na fasa nima,zanci gaba da daurewa har sultane ya qara so,na kuma nemi izini daga gareshi,hakan sai yafi kima a idanunshi". Maleek ya fadi yana bin bayansa,still murmushin dake kan fuskarsa bai bace ba.

*MAMMINA*

Murmushi ne kawai yake fita saman fuskarta kadan kadan,tana jin wani nishadi yana ratsata,tana kuma hangen nesanta tana dab da zuwa kusa.

Tana hangen ranakun dariyarta,ranakun walwalarta,da ranakun jin dadinta suna dab da riskarta.

Hankali kwance kuma cikin nutsuwa tayi zaune saman sofa,ta dora qafarta daya kan daya tana girgizata a hankali. Tana ji ne kamar an mata kyautar duniya da abinda yake cikinta. Tana jinta a wata sabuwar duniya sabuwar rayuwa da zatazo mata da FANSA akan dukka wanda ya taba yiwa rayuwarta katsalandan,ya kuma jefata a dawwamammen baqinciki.

Bata da wani haufi,bata kuma da wata sauran matsala akan masaniyar abinda yake gudana tsakanin akhnan da almaz,don ta zuba dukkanin mutanenta da zasu bata labarin koda motsa yatsa ne almaz ko shehnaz sukayi.

"Allah ya baki yawan rai.......tamim yanason ganawa dake,saidai dokoki da iyakoki basu bashi daman shigowa ba kamar yadda aka saba" Raliya daya daga cikin hadimanta kenan dake iya karbar aiki sanda yalwa ke nesa.

Wayarta dake hannu ta dakata da dannawa,ta xubawa raliya idanu. Har tsakiyar ranta da zuciyarta tana jin yadda wadannan dokokin suke caccakar ranta. Har cikin ruhinta tana jin zafin yadda suke sake karo da muradanta,suke kuma kawo mata rauni wajen samun dukkanin wani information da take da buqatar samu.

"Ya dakata a sansanun ganawa,zan fito yanzu" Ta amsawa raliya din. Cikin ranta tana jin ba normal abu bane ya sanya tamim nemanta a irin wannan lokacin ba,don haka ta miqe tsam tana gyara alkyabbarta.

*AKHNAN*

Dukkanin hadiman da suka mata rakiya dama wadanda ke gurin tuni sukayi biyayya suka tsaya bisa sahu da tsarin na umarni cikin salo na sarauta da akhnan ta basu. Akwai hadimai sosai a gurin,wadanda suka samu a gun suna aikin gyara shukokin gurin yankesu daidaitasu da kuma rage musu tsaho. Sai kuma nata data taho dasu wadanda suka yiwa kansu gurin tsaiwa nesa kadan da ita,ta yadda zasu iya ji da ganin komai dake gudana kamar yadda ta zabi hakan.

Idanunta fes akan fuskarsa,fuskar data gaza tantance bambancinta da wancan fuskar ta waccan ranar. Ci gaba tayi da takawa a qasaice tana duban idanunsa,idanun da bata iya hangen komai ta cikinsu. Shima ita yake kallo,ya kuma qureta da dukkan kallonsa daya quntata zuciyar akhnan,sannu a hankali ta hadiye wani abu me kama da bacin rai,tana zama hannun kujerar dake kusa da ita,ta tsani yawan kallo,ta tsani a zuba mata idanu,batason a fiya kallonta,wannan ya sanya kamar ya zama doka akan dukkan wani bawa ko hadimi da zai sanya idanunsa cikin nata.

Cikin izza ta motsa labbanta tana dubansa bayan tadan kalli agogo.

"Kazo a makare,ina faran zaka fadi duk abinda ke ranka akan lokaci,ina da abunyi a gaba me yawa" Sosai maganar ta sauka akan kunne da zuciyar almaz,maganganun tamim kuma suna dawo masa tarwai cikin kansa kamar lokacin yake gaya masa su.

"Bata da kunya,bata iya girmama kowa". Maganar kuwa ta motsashi,ya tashi ya zauna sosai yana dubanta duk kuwa da yadda yakejin kansa ya masa wani irin nauyi.

Idanunsa dake lullumshewa ya waresu kadan a kanta,ware idanun kuma daya sanya akhnan din taji wani abu kadan ya fusgeta,taci gaba da barin idanunta a kansa.

Tana da kyau da gaske ne,wani irin sassanyan kyau me burge idanun me kallo. Sabgar mata tana daya daga cikin sabgogin da basa cikin tsarinsa sam. Bai taba tarayya da kowacce diya mace ba ko soyayya,saboda kayan mayensa kadai sunfi masa kowacce mace a gurinsa. Amma baisan me yasa ya kasa jin komai a kanta ba,wani abu me kama da soyayya ko sha'awa sam baiji ya masa tasiri a rai ba.

"Ke!" Ya kirata a dan tsawace,abinda yayi matuqar saukarwa da akhnan mamaki ta daga kanta tana dubansa kai tsaye.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
Chapter 64 · 0% Book details