← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 101

Sashe 67

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Qarar wayarsa ya tsinke zaren tunaninsa,a hankali kuma ya miqa wayar ya daukota,saidai.sunam sultane daya gani kan video call din dake shigo masa ya sanyashi zama sosai,cikin kuma girmamawa ya daga kiran yana aje wayar a gabansa cikin cikakkiyar sallama.

Tarwai fuskar sultane ya bayyana,da wannan kwarjinin nasa. Kamalar nan tasa shimfide saman fuskarsa wadda haisam yake ganin kamar ta qaru bayan tafiyar tasa.

"Da alama riqon masarauta ya shagaltar da yaro na,baya nemana sam sam.....ina nan ina masa addu'o'i masu yawan gaske na dacewa duniya da lahira". Kwantaccen murmushi ne ya qwacewa haisam,yana jin qaunar sultane har ranshi. Yadda yake masa magana tamkar yana masa magana da motii ne,cikin nuna zallar qaunar da yake ganinta cikin idanun sultane din ta gasken gaske.

"Aikinku sultane ba qarami bane......na yadda da cewa kudin zababbu ne kuma na musamman ne" Murmushi sultane yayi yana gyada kai,background din bayansa kuma yana nunawa haisam a cikin farfajiyar masallacin madeena yake.

"Kai dinma na musamman ne muhammad,don ba kowanne mutum bane yake iya riqon qwarya ya kuma gyara masarauta cikin qananun lokuta irin wannan ba. Koda baka gayamin ba amma komai da yake gudana cikin masarautar ina da masaniya........wannan ya sanya bazan gushe ba na juyar da mafi rinjayen addu'ata a kanka,ina fatan Allah yasa kaci gaba da zama d'ana halak malak" Sosai addu'ar sultane a guri me tsarki irin wannan ya ratsa haisam din. Wani irin yanayi yaji yana bun zuciyarsa,wani rashin jin dadi kadan daya tuna barazanar da akhnan ke fuskanta. SHIN YA KYAUTA KUWA IDAN YA BARI TACI GABA DA FUSKANTAR MUMMUNAR BARAZANA IRIN WANNAN DA ZATA IYA RUSA RAYUWARTA?. Hakan yayi daidai da kalar qauna da amincin da sultane ya bashi?.

Kafin yace komai yaji wata murya na magana kusa da sultane din,muryar da yaji kamar ya santa,sani kuma na sosai sani na haqiqa tana cewa.

"Yauwa.....zanso ganin wannan d'an naka kuwa muhammad" Juyawa sultane yayi ya kalli me maganar yana sakar masa murmushi.

"Ako ina alfaharin nuna d'ana DAWUD.....don nasan zaiyi wahala samun irinsa a kaf matasan yanxu......kokai na samu yaro kamarsa......irinsa dai sak,ba shakka abun ayi tattakin yi maka murna ne" Qasa haisam yayi da kansa,yana jin kamar sultane yana sake jibga masa wani nauyinne,yana jin kamar sultane yana qalubalantarsa ne......kamar yana qalubalantarsa akan amanar daya bashi ta akhnan.....ME YASA BAI GAYA MASA BAZAI IYA YIN YADDA YAKE HASASHE BA?,ME YASA BAI GAYA MASA BAZAI IYA YADDA YAKESO SAK DA SAK BA?.

"Muhammad" Ya tsinci muryar sultane yana kiransa. Da wannan murmushi da nutsuwa ta yiwa ado ya dubi sultane yana amsa masa,abinda ke sake jefa qaunar haisam din cikin zuciyarsa kenan.

"Kasan tsohuwar zumunta nawa gurin nan ya sake hadawa bayan rabuwa ta shekara da shekaru?" Kai haisam ya jinjina a hankali.

"Sau da dama zaka rabu da mutanen da zaka yita begensu,zaka yita begen haduwa dasu......amma idan har zasuci gaba da zame maka alkhairi a rayuwarka,sai kaga watan watarana kun sake haduwa dasu...... Muhammad dawud.....tsohon amini na farko dana fara gasgata amintarmu.....aminin daya bani kyautar jininsa a wani aikin hajji da muka tabayi shekaru masu dan dama abaya,jinin da a lokacin banda ya bani shi,da tuni yanzun ba nine wannan sultane din nake magana ba,ya zauna dani yayi jinyata......ya fasa barin qasar nan saboda ni,har sai da bayan na warke ya kumayi tattaki ya maidani Egypt inda daga can na taho aikin hajjin har gidan da nake zaune a sannan......"

"Amma dai kana yimin rowar ganin yaronka ne kawai Muhammad" Yaji muryar tadan fadi da barkwanci,abinda ya sake saka sultane dariya.

"Inaso na gaya masa ne zaman shekara goma a Egypt na nemeka na rasa,bayan an gayamin kayi qaura Ethiopia,bakai ba labarinka dawud......sai daga baya na samu lambarka,zumuncin da ba'a ganin juna yaci gaba da dorawa

"Bani na fada masa da kaina" Yaji ya fada,sai sultane din ya miqa masa wayar yana cewa

"Kamar zaifi" Yana dariya kadan kadan.

Fuskar muhammad dawud(bobbo)ce ta mamaye screen din wayar haisam din,abinda yazo musu dukkaninsu su biyun a bazata. Wani irin mamaki ya kamasu dukkaninsu,yayin da muhammad dawud ya furta.

"Haisam" Yana sakin murmushi. Murmushin shima haisam ya maida masa,don ya tabbatar tunda yaga bobbo dawud din yayi hakan,baida matsala kama sunanshi da yayi.

"Ka sanshi dama?" Sultane ya fadi yana duban bobbo dawud.

"D'ana ne.....dan dan uwana ne......neman ilimi ya kaishi agadez ai watannin baya da suka wuce" Bobbo ya fadi,a ransa yanajin da gaske motii aba jifar kamar dan uwa yake a gunsa,hakanan haisam din neman ilimin ne ya kaishi agadez ba qarya a ciki.

"Ma sha Allah,ba banza ba nakejin qaunar haisam daban cikin raina.....sak irin qaunar da nakewa khadeejatu da falaak" Sultane ya furta maganar yana dawo da fuskarsa cikin screen din.

Zare wayar a hankali haisam yayi bayan sun kammala wayar yana ajiyeta saman table din gabansa. Yatsunsa dukka ya cusa cikin tattausar sumarsa yana shaqar numfashi gami da furzar dashi ta bakinsa.

Me yake faruwa ne?,ta ko ina alaqa take sake danno kai?,me yasa ta kowacce fuska ake samun ginuwar sabbin alaqoqi?. Alaman shigowar saqo cikin wayarsa ne yaja hankalinsa,yayi scrolling ya bude wayar tasa sannan ya shiga kan saqon. Daga muhammad dawud ne,ya sanya idonsa a nutse yana dubawa,rubutaccen saqon daya shigo cikin yaren oromo.

"Kada ka damu,kana cikin aminci,koda abinda ka shigo yi agadez zan iya gayawa sultane,amintaccen mutum ne me wata irin nagarta,nasan kai kanka kasan da haka,QASARMU da HUKUMARMU GABA DAYA SUN ZUBA IDANU SUNA JIRAN SAKAMAKO DAGA GAREKA".

Wannan kalmar tasa ta qarshe yaji ta sake zuba masa qaimi. Wannan kalmar yaji ta sake zungurinsa,wannan kalmar ta sakashi ya sakejin ya zame masa DOLE ya cika wannan imanin da dogara dashi da qasarsa dama mutanensa sukayi.

*MAMMINA*

A wani mugun birkice da wani fusataccen yanayi take kutsa kai cikin parlor din,ba wanda takeson gani a lokacin irin almaz da kuma tamim.

Ta mance da wani sallama ballantana neman iso da dama tuncan bata sanshi ba. Itake juya komai,ita ke sarrafa komai,itake bada umarni.

Tun bata qaraso ba take iya hangen almaz yashe saman kujera,rabin jikinsa saman kujerar,yayin da gwiwoyinsa zuwa qafafunsa suke dire a qasa da salon kwanciyar rub da ciki wadda tayi kama data mashaya sosai,abu na farko daya fara daga hankalin mammina din,taji kamar an dauki wani abu an doka saman kanta.

Idanunta suka sauka kan tamim,yana durqushe gaban almaz din,cikin wani irin mawuyacin hali dake nuna rashin sanin abunyi. A hankali ya dabo yana duban mammina dake tsaye a kansu da idanunsa da suka canza launi,yanayin dake gayawa mammina yana cikin tashin hankali da kuma tsaka me wuya kamar dai yadda takeji a jikinta,saidai a daidai wannan lokacin akwai wata halitta data kaita shiga tsaka me wuya.....akwai wata halitta data kaita jin tashin hankali.

"Meye wannan tamim?.....me nake gani?" Mammina ta tambaya tana nuna almaz dake kwance yana baccin kashirban abinsa a qasa.

Baya tamim yaja yana yin qasa da kansa ba tare da sanin abinda zaice da mammina din ba,a yanayinsa na zahiri kenan,yayin da badininsa ta cika da wani irin farinciki da ya jima bai tsinci kansa a ciki ba.

"Kiyi min afuwa.....nayi dukkan iyawata,nayi dukkanin qoqarina,nayi duk yadda na saba,nayi kuma abinda nasan zai gamsar dake,amma hakan bata samu ba,ya sha abun maye ba tare da sanina ba,yayi buguwar da har ya iya....." Sai ya gaza qarasawa yayi qasa da kansa ruwan hawayen dake tare a idanunsa yana disa a qasa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Da gaske ya saketa?" Mammina ta zubawa tamim idanu tana masa kallon dake dauke da tsantsar tsoro da firgicin sake samun tabbacin labarin data riga ta gama samun tabbaci din.

"Ya saketa,har saki uku" Tamim ya furta da wani irin sanyi.

Wani abune ya tsaye mata a wuya,tana jin kamar numfashin dake qirjinta zai tsaya cak. Ta miqa qafa ta daki qafafun almaz tanajin kamar ta shafe babinsa daga duniya.

"Dan banza asararrriyar halitta.....mara alfanu,dan iskan yaro. Na gama wahalar shekara da shekaru amma ka ruguxamin dukka wata sa'ata cikin kwanaki uku kacal?,cikin awa saba'in da hudu?......wanne irin mara sa'a ne kai a rayuwa?.....wahalar dubban awanni amma lalacewar awa saba'in da hudu?.....wanne irin dabba ne kai maras amfani da bazaka iya haqurin wata uku kacal ba har sai ka samu amincinta?,har sai ka fara hada shimfida da ita!" Wani tsayewa cak maganar tayi a maqogoron tamim,har yaji bazai iya tsaiwa ba a gurin,sai ya taka yana matsawa bakin qofar parlor din,yana kallon yadda mamminan keta kaiwa almaz duka da qafafunta,dukan da sam baisan ma anayinsa ballantana yaji a jikinsa.

Hannuwansa kawai ya harde a qirjinsa yana dubanta,idan har tanaso gauraya asalin yarinyar ne da wani asali mara tushe,asali maras cancanta me yasa shi ba zata zabeshi ta bashi wannan ragamar ba?. Me yasa zata dauko wani baqon yaro duk da da irin wahalar daya kwashe yana yi mata?,tun yana da qananun shekaru na can can gashi yanzu har shekarunsa sun fara haurawa?.

Wani irin sauti qashin qafartata ya bayar,abinda ya dakatar da ita daga kaiwa almaz duka kenan. Wani irin sabon radadi da zafi ya soma ratsata har kwanya,abinda yasa tafisu riqeta da kyau.

"Dukka wannan ba girmanki bane,idan ma hukuntashi kikeso kiyi saidai ki bada umarni kawai ayi miki duk yadda kikeso dashi".

"Sai nasa yayi nadamar haihuwarshi da akayi,sai na sakashi yayi nadamar sanin kayan maye da yayi a dukka rayuwarsa" Mammina ta fadi tana nunashi da yatsa tana jin kamar ta cinna masa wuta.

Komai nata ya tafi,tarin burika na shekaru masu yawan gaske,kudaden da batasan lissafinsu adadinsu ba data dauki shekaru tana batarwa,har kuma yanzu da take tsaye cikin wannan qasaitaccen gidan data siya da nufin gidan iyayen almaz dinne.

"Ku killaceshi mafi munin killacewa" Abinda ta gayawa tamim kawai tana riqe da hannun tafisu suna takawa a hankali suna ficewa a gidan.

Wani shu'umin murmushi tamim ya saki,dama wannan damar yake jira. A irin izza da girman kan da almaz ya dinga gwada musu a kwanakin baya kamar ubansa wani ne,yana ji a jikinsa a yanxun sai ya fanshe komai,sai ya sanyashi yayi dana sanin basu umarni cikin izza daya dinga yi a kwanakin.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862
Chapter 67 · 0% Book details