← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 101

Sashe 23

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tsaiwarku a nan kuskure ne,kuma hadari ne,don lokaci ne na hana zirga zirga ga kowanne mazaunin cikin fada.......idan lokacin dawowarta yayi kowacce hanya zata kasance mata a bude.....muje ciki zan saita hakan" Tamim ya fadi sannan kuma takunsu ya dadu alamun dukkaninsu suna komawa ne ciki.

Wani irin mamaki ya hanashi motsawa daga gurin har zuwa shudewar wasu mintuna daya tabbatar ba za'a samu wanzuwar kowa a gurin ba,koda me jira da bibiya ne sannan ya ciro jikinsa daga gurin yana takawa a nutse yana nufar katafaren ginin masarautar dake gabansa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/12, 20:06] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE PAGE 21*
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________

Kenan ba mutum daya ba kawai.....ba kuma mutum biyu ba,akwai qarin wasu mutanen dake jin da amfani da yaren oromo?.

Yana takawa a nutse amma yanason tantance waye asalin TAMIM cikin mamallaka sunan guda biyu?. Suna ne baqo da ba kasafai aka fiya sakashi ba cikin qabilar oromo......tabbas dole akwai mamallakin sunan na asali.....akwai wanda kuma ba asalin sunansa bane.

Cikin kulawa ya zagaya ta shiyyar da yakan koma cikin gidan. Ya tarar da HILAL tsaye bakin qofar cikin shiga ta masu tsaron qofar kamar yadda suka saba tsaiwa da kuma sanya suturarsu,ya dage masa qarfen tsaron da akan rufe qofar cikin matuqar girmamawa yana bashi hanya. Hannunsa kadan ya motsa alamun yabawa hilal da jinjina yana wucewa cikin gidan.

Kansa tsaye ya wuce sashensa yana qoqarin jingine tunanin don bibiyar beno akan aikin daya turashi. Agogo ya kalla,zuwa sannan ya tabbatar beno yana dab da isa gurin indai ya isa akan daidai lokacin da ya tsara masa,don haka ya qara sauri yana murza key ya buda sassan yana shiga yana motsa labbansa da sallama.

Saman kujera ya hangeshi,abdii ne kwance rigingine,ya kife wani littafi saman qirjinsa da alamu suka nuna yana tsaka da karantawa bacci ya daukeshi.

Can qasan ranshi yayi murmushi wanda sam bai nuna ba koda saman labbansa,ya taka a hankali ya zare littafin yana ajiyewa gefe.

Ko yaushe abdii yana maida kansa yaro saboda shi. Koda yaushe abdii baida zuciya indai a kansa na,baya fushi sam,ko me zai gaya masa don yayi nesa dashi kaman yadda ya buqata baya yarda da hakan,baisan wanne irin qauna haka yake masa ba. To amma a irin wannan yanayin da al'amura suka fara bayyana kansu sam bayason abdii din ya cika kusanci dashi.

Gefan qafafunsa ya tsaya ya miqa hannunsa kadan ya tabashi,sai ya bude idanunsa kuwa da sauri.

"Ka koma ciki ka kwanta" Yace masa kawai yana haurawa sama idanunsa kan agogo yana ci gaba da lissafa lokaci.

Kayan jikinsa ya zare bayan ya samu signal na beno,ya kuma musanyasu da wasu farare qal din pyjamas masu dogon hannu da tsananin taushi. Wani irin kyau yayi duk kuwa da cewa ba tufafi bane na ado,sassalkar sumarsa ta kwanta luf saman kansa ta kuma dan hargitse kadan garin sanya pyjama din jikinsa,sai ya qara fita ya duba ma'ajiyar coffee dinsu,ya sameta cike da zazzafan coffee. Yana da sauqin kai a abubuwa da dama,da kansa ya zuba cikin wata qawatacciyar tea pot.

Sosai balcony din ke masa dadi,wannan ya sanya ya taka zuwa ciki dauke da tea tray din,ya kuma dora saman wani stool dake da wata zagayayyar sofa me taushin gaske.

*AKHNAN*

Tafukan hannayenta duka biyun ta shafa saman lallausar fuskarta data haska cikin rolling din dake saman kanta,wanda ta yishi da mayafin after dress din jikinta data sanya saboda sallar isha'i da tayi yau a makare.

Duka yau din bata iya tsinana abun arziqi ba,tun bayan da sukayi magana da mammina akan gobe zata gabatarwa da sultane mijin data zaba. Zataje ita daya,ba zata mata rakiya ba wannan karon,fuskarta kuma ba zata bayyana ba,don magana ce tsakanin uba da d'iyarsa.

Tana jin nauyin sultane har cikin jininta na yadda zata iya kallonsa ta gaya masa ga mijin da ita take so ta aura,ga kalar zabinta. Mijin da ko sau daya taqi yarda taga koda hotonsa.

Maida idanunta tayi ga aisa dake kwance rub da ciki sama gadonta,yau haka kawai tayo qaura ta taho dakinta kwana. Ta taho da dukka ayyukan sahel couture tace a nan zatayi,wai ko hakan zaisa hankalin akhnan ya koma ga kamfanin. Tun dazu take aikin tana kuma mita.

"Komai na enterprise ya tabarbare.......komai baya tafiya akan tsari da doka,kina wasa sa shugabancinki,komai yana shirin lalacewa,iya abinda zamu iya riqawa nida shehnaz munyi......mammina ta kasa aiwatar da komai akai,ban sani ba,tsananin yardar data bawa mutanen ne ko kuwa?" Aisa ta fada da gasken gaske tana hango downfall na kamfanin. Tana gano yadda wani taqi kadan ya rage kamfanin yakai qasa warwas,ta soma jin kishin wahalar da sukasha a kamfanin,ta soma jin ANYA BA ZATA KARBA ba kamar yadda mammina ta fada?.

"Ta rayuwar me sahel couture din ake yanzu haka........idan sahel ta fadi dasa hannunki a ciki......mammina tace ki karba saboda tasan a yanzu banda energy din komai amma kin wofantar......ki daina complaining min komai aisa" Ta furta tana miqewa daga saman abun sallar. Iska me kyau takeso ta shaqa sama da wadda ke cikin dakin ko zatayi tunani me kyau,saita ware rolling din,saidai bata sauke dankwalin duka a kanta ba,ta doshi qofar da zata sadata da private bedroom balcony dinnata.

Da kallo tabi akhnan,ba wani abu da yake daidai a yanzun a tare da ita da gaske ne........tana jin kawai zata karba......zatayi accepting,ba tare da TUNANIN KOMAI BA ta soma rubuta doguwar wasiqa me dauke da sharhin karbar office din akhnan din a madadinta wadda za'a sanar da kowanne department.

A hankali take takawa a cikinta tana zuqar fresh air din da kyau tana aikewa hunhunta,ta kama dankwalin da kyau cikin jikinta tana curewa guri daya saboda sassanyar iskar dake kadawa wadda keda dan qarfi kadan kadan. Gaba ta matsa jikin qarfen da ya yiwa gurin qawanya ta sanya hannunta ta dafeshi tana duban qasan stairs din daya kasance wata farfajiya dake bayan gidanta da takan zauna lokaci lokaci.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Iska ta fitar sirirya daga bakinta,tana dan ji a jikinta kamar ba ita kadai bace tsaye a gurin,saidai ta sani,ba wani mahaluqi daya isa ya tsaya a inda take tsaye a lokaci irin wannan idan ba aisa ko shehnaz ba,wanda dukkansu ba daya daga ciki. Ido ta lumshe sannan ta budesu tana jin wata kewa tana ratsata,a wasu watannin baya da suka shude,ba wani abu da yake bata nishadi irin wannan lokaci. Tana jin dadin tsaiwa a wajen,tana jin dadin irin iskar da gurin yake bayarwa,tana kuma sake samun cikakken nishadin da tunda ta tashi a rayuwarta nishadin kawai ta sani,batasan wani abu waishi baqinciki qunci ko bacin rai ba,sai a wadannan kwanakin,sai a wadannan lokacin da aka hana rayuwarta da tunaninta sakat akan 'YA'YA MAZA!.

Yunqurin shigarsu rayuwarta kawai yana neman gigita mata rayuwa,ina ga ance yau gasu cikin rayuwartata?.......da dukkan qarfin ikon da zasu mallaketa su kuma sarrafata?.....ita ta dade da fahimtar sam BA ALKHAIRI ciki wannan halittar a rayuwar mace me gata da 'yanci irinta.

Siririn tsaki taja tana dauke idanunta daga qasa tana dawo dashi sama saboda wannan kalar qamshin da take jiyoshi kamar nesa kadan da ita. Kai tsaye kuma idanun nata suka sauka a kansa,sanda yake tsaye gaban nasa qarfen balcony din,ya maida hankalinsa sosai ga wayar hannaunsa yana dannata da wani irin sauri kamar me wasa da abun wasan yara saboda tsananin haddade mazauni da muhallin kowanne keyboard dake fuskar wayar.

Beeno yake maidawa amsa da sauri gudun faruwar kowanne kuskurd,ya fadi masa kada ya sake yayi magana dashi saidai ta hanyar tura saqo,yaci gaba da zama a gurin kuma har zuwa sanda zasu tabbatar ba fita ko motsin wani,sannan yanaso ya yiwa gurin alama......gobe akwai na'urar da yakeso su sanya a gurin.

Tsaiwa yayi cak bayan ya tabbatar saqon yaje,sai kiran omar ya shigo masa,abinda ya sanyashi daga kansa daga kallon wayar ya karata a kunnensa wannan. Shuru yayi manyan fararen idanunsa suna dan juyawa kadan,kafin a nutse ya motsa kyawawan labbansa da dumin coffee din daya fara sha ya sake sanyasu suka zama masu laushu,color dinsu kuma ya fita sosai

"Yes...." Ya amsa maganan omari da wani irin calmness da haka kawai yakejin jikinsa yana mutuwa.

"No omari......" Ya sake amsawa yana lumshe idanunsa da mamakin baqon yanayin dake shiga jikinsa lokaci daya.

"Continue observing......don't act yet.....I'II handle it" Ya fadi yana gyada kansa a nutse. Zare wayar yayi daga kunnensa,hankalinsa yana kan device din dake maqale a kunnen nasa wanda yake monitoring motsin beeno da kyau.

"Reduce the noises beeno,motsinka ya danyi yawa" Ya fadi a hankali a nutse yana jj kaman shine a gurin yana sake matsawa gaban balcony din hankali da idanunsa suna kan wayarsa. A hankali ya zare dubansa daga kan wayar yana daga idanunsa a sanda yake sanyata a aljihun wandon jikinsa.......kai tsaye idanun nasa suka zarce kanta,sanda take tsaye cikin wani haushi da bacin rai dake tsirowa daga qasan ranta.

Tana sanye da fararen kaya yana sanye dasu......ashe bayan jubah da jallabiyyar da yake sanyawa har yana da zabin sauya kaya cikin dare haka don ya samu sakewa cikin masarautar da take mallakin ubanta?.......tana tattaki saman farfajiyar data kasance tata ita daya a matsayinta na 'YA GUDA kuma mallakin sultane muhammad hammud......shima ya samu irin wannan chance din a matsayinsa na BAGIDAJEN malamin da ba abinda ya sani sai zallar litattafai larabci da yaren da qila na uwa ne.......sai hausarsa da yake yinta da qyar wadda sam bata mata dadin saurare.
Chapter 23 · 0% Book details