← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 101

Sashe 24

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/12, 20:07] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 22*
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Ta mallaki sashe guda......shima sultane ya mallaka masa sashen daya kasance cikin sassan masu girman daraja cikin gidan. An bashi masu tsaronshi......an wadata shi da dukkan abinda aka wadatata dashi.....to wai shinma mens bambancinta da wannann BAQON kuma DAN CI RANI wanda ya shigo cin arziqin mahaifinta?.

"Morsa safiyya ce sila" Sashen Zuciyarta dake cike da tsanarta ya gaya mata kai tsaye. Ta gamsu sama da dari bisa dari ba,duk wata matsala daga matar yake,duk wani hanya da zata tozarta gami da qasqantar da matsayinta itace a gaba gaba......waishin TA YAYA ZATASO WANNAN MATAR?.....HAR GABAB ABADA!.

Kai tsaye idanunsa suka gauraya guri daya,wanda kafin yakai ga hakan idanunsa suka soma sauka ga sassalkan gashinta da iska ke wasa dashi tana watsashi daga hagun fuskarta zuwa dama. Bata kwanciya da kowanne nau'in ribbon saboda takura,wannan ya bawa iska daman kada gashin nata duk yadda taga dama bayan ta zame dankwalin nata daga kanta zuwa kafadar hagunta ba tare data sani bama saboda tsabar yawan tunani da bacin ran dake cunkushe fal qasan zuciyarta.

Sosai ta kafeshi da dukka kallonta.....wadannan idanun ababen zargi ne a gurinta.....wadannan idanun da take da muradin musu zuzzurfan kallo,wanda ta tabbatar idan tayi hakan tsaf zata iya ganewa da fahimta.....SHINE NA HIPPODROME?.

"SHINE" Wasu lokuta zuciyarta ke gaya mata. Ta tabbatar qaqqarfan haushi da tsanarsa da takej bayan rashin jituwa na cikin jini da jijiya da takeji akan dukka gidadawan malamai irinsa......wanda basu da wani arziqi daya wuce na zama su karantar da takarda.....akwai wani kwantaccen abu na daban kuma daya qara assasa hakan.

A yau tana jin zata zurfafa kallon wadannan idanun da batasan me ya banbantasu da sauran idanu ba .......duk da kaifin da takeji yana shigarta.....duk da kaifin da takeji kamar suna dashi,shigen kaifin da takanji cikin idanun sultane wasu lokutan da suke hanata duban sultane din kai tsaye a yawancin lokuta.

Duk da 'yar qaramar tazarar dake tsakaninsu amma hakan bai hanashi hangen tsananin IZZA da GIRMAN KAI gami da TSIWA me qarfin gaske cikin idanunta ba,ya barta ne taci gaba da duban qwayar idanunsa kaman yadda ya fahimci muradinta kenan......kamar yadda ya fahimci tanaso ta karantashi ne ta idanun da yayi imanin koda shekara guda zasuyi tsaye a gurin ba zata iya karantar duk abinda takeson ta karanta daga gareshi ba......sai idan shi yaso......sai idan shi yaga dama ya buda mata hakan.

Duk wani motsinta na binciken abokin tseren wasanta yana da masaniya akai.....zuwan tamim na qarshe....wanda shi ya yarje su bashi gwajin tsahon da komai nasa. Yayi hakanne saboda yana son tantance zurfin kwanyarsu,yana son gane zurfin tunaninsu da tsinkayensu,amma sai yaji duka ya rainsu da wannan gwajin ya kasa kaisu inda ya kamata ace sunkai.

Har gwara ita yana mata kallon mace me rauni ta kowanne fanni,amma ga tamim fa?,da yake cikakken namiji daya zama amintacce a wasu kebantattun ayyuka na musamman cikin gidan?.

Damqe qarfen tayi da kyau tana qwararawa kanta gwiwar ci gaba da kallon tsakiyar qwayar idanunsa a sanda taji wani abu me haske yana ratsa cikin idanunta,yana soke duk wani confidence nata.......a sanda take hangen kallon da yake mata da bai nuna komai ko wani yanayi na ita din ta masa kwarjini ba kaman yadda ta saba yiwa kowa da zai kalli idanunta haka kai tsaye a gurare daban daban,wani irin calmness duba yake mata don qure qarfin gwiwar da takeji tana dashi.

Da wani irin mugun sauri kamar numfashinta yana shirin qwacewa daga hunhunta ta kauda fuskarta gefe tana sauke wani kalan numfashi me tsananin nauyi. Sai ya janye idanunsa shima daga kanta yana sake fiddo wayarsa a nutse abinsa saboda duba mintunan da beeno ya shefe ba tare da ya sake jin motsinsa ba kwata kwata.

"Me yasa na kasa?" Ta tambayi kanta.

"Me yasa yake kasancewa a duk inda bana buqatarsa?" Ta sake tambayar kanta a wannan karon baqinciki da bacin ran yadda ta gaza ci gaha da dubansa yana mamaye Zuciyarta. Bata samu sakamakon komai ba,sai rikicewa da kokwanton SHINE?....BASHI BANE da Zuciyarta ta sake afkwa a ciki.

Sake matse qarfen tayi da hannunta tana sake jin baqinciki da sabuwar tsanarsa tana ratsata. Ta kasa Karantarsa ta cikin idanunsa,ta kasa gano komai.....me yasa?.

"Are you on the line?" Ya tambayi beeno muryarsa can qasa.

"Yes obbo.......inajin ba zamu qara minti takwas ba a gun.....naji kaman akwai alamun koda kowanne lokaci za'a iya fitowa" Kai ya jinjina.

"Good.....use silent device kayi snapping min pictures na wadanda suka fito......shut the flash and sound"

"Yes sir" Ya fada cike da girmamawa. Katse wayar yayi,daidai sanda yaji muryartannan da yawancin lokuta tana zuwa kunnensa ne da sautin tsiwa tana fadin.

"Masarautar mu tana da doka......tana kuma da qa'idojin da bai kamata a dinga yawo barkatai a cikinta ba a dukka lokacin da mutum yaga dama......wasu suna da buqatar sirri sosai......da janye sanya idanu a kansu". Shuru yayi yana dubanta duba na kai tsaye. Yana hasashen inda a jimma ne......inda a Ethiopia ne lallai sai wannan attitude din nata na tsiwa ya sauya.

shirunsa ya haifar mata da kokwanton daya tilasta mata waiwayo ta dubeshi,sai ta sake kawar da kai.

"Har yanzu baka haddace dokokin rayuwa cikin masarautar agadez ba.........idan kanason tsira da idanunka lafiya ka guji kallon gimbiya akhnan haka kanka tsaye babu ko martabawa da girmamawa bare rusunawa". Baisan wani siririn murmushi ya kubce masa ba,yayi qasa da idanun nasa bawai don cika umarninta ba.....aah....saidai yadda namakinta ya sake cikashi.

Tana rayuwa a wannan 'yar qanqanuwar duniyar tata ba tare da tasan cewa duniya ta cika da manyan masarautu ba......duniya ta cika da manyan sarakuna dake da tsananin girma qarfi da tasirin da inda a zamanin yaqe yaqe ne loma guda zasuyi da masarautar tata da abinda ke cikinta. Wani sashe na fadar aba jifar ya tuna......wanda ba kowa a ciki.....wanda yake yashe cike da kayan alatu na alfarma da ake sauyawa duk shekara......amma ba kowan da zai zauna a ciki duk tsaruwa sa tsadar abubuwan daya qunsa.....muhallin da ya kusa girman sassanta da wanda yake ciki da wanda iyayenta mata biyu dukka suke ciki.

"Wanda ke buqatar sirri da wanda ke cikin nutsuwa.....mutanen da qirjinsu bai nauyaya sa zuzzurfan tunani da tsoron rushewar gobensu ba.....a irin wannan lokacin suna cikin dakunansu kwance suna bacci cikin cikakkiyar nutsuwa" Yayi maganan da wani irin salo da harshe da ya sake sanyata kallonsa a sace a karo na biyu.

Kansa ya daga shi kuma yana duban taurarin dake sararin samaniya,ya rage duban nasa kadan yana sake motsa kyawawan labban nan.

"Duk wanda shimfidarsa ta gagareshi......tabbas damuwa da neman mafita dole ya watsoshi waje". Wani iri shock taji ya kamata,wata irin tsarguwa ta saukar mata.

Damuwa da rashin mafita?.....anya baisan komai ba?,baisan abinda yake faruwa dama wanda zaya faru gobe ba?. Wani irin fargabar rasa izzarta da girmanta ya sanyata lumshe idanunta sannan ta budesu. Zaya zame mata babbar barazana da abun kunya indai har sultane ya gama sanar dashi komai. Bataso bata kuma barin abinda zai taba izzarta sam,bata bada qofar gano lagonta,don haka ta sake maida dubanta kanshi cikin wani irin fushi,dai dai sanda yakai cup din coffee dinsa bakinsa hankali kwance idanunsa cikin cup din yana duban abinda ya rage bai shanye ba.

"Ka sake da yawa cikin masarautar nan" Ta furta tana jinjina kai bacin ranta yana bayyana muraran saman fuskarta. Baikai ga sauke cup din ba wata iska me qarfi ta taso ta yaye dankwalin kanta gaba daya,bata kuma direshi ko ina ba saikan fuskarsa ta lullube idanunsa harma da cup din coffee din da yake sha.

Tsaiwa yayi cak da hadiyar coffee din,lallausan qamshin dake jikin dankwalin ya soma shigewa hancinsa sosai. A hankali ya saka hannunsa guda daya ya yaye dankwalin,riqeshi yayi a hannunsa yana dubansa kafin ya maida idonsa kanta.

Duba yayi mata irin na dazu,normal duba ne amma sai takejin kamar wannan kallon da yayi mata yasha banban da wanda yayi mata dazu. Wani irin nauyi taji yana cikata,sai take jinta kamar tana tsaye a tsakiyar waje ne dake da tarin al'umma ba tare da cikakken kallabi ko hijabi ba,duk da yalwatacciyar after dress din dake jikinta wanda a qasanta wasu lausasan riga da wando na bacci ne kalan farare suma.

"Subhanallah" Ya fada a hankali yana zare idonsa a kanta,gashinta wuyanta dama saman qirjinta dukka sun bayyana,duk da yadda take hade jikinta guri guda dashi baisan meye ma'anar hakan da takeyi ba. Jira take ya cillo mata dankwalin amma tana jin girman kai da izzar tambayarsa,saita ci gaba da hade jikinta guri daya kawai fushi yana sake mata tasiri da tunzura Zuciyarta.

Takowa ya sakeyi a nutse zuwa gaban qarfen balcony din,zura dankwalin ya soma yi ta cikin qarafunan.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Bama wanzuwa a gurbin da ba'a gayyacemu ba......kaman yadda bamu aminta da fita cikin dare ba idan ba damuwa ce sila ba......"

"Wannan ba abinda ya shafeka bane" Ta fada da hanzari saboda zuwa yanzu tana jin kamar yasan komai daya shafeta,kamar yasan dalilin fitowarta,ita kuma ba abinda tafi tsana a duniya irin kasan weakness dinta.

Cak ya tsaya bayan ya kammala dauren mayafin daidai sanda ta fadi ba damuwar tasa bane,sai ya daga shanyayyun idanunsa da zuwa yanzu suka sake janyewa ya zube mata su.

"Na sani" Ya fadi kansa tsaye,sannan ya juya da wata irin nutsuwa ya kwashe tray dinsa da wayarsa yana takawa cikin ginshirar nan tasa yana wucewa.
Chapter 24 · 0% Book details