← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 101

Sashe 28

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da farko ta dauka iya wannan kawai shine dalilin da ya sanya ta fara jin rashin jituwa a kansa,sai daga bisani ta fahimci KWARJINI yake mata......yana da tasirin IZZA cikin jininsa,wanda ta saba kowanne malami ma da yake cikin masarautar neman gindin zama yake a gurinta don ya samu karbuwa daga sultane......amma shi wannan koda sau daya bai nemi ganawa da ita ba.....hasalima kamar baida labarin komai a kanta.....,kamar kuma baida labarin irin TASIRI da qarfin IZZAR da take da ita cikin gidan gaba daya.

Kwarjininsa da take yawaita gani ya sake dasa mata qatuwar ayar tambaya......yadda yake iya girgiza tsarinta da idanunsa kadai ya sanya takeson sanin komai a kansa,don tana jin kamar ba ordinary mutum bane.

Tunaninta ya yanke sanda tafisu ke shigowa ciki bulama na bayanta. Ya qaraso jikinsa na rawa ya zube a gabanta yana kwasar gaisuwa.

"Ina labari......wanne abune na daban daka samu ganowa cikin aikin dana baka?" Ta fada tana watsa hannuwanta kamar wadda ke jiran ya bata wani abu.

"Allah ya baki tsahon rai......ko a yanzu a bakin aikin nake kika sanya aka nemoni.......bana taba daga masa qafa tun daga safiya har zuwa sanda dare zai shigo......to amma komai da kike zato a kansa ba haka bane.......ba kasafai yake fita ba don baisan kowa a garinnan ba.......yafi zama yayi karatu shi kadai cikin dakin litattafansa. Abu daya ne da zan iya cewa na gani shine,kawai zuzzurfar alaqa ta aminci tsakaninsa da sultane da tsahon shekaru ban taba ganin wanda ya bawa aminci irin haka ba,yana kebewa dashi,daga shi saishi......yana kuma iya bashi ragama r yanke wasu hukunce hukunce da suka shafi lamuran masarauta,harma yana iya cin abinci tare dashi kamar dan cikinsa.....kamar dai yanzun,suna tare da zummar cin abincin safe shi dashi da gimbiya falaak,darensa duka bacci yakeyi,koda sallar dare a farkon dare na fahimci us fiya yinta,yana kwanciya bacci da wuri bai fiya wanzuwa ido biyu ba har zuwa asuba.....na biyu kamar yana da zurfi da kaifin tunani dana hangen nesa......akwai motsi da yawa da yayi wanda ya sanyani a zargin yana ganina koma ya ganni,to amma sai daga baya na fahimci bai fahimci ina biye dashi din ba kamar yadda na zata......yana tsarguwa ne da hakan".

"Indai zai tsargu da ana bibiyarsa kuwa tabbas akwai wani QULLI cikin zuciyarsa.... Wanda ke rayuwa sak baya raya wani zaya bishi.....koda an bishi ma yasan ba wani abu da za'a tsinkayo bare a bankadashi,ka sake kusantarsa kadan......ka kula da takunka da kyau......bana buqatar samun wani akasi ko wani abu na ba daidai ba" Tayi maganar da kakkausan gargadi cikin idanunta.

Qasa ya zube kansa yana maimaita mata shima.

"Ba zaki samu wani akasi ba ko sau daya na Miki wannan alqawarin" Ya amsa kanshi a qasa

"Kana iya tafiya,an sallameka" Tafisu ta bawa bulama umarni,ya yunqura yunqurawar data bayyana tsaho da fadinsa,ya fice a gurin da sassarfa don zuwa ya dora daga inda aikinsa ya tsaya.

"Duk da a daidai wannan lokacin nake sanya ran akhnan zataje gabatar da almaz wa sultane......ina buqatar shiga gurin" Ta furta a fili tana jin buqatuwar zuwa gurin sultane din don komai ya wanzu a idanunta.

"An gama" Tafisu ta fadi tana miqewa don bawa mammina daman shirya kanta.

"Ki nema tamim ki shaida masa.......nan da minti ashirin zan fito,zan kuma ganshi kafin na wuce gurin sultane".

"An gama" Ta sake fada tana rusuna mata sannan ta juya tana ficewa.

Cikin mintuna ashirin da biyu ta shirya tsaf,cikin madaukakin adon dake bayyanar da kalar cikar kamalar izzarta da kuma amsa sunan GIWAR SULTANE. Sunan dake matuqar yi mata dadi,sunan data tabbatar a duk sanda safiyya zata jishi yana haifar da wata susa sai qwarzane cikin zuciyarta.

"Tamim yana dakin baya yana jiranki" Tafisu ta gaya mata sanda ta fito cikin qasaitarta,da zubin taku da yanayin da baka isa ka tsinciki damuwa da firgicin da zuciyarta ke ciki ba tun daga daren jiya zuwa yau din ba.

Ita daya ta isa shiyyar,ta samu tamim din a tsaye,sanye d wadannan kayan dake sake nuna irin girman jikinsa da kuma dacewa da muqamin BAUTA. Ginannen jikin da ka iya razana me shirin kawo wargi.

Bayyanarta ya sanya tamim lanqwasa gwiwarsa ya kuma zube a kansu yana miqa gaisuwa,tamkar yadda dabi'arsa take a duk sanda yake gaban mammina ko gaba wani daga cikin ahalin sultane din.

"Tamim!" Ta kira sunansa da sautin daya tabbatar masa magana ce me tsananin muhimmanci a tattare da ita.

"Ki dade kiyi qarko" Ya amsa mata yana daga kuben takobin dake rataye a qirjinsa.

"Me yake faruwa a Ethiopia?" Ta masa tambayar Kai tsaye,tambayar data sanya shuru ya ratsa a gurin na wucin gadi,kafin tamim ya amsata.

"Komai yana nan kamar yadda yake.....komai yayi bacci,wasu abubuwan sun sume kuma suna dab da mutuwa......ba wani tashin qura ko razanannen motsi da zai farkar ko rayar da wadannan abubuwan" Kai ta girgiza tana duban tsakiyar qwayar idanunsa.

"Banajin gamsuwar haka a jikina......inaso a sake bincika min......idan nace a bincikamin bawai bincike na kwana daya zuwa sati daya ba.......a'ah,bincike na iya adadin kwanakin da komai zai fita da anihin amsarsa.........bana buqatar amsa da gaggawa,sakamako me kyau nake buqata.......sakamakon da shine zai zame mana jagora zuwa tayar da tsohon aiki ayi masa kwaskwarima zuwa sabo......na gaji da wanzuwa akan wasu turbobi da suke tsikarina suna tauyeni.......ina buqatar a kammala shirin komai a kuma kawo qarshen komai,koda kowa da komai zai mutu" Kansa ya kafe a qasa cikin tsananin biyayya.

"An gama" Ya fadi yana cake takobinsa a qasa,ya dogara da ita sannna ya miqe.

*akhnan*

Ta gama shiryawa cikin wani yadi me sauqi dake bayyana asalin qabila da yarenta na cikakkiyar buzuwa gaba da baya,shigar da take sanya ran zata sanyaya zuciyar sultane ya kuma kalli magana da zataje dashi da sassaqan harshe. Tana fatan yadda yake qaunar ganin safeena cikin irin wannan suturar,a yau ya dubeta da idanun da basu da maraba da irin duban da zaiwa safeena din,cikin soyayya qauna da martabawa. Ba mammina a gefanta......amma ta samu qwarin gwiwa me yawa daga gareta.

Ta yita kallon kanta da kanta a madubi,tayita kallon fuskarta a madubin tana juya yadda zata fuskanci sultane yau.....da zabin daya jima yana mata tana wofantarwa.......ta ture nasa muradin.....ta tunkude zabubbukansa har goma sha hudu.....ta kuma zo da nata zabin.

Amma tana ji a ranta akwai daidai me yawa cikin nata zabin data yiwa rayuwarta.....bawai tayi bane don ta watsawa sultane qasa a idanu.....bata yi bane don tozartashi ba.....ba kuma tayi bane don ta nuna masa bai isa ba......tayi ne saboda tattalin kanta da rayuwarta da a nan gaba take da tabbacin zai fuskanci haka duk daren dadewa.

Baya taja a hankali jikinta na fidda sassauyan qamshin turaren kabbasa na kamfanin INCENSE BY KABODAUGHTER daya mamaye ilahirin suturun sawarta,wanda ba wani cikakken motsi da zatayi sai sirrin wannan sirrintaccen qamshin ya fita.
(Tasted and trusted,duk wani turaren wuta da khumras da zaku gani cikin novel dinnan ingantattu ne dana tabbatar da iyawarsu d qwarewarsu fiye da yadda kuke zata +2348032119803).

Birra kawai ke take mata baya,suna tafiya a nutse har zuwa sanda daya daga cikin wayoyinta dake hannun birra suka dauki tsuwwa. Cikin girmamawa ta matso dab da bayanta da zummar mata bayani,bata barta tace komai ba ba tare data waiwayo ba ta daga mata hannu

"Ko waye ki daga ki sanar dashi bazan iya daga kira ba a yanzun" Komawa tayi da baya,neesha ce ta kuma shaida mata abinda akhnan din tace. Batace da birra komai ba sai da suka kawo gabar da iya matsayin birra kenan kuma dole ta koma.

"Ki sake kiranta ki gaya mata,duk wani damuwan office tayi maganan da aisa,idan bata sameta ba shehnaz". Sannan taci gaba da takawa a nutse kamar wadda ke irga adadin takun da zata iyayi.

Da lallausar muryar nan tata dake da wani irin value da tsada gami da wahalar ji a kunnuwan maza da yawa tayi sallama,sallamar da bata bada wani sauti me yawa ko qarfi ba,amma ta bawa dukkan wanda ke cikin parlor din damar jin siririyar sallamar,ciki harda sultane dake zaune saman wani tattausan kilishi na daban yana fuskantar falaak da kuma haisam dake zaune saman wani kilishin na daban,gabansa shiryayye butar shayi ta wani nau'in qasa da tab'o da aka sarrafa me tsananin riqe zafi saboda gidan sarauta irin wannan.

Tea set ne da sultane ke ji dashi sosai,wanda ita daya a duniya ya iya mallakawa irinsa saboda girma da zurfin soyayyar dake tsakaninsu.

Ya tanqwashe qafarsa cikin nutsuwa,har kana iya hangen lallausar socks din qafarsa,duka hannuwansa biyu riqe da wayarsa yana sarrafata,don ba kasafai ya fiya son aza hankalinsa akan abinda bai shafeshi ba.

Magana ce tsakanin 'ya da mahaifinta,changing course falaak din ke sonyi kai tsaye zuwa bangaren qur'anic science.

Cikin sanyin murya take bawa sultane hujjojinta,saidai can qasan muryarta shi ya dago wani abu da sultane din bai hanga ba. Saidai baice komai ba,don yana ji a ransa na huruminsa bane.....bai shafeshi ba.

Hasalima ba komai yakeson sultane yaci gaba da sanyashi a ciki ba......don zamansa temporary ne,baya son sultane din yayi mugun sabon da rashinsa a kusa zai iya zame masa matsala da kuma damuwa.

A karon farko idanunta suka fara sauka a kanshi sanda sultane da falaak duka suke daga kansu zuwa gareta,saidai shi din labbansa ne kadai suka motsa alamun ya amsa sallamar,amma koda gashin idonsa bai motsa ba da nufin daga kanshi har ya sauke dubansa a kanta.

Wani irin abu taji ya saukar mata,zuciyar ta taji tana quntacewa guri guda tana matsewa a qirjinta. Banda sultane ya riga daya ganta.....banda irin wannan ranar yafi dacewa suyi magana da sultane su qare don ta samu daman komaqa Niamey a cikin wannan satin ba shakka da ba abinda zai hanata komawa da baya saboda ganinsa da tayi a wajen

"Me yasa ko yaushe?.....ko yaushe nake buqatar 'yancina?,ko yaushe nake buqatar magana da mahaifina shi din yake kasancewa a gurin?......me yasa na rasa 'yancinnan......wannan matsayin na kebancewa daga ni sai sultane tun daga sanda ya wanzu a masarauta?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar tana jin wani irin bacin rai yana sauka matar gami da gusar da dan guntun freshness din data samu na samun bulalliyar mafita.
Chapter 28 · 0% Book details