← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 101

Sashe 60

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'ai d'ai take takawa tana kallon gidan,da yadda ko ina dokar haisam ke aiki duk da yana kwance baida lafiya. A baya qona mata rai abun yake,amma a yanzun saita saki dariya hankali kwance. Tana wassafa yadda aikinta zai sauka a kansa hankali kwance bayan ta ga tabbatuwar dinkewar alaqa me danqo tsakanin akhnan da almaz. Taci alwashi ta kumayi rantsuwa tabbas saita sanyashi ya kwashe kayansa cikin dare yabar agadez,don ko guduwar tasa bazaya iya bari kowa ya sani ba saboda munin abinda zata sanyashi ya aikata. Da wannan hasashen ta isa sassan akhnan din hankali kwance cikin tarin girmamawa da dukkan hadiman sassan suka zube suna bata.

*AKHNAN*

Kwanaki ukun nan da suka shude gaba daya bata da aiki sai kwanciya,bata da wani aiki sai kebe kanta ita kadai. Bata qaunar wata hayaniya,bata son doguwar magana ko dogon surutu. Kusan salla ce kadai ke tayar da ita,sai wani lokaci da takan bude wani sashe na balcony dinta. Shima ba kasafai ba,don bata son ganin kowa kamar yadda batason kowa ya ganta. An shaida mata saqon morsa safiyya harma da Nannie dakeson ganinta,amma tayi biris da aiken kowa,kamar yadda taqi yarda kowa ya ganta. A yadda take jinta ma gaba daya ko mammina ke son ganinta saidai tayi haquri,kawai tana qoqarin digesting din komai ne,tana qoqarin haqurqurtar da zuciyarta nema tayi accepting wai an daura mata aure......wai ta zama matar aure....mafarkin da take hangoshi da nisan gaske gashi ya cimmata a lokaci qalilan.

Tayi juyi tayi juyi,tayi tsaki har batasan adadinsa ba. Yanzun meye ribar wannan abun da sultane ya tursasa tayi?. Wannan aure da suka dage a kansa meye ne ribarsa?. Ita bata hangen komai a cikinsa sai wata irin rayuwa maras 'yanci,sai wata zallar takura da kashe dukkan burin rayuwa da yake cikin ruhi da gangar jiki. Saita maida idanunta ta lumshe tana qoqarin tsara yadda zata maida rayuwarta daidai kaman yadda take a baya.

Kai tsaye taji an murza qofar dakin nata a hankali,bata wani damu da bude idanun nata ba,saboda tasan koma waye da zai taks dokarta,ya tsallake mata doka to bazai wuce MAMMINA ba.

Bata motsa ba har zuwa sanda mammina ke takowa inda take a kwance. Can qasar zuciyarta tana mamaki,tasan da gaske taji motsinta,ta kuma ji shigowarta,amma bata motsa da nufin tarbarta ba kaman yadda ta saba?. Wani shu'umin murmushi ta saki kawai tana danne zuciyarta.

"Saura qiris ki rasa wannan gatan......saura qiris ki rasa wannan izzar.....saura kadan ki fahimci ke wulaqantacciya ce abar qyama,zaki biya dukkan wani farashi da safeena ta tafi bata biyashi ba". Ta fadi qasan ranta a fili kuma tana zama daidai qafafunta.

"Biftu?" Mammina ta kirata a tausashe. Kamar ba zata amsa ba,sai kuma ta tuna MAMMINA ce fa.....mammina dinta,wadda ke tsaiwa kaida fata wajen farincikinta,sai ta motsa labbanta a hankali.

"Na'am" Ta amsa a hankali.

"Tashi biftu" Shuru ya ratsa kadan,sannan a hankali ta juya tana miqewa,ta zauna sosai hadi da sanya hannunta tana tattare sassalkar gashinta da ya ware ribbon din yayi nasa gurin daban.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/2, 22:22] +234 903 768 6798: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 55*

Sallamar nanay dinne ta sanyashi bude idanunsa a hankali yana amsa sallamar gami da bude idanunshi. A nutse nanay ta miqawa saamee wayar sannan ta yunqura a hankali tana fadin

"Ki sameni a parlor idan kin gama". Kanta a qasa tana jin takun ficewar nanay din,sai ta koma ta zauna sosai saman carpet tana jin qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba.

Muryar nanay yake jiran sake ji,sai yaji muryar saamee ta maye gurbinta da sallamar nan tata cikin yanayinta me sanyi.

Numfashi ya aje a hankali yana amsa mata sallamar,husky voice dinnan nashi ya ratsata ya shiga kunnenta yana motsa wani abu dake boye can saqon zuciyarta.

"akkam jirta obbo(barka da warhaka,kana lafiya yaaya)" Ta fadi a hankali tana ganin kamar xai iya jiyo bugun zuciyarta daga nan inda take zaune.

"Ani gaarii dha,akkamitti?(lafiya nake,kefa?) Ya tambayeta tana qoqarin kwatanta kyautatawa a gareta kamar yadda yasan tana qoqarin yin hakan ga nanay dinsa.

"Alhamdulillah" Ta amsa duk wani sauran magana kuma yana dauke mata gami da tsaya mata a maqogaronta. Wani irin kwarjini yake mata koda a bayan idanunta ne,ta jima da sanin shi din wani irin namiji ne daban da sai zallar sa'a zata sanya mace ta samu damar mallakarsa.

"Makaranta fa?" Yayi qoqarin tambaya don kada ta dauka ya wofantar da qoqarinta.

"Komai lafiya alhamdulillah" Ta furta a hankali,har qasan ranta tana son tambayarsa sai yaushe zai shigo jimma?....don tayi wata muguwar kewarsa,amma takejin ba zata iya ba.

"Ma sha Allah,Allah ya taimaka,nanay fa?"

"Zan kai mata yanzun" Ta fadi a sanyaye,tana sanya rai ne hirarsu ta zarta haka,tana sanya ran maganarsu ta wuce haka,amma sai gashi da wurwuri ya gajarta maganar.

A nutse ta miqawa Nanay sannan ta taka tana fita a parlor din. Nanay ta bita da kallo sanda take sanya wayar a kunnenta.

"Barka da warhaka nanay"

"Barka kade muhammad.....fatan ka yini cikin aminci"

"Alhamdulillah nanay.....komai da kowa lafiya?"

"Lafiya Muhammad,inata tunaninka omar yace wani aikin daban ka shiga,shi ya sanya ba'a samunka" Idanunsa ya lumshe a hankali yana gyada kai,cikin ransa yana jin dadin yadda omar ya boyewa nanay rashin lafiyarsa.

"Na fito alhamdulillah nanay.....ko kin samu sunan abokiyar zaman Obbolettii n ki?" Kai ta gyada a hankali.

"Eh muhammad.....na samu amma da qyar,na rubuta don kada na manta,duk da nasan mantuw tayi kadan ta goge sunan azzalumin mutum irinta a kaina....."

"Meye sunan nanay?" Ya tambaya cikin tattarawa Nanay hankalinsa.

"ZEENATU" Wuta ce ta daukewa haisam na wasu daqiqu,kafin a hankali wani murmushi me cike da madaukakin mamaki ya mamayeshi. Zeenatu a Ethiopia......zaituna a agadez? Ya tambayi kansa da kansa yana kuma sake jinjina kansa.

"Matar ajani da ake zargi ZEENATU.......matar data fidda Obbolettii (sister) dinki daga gidanta ZEENATU.....ba wani alaqa tsakanin mutanen nan biyu?". Dif wuta ta daukewa nanay,tunaninta yana yin zurfi da kuma nisa.

" Ajani ya taba aure shima!.....na shekara daya muhammad kamar yadda safeenata tayi!!" Nanay ta fuusgi kalaman cikin wani irin rudani.

"Good nanay......zan iya samun wani abu game da rayuwar gidan ajani.....kaman ta hannun uwargidansa?"

"Ta rasu muhammad.....sati daya da suka wuce.....amma,bari na kira safuura" Nanay ta fadi tana yanke kiran. Ko ina na jikinta kyarma yakeyi,tanaji jikinta kamar taga Obbolettii dinta har guda biyu,tana jin kamar an gano ind sisters dinta suke,tanajin kamar an gano bakin zaren ne.

Kai kawai haisam yake juyawa a hankali,maimakon bacin rai ya mamayi fuskar nan tasa ma'abociyar Kwarjini,kawai sai wani qaramin murmushi ne yake fita a fuskarsa. Ganin komai yake tarwai.....kowanne lissafi nasa da yake sarqewa a baya a yanzun ya fara zuwa masa da warwara......yan hangen komai kamar an saka rariya ana taceshi.

Hujja daya tak yake nema da zata sake bashi tabbaci itace MATAR AJANI......hujja daya tak da yakejin a yanzu ya shirya shiga kowanne sashe kowanne lungu na masarautar agadez don ya fiddo ta. Idan ya tabbata INA MAKASHIN?.....waye wanda ya aikata kisan da shima yayi batan dabo?. Ta yaya lokaci bayan lokaci suke iya aiwatar da bazaranarsu ga motii aba jifar?,ta yaya?,su waye rassansu?,su waye mataimakansu?.

Yatsunsa kawai yake murzawa a hankali yana sake baje sabon lissafi. Kebantaccen dakin ajiyar mammina.....shi kadai ne abinda ke masa yawo a ransa da kansa....kebantaccen dakin da jikinsa ya bashi tabbacin lallai akwai BOYAYYUN SIRRIKA. TAMIM har guda biyu dake da alhakin kula dashi,da masu jin yaren oromo da yake da lissafin sunayensu yanzu haka fes dama fuskokinsu gaba daya!..

Turqashi......ya zuwa yanzu nasan me karatu yana tunanin KOMAI YAZO QARSHE......QARYA TA GAMA QAREWA......GASKIYA KUMA TA GAMA BAYYANA......SAIDAI NACE KUXO MUJE

MAJI
MA GANI

Maleek ne ya shigo a nutse bayansa daya daga cikin hadiman haisam ne. Dauke da wani kyakkyawan royal tray da aka jera masa qananun bowls masu kyau.

Idanunsa ya zare ya maida kan maleek,shima maleek din shi yake kalla.

"Ina fata wannan aikin ya kammalu?" Tashi haisam din yayi ya zauna sosai yana duban maleek sanda hadimin ya ajiye abinda ke hannunsa yana fita.

"Yadai kusa......inaso na shiga masarauta,yau zanyi kwana uku ko biyu kuma kafin na fito.....ka kira likitan nan yazo ya ciremin wannan abun" Ya fadi yana daga hannunsa dake dauke da Canular.

Kai maleek ya girgiza yana zama saman sofa.

"Amma kasan akwai ragowan drip da zaka sake sha?"

"Ya isheni haka maleek,ina buqatar kammala wani abu dole.....inaso na gama komai qasa da sati daya". Ya amsa masa yana yarfar da hannun nasa,don har yadan fara tasawa saboda zaman allurar na kwanaki a jikinsa.

"Okay " Ya fadi yana lalubar wayarsa don kiran hadiminsa da suke agadez din tare.

*TAMIM*

A nutse ya miqawa almaz alkyabbar data zama sutura ta qarshe da zai sanya a jikinsa,bayan tarin kayan ado da qawar daya fara sanyawa a jikinsa na tsadaddar suturar ALHARIR.

Shi kansa tamim din a yau yana hangen wani irin kyau da biyayya da suturar tayi a jikin almaz din,tamkar dai dama ya saba da ire iren wadannan tufafin a jikinsa. Duk da haka ba abinda ya rage qudirinsa a zuciyarsa,ba abinda ya rage kaifin abinda yakeji a zuciyarsa.....hakanan ba abinda ya sauya daga aikata abinda yayi niyyar aikatawar.

A nutse almaz ya taka cikin wani salon izza da yaji ya saukar masa,ya matsa gaban tamfatsetsen madubin dake ajiye a wani bangare na daban na dakin.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Chapter 60 · 0% Book details