Sashe 27
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin girmamawa da martabawa sultane ya miqe da kansa don tarbarsa kamar yadda ya saba. Yana ganin girma da martabar dattijon basaraken da yakeji a jikinsa akwai abubuwa da yawa da suke boye daga saninsa. Akwai abubuwa masu yawa daya kamata ya sani smma baisan dasu ba,akwai al'amuran da suka yiwa saninsa b'atan dabo da badda bami. Cikin girmamawa daidai da yadda zaiwa motii ya bashi hannu sukayi musaba,murmushi kwance saman fuskar sultane,yana jin wannan feeling din wannan yanayin na tamkar yana tare da dan cikinsa daya rasa shekarun baya AHMAD.
"Bismillah" Sultane ya fadi yana nunawa haisam daya daga cikun kujerun dake kewaye da gurin,wanda dab dasu wata kyakkyawar table mat ce me girma da aka soma zube royal warmers da spoons na cin abincin sultane din.
Kafin su fara tattauna komai akayi sallama daga bakin qofar parlor din. Falaak ce sanye da baqar doguwar riga yalwatacciya sosai,ta kuma lullube kanta zuwa kafadunta da baqin mayafi mahadin doguwar rigar. Duk da kasancewarta me dan duhun fata amma shigar tayi mata kyau sosai,ta kuma fidda sanyin halin da take dashi.
A kansa idanunta suka fara sauka,gabanta ya fadi da wani irin kwarjini me yawan gaske da taji yayi mata. Dan kwanakin da suka tafi hutu kawai na tsakiyar lokacin karatu sai taji kaman ta jima sosai bata ganshi ba.
Ta nema dukkan wani dalili da zaya sa ta ganshin amma kuma babu,yau dinma ba zata ne,bata sanya ran zata ganshi ba,amma hakan sai ya mata dadi sosai.
Cikin tsanaki da nutsuwa take shigowa cikin parlor din,kanta a qasa tana jin wani irin nauyi fargaba da kuma faduwan gaba yana saukar mata.
"Ta kasa zaune ta kasa tsaye.....kada a rabata da dan tsohon babanta ko?" Sultane ya fadi cikin murmushi da salo na tsokana daya alamtawa haisam akwai sakewa sosai tsakaninsa da ita,da kuma kalar qauna da jituwar data banbamta dana 'yar uwarta.
Murmushi kawai ta saki,bata tsaya biyewa sultane yadda ta saba ba,ta qarasa gaban haisam ta tsugunna tana gaidashi.
Cikin girma ya amsa mata,abinda ya yiwa sultane dadi,saboda yanayin ya masa kama da yadda babban yaaya yake daukan girma wa qannensa.
"Abincin ya iso,a nan zan zuba maka bappi?,ko saman table?" Tayi tambayar idanunta akan sultane,amma duka hankalinta yana kan haisam da kacokam idanunsa akan wayarsa suke yana karbar wasu bayanai daga maher na abinda ya faru daren jiya.
"Aah zuba mana a nan,ga yayanki nan ma tare zamu karya dashi" Miqewa tayi a tsanake,duk da yadda takejin qafafuwa da hannayenta suna dan rawa,saboda har yanzu kwarjininsa dukanta yakeyi,abinda ya danja hankalin sultane kadan kenan a kanta,yaci gaba kuma da noticing yadda ta zagaya rukunin kujerun dake gabansu inda table mat din yake tana zuba abincin kamar ba nutsuwa sosai a tattare da ita yadda ya santa.
"Muhammad" Sultane ya kira haisam bayan ya maida dubansa kansa. Qaramin murmushi dake dauke da girmamawa ya saki,yana ajiye wayarsa gefansa.
"Ya mukaji da alhinin abinda ya faru damu a jiya?" Haisam ya fadi cikin girmamawa da son ya fara dora tattaunawarsu a gurbi da muhallin da zai sanyo buqatarsa.
"Mun godewa Allah.....ba wanda ya rasa rai ko yayi rauni me yawa,sai hadimi guda daya da akace shine ya bawa sassan zaituna kariya......ba'a samu rayuwarshi ba sai dazu da safen bayan qarfe takwas saura" Kai haisam ya jinjina,ko sultane bai dora komai ba yasan akan maher yake magana. Maher din yayi aiki me kyau har fiye da yadda ya zata,kuma komai ya tafi daidai da harshi kansa ya gamsu da acting din da yayi. Wannan dalilin ya sanya shi da kansa yake saluting kalar team din da yayi raising da kanshi cikin national intelligence security service. Team ne da babu rago.....babu malalaci a ciki,kalar team din da sai aiki na musamman ake fita dasu KAMAR KUMBO KAMAR KATANTA.....da gaske yadda shugaba ya kasance haka dole mabiyansa zasu kasance,yadda SHEIKH MUHAMMAD HAISAM yake jajirtacce......haka kowanne namiji dake qarqashinsa yake tashi da kalar wannan jajircewar....da kalar wannan qwarin gwiwar....da kuma kalar wannan jarumtar tabbatacciya daga ZUCIYA DA QWANJINSU.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Duk da inaji a jikina lamarin ba wani babba bane......amma zaituna ta tashi hankalinta da yawa......tun jiya har yau qoqarin fahimtar da ita nakeyi ako ina ana iya samun irin wannan yanayin amma bata fahimta din ba.....tadai nunamin damuwarta ba tata bace karan kanta,damuwarta kan mutanenmu ne,jama'ar da muke mulka wadanda suka cancanci samun zaman lafiya da tsaro me kyau qarqashin shugabancinmu". Idanunsa ya lumshe a hankali yana jinjina kanshi sannan ya sake budesu akan fuskar sultane.
Jinjina kansa bawai na gamsuwa da bayanai da sultane ya bashi ba......ba na gamsuwa da abinda mammina ta fada bane......na gamsuwa da cewa lallai matar ta iya buga wasanta yadda ya dace.....lallai ta iya amfani da kowacce kalar dama da zata gifta ta gabanta ne.
"Na fahimci akwai gaskiya cikin kalamanta,don ita daya ce damuwarta ta zama gaba da abinda zai sameta ita a karan kanta.......wannan ya sanyani tunanin irin tsaron da zamu qara cikin gidan nan don kaucewa faruwar irin abinda ya faru a jiya ko wanda yafi haka a gaba".
Komai sai haisam yaga yazo masa da wani irin sauqi da bai taba zata ba,duk da zai wahala ya kafu saman abun sallah ya yiwa Allah naci da neman dafawarsa akan wani abu kuma hakan bata tabbata ba.
"Gaskiya ne,haqqin kowanne shugaba ne ya kula da rayuka da lafiyar mutanensa......don kuwa Allah SWT zai tambayeshi ranar qiyama game da kowacce rai qwaya daya data yaya ta rayu qarqashin mulki da ikonsa" Kai sultane yake jinjinawa kawai,zamansa da haisam yana sake tuna masa girman nauyin dake kansa,wanda koda iya wannan kadai ya rabauta ya isheshi,ballantana kuma zuciya da ruhinsa cike suke da dorewar alaqar tafi haka. Gyara zamansa sosai sultane yayi yana tattara hankalinsa ga haisam
"Yanzu me kake ganin za'ayi?,wacce hanya da shawarwari zamu bi?" Ya tambayi haisam yana so yaji ta bakinsa.
*Mammina*
Ko qiftawa idanunta basu sakeyi ba tun daga lokacin da kunnenta ya jiyo mata babban motsi qararraki da ifce ifce. Daga sanda yalwa ta shaida mata kamar an kawo farmaki cikin masarautar kuma tunda ta sauka daga saman gadonta bata sake hawa kanshi ba.
Ba zatace bata zauna......ta zauna amma yayin da take tahiyar sallah,amma banda hakan,har yanzu da agogo ke nuna sha daya ta gota ba wani data aiwatar na dukka al'adun data saba yi daga safiya zuwa wannan lokacin.
Farmaki ne da aka kawo cikin gidan,farmakin da za'a iya cewa idan ya qazanta kai tsaye ya shafi kowa.......to amma cikin jininta da jikinta takejin kamar an kawo farmakinne kai tsaye saboda ita.......tamkar itace abun hari takai tsaye da aka nufata.
Hankalinta ya tashi qwarai sanda ta kalli maher da yayi kaca kaca da jini......abinda ya sake tabata,ya kuma saka mata shakka kokwanto da rashin nutsuwa me tarin yawa.
Da tafisu ta fara ganawa,don a ranar ba wanda ya smau ganinta cikin hadimanta,don ko wanka ma bata samu damar yi ba don tana jin a yanzu bata wannan take ba. Bata bari matsala ko yaya ta gilma mata,don ta riga ta canfa.....kowacce matsala daga qarama take farawa kafin ta zarce zuwa babba.
"A jiya naji a jikina akwai wani a sanda muka fito daga ganin almaz.......bayan na zargi wani abu kuma saiga wani baqon lamarin da nake zargin ba daga can ya biyo diddigi da sawunmu ba?" Ta furta tana duban tafisu.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 25*
Kai ta girgiza a hankali tana duban mammina.
"Inda akwai wani mahaluqi tabbas zan iya jin dumin numfashinta daga tazarar dake tsakaninmu......ba numfashin wani dan adam ta gurin sam sam......bana tunanin akwai wani daya wanzu a gurin" Kai mammina ta girgiza cikin rashin gamsuwa da bayanan tafisu.
"Lallai akwai wani baqon abu......akwai wani abu daban dake wanzuwa a muhallin da ba nashi ba.....a muhallin da ada babu shi a gurin"
"Akwai shigowar baqi ne masarauta?......ina cewa kin datse duk wata hanya da qofa da zata bawa baqo daman shigowa ko zama cikin masarauta?". Kai ta gyadawa tafisu,amma gefe guda tana zurfafa tunaninta.
"Ba wani sabon baqo da aka sake samu........saidai akwai baqon da yashigo tun kafin wannan lokacin..????" Ta qarasa maganar kamar tana yiwa kanta tambaya ko tuhuma game da haisam.
"Tafisu........maza kiramin bulama" Ta fada a dan rikice. Sama da qasa tafisu ta girgiza kanta alamun girmamawa sannan ta tashi zuwa hanyar fita.
Fitar tafisu tana jin kamar ta jawota ita da bulama din ta tsincesu a gabanta. Ta manta shaf ta bada aikin bibiyar mutumin,ashe tana da tarin hangen nasa har haka ita kanta bata sani ba?.
Samun kanta tayi cike da fatan ta samu wani abu da zaya bata haske game dashi,wasu bayanai da zasu iya haska mata shi......ba shakka idan har haka ta kasance YA SHIGA UKUN DA BABU FITOWA.
Abubuwa da yawa ta dinga hadawa game dashi cikin kanta. Bata taba samun halittar da take ganin kwarjininta sama dashi ba,hakanan kuma zuciyarta da ruhinta sam sun gaza jin aminci game dashi.....gefe daya tana jin wani qaqqarfan rashin jituwa dangane dashi dake zabalbala daga jininta a kansa.
Duk wani baqo daya samu gindin zama ya karbu hannu bibbiyu itace ta karbeshi.....dalili......bata abu a banza......bata aikata aikin da bazata samu yabo ko kwarzantawa ba daga bakin sultane mazauna gidan dama talakawan AGADEZ. Ta buda hannuwanta bibbiyu tana karbar baqi da 'yan gari dama dukka wanda rayuwa ta raunatashi......wannan yaja mata soyayayya farinjini da qauna me tarin yawa daga garesu.....don haka sai taji kamar FADUWA ce ace mutum kamar haisam din daya samu karbuwa a gun sultane da wani yanayi da har yau yake bata mamaki ace kuma SAFIYYA ce silar shigowarsa masarautar ba ita ba.