← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 101

Sashe 54

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin muryarnan tasa dake da nauyi da zurfin daya kutsa har tsakiyar zuciyar akhnan da batako daga idanunta ba tunda ta zauna yayi cikakkiyar sallama. Idanunta ta lumshe a hankali tana jin yadda sautin ya karade hall din,tamkar yana tsaye a gurin,da yadda muryoyin mutanen gurin ke amsa masa can qasa.

Tazarar wasu sakanni ya bada yana qoqarin hada taqaitaccen bayanin da zai gaya musu da yaren abzinawa daya soma koya......shurun daya kutsa can cikin zuciyar akhnan din,a hankali kuma ya soma tilastawa idanunta dubansa.

Fes ta zube idanun nata kan babban allon dake a gabanta. Ya bayyana tarwai har fiye ma da bayyanar da zaiyi a gabansu. Fararen kayan dake jikinsa gaba daya sune abu na farko da zai fara kashema me kallonsa idanu,wani irin kwantaccen kwarjini ne saman fuskarsa da tayi wani irin fresh da fatarsa dake glowing tamkar wani wanda ke shiga gyaran jiki duk wata.

Baqar sumar dake kumatunsa habarsa da qasan hancinsa ta sake fidda sirrintaccen kyan da Allah yayi masa. Uwa uba shemagh din dake kansa daya zauna masa kamar yadda matasan larabawa masu jini a jika kanyi.

Idanunsa da suka dan rusuna kadan saboda ciwon kan da yakeji kadan kadan sun sake zama wani ado me jan hankali a tattarre dashi,duk da rusunawan nasu kuma hakan bai rage hasken da suke dashi da kyansu ba.

Batasan sanda idanunta sunkai kan labbansa ba sanda ya fara sarrafa harshensa da yarensu na abzinawa ba. A nutse yake gabatar musu da kanshi gami da neman afuwa,gami da kuma gabatar da sunan omari a matsayin wanda zai jagoranci taron,sannan ya tura kujerarsa baya,hoton omar sanye da baqar jubah ya mamaye screen din.

A hankali ta zame idanunta ta maida qasa,tana jin wani shuru cikin qirjinta,shurun daya mamaye qirjin da sautin bugun zuciyarta da takeji har cikin kunnenta.

"Me yasa ko a screen ma yake min kwarjini?" Ta tambayi kanta tana jin wani haushinsa yana mamayarta. Ta tsani wannan kwarjinin......wannan kwarjinin dake tattare dashi tayi matuqar tsanarsa. Bai kamata ace yana da kwarjini har irin haka ba,baida mulki ko sarauta don me zaiyi kwarjini sosai?.....har ya zama wani abu dake ratsa tsakiyar izzarta?.

*HAISAM*

A hankali yake takawa shi kadai yana dawowa sassansa,can qasan zuciyarsa cike da mamakin yadda yakejin zuciyarsa wani iri cike da wani yanayi maras dadi da baisan me ya haifar dashi ba.

Shamagh din kansa ya zare a nutse yaa ajiyewa gefansa bayan ya nutse sosai cikin sofa yana relaxing bayansa jikin kujerar da yake zaune akai. Idanunsa ya lumshe,a hankali yana zuqar iska sosai yana fesarwa a hankali. Ya jima a haka kafin ya bude idonsa yana furta.

"Subhanallahil azeem" Sai ya miqe ya zauna sosai. Yanayin da yakeji a jikinsa da zuciyarsa wani irin yanayi ne da yakanji idan yana kewar wani abu,musamman ma nanay,wannan ya sanya ya yanke shawarar kiranta,ko wataqila zuciyar nanay din take muradi.

Dab da zata tsinke aka daga kiran,nutsatsiyar fuskar matar dake cike da kamala da nutsuwar da tunda ya tashi a rayuwarsa yasan nanay din da ita ta bayyana.

Murmushi sosai ya wadaci fuskarta da ganin gudan jinin nata,saidai a kallon farko kadai da yayi mata ta cikin siririn farin gilashin idanunta ya fuskanci wata qanqanuwar kwantacciyar damuwa a tattare da ita ba.

Wani irin mutum ne me baiwar kulawa da duk wanda yake rayuwa dashi. Yakan damu da damuwar wasunshi,ko yaya damuwa take a tattare da kai yana iya fahimta daga kallon farko,muddin ya kalli qwayar idanunka,musamman ma mutum me matuqar muhimmanci a gurinsa irin nanay din.

"Ina cikin maganarka a raina saiga kiranka ta hannun noorah". Ta fadi bayan ya gama gaidata cike da qauna da kuma kulawa cikin asalin harshen oromo me zubi da yaren fulani a Nigeria.
Murmushin ya danyi kadan yana qoqarin danne harbawar da kanshi keyi.

" Me ya samu nanay dina yau?" Ya furta a tausashe idanunsa a kanta.

"Yau ta tuna ne da obboleetti abaayo" Siririyar muryar noorah ya shiga kunnensa.

"Noorahty" Ya kira sunanta a hankali,abinda ya sanya yarinyar matsowa kusa da camera tana murmushi.

"Captain obbo" Ta fadi tana murmushi gami da daga hannunta alamun saluting nasa. Maida mata shima yayi kafin ta soma gaidashi da yaren oromo.

"Kina kula da nanay kuwa nurahty?" Ya tambaya da salon kulawar nan tasa.

"Sosai......amma yau har qwalla nanay tayi,har hoton obboleetti abaayo ta dauko" Ta fadi qasa qasa tana saukan da camera din kan hoton.

Shuru yayi yana qurawa hoton idanu kamar yau ne karon farko daya soma ganinsa. Hoton sam ba baqonsa bane,tsahon shekarun da yayi wayo a duniya yake ganin hoton,amma yau daya sai yaga hoton ya zama sabo a idanunsa. Yau daya sai yake ganin kamar yasan fuskar dake cikin hoton.

"Noorahty" Ya sake kiranta a hankali

"Eeyyee obbo(na'am obbo)"

"Suuraa naannessaa(juya hoton nan)" Ya fadi hankalinsa yana sake kaiwa ga hoton.

Yadda ya buqata haka tayi masa. Cak ya dakatar da komai ya zubawa hoton ido yana kallonsa,duk sai wani jijiya ta jikinsa yaji kaman ta tsinke. Kamar yasan fuskar,sani kuma na kurkusa ba na nesa ba......kamar akwai inda yake ganin wannan fuskar lokaci bayan lokaci.

"Akhnan" Sunanta yazo ya tsaye masa a rai,abinda ya amsa kuwwa har cikin zuciya da kunnensa.

"Ina nanay?" Ya tambayi noorah. Sai data waiwaya ta kalli bayanta sannan ta bashi amsa.

"Gata nan ta fito daga toilet,alwala tayi" Kai ya gyada a hankali.

"Idan mun gama magana da ita ki dauki hoton da wayarta ki turamin,ki tambayeta idan da wani ma ki dauka duka ki hadomin".

"Me zakayi da hotunan obboleetti abaayo na?" Nanay ta tambayeshi tana karbar wayar daga hannun noorah.

"Ina buqatar labarinta nanay......inaso a wannan karon ki bani labarin abaayo" Dan qaramin murmushi ta saki tana gyada kai.

"Zan baka......amma ka biyoni bashi gobe.....yau din akwai.mutanen da zan rabawa tallafi,suna zauren jira suna jirana". Kai ya jinjina a hankali,ya qara da tambayarta motii.

"Ya shiga hidimar al'umma sosai kwana biyu,baya zama sosai,akwai qananun qauyukan da yaketa zuwa duba mutanensa" Dan shuru kadan haisam din yayi,ya sani koda ya hana motii yace ya sa ya wakili bazaiji ba,shi kuma a wannan qadamin da ake kai yana buqatar yawaitar zaman motii dinne guri daya maimakon zirga zirga,har yanzu bai amince da safety dinsu ba,duk da tarin jami'an tsaro harda na farin kaya dake tare dashi wanda shi kansa motii din wasuma baisan suna biye dashi ba.

"Allah ya tsare,a miqamin gaisuwa kafin na samu layinshi,Allah ya tsare"

"Allah yayi maka albarka duniya da lahira,ya tsareka daga dukkan sharri". Nanay ta fadi cikin jin soyayyar yaron nata. Baiwar haihuwa ta farko data samu,kuma ya zame mata baiwa ta gasken gaske.

"Idan na kira gobe zanyi magana da rumaisa da anani.....su zama a kusa"

"In sha Allah" Nanay din ta amsa cikin tsananin kulawa. Saboda yanayin aikin sai ya kasance shi daya ke kiya kiransu,ya tsara hakanne kuma saboda tsaro a garesu gaba daya.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

★Cikin wani irin salo gami da qwarewar da basu taba ganin irinta ba a yau karon farko yake gabatar da khudubar sallar juma'a a babban masallacin agadez me tsohon tarihi.

Kyakkyawan matashin me zubi da kamanni da BUZAYE kuma ba'anzine SAK!. Wanda ke sanye da cloak robe me daukan hankali fara tas da kuma ratsin adon zaiba,kamar yadda yayi amfani da kuwaiti thobe(jallabiyya zubin saqa da adon qasar Kuwait) fara qal itama me wani irin sulbi da daukan hankali,hakanan shill shamagh din dake kansa dan asalin qasar Kuwait daya yafashi saman kyakkaywar maroccon cap din dake kansa ya sake qarawa fuskarsa wani irin kwarjini na daban.

Yadda khudubar ke shiga zukatan al'umma da yadda sheikh haisam din yayi musu wani irin kwarjini da yanayin tsakanin burgewa da samun matashi me tarin ilimi haka wanda haskensa ya bayyana,yanayin ya bayyana akan duk wani wanda ya halacci masallacin da zummar yin sallar juma'a a masallacin,gami da shaida daurin auren diyar sultane din,gudan jininsa da mutane da dama suka gama saddaqarwa cewa ba'a haifi mijinta ba a duniyarmu ta yanzu.

A cikin jikinsa yakejin hucin zazzabin yana ratsashi,abinda ya sanya hudubar zafafa sosai da wani irin husky voice data qara kaifi sanadin madaukar sauti masu kyau da masallacin yake dasu,take kuma watsa sautin har cikin gidan sultane har kuma kunnuwan mutane irin akhnan da mammina,wadanda zukatansu ke dauke da mabanbamtan burika da kuma tsammani.

A nutse ya kammala huduba ta biyu,sannan ya sauka daga saman minbarin da wata irin nutsuwa yana fuskantar alqibla sannan ya tayar da sallah.

Cikin wannan sautin.....wannan muryar wannan qira'ar dake kamaceceniya da muryar sheikh afif taj sautinsa ya fara karade masallacin,yana kuma saukar da wats irin nutsuwa a zukatan mahalarta sallar. Ba iya su kadai ba,hatta da akhnan dake kwance cikin kebantaccen dakin tana iya jin sautin tar,ta maida idanunta ta lullube sautin yana sauka saman zuciyarta duk da yadda taketa qoqarin hana kanta hakan.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/30, 19:53] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 49*

Wata kalar nutsuwa ce da batasan daga inda ta sameta ba take ratsa zuciyarta,duk da yadda taketa kokawa da kanta wajen hana kanta da kanta sauraro ko jin dadin sautin karatun nasa.

A nutse ya sallame sallar,yana jin yadda jikinsa ke sake daukan dumi sosai da wani irin weakness. Ya waiwayo cikin girma da dattako yana fuskantar manyan mutanen dake fada aji a agadez da sukayi sallah a bayansa ya soma musabaha dasu kaman yadda ya saba yi a jimma.
Chapter 54 · 0% Book details