← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 101

Sashe 77

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akwai kusan mintuna talatin zuwa arba'in da suka rage kafin cikar lokacin ganawarsa da morsa safiyya din. Yana ankare da lokacin,yana qiyasce yana kuma lissafe. Yana jin wani girmamawa daga qasan zuciyarsa dangane da ita,yana jin bazai qara mata koda minti daya ba cikin mintunan da ya kamata ace sun hadun. Wani girma nata yake ji,yana jinta a matsayin nanay kamar yadda musulunci ya shimfida cewa qanwar uwa itama uwa ce. Qanwar uwar ma irin morsa safiyya din,daya tabbatar rayuwarta na zagaye da wasu tarin qalubale,bai sani ba itama ta sani?,ko bata sani ba?,ta fahimta ko nata fahimta ba.

Maleek yana daga gefansa yake ci gaba da duba gidan,ya maida idanunsa kan maleek a hankali.

"Kowanne gidan sarauta ya banbamta da waninsa,saidai akwai gidan sarautar dake binne da tarin sirrika masu nauyin gaske dake dilmiyar dashi sannu a hankali har zuwa wani mataki" Kai maleek ya jinjin a hankali,duk da hankalinsa ma yayi nisa gurin tunani da fatan inama ace zai samu ganin falaak koda daga nesa ne.

Basu kai ga cewa komai ba muryar ta soma tashi,cikin daga murya da rikici yake fadin.

"Ya tsinke haadi....daya daga cikin dawakan ne......bansan me ya sameshi haka ba.....na kasa sarrafashi" Akayi maganar da yanayin daya ja hankalin haisam. A nutse ya dubi sashen da maganar ke fitowa,bargar dawakai ce dake wani kebantaccen guri a gidan. Yasan da ita,amma baisan mallakar waye ba,bai kuma taba shiga gurin ba duk da yadda yake mararin hawan doki,musamman dadewar da yayi bai hau ba a yanzu.

A jininsa yake,yana jin wani iri idan yaga dawakai ko raquma,wani lokacin har cikin kansa saboda tsananin sabo da rayuwa a cikinsu,suna tuna masa da nasa dawakan daya tabbatar zuwa yanzu sosai sunyi kewarsa suma.

Maleek ya waiwaya a hankali shima yana maida hankalinsa sashen da maganan ke fitowa,sannan a nutse ya dubi haisam.

"Kamar fa akwai matsala.....inajin kamar akwai dokin da ya balle.....ina kyautata zaton loosing control ñasa sukayi". A nutse haisam din ya dubi maleek,sai kuma ya zare dubansa daga kansa yana maidawa qofar shigar bargar,ya fara takawa a hankali yana nufar gurin,abinda ya alamtawa maleek shiga zaiyi,miskilancinnan nasu na cikin jini ne kawai bazai barshi ya furta da baki ba.

*AKHNAN*

Zuwa yanzu idan tace ba komai cikin 'ya'yan hanjinta ta tabbatar batayi qarya ba. Ta manta a daidai wanne lokaci......ta kuma manta wanne abinci ne na qarshe daya shiga cikinta cikin salama.

A wannan yammacinne kawai data gama tabbatarwa gami da amannar ba zata rayu ba tare da abinci ba ta amince ta karbi zazzafan ruwan tea din da birra keta mata nacin ta karba tasha din.

Sanye yake da wata cotton gown ta wani irin tattausan material fari qal wanda aka yiwa adon gold d'aid'aiku a jiki. Hade yake da hularsa da kuma yalwataccen cotton din mayafin da tunda birra ta ware mata kayan batabi ta kansa ba. A yau ko hula bata sanyawa sassalkan gashin kanta ba,ta sakeshi ne kawai yana kwance a bayanta wanda tsahonsa yayi kusa da mazaunanta. Abune me wahalan gaske ka samu gashinta a cukurkude ko a yamutse,ko a yanzun ma da take cikin wani irin mode da batasan sunan da zata bashi ba,gashin a kwance yake a gadon bayanta da wani irin glowing da darkness dake nuna kulawar da yake samu,saidai daga gaban kanta yadan tashi kadan,tashin da bai hana kwantacciyar sumar data kwanta daga goshinta har gefunan kunnuwanta bayyana ba.

Fuskarta tayi wani irin haske,tayi fresh sosai,blue eyes dinta haskensa ya sake fitowa qwarai. Kana iya ganin yadda labbanta suka sake sirancewa,labban da basa rabo da kyakkyawan lip gloss ko lip balm.

Wani irin zurfi tayi a tunani,har yanzu tana jin emptiness dinnan a zuciyarta dama rayuwarta gaba daya,har yanzu zuciyarta ta kasa miqa wuya dari bisa dari akan cewa bada taimakon mammina ta tsinci kanta a hali mafi muni da tozarci a tarihin masarautar agadez dana family dinta ba.

Bata zargin mammina da cutar da ita......amma tana zarginta da gaza maida hankali ta zaba mata CANCANTACCE da zata rayu kalar rayuwar da mamminan tasan ta jima tana mafarki,kalar rayuwar da tasan ta jima tana mararinta,RAYUWAR 'YANCI BA QARQASHIN DOKA KO UMARNIN KOWANNE D'A NAMIJI BA.

"Ranki ya dade......akwai matsala....." Taji muryar bushira daga bayanta,abinda ya sanyata waigowa da sauri tana dubanta,zuciyarta kuma na cike da fata da kuma neman tsarin sake jin wani abu da zai kassara farincikin da taketa tattalin dawowa dashi.

Da idanu ta tambayi bushiran,wani yare da sun jima da saba magana dashi da ita da kuma haddaceshi,don haka ba tare da jinkiri ba ta amsa mata.

"Thunder ne ya tsinke.....yace ko zaki iya wani abu akai?,dukka dabarunsu ya qare". Bata tsaya sauraren sauran maganar bushira ba ta dire cup din dake saman d'an plate din da take zuqar coffee din a gaggauce,ta soma baro harabar dake liqe da dakin hutawar tata tana shigowa ciki da wannan zazzaqar siririyar muryartata take bawa bushiran umarni.

"Bani mayafi". Da hanzari bushiran ta dauko mata tana yafa mata,gami da saita mata lausasan takalmanta.

Bata wani damu da boyon kanta da takeyi na kwana da kwanaki ba,kamar yadda bata damu da gaisuwa da kuma kallon da hadimai keta binta dashi ba. Wasunsu kallo ne na gulma da munafunci,ta fito a yau din bayan kwanakin data shafe ba wanda yaga koda qyallin idanunta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Hankalinta sosai yana kan dokin,doki ne matuqar tsada da sultane ya sanya zunzurutun kudade na qasar dubai ya siyo mata shi,ya siyo mata shine kawai a matsayin kyautar kammala degree dinta,ta kuma fita da kalar sakamakon da sultane din yake buri,harma sama da yadda yake hasashe. Takanas tasa aka dawo dashi agadez tun a wancan abun daya faru a hippodrome,tasa ake bashi kyakkyawar kulawa,sai ta qara saurin tafiyarta wanda duka duka baifi takun tafiyar wata macen tafiya ta al'ada ba......bata soma jin nutsuwa ba sai data kawo bakin gurin ta kuma sanya kai kai tsaye ba tare data tsaya sauraren jawabin hadimin data samu a tsaye bakin gurin ba.

Tun daga nesa idanunta suka sauka a kansu,yana zaune saman bayan thunder din,saidai yayi kaman rub da ciki ya riqeshi da kyau. Sukuwa yake faman yi tare da qoqarin kayar dashi,amma cikin wata irin qwarewa yaqi bashi wannan damar. Magana yake masa da dan qarfin da zaka iya jiyowa tamkar yana magana da dan adam. Da dukka jarumtarsa ya sake rungume gadon bayan thunder din da yayi wata irin haniniya yana daga qafafunsa na gaba,abinda sukasan tabbas idan ba gwanin sarrafa doki ba ba abinda zai hana mutum faduwa qasa war was a gurin.

Idanunta ta lumshe,tana jin wata irin matsananciyar faduwar gaba,tana hango yadda thunder zai watsar dashi ya kuma tattakashi yabi ta kanshi ne kawai. Faduwa a doki wani mummunan abune da bata qaunar kalla,saidai kuma yadda taji gurin ya fara nutsuwa ya sanyata bude idanunta a hankali. Ga mamakinta thunder ya fara nutsuwa,still bai sauka a kansa ba yana ci gaba da shafashi a hankali gami da yin magana qasa qasa dashi,har zuwa sanda ya tsaya cak ya daina bige bigen da yakeyi,sai yayi wani tsallae tana direwa a qasa daga bayan thunder din.

Sosai ya qarewa dokin kallo bayan ya samu nasarar maidashi nutsuwarsa. Ya aza hannunsa gadon bayansa yana sake shafashi a hankali,abinda ya sake bawa dokin nutsuwa sosai,sannan yaja akalarsa zuwa gefe,ya kuma tsugunnar dshi,cikin ladabi yayi biyayya ya tsugunna saman qafafun nasa,sai shima ya tsugunna daga daya side din yana ci gaba da magana dashi,maganan da ba wanda yasan me yake fadi.

Idanunta ta ware sosai,tana jin wani irin kishi yana saukar mata. Don me zai sarrafa mata doki bayan bata da tabbacin iya komai a tare dashi?,meye hadinsa ma da doki?,tunda ba magana ake ta takarda ko bada karatu ba?. Batason yayi mata komai da yayi kama da taimako tallafawa ko dafawa,da wannan tunanin nata ta fara takawa zuwa inda ya tsugunnar da dokin.

Bai lura da ita ba sam,cikin sassanyan sautinnan nasa maras amo yake ci gaba da karantawa thunder wasu ayiyo na qur'ani. Yayi relaxing sosai tamkar me fahimtar ma'anonin ayoyin.

Ta daya bangaren thunder din ta tsugunna,tana qanqance idanunta. Zataso ko sau daya ya kalleta don ta karanta masa a karance cewa din bashi da hurumi akan komai nata,saidai baiyi hakan ba,don baikai qarshen ayar da yake karantawa ba,wadda sautin ya fara shiga zuciyarta a hankali yana saukar da wani yanayi,saita janye dubanta daga kallon mutumin da ko sau daya bai daga idanunshi a kanta ba,ta soma shafa fuskar dokin.

Shafar fuskar tasa ya sanyashi yin wani qaqqarfan yunquri kamar zai tashi,abinda.ya sanyasu dukkaninsu miqewa da hanzari da niyyar riqe akalarsa,lokaci guda.....cikin sakanni guda,abinda yayi sanadiyyar haduwarsu gaban fuskar dokin.

Haduwa hannuwansu sukayi guri guda,kowanne ya janye da wani irin sauri. Lokaci guda dukkaninsu suka daga kai. Idanunsu ne suka gauraya dana juna,wani irin zuzzurfan kallo suka sakarwa junansu,iskar dake kai kawo a gurin tana kada sassanyan qamshin da ya kama jikin kowannensu. Musamman nasa scent din,wannan unique turaren da shi daya ya mallaki irin qamshin a duniya.

Hasken ranar da yayi saura a sassanyan yammacin dake sake hada wani irin nau'in hadari ya haske fuskar nan tata,fuskar data mallaki wata irin kwantacciyar fata kaman da madara take wanka.

A nutse ya janye idanunsa daga kanta yana mamakin samun blue eyes a yankain africa a tattare da wata mace har haka. Launin idanun da suka jima suna bashi mamaki kafin a hankali su juye su soma burgeshi tun daga sanda ya fara mallakar hankalin kansa. Nata idanun sunyi wani irin dacewa da zara zara eye lashes dinta,da kuma gewayayyar fuskarta dake dauke da kwantaccen gashin gaban yalwataccen goshinta.

Wani abu ya taba zuciyarsa,sai ya samu kansa da tuhumar kansa da kansa da ganin baikensa na qare ma fuskarta kallo.ya sunkuya a hankali yana daukar akalar thunder dake zube a qasa,abinda ya sanya akhnan din ja da baya a hankali.

Idanunta ta sake lumshewa tana sake budesu lokaci daya sanda ya sake zaunar da thunder sosai. Ta budesu fes a kansa,ta tsani duk wani mutum da zataji yayi mata kwarjini......ta tsani wani mutum ya fits kwarjini,ba'a taba samu ba tsahon rayuwarta tsakanin mutanen da duk suke kewaye da ita,sai yanxu?,bama kuma akan kowa ba akan wani malami can?.
Chapter 77 · 0% Book details