← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 101

Sashe 100

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Omar!" Haisam din ya fada da sauri yana dan dukan table din gabansa kadan.

"You know my mission omar.....kada ka lalatamin target mana.......baya ga haka I married her to protect her,she was in a tough spot ba tare da tsukakken tunaninta ya barta ta fahimci haka ba......zanyi hakanne kuma ba don ita ba.....zanyi hakanne badon so ko qauna ba.....zanyi dukka haka ne saboda JININ SAFEENA da take tare dashi.......saboda darajar wasu mutane data d'amfara da rayuwarsu.....nothing more.....hope you understand guys?" Ya qarashe maganan yana bude idanunsa sosai a kansu yana duban fuskokinsu daya bayan daya.

"It's okay.....mun fahimta......amma,why not ba zaka bude mata zuciyarka ba......why not ba zaka bada qofa zuwa ga wannan killatacciyar zuciyar ba?" Maleek ya fada a nutse dukkaninsu fuskokinsu suna nuna seriousness dinsu.

Girman idanunshi ya rage ta hanyar lumshesu sannan ya budesu fes akan fuskar maleek. Baisan me yasa suke putting pressure a kanshi ba game da maganan ba.

"Wannan zuciyar budeta shine babban kuskuren da zan aikata.......na gaya muku a baya.....yanayin aikina banajin zai bani daman budewa wata mace zuciyata harta shiga ciki.....zata iya zama weakness dina....mafi girman abinda na tsana kuma kenan......wannan zuciyar" Ya furta yana nuna qirjinsa da yatsarsa

"Idan tanayin so bata yinsa d'an kadan......bata kuma yinsa da sauqi.....wannan ne ya sanya nake qoqarina sosai gurin ganin ban tsani mutum ba.....gurin ganin ban tsani kowa ba,saboda nasan idan na fara QIYAYYA itama bata zuwarmin da sauqi......ina dukka qoqarina na canza kaina.... Amma haka aka halicci wannan zuciyar.....shi yasa nake qoqarin fahimtar kowa....shi yasa nake qoqarin bada uzuri ga kowa.......shi yasa bake qoqari sosai kar naqi kowa......ina fatan wannan bayanin ya gamsar?". Shuru ne ya dauki falon gaba daya,na wasu sakanni ba wanda ya motsa ba wanda kuma ya sake cewa komai. Ya musu magana da wannan yanayin nasa na seniority da dukkaninsu suke shakkarsa idan ya juye,sun gama fahimtar kuma da iya gaskiyarsa yake maganar.

Tsam ya miqe a nutse bayan ya tura kujerarsa baya

"Bazan hanaku yin komai ba.....don kun isa ku zartar da komai a kaina.......amma kuyi qoqari kada ku zafafa abun da yawa,don ba tabbas a cikin komai"

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/14, 19:12] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 88*

"In sha Allah saika jarabtu da soyayyar da zaka zauna a gabanmu kamar haka kana maimaita bayanin mahaukaciyar soyayya" Dan dakatawa kadan yayi daga saukar da yakeyi daga step din dining area din,wani murmushi ya subuce masa,yana jin maganar omar cikin kansa kaman wani wasan yara,murmushin ya zarce har cikin zuciyarsa yana sake jin abun da fatan omar ba wani magana bace me muhimmanci ba a gurinsa,sai kawai yaga tsayawa yayi magana dashi tamkar batawa kai lokaci da baki ne.....don TABBAS yasan abune da bazaiyiwu ba.

Samansa ya haura ta stairs din baya,saboda yanason sake wankan juma'a irin na sunnah da shari'a ta koyar saboda qarin samun ladan ranar,yana taka step din a gaggauce yana duba agogonsa. Yana shiga dakin tunanin motii ya fado masa,sai ya tuna jiya sunyi dashi xaije qauye,don haka ya kira number dinsa kai tsaye yana zare kayan jikinsa yana musanyasu da towel.

A kashe wayar tasa take,haka na'ura ta fada masa,sai ya maida akalar kiran nasa ga hussam da hanzarce. Ya kirashi ya kusa sau uku ba amsa,sai ana hudun ya daga. Ya hasala sosai,don ko waye kai idan ya maka kira daya baya sake qarawa,duk kuwa muhimmancin kiran da yayi makan,saidai idan ka gani ka biyoshi daga baya,abinda ya sake tunzurashi kenan amma yayi qoqarin calming kanshi.

"Barka da warhaka captain obbo" Hussam din ya furta da girmamawa,can qasan maqoshinsa kuwa maganganu ne fal da kwarjinin haisam din dake bugunsa cikin waya ne kadai hanashi xolayarshi da sunan ango.

"Barka.......motii fa.....ina fata kuna tare?"

"Ya fita wani aiki obbo...."

"Shi kadai?" Ya tambayi hussam a hanzarce. Adan tsorace hussam ya amsa masa

"Eh obbo.....ni" Bai ko tsaya yaji bayaninsa ba yau balbaleshi da masifa. Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Shuru kawai hussam yayi,baice komai ba,saidai zuciyarsa cike take da mamakin abinda ya hasala obbo din nasa har haka.

Har sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita yana maida numfashi,haka kawai yakejin wani bacin rai duka yau din,yana qoqarin dannewa ne kawai.

"Kayi haquri obbo,aikin company ne ya tsareni,kace lallai lallai mu tsaya mu lissafa adadin masu shops na saida turaruka da zaka bada tallafin manyan drum na turaruka a qarshen shekarar nan......inataso na gaya maka kaman shops din suna da yawa....."

"Ina ruwanka?....ko adadin shops nawa ne a lissafa,masu qananun tebur fa?"

"Su mun gama dasu" Ya fada a raunane. Bayason fadan obbo din nasa,kuma shima din ba kasafai ya fiya buda baki ya masifeka ba,amma kuma duk sanda ya fusata shikam ko fuskarsa baison kallo,saboda baida sauqi idan ya hasala. Ajiyar zuciya ya sauke don sauqaqawa zuciyarsa abinda yakeji.

"Amma ka manta na gaya maka.......kulawa da motii yana hannunka har zuwa sanda zan dawo?".

"Ina bakin qoqarina obbo......kafin su fita na tabbatar ya fita qarqashin security da guards masu yawa......sannan Aareef ma yana tare dashi".

"Aaareef fa?......makarantar fa?"

"Obbo an musu hutun tsakiyar zangon karatu ne".

"Karka sake turashi nesa shi da yazo baqunta.....Kun maraatummaadha(rashin hankali ne wannan)"

"Dhiifama obbo(I'm sorry big brother)" Shuru ya sakeyi

"Tole(alright),yana dawowa gida ka sanarmin.....sannan ka bibiyi isarsu lafiya,inaso ka sake kula da duk wani tsaro na gidan.......ina ebba da adeel?"

"Dukkansu kowa na bakin aikinsa"

"Shikenan.....sai munyi waya" Ya fadi a nutse yana yanke kiran. Wayar ya ajiye yana fesar da iska daga bakinsa,a hankali ya kira sunan Allah yana qoqarin bawa zuciyarsa daidaito,sannan ya taka a nutse yana wucewa toilet din sabe da lallausan towel a faffadar kafadarsa.

*MORSA SAFIYYA*

Cikin lokaci qanqani ta sanya aka tashi qwarya qwaryar abinci. A yau din a wannan rana ta juma'a tanaso ta ciyar da adadin mutane masu yawa........tanaso cikin masarautar kowa ya shaida abun alkhairi ya fara samunta....abun alkhairi ya fara samun me babban daki ta farko wato safeena. Tanason nunawa Allah godiyarta abinsa amsa addu'arta da yayi.....a bisa ceton rayuwar akhnan da yayi.....bisa cika fata buri da kuma addu'ar 'yar uwarta dake kwance cikin kushewarta tsahon shekaru masu yawa.

Komai akwai,don haka lokaci qalilan girki ya kusa kammala,wanda takeso bayan sallar juma'a ciyar da mabuqata.

Ranta fes ta shiga tayi wanka,ta kuma fito ta soma shiryawa cikin wata atamfa 'yar gaske,daya daga cikin kayan atamfofin da falaak tayi musu order daga HUGUMA CLOSET 08187255862(maza garzayo ki gwangwaje da laces da atamfofinmu,masu sauqi da rahusar da gurinmu kawai zaki samu,kizo kiyi joining group dinmu ki rabauta da kaya 'yan gaske,online business kikeyi ko boutique gareki,ko kuma shaguna kika bude?). Tana ji da atamfofin qwarai,dinkuna ta sanya aka musu na isassun mata,wannan ya qara fidda kyansu da martabar atamfofin ya kuma qara mata kwarjini sosai.

Tana cikin lanqwasa tattausan dankwalin atamfar da har wani qamshi ita kanta atamfar take,wadda aka saqata da rose water daya sanyata qamshin da taushin taji an buda qofar da sauri. Da saurin itama ta waiwaya,sai suka hada idanu da falaak.

"Ke lafiyanki kuwa?" Morsa ta fadi cikin mamakin yanayin da taga falaak din a ciki.

"Ya biftu ce momma......"

"Me ya sameta?" Morsa ta fada tana jin wani abu yana tsarga mata,dankwalin dake riqe a hannunta yana zamewa.

"Suma tayi......kuma bata farfado ba har yanzu......ya hairaan tace kizo". Da sauri ta lanqwasa dankwalin saman kanta,ta dauki yalwataccen mayafin dake ajiye gefe ta lullube jikinta,sannan ta zura bedroom slippers dinta tana yin gaba ba tare data jira falaak bama.

A hanya suka kusa karo da samia.

"Ranki ya dade......an kammala,za'a iya fara rabawa?" Samia din ta tambayeta tana binta da kallo cikin mamakin saurin da taga tanayi,don ko kallon fuskar samia dake mata magana batayi ba.

"A raba samia......da alama uzuri ne me qarfi ya taso mata" Armelle da itama tayi sararo da farko a tsaye ta fada.

"Tom" Samia ta amsa cikin girmamawa tana juyawa. Shuru armelle tayi tana sake bin bayan falaak data wuce da kallo. Fatanta daya addu'arta daya kada Allah yasa wani mummunan abune kuma ya sake tasowa.

Ita kadai a karan kanta tana tsananin tausayin wadannan bayin Allahn......zuwa yanzu tana ganin ya kamata hankulansu ya fara kwantawa.

Dauke idanu kawai hadimai da bayi suke don girmamawa ga morsa safiyya din ganin yanayin tafiyarta na gaggawa ba yadda suka saba ganinta ba. Ma'abociyar nutsuwa ce da kamala amma a yau hankalinta kamar baya tare da ita,abinda ya sake tsananta tsaigumin dake tashi a gidan tun daga awannin dazu na jita jitar daurin auren sheikh Muhammad haisam da kuma gimbiya akhnan din. Wasunsu sun samu damar ganin daurin auren ta wayoyin hannunsu ta manhajar YouTube,take kuma suka fara yadawa a tsakanin dukkan wani me wayar hannu,wanda baida itama yana kalla a hannun dan uwansa,wannan ya sanya cikin qasa da awa biyu tsaigumin ya zagaye ko ina ya kuma yawata,maroqan fada da masu busa kuma suka fara tunanin ta inda bushasharsu sabuwa zata balle,suna fata tafi ta wancan auren da akayi,don alamu suna nunawa kowa cewa wannan shine auren da mai martaba yake maraba dashi.

*MAMMINA/HAISAM*

A sukwane motar dake dauke da giwar sarkin wato hajja zaituna ta qaraso makekiyar qofar masarautar agadez din,wanda a wannan karon shiga da fita daga cikin masarautar yake bisa tsari doka da qa'idar da sheikh haisam ya zartar.

Qa'ida ce tsaiwar motar na mintuna gaban gate din kafin a bata daman shiga da sauri idan ta zama motar sultane ne kota iyalinsa. Ko yanzu motar mammina din gangarawa tayi zuwa bakin gate din ta tsaya tana jiran cikar mintunan.
Chapter 100 · 0% Book details