← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 101

Sashe 32

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ya koma da baya bayan kammala jawabansa ya bawa ME WADA guri. Shine kusan dukkanin shugaban hadimai maza dake gidan,wanda haisam ya zauna dashi na mintuna goma sha biyar kafin su shigo nan din,ya kuma bashi tsarin abubuwan da zai gabatar musu.

Akwai sabbabin dokoki da tsare tsare daya shirya gabatarwa daga sanda sultane ya tashi zuwa umra. Sai a yanzu yake jin kamar wata dama ya samu da zai bude wuta akan aikinsa ba tare da tunanin sultane zai hango komai daga gareshi ba. Sabbin dokoki ne da zasu zama wajibi akan kowa dake rayuwa cikin gidan,yanaso kuma ya gabatarwa da sultane su ya sanya hannu a jimlace su zama TABBATACCIYAR DOKA da zai rarrabata tsakanin dukkan hadimai da bayi na gidan.

"Be fast abdii" Haisam ya furta qasa qasa yana duban tsakiyar tafin hannunsa da na'urar ke maqale,wanda zaka dauka tasbihi yakeja.

"Na kusa qarasawa ainihin muhallin da take kebancewa" Ya fada cikin qwarewa da takatsantsan da dukka motsinsa,duk da taswirar hannunsa da haisam ya tsarata tsaf tana nuna masa kowacce hanya daya kamata kayi.

Qofar glass din ya zuge gefe daya,ya kuma shiga a hankali. Tafkeken parlor dinta daya zama na musamman ne ya soma bayyana,wanda yake dauke da wani irin nau'in ado da yaja hankalin haisam din.

"Obbo......oromian....."

"Dakata!" Haisam ya tsaida abdii.

"Ba wani hatsari?" Abdii ya tambaya saboda tsayuwar data zama ta ba zata.

"Turn to your left side" Ya bashi umarni yanason ganin wani abu da yaga gilmawarsa. Yadda haisam din ya fadi masa hakan yayi,take tafkeken frame din dake dauke da wani nature drawing ya bayyana.

Sosai haisam ya zubawa frame din idanu,wasu abubuwa suna dawo masa akai. Wasu shekaru can baya da wasu memories da suka ja hankalinsa sosai.

"Ka dauki hoton frame din ka turamin......kafin ka shiga ciki.......kaje ka duban dining table na sassa......idan baka samu komai ba a nan ka qarasa store da yake manne da babban kitchen dinsu".

"An gama obbo" Abdii ya fadi yana ciro wayarsa yayi snapping frame din sannan ya soma laluben bangaren dining.

Ba jimawa ya sameshi,tun bai qarasa ba ya hangeshe sheqi da kwanukan abinci na alfarma da suka janye hankalinsa. A yanayinsa kamar anci abinci ba jimawa a wajen.

"Inason ganin kwanukan da kyau.....da abincin dake cikin kowanne......ka hanzarta,don kowanne lokaci hankalinta yana iya karkatowa gida" Haisam ya fada yana duban agogon dake harbawa saman device din.

"Ko da zatazo ta ritsani,ba shakka sai na yiwa obbo wannan sadaukarwar,koda wannan shine abu na qarshe da zan aiwatar cikin rayuwa ta" Abdii ya furta da wani irin confidence da ya sanya haisam sakin sassanyan murmushin da baiyi niyya ba.

"Obbo....."

"Stay silent abdii.....just be quick......you know idan ta sameka a nan you finished"

"Obbo......English dina baiyi qarfi ba ka sani...."

"Abdii" Ya kirashi da zuzzurfan muryarsan nan me kauri cikin sigar jan hankali. Ya sani sarai halin abdii,komai sai ya sanyo wasa a ciki,idan kuma baiyi da gaske ba lallai lokaci zai iya qwace musu.
[1/16, 17:27] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 29*

Daya bayan daya abdii ke musu hotuna,bakinsa cike fal da zance d kuma mamaki. Komai na abincin kamar suna cikin yankin jimma.....komai kamar suna sassan qabilar oromo.........hatta da shayin.

Kai tsaye haisam yaci gaba da guiding nasa,yana yi yana kasa hankalinsa biyu omari yana riqa masa,har zuwa lokacin daya isa ga bedroom dinta da bincike ya nuna masa tafi zama a cikinsa,saboda gwaji da awon yawan saukar numfashi a dakin da yayi daga bayan gine gine gidan.

"Finally obbo......from where i should start?". Ya tambaya cike da jiran umarni.

*MAMMINA*

"Idan ka qarasa villah street ka tsaya a nan" Mammina ta bawa driver din nata umarni nakai tsaye bayan fitowarsu daga duba Maher da aka bata tabbacin sallamarsa a yau din. Sosai Maher ya cika da mamakin ganin zuwanta ita daya qwallin qwal,ba wani tarin motocin dake take mata baya a duk sanda zatayi fita irin wannan.....ba wani hadimi ko me tsaronta kamar yadda ta saba fita irin wannan?,wannan yabar masa ayar tambayar da tana fita ya aikewa haisam da hasashensa da kuma abinda ya gudana tsakaninsu.

Villa street din wani guri ne daya zam emata wata mahada......wata mahada me tarin sirri,zuzzurfan sirrin da ba wani hankali ko tunani a nan kusa da ya taba tsinkayoshi. Rufaffe kuma adanannen sirrin da duk tsananin kusancinka da ita bata lamuncewa kowa saninsa ba.

Wayarta ta fiddo,ta kuma soma shigar da wasu lambobi da ko da wasa bata taba ajiyarsu cikin wayar ba,iyakacin zamansu cikin kanta,da zarar kuma ta sakasu a wayar ta gama duka amfanin da zatayi dasu take sharesu.

Tana shirin danna dan maballin kira kira ya shigo wayarta,ta tsaya cak ta zubawa kiran ido tana kallonsa. Siririn tsaki taja,akhnan ce.....a irin lokaci irin wannan bata qauna ko fatan abinda zai katse mata dukka shirinta,to amma a yanzun tana buqatar yarinyar a kusa......tana buqatar nuna mata tausaya sama da yadda ta saba a baya,don haka ta yanke nata uzurin ta daga kiran.

Iya daga kiran mammina din kawai ya sanyata sakin wata nannauyar ajiyar zuciya. Ta kowanne bango ji take rayuwar ta matseta,komai kuma baya tafi mata daidai. Wani muzanci takeji har cikin jininta.......wani fusataccen yanayi takeji da dukkan abinda sultane yayi mata a gaban malamin.

"Mammina.......ina buqatarki......ina buqatarki a kusa dani" Sirrintaccen murmushi ne ya subuce mata saman labbanta. Yadda dukka rayuwarta numfashinta da kowanne kalar motsi nata ta dogara da ita yana burge mammina din.......yana mata dadi idan ta tuna yadda ta sanya dukkanin motsinta ta ta'allaqa da ita.

"Na sani akhnan.....karki wani damu......fitar gaggawa ce ta sameni,naje duba mara lafiyan daya raunata ta sanadinmu......ina kan hanyar dawowa nan da awa daya".

"Okay" Ta amsawa mammina din da wani irin yanayi. Wani boyayyen rauni ne da ita daya ita zaituna take iya ganeshi..... Murmushi ta sake saki,a hankali dai wannan taurin kan......wannan kafiyar.....wannan zafin kan yana juyewa zuwa wani irin rauni da laushi.

"Muje zuwa.....sakamako ne wannan zuwa gareku gaba daya ahalin diory hamani". Ta furta a sarari qasa qasa.

Lambobin ta sake zubawa ta kuma kira,dab da zata katse wata kakkausar murya mara dadin amo ta amsa da

"Alo"

"Ina bakin iyaka" Ta fada a taqaice,ba tare kuma da an amsa mata ba aka kashe kiran,sai itama bata damu ba,don tasan hakan wani tsari ne dadadde da suka jima akai. A nan duk wata mota data daukota take sauketa,ta kuma juya ta koma ta tsaya a duk nisan inda aka umarceta......sannan wata motar daban ta dauketa ta qarasa da ita zuwa SANSANIN SIRRINTA!.

Tana maida wayarta jakarta wani irin mummunar faduwar gaba da batasan daga inda ta yanko ba lullubeta. Har cikin kunnuwanta takejin sautin bugawar da zuciyarta tayi,saita maida idanunta ta runtse.

Tsahon sakanni talatin ta dauka tana qoqarin saita kanta da wani irin tashin hankali. Wani yanayi da ba kasafai yake alamta mata komai yana nan a daidai ba......wani yanayi da a cikin kaso dari kaso sittin idan ta jishi akwai wata matsala ko damuwa da batasan da ita ba a bayan fage.

"Juya mu koma" Ta bawa driver dinta umarni kai tsaye. Haka kawai takejin hankalinta yayi gida,haka kawai takejin kamar akwai abinda ta manta,kamar abinda ya kamata ta dauka bata dauka ba,kamar akwai abinda ta bari ba'a muhallin da ya kamata ta barshi ba.

Cikin cika umarninta ya karya kan motar yana fadawa hannun dake daura dasu yana qarawa motan sauri kamar yadda ta buqata.

Wayarta ta sake cirowa,tana tuna cewa taga tarin missed calls din yalwa. Da gaggawa ta maida kiran tana tsammanin dagawa daga bugu daya kaman yadda ta saba,saidai har ta gama ruri ba'a dauka ba. Abun ya bata mamaki qwarai,don ba wanda yake da zarrar da zata kirashi a kiran farko ba tare daya daga mata waya ba,don ba kasafai suke kiran hadimi ko bawa ba,saidai susa daya daga cikin hadimansu su kira musu duk wanda suke da muradin magana dashi,wannan shine cikakkiyar izzarsu....qasaitarsu da kuma sarautarsu.

A kira na biyar data yiwa yalwa sai taji kamar ta rufe idanunta ta bude ta ganta a gida

"To waye zata kira?" Ta tambayi kanta da kanta,kafin tunanin tafisu ya fado mata. Saida na'ura ta gaya mata ba zata iya sadata da tafisu ba sannann ta tuna,yau tunda asussuba tafisun ta wuce zuwa fataucin data saba yi duk bayan wani zango don kadar da hankalin me hankali a kanta.

"Ina buqatar nan da mintuna goma mu isa gida" Kawai ta fada cikin umarni nakai tsaye

"An gama ranki ya dade" Driver din ya amsa mata yana qarawa motar gudu kaman yadda ta umarta.

"DONE!" Shine abinda abdii ya fada da muryar nan tasa da akan komai ma saita alamta wasa a cikinta.

"Tamam" Haisam din ya furta wanda kalman ya aike da saqon zuwa kunnuwan omari beeno da salawi. Damqe komai yayi cikin tafin hannunsa,sannan a nutse ya kira sunan salawi.

"Daga hannun hagunka,ka matsa kadan a sanda aka fara bada damar fita.....da yawansu ba zasu fita ba......saidai na tabbatar akwai masu fita a cikinsu bayan fitata......ka gayawa beeno wannan aikinsa ne qidddigesu.. Akwai wayoyin dukkan wanda ke amfani da waya a ciki da aka zube......inason ka bincike min wayar da aka fi samun adadin kira......kiran daya kasance number daya ce......ina buqatar safarar dukka bayanan cikin wayar zuwa ga email dina......banason aikinka ya haura minti uku kacal"

"An gama" Ya amsa masa kamar yadda suka horu da karbar umarni kai tsaye ba tare da musu ba.

Kunnuwansa suna iya jiye masa yadda gurin ya hautsine da yabo kan horaswa da aka basu cikin awa daya kacal da basu san da ita ba......tarin ilimin daya fadakar dasu abubuwa masu tarin yawa,da tarin godiyar da bai iya bambance muryoyin dake maganan saboda sanarwar da me wada ya bayar kan tsibin envelope din da aka zube masu dauke da kudaden da yace wata qungiya ce tace a raba musu kyauta.
Chapter 32 · 0% Book details