← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 101

Sashe 6

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni kaina Nannie banda an gaya min dama a jiya da magabatan hakeem suka iso da dukiyar aure ta fadi saita sha gubar,a gaban aisa da shehnaz da sauran hadimanta,wanda duka sai dana bisu daya bayan daya na tabbatar ta fada din......to amma kuskuren da nayi shine dana dauka abun shirme ne kawai,bawai tana fada bane da gaske.......ashe da gasken take,don Allah ku yafemin Nannie.......ki bawa me martaba haquri,a yau a karon farko yarda da tabbaci da ya bani akan d'iyarsa.....a karon farko na kasa.......na gaza,nayi sakacin barin magana irin wannan har taso tayi sanadin d'iyarsa tilo" Ta qarasa fada tana kama dukkan hannuwan Nannie ta riqe cikin nata tana sakin kuka me qaramin sauti.

Sosai abun ya taba Nannie,bata taba ganin soyayya irinta mammina da akhnan nan,saita riqe hannun mammina din sosai itama.

"Haba zaituna?......meye haka kikeyi?,kin manta matsayinki cikin gidan nan kuwa?,idan wani cikin hadimai yazo wucewa fa?".

"Na cancanci inyi wannan kukan Nannie,ku barni nayi ko zan daina jin kasawata akan akhnan"

"Baki kasa ba zaituna......shekara nawa take qarqashin kulawarki?,daidai da mummunan zazzabi bata taba yinsa ba,duk mutumin da zai kwashi wannan shekarun.....dondai kwana daya faruwar abinda baida ikon tsaida faruwarsa bai kamata a tuhumeshi ko ya zama abun tuhuma ba akai". Ta fada da sigar lallashi.

"Allah yasa morsa safiyya ta fahimci hakan.....Allah yasa ta gane haka" Ya fada muryarta tana rawa.

"Zata fahimta muddin ita din ba butulu bace" Nannie ta amsa da dukkan confidence dinta.

Murmushi ta saki sirrintacce a sanda suka juyawa juna baya. Nannie tayi hanyar da zata sadata da sassanta,itama kuma ta juya son isa ga nata sassan.

~
"Idan har tasan tayi iqirarin shan wani abu da zai iya cutar da lafiyarta......idan har tasan halinta na shekara da shekaru a matsayinya na wadda ta raineta.....idan har ya kasance ta kauda kai daga dukkan wannan ba tare data shaidawa kowa ba koda barazana ne ayi don dakatar da afkuwar abun.......lallai akwai babbar ayar tambaya a ciki.......akwai wani shiryayyen mission da nake iya sansanowa......" Omari yayi maganan yana qanqance idanunsa ciki,yana jin kuma wani abu yana jan hankalinsa sosai akan maganar.

"Omar" Haisam ya kira sunansa da alamun gajiya cikin muryarsa.

"Ba wannan maganan nakeso ka maida tunaninka akai ba......duk abinda mukaji......ko muka gani haka zamu barshi a yadda muka sameshi.......ba saboda wannan matsalar muka shigo masarautarsu ba.......ba qididdigar alaqar dake tsakanin junansu mukazo tantancewa ba......abinda ya kawomu kawai shine neman gujajjen me lafin da yaso bata mana alaqar diplomatic na qasashenmu........let's prioritize the mission" Ya furta da seriousness dinsa.

A nutse omari ya daga kai ya dubeshi. Ba tun yau ba,ya sani cewa mutum ne bame yawan shiga sharafin wasu ba,amma kuma hakan ba yana nufin bashi da tausayi ko taimako ba...... Yana da wata irin zuciya me taushi,duk da cewa wasu lokutan yana da kafiya da kuma zafin rai akan abinda yake gaskiyarshi kenan,amma a nan bai dauka zai wofantar da al'amarin da a yanzun da kanshi ya gama zube masa lissafin yadda hasashensa yake iya hangen komai ba.

"Amma.......what about your....."

"Ban hada maka zancansu dana aikinmu ba don ya zamana zamu sakashi lallai lallai cikin ayyukanmu ba......na hada maka ne don ka fahimta,ka kuma gane hasashena yayi daidai na sanya matar ta zama cikin sahun mutane na gaba gaba da zamu tsananta sanya idanu a kanta ita da duk wanda ya rab'eta?.......that's it" Idanu suka zubawa juna shida omari din,kafin omari ya janye nasa kallon bayan wasu sakanni.

"Amma ka sani.......ko akwai wani dalili da Allah ya aikomu a irin wannan lokacin cikin gidan?......ba lallai ya zamana dalilin kawai shine ceto martabar Ethiopia kadai ba........."

"Da kuma ceto rayuwar halitta mafi soyuwa a gareni MOTII.....kammaluwar aikin nan shine zai bani guarantee na safety din motii,bama motii kadai ba.....harda nanay dama duk wanda ya kwana ya tashi cikin aba jifar palace" Ya qarashe maganan da wani irin yanayi a muryarsa da idanunsa.

"Bazan hanaka ba taimako ba idan ka shirya yi......amma dole ya zamana bayan aikinmu ne bawai a ciki ko a gaban aikinmu ba........take heed.........akwai wasu mutane cikin masarautar da zargina ya soma sauka a kansu......akwai wasu mutane da bansan yawan adadinsu ba a masarautar da nake da tabbacin suna da alaqa me qarfi da oromo.......bansan su nawa bane,amma mutum biyu daga ciki masu suna iri DAYA sune suspect dina na farko. Tabbas akwai alaqa tsakaninsu da matar......saidai bansan iya zurfin alaqar da adadinta ba......sannan su nawa ne masu jin yaren?,tana cikin masu jin yaren ko wata qabila ce ita daban cikin Ethiopia bawai oromo ba?,akwak.kebantaccen dakin dakin daya zama na musamman kuma mallakarta ita daya,ta yaya zamu kai ga cikinsa?.......ta yaya hakan zai taimakemu zuwa ga inda ainihin me laifinmu yake?,.....wadannan sune abubuwan da zamuyi aiki akai yanzu.........salawi da beeno dukkaninsu zasu tattaro su dawo daga garuruwan da aka turasu,zasu kama haya cikin daya daga cikin gidajen dake daura da masarautar.......sannan kaima......" Sai kuma ya dakata kadan.

"Nima zan antayo cikin gidan?" Kai ya girgiza a nutse.

"Bana tunanin zaka hau wannan position din,saboda tunaninka da daidaiton da nake da buqata a gareka kaman yayi low,baikai adadin da nake buqata ba". Qaramin dariya omari ya saki,ya sani haisam ya fadi hakane saboda ya shigo da batun akhnan da case din cikin gidan cikin aikinsu.

"A duk sanda ka shirya kawoni kusa da kai ina maraba" Ya furta yana miqa hannu gami da tashin motar. Dubansa yayi kaman zai tambayeshi sai kuma ya fasa,omari din ya fahimci haka,yasan kuma tunda yayi hakan miskilancinsa bazai bari ne ya tambaya din ba,sai ya buda baki a nutse.

"Zan kaika wani guri......ina sanyan ran zaka samu kalar yanayin da kake buqata" Be amsa masa ba,saidai ya jawo system dinsa da yasa omari din ya fito masa da ita,ya azata saman cinyarsa ya kunnata sannna ya fara shigar da bayanan da yake da buqata. Ganin haka sai omari din ya maida karatunsa yana sanyashi a matsakaicin sautin da bazai dameshi ba.

★★★
Idanunta ta sake maidawa ta lumshe gami da jinginar da kanta da fuskar gadon da take kai. Kusan dukkan wanda ya shigo tsakanin Nannie.....mammina......aisa...shehnaz.....harma da falaak maganganunsu dukka akan abu guda daya suke maimaitawa. Abu guda dayan da itadai batasan dashi ba,batasan kuma da zamansa,batasan ma yaushe ya faru ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Abu daya ta sani tasan kuma ta furta,ZATA SHA GUBA wanda bayan janyeta da shehnaz da aisa sukayi zuwa daki maganganunsu sun sanya wannan kalamin ya zagwanye daga zuciyarta tas ya fice,taji kuma bata da wani sauran marmari ko niyyar aikata komai,ta kuma kwanta ranta ba komai face zallar zugi radadi da fatan janyewar sultane daga dukkan qudurinsa da yasha alwashi akai......ta kuma kwana ne da zazzabin data dinga jinsa sosai cikin jikinta,baya ga haka ba wani abu data wayi gari dashi a ranta a ranar.

Abu na biyu birra.....birra na cikin amintattunta da tayi imanin koda zabin a kashe akhnan ko a kashe birra dinne.......yarinyar zata zabi mutuwarta akan wani abu da zai taba lafiyar akhnan din. Uwa uba kuma ma shine,a gabanta birra ta gama hada komai suka fita a tare. Ba wai tana wani guri bane na daban aka hada mata tea din,da normal ruwan da ta saba amfani dashi cikin gidanne,to amma yaya akayi aka samu wani abu ya shiga har cikin tea din dabai dauki tsahon lokaci ba daga hadashi har zuwa shanyeshi?.

Wani irin daurewa kwanyarta kawai take sakeyi da wani dogon tunanin da bata hangi hanyar da zata samu tarin tambayoyin dake sarqafe da ita ba,uwa uba ba wanda ya tsaya ya saurari komai daga bakinta,sai tarin fada da nuna mata kuskurenta da kowa yake qoqarin yi. Abinda yafi daga mata hankali rashin ganin koda gilmawar sultane tun jiya kawo yau din,ba kuma wanda ya mata maganarsa ko yace komai a kansa. Abu irin wannan idan har zai sameta ta tabbatar sultane zai iya zama mutum na farko da zai kasance tare da ita bayan mammina.........idan bai zama na farko ba saboda tsananin kulawa da damuwa da al'amuranta da mammina takeyi to lallai babu abinda zai hanashi kasancewa na uku.

Itama batayi yunqurin kare kanta ba ko kadan,saboda batasan ma idan ta bude bakinta me zata ce ba?. Da wannan kalar tunanin birra ta nemi izinin shigowa dakin,ta kuma murda handle din ta turo qofar da sallama ta shigo.

Idanunta ta ware a hankali tana dubanta,a nazarin farko ta karanci zallar tashin hankali da rudanin dake kwance saman fuskar yarinyar. Ko digo a ranta bataji akwai wani mugun nufi da zai fito daga bangaren birra din ba,muryarta can qasa tace.

"Ranki ya dade......lokacin wankanki yayi.....zan shiga na hada ruwan wankan,nace ko zaki kasance tare dani a yayin hada ruwan?" Ta tambaya jikinta yana rawa da zaka iya hanga idan ka zuba mata idanu.

Zare dubanta akhnan tayi daga dubanta,muryarta can qasa ta bata umarni nakai tsaye.

"Shiga ki hada" Kawai tace da ita. Ba musu ko saba umarni tsakaninsu daga gurin uwar gijiyarsu,hakan yana daidai da aikata laifi me girma,don haka ta taka tana wucewa shiyyar da bandakin yake.

Bata jima ba ta fito dauke da bathrobe me azabar laushu fara qal da takalman wanka,wanda kusan duk bayan kwanaki ake sauya mata su,kuma idan aka fiddasu ba'a dawowa dasu sun gama aiki kenan.

Tsugunnawa tayi ta ajiye mata takalman,ta ajiye rigar a gefanta sannan ta taka a hankali ta nufi wani sashen na daban inda facial care products dinta suke da tame using wasu kafin ta shiga wanka wasu bayan ta figo ta dauko box dinsu gaba daya don sauqaqe mata tashi zuwa inda ta saba zama tayi amfani dasu. Saidai tana takowa ta mata alama da hannu ta juya ta maidasu.

Da taimakon birra din ta shirya cikin wasu sauqaqan English wears riga da skirt. Sai fuskarta tayi wani fayau,ramar da tayi tsakanin jiya da yau ta fito sosai kamar wadda ta shekara tana ciwo.

Skin cream perfume dinga ta matsa tana shafawa a hannunta. Idanunta suka sauka daidai inda yayi mata allurar a jiya wanda ya bada wani dan siririn tabo kaman an diga baqin lalle a gurin saboda zafin allurar. Yatsanta takai ta shafa gurin,tana son tunawa,yayin da tunawar tazo mata da wani irin mummunan faduwar gaba.

Stool din dake bayanta ta koma ta zauna akai tana tuna komai.....
Chapter 6 · 0% Book details