← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 101

Sashe 40

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tabbas.....yace zaizo idan ya samu sararin hakan bayan kammala uzurorinsa". Kai take sake jinjinawa cike da wani tarin mamakin.

"Zaizo a wani lokaci?,idan ya samu sarari" Ta sake maimaita maganar cikin jin wani abu yana girgiza girmanta. Kai ta jijjiga da qarfi sannan ta,waiwaya ga tamin
"Tashi kaje.......ka qarasa aikinka......inaso almaz a gobe ya fito a cikakken mutum......inaso almaz a gobe ya fito da fitar da yanayin da zai sace zuciyar akhnan lokaci daya,banaso mu rasa wannan damar......." Ta fadi tana kauda tattauna zancan haisam a tsakaninta da tamim,duk da ita daya ce tasan abinda takeji,amma batason abinda zai dauke hankalin tamim daga shirin zuwan almaz a gobe.

Kai tamim din ya girgiza a hankali,yana jin zallae rashin adalcin da ake shirin gwada masa. Ya kwantanta buda abinda ke cikin baki da zuciyarsa,amma a duk sanda ya zauna gaban zaituna da zummar fadin irin tukuicin da yake buqata daga hannunta na bautar shekara da shekaru sai yaji ya kasa,sai yaji ya gaza.......amma a yanzun da ake shirin sanya almaz gaba dashi......ake shirin sanya almaz gaban buqatarsa,sai yakejin kamar wani abune da zuciyarsa ba zata iya jura ba.

A nutse yayi sallarsa ya gama,ya kuma yi addu'o'insa,wanda yana shafasu kira ya shigo wayarsa. Baikai ga ciro wayar ba,wadda ba ringing take bayarwa ba ba kuma vibration ba,wata alama ce da shi daya yake gane shigowar kira ya fahimci waye yake kiran. Sanda ya daga wayar muma qaramin murmushi ya subuce masa. Maleek ne,sai ya taba na'urar kunnensa ya maida wayar aljihunsa ya miqe yana yiwa maleek cikakkiyar sallama,baya amsa waya a masallaci saboda girmama muhallin da kuma girmama wanda ake bautawa a gurin.

Yana amsa wayar a nutse yana bin hanyar da zata sadashi da sassan mammina. Ya shirya tunkararta ne dama bayan yayi sallah,bai shirya zuwa gareta ba a kiranta na farko.

Hankalinsa yana ga yanayin yadda gidan ya fara daukan saiti da sabbin dokokin da tuni suka karade gidan,suka kuma ratsa kowanne bangare na gidan,suka isa hannun kowanne hadimi bawa da wanda keda alhakin tsaro na gidan.

Duk inda ya gilma ko ya taka qafarsa gaisuwar girmamawa ce take biyo baya,saboda kowa na cikin gidan yana qoqarin ganin ya cika umarni da burin sultane na daukar haisam tamkar dan cikinsa.

____kyakkyawar fuskarta shimfide take da wani irin yanayi dake cike da miskilanci,rashin walwala da kuma takurar da takeji tun daga zuciyarta harma da ilahirin rayuwarta gaba daya. Saidai duk da hakan ba zaka rasa hangen wannan sassanyan kyan a tattare da ita ba sanda take saukowa daga cikin motar data kasance mallakinta,bayan ta raka aisa ta tashi zuwa Niamey ta filin sauka da tashin jiragen sama dake agadez din.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/21, 19:16] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 36*

Kamar kowanne lokaci hadimanta guda biyar din dukka suka kasance tare da ita cikin hidimarta,birra na cire sauran diguwar rigarta data rage a cikin mota,buhaina na gyara mata lullubin matsakaicin mayafin dake jikinta,bushira na qoqarin rufe murfin motar,yayin da barratu ke clearing mata hanya. Wani abu guda da a kullum yasa take sake jin jinin sarauta da izza cikin kanta da jikinta,yake kuma qara mata nishadi da jin dadin irin tsatson data fito.

Saidai a yau din wannan zuciyar tasha banban da ko yaushe,wannan walwalar da nishadin da take samu can qasan zuciyarta a yanzun babu shi ko kadan a tare da ita,zuciyar cike take da rudani,tana jinta a quntace tamkar wanda aka sanya a wani saqo daban aka killaceta.

Shehnaz na daga bayanta tana amsa wayar jamaal a nutse,ba wani daga murya ko hayaniya,wannan zai sanya daqyar ka iya jin abinda take fada.

A yanayi irin wannan baushin shehnaz da aisa ke kamata. Sunayi kaman basusan ciwo da dadin rayuwarsu ba?. Namiji ne kawai halittar da zai iya daga hankalin mace,ya sanyata cikin tsananin damuwar da zata iya qare rayuwarta a ciki,amma a hakan dukka sun runtse idanunsu daga ganin kowanne aibu nasu?.

Misali me sauqi a kanta,bata shimfida hannayenta ta karbi kowanne namiji ba......bata marabci kowanne d'a namiji cikin rayuwarta ba.....amma duk da hakan gigita rayuwarta suke shirin yi?.

Ranar gobe tana lissafata cikin mafiya munin ranaku a rayuwarta da bata taba zuwa mata ba. Wata rana da bata taba lissafinta cikin kwanakinta ba na duniya kaf,koda kuwa zatazo bata lissafa zuwanta a nan kurkusa har haka,ta yaya zata manta da MORSA SAFIYYA cikin rayuwarta ne?.

Wani nauyi takeji a qirjinta sosai idan ta tuna qalubale ne yake tunkarota ta kowacce fuska. Mammina ce kawai qarfinta......banda tana da mammina bata da tabbacin ina rayuwa zata kaita.

Wani siririn iska ta fitar daga bakinta.......ba abunda ke sanyata cikin jin qasqanci idan ta tuna waliccin aurenta a hannun waye ya rataya a yanzu?...... MALAMI......BAQON MALAMI.......TSINTACCIYAR MAGE!. Duk da irin tarin darajar da take dashi......tarin dangi da ahalin da zasu iya aurar da ita?......amma sultane ya zabi horar da ita ta hanyar damqa waliccinta a hannun wanda ko cikakken asali bayi dashi?.

Idanunta ta daga a hankali sanda tunaninta ya kawo wannan gabar don yanke hukuncin sassanta zata nufa ko zata shiga daya daga cikin guraren dake bats relief cikin gidan a duk sanda ta shiga rudani irin wannan?. A daidai lokacin ne kuma idanunta suka sauka a kansa,wanda da saukar nata idanun shima ya daga manyan fararen idanunsa suka sauka saman fuskarta dake da wani irin kwantaccen kyau......kyan daya bayyana tarwai cikin dan qaramin hasken ranar daya haske farfajiyar ya kuma nuna ainihin kalar qwayar idanunta.

Idanunsa ya zare a hankali sannan tattausan murmushi ya kubce masa wanda labbansa da suka motsa ne kawai suka bayyana murmushi yayi saboda maganan da maleek ya gaya masa ta cikin wayar.

Idanunta ta janye itama da wani irin hanzari tana jin wata irin faduwar gaba data saukar mata. Wani irin kwantaccen kwarjini da wata ajiyayyar izza ta hanga tattare dashi,abubuwan biyu suka ciccibi tunaninta suna jefashi wani sashe na daban dake cike da zallar mamakin
"MALAMI DA IZZA?....MALAMI DA KWARJINI?" Ta tambayi kanta da kanta wani abu yana mata tsaye qasan ranta.

Me yasa a kowacce siffa data kebanta dasu?,a kowacce siffa da tafi dacewa dasu?,a kowacce siffa data kasance mallakinsu ce sai ya cusa kansa yayi tarayya dasu?.

Meye hadinsa da wannan izzar?,meye hadinsa da wannan kwarjinin da yake nunawa saman fuskarsa?. Abu mafi qona mata rai shine......ta lura a duk sanda idanunsu zasu hadu guri daya faduwar gaba itace abu na farko dake fara ziyartarta......a duk sanda zasu hada idanu da ita shine yake fara janye idanunsa kafin ita. Baisan ma zunubi bane kallonta haka kai tsaye ido cikin ido?. Koma meye sultane ne ya janyo mata,ya bashi dama da yawa,damar kuma har takai ya bashi wuqa da naman zartarwa cikin rayuwarta.

Yadda ta lumshe idanunta haka ta dauke numfashinta a sanda yake shirin giftata. Zuwa yanzu tana tsoron shaqar wannan qamshin.....qamshin da ta soma zargin akwai wani sihiri a cikinsa. Ba wani rana.....ba wani lokaci da zata shaqi wannan qamshin bai maqale mata a hanci da tunaninta ba a yinin ranar gaba daya. Kowanne qamshi a duniya yana da asali da kuma inda aka samoshi,amma wannan mayen qamshin ya rasa asali da dukka wani bin diddigi da tayi masa.

"Barka da warhaka sheikh" Ta tsinci muryar shehnaz a bayanta tana gaidashi cikin tarin girmamawa.

"Barkanki" Amsar daya bata kenan yana maida wayar maleek kunnensa yana ci gaba da takawa.

Idanunta akhnan ta qanqance tana jin wani abu me nauyi yana sauka qasan zuciyarta. Wani irin bacin rai sabo ya soma tasiri cikin ranta tana kuma iya sauraren yadda shehnaz ta qaro sauri tana qoqarin jera kafadarta da tata.

"Me yasa kike qoqarin zubda girma da kimarki shehnaz?.....me yasa kike qoqarin nunawa duniya ke din ba kowan kowa bace?" Dubanta shehnaz takeyi cikin zallar mamaki.

"Kamar yaya biftu?" Ta tamabaya maganan tana warwarewa shehnaz kai. A nutse ta waiwayo tana ajewa shehnaz wani kallo kafin ta dauke kanta,a hankali cikin izzarnan ta fara magana.

"'Yar asali kike.....jinin sarauta cikakka daga agadez.....me yasa zaki zubda kanki akan wancan tsintacciyar magen da ba wanda yasan asalinshi?,ke ya kamata ya fara gaidawa......yakai har qasa gurin matuqar baki girma,amma kuma baiyi hakan ba saboda sultane ya bashi dukkan wata dama,tsananin girman kai yana sanyashi jin cewa wai shin wani ne......bayan ba kowa bane face wulaqantaccen......"

"Biftu mana!" Shehnaz ta fada tana duban akhnan da mamaki,yadda take maganan da wani birkitaccen fushi.

"Kina manta darajar da Allah ya yiwa malamai ne?" Hannu akhnan ta dagawa shehnaz ba tare data waiwayo ta kalleta ba,idanunta na bayyanar da zallar bacin ranta

"Bana buqatar naji komai.......ya isheni" Ta fadi har cikin zuciyarta tana jin takai geji,a yanzun bata buqatar maganan kowa akan komai.

Ta Jima shehnaz tana dubanta kafin ta dauke idanunta a hankali ta maida gabanta. Mamakin yadda kullum akhnan ke qara birkicewa yana kamata,tuna maganganun da sukayi da aisa kafin ta wuce ne kadai ya hanata cewa komai,saitaci gaba da lissafe lissafenta a ranta,tana kuma nema mata shiriya gurin ubangiji.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A nutse ya zare device din daga kunnensa bayan ya yiwa maleek sallama,dab da zai shiga sassan mammina ya hada sabon connection da omari ya maida device din kunnensa a nutse yana sake takawa zuwa ciki.

Wani abune ya gilma cikin idanunsa daya tilasta masa sanya yatsansa babban da manuni yadan shafi idanunsa yana furta
Chapter 40 · 0% Book details