Sashe 39
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Idanunsa ya sauke daga kan fuskar sadam yana dan sakin boyayyen murmushi. Hasashensa da dukka zarge zargensa sun tabbata,tarko ne ya d'ana kuma ya kamata,wannan kiran ko wani motsi daga gareta yake jira gashi kuma ta motsa din,iya haka kawai ya bashi tabbaci.
Saidai kuma tazo a gabar da 'yan miskilancin nasa suka motsa,real version dinsa na introvert ya soma aikinsa a jikinsa,don haka ya maida bayansa jikin kujera yayi relax yana amsa masa.
"Naji,na kuma karbi kiranta,zan kuma isketa,amma ba yanzu yanzu ba,akwai qananun abubuwa da nakeso na kammala". Cikin matsanancin mamaki da kuma tsoro sadam ya daga kansa yana duban haisam din. Karon farko!.....a karon farko giwa ta kira wani yana sanar mata bazai samu daman amsa kiranta ba har sai a sanda shi hakan yayi masa?. Harara kawai abdii yake zabgawa sadam ganin yadda ya qame a gurin,da alama amsar haisam din ke tabashi,inda yasan girman wanda ke a gaban nasa wannan sai yafi girgiza hankalinsa akan amsar da aka bawa uwar dakin gidan gaba daya.
Shurun da haisam yaji ya sanya ya zare littafin daga fuskarsa ya zube idanunsa akan sadam yana kuma tambayar lafiya?,da idanunsa kawai ba tare da ya buda bakinsa ba.
Wani abu me tauri sadam ya hadiye maimakon tuni da yakeso ya yiwa haisam akan wace giwa? Da kuma irin girman matsayinta a agadez dama nijer gaba daya. Wani mugun kwarjini haisam din yayi masa,har kwarjinin dake cikin idanunsa suka danne girman mamaki da kuma girman matsayin zaituna dake gilmawa cikin zuciyarsa,sai ya miqe a hankali yana juyawa,cikin ransa dauke da zulumin yadda zaya isar da saqon ga sarkin gida daya tabbatar zai gayawa yalwa ne ba tare da shi ya kasance mai laifi ba.
"Obbo" Abdii ya kira sunan haisam a hankali.
"Ya akayi?" Kawai yace dashi ba tare daya dauke idanunsa daga kan littafin ba.
"Baikai lokacin da zasusan naka matsayin ba da kuma waye kai?" Shuru haisam din yayi,har abdii ya fidda ran amsawarsa,sai kuma ya zame littafin yana duban abdii da dukka idanun nan nasa masu tsananin kwarjini.
"Banzo nan na zauna na rayu dasu don nuna musu girman matsayina koni waye ba......nazo ne don cimma nasara.....nasarata nake nema bawai jaddada matsayi ba". Shuru abdii yayi,yana duban sanda haisam din ya miqe yana ajiye littafin
" Ka shiga dashi ciki......lokacin sallah saura mintuna kadan,kayi alwala zamu wuce masallaci,sannan ka shaidawa salaana,gobe da dare yazo ya daukeni a hanya.....zanje gida" Dan dubansa kadan abdii yayi sanda yake tattare litattafan,daga yadda yayi maganar kamar ya gaji da komai ma,sai ya amsa masa yana dauke sauran takardun ya fara wucewa ciki.
Parlor din farko ta dawo ta zauna,muhallin da hadimanta suka fiya kai kawo a cikinsa. Tanaso a yau ta sauke masa wani kaso mafi girma cikin izza da girman da yake tunani ya samu,tanason ta rage masa kaifin abinda yakeji a kansa idan ma har wannan ya soma tasiri a kansa. Ta zabi tayi hakanne gaban hadimanta mata don yafijin kunya,yasan kuma shi din ba kowan kowa bane,ba kuma komai bane.
Wayarta ta ajiye gefe tana duban yalwa sanda take shigowa Parlour din,daidai sanda hadimanta uku ke aikin shirya mata gabanta da kayan marmari dana motsa baki duk da bata buqaci hakan ba,amma ta maida musu shi al'ada saboda nuna cikar izzarta.
"Ina fata kin sanar dashi saqona.....don bani da lokacin zaman jira,ina da abubuwan yi da yawa a gabana" Ta fada cikin zaquwa da son isowar tasa,saidai tana qoqarin binne hakan da izzarta.
"Kiyimin aikin gafara,amma yace bazai samu isowa yanzu ba......akwai qananun abubuwa da yakeso ya kammala". Ba hadiman dake kai kawo da masu shirya mata kayan maqulashe a gabanta kadai bane suka kadu da maganan ba......hatta da wadanda ke nesa kadan da gurin saida hakan ya nuna jikkuna da fuskokinsu,don daya daga cikinsu saida apple din da take qoqarin yankawa ta subuce a hannunta.
Mammina tabi apple din dake gangarawa gefe da kallo tamkar tana kallon faduwarta da kuma gangarewar mutuncinta da tsiyayewarsa a idanun duk wani wanda ke qasanta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/21, 19:16] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 35*

Ta tabbatar apple din ta fadi ne bawai don abun yazo bane a al'adance yadda aka saba......ta tsinkayi dalilin faruwar hakan da kallon data yiwa idanun kowaccensu. Wani irin abu me ciwo yana sukar mata zuciya ta maida dubanta ga fuskar yalwa.
"Hukunci ya shafeki.......ta yadda nan gaba zaki san yadda zaki dinga isar da saqonnin magana kunnuwan zaituna.....dole ki koyi ladabin isar da saqo yalwa.......ki tashi ki nemi tamim kice ya tabbatar ya kawomin sheikh gaba nan da mintuna talatin.......a gaya masa bijirewa kirana bazai haifar masa da d'a me ido ba,bijirewa kirana kuma yana daidai da qarewar kwanakin zamansa cikin masarautar nan". Gaba daya jikin yalwa kama rawa yayi,tsananin tashin hankali yana saukar mata,abinda taketa tsoro kenan,wannan ya sanya ta dauki kusan mintuna goma tana juya da sigar da zata isar mata da saqon,don amsarsa ta gigitata fiye da yadda zaitunan ta gigita. Dole ta tashi,don bata bata damar yin magana ba,idan kuwa har ta sake tayi tayi imanin qaruwar laifi da kuma hukunci ne a kanta,saita juya ta sauka tana fita a gurin da sassarfa.
A nutse ya kammala alwalarsa,ya kuma yi taku biyu yana bari muhallin da aka gewaye a farfajiyar tasa saboda alwala irin haka. Tattausan handkerchief ya zaro daga aljihunsa yana rage lemar hannuwansa dake dauke da gargasa,wanda hannun jubah din jikinsa yana tattare ne har saman gwiwar hannunsa dab da dantsensa.
Ba alamun takun takalma saboda gurin shimfide yake da lafiyayyar grass carpet.......amma cikin jikinsa yakejin kamar akwai wanda idanunsa ke kansa,kamar akwai wanda ke tahowa nan inda yake.
A nutse ya cira idanunsa yana duban shiyyar da yakejin motsin takun na tunkarosa,sai ya zube idanun nasa gaba daya akan tamim dake takowa da wani irin karsashi da cikakken kuzarin dake nuna da dukka lafiyarsa yake isowa gareshi.
Tun daga saman kansa zuwa qafafunsa wani irin abu me qarfin gaske ya ratsashi,wanda ya fito kai tsaye daga idanun haisam zuwa nashi idanun. Samun qafafunsa yayi da yin laushi,kuzarin daya shigo dashi gurin da zummar tasa haisam din a gaba har zuwa gaban mammina sai ya nemeshi ya rasa. Sai haisam din ya zare idanun nasa cikin nutsuwar nan tasa yana sake hannun rigarsa a hankali. Ya karanci komai dake cikin idanunsa,ya kuma karanci da yanayin da ya tunkaroshi,saidai ya sani.....koda wanda yafi tamim hadari ne.....koda wanda yafi tamim jin power ne ba abinda zai iyayi a kansa.
(Akwai addu'o'in da muddin suka ratsa jikinka ba wani abu dake karyaka sai qarfin ikon Allah.....tsananin ambaton Allah yana bada wannan kariyar,ba sihiri bane,ba kuma tsafi bane).
"Barka da yammaci" Tamim ya samu bakinsa da furtawa
"Kana lafiya?" Kawai ya amsa masa gaisuwar da tambaya
"Lafiya qalau alhamdulillah......" Sai ya danyi shuru sannan ya tattara dukka jarumtarsa.
"Saqo ne daga uwar gida giwa......tace na shaida maka,mafi girman kuskuren da zaka aikata a rayuwarka shine ka bijirewa kiranta........yin hakan daidai yake da kawo qarshen zamanka cikin gidan nan dama yankin agadez gaba daya.......ta umarceni dana shaida maka cewa,kayi gaggawar amsa kiranta,ka ajiye dukkan abinda kakeyi ka sameta a inda ta buqata cikin mintunan da basu haura biyar ba". Yakai qarshen zancan yana zubawa haisam idanu don ganin iya adadin tasirin da maganar tayi masa. Saidai baiga komai tattare da haisam din ba,baiga sauyin nutsuwa ko kadan a tare dashi ba,hasalima wani tattausan murmushi yaga ya saki,sannan a nutse ya daga idanun nan dakewa tamim wani irin tasiri ya dubeshi.
"Ka shaida mata ka gayamin,kuma naji......zan amsa kiranta idan na kammala uzurin gabana kaman yadda na fadi da farko" Abinda ya fadiwa tamim kenan a nutse,sannan ya fara zura takalmansa a dogayen fararen qafafunsa ya soma takawa a nutse yana barin gurin.
Da kallo kawai tamim ya bishi yana jin wani irin madaukakin mamaki yana ratsashi. A karon farko,a kuma tarihin mammina......a tarihin rayuwarta kaf cikin agadez an samu wanda ya tsaya ja in ja da umarnin mammina giwar agadez.
Har wani irin tashi tsigar jikin tamim takeyi,don yana auna irin girman hukuncin da mammina din zata sanya ayi masa. Yana hangen irin baqar azaba da baqin hukuncin da zai fuskanta daga gurinta,yana tausayin yadda daukakar da sultane yayi masa ya rudeshi.....shi kansa a yanzun da yake takawa don isarwa da mammina saqon abinda ya fada cike yake da fargabar yadda zata karbi bayanin.
"Fadi abinda ya gaya maka kai tsaye,ban kuma lamunce ko boye ko ka sauya koda harafi daya cikin zantukansa ba" Ta fada tana jin jikinta yana tsuma saboda tsananin mamaki da bacin ran daya shayar da ita.
Ajiyar zuciyar samun sassauci tamim ya saki. Wannan damar data bashin sai ya zamana kamar sassauci a tare dashi,don haka bai boye din ba,ya fadi ya kuma dora da fadin.
"Ya cancanci ya fuskanci kalar hukuncin da wani a yankin nan da gidan nan bai taba ganin irinsa ba......saboda me sha'awar gwada koda irin hakan ya kiyaye" Tamim din ya fadi zuciyarsa cike da hassada da kishin haisam. Guraben da ya samu a gurin sultane da morsa.....gurabe ne da matsayin daya jima ya shafe lokaci me tsaho yana nemansu bai samu ba. Wasu matsayine da suka kasance qarshen mafarkinsa a kowacce rana,amma rana tsaka an samu wanda ya samu wannan gurbin a taqaitaccen lokacin da idan aka kwatanta da nasa shekarun daya kwashe daidai suke da qiftawar idanu.

"Shi yake da ikon zabar lokacin amsa kiran masarauta?"