← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 101

Sashe 42

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru ya ratsa dakin,haisam kallonta da wani irin duba da takejin kamar yana toxartata ne ko kuma qoqarin karantar dukkan wani plan nata.

"Zai iya yiwuwa......amna zartarwa a yanzu ba na daya daga cikinmu bane....saidai ki taimaka wajen tabbatuwar amincin amanonin rayukan dake tsakanin hannunki da na sultane.....saini yanzu da aka sakani a ciki zuwa lokacin da zan miqa muku amanarku" Yakai qarshe yana miqewa a nutse,yana kuma jin yakai gejin maganganunsa,yana sake ji a ranshi tako ta ina matar ta tabbatar ABAR ZARGI TA FARKO!.

Yadda take takawa a nutse yake tabbatar mata fita zaiyi,hakan kuma yana nuna zai tafi ne koda bada izininta ba,koda batace ba,koda kuma bata gama fadin abinda ke ranta ba,wanda tana da tambayoyin da amsarsa ce kadai zata gamsar dashi.

"Kabi a hankali sheikh haisam......masarauta tana iya hadiye baqi ba tare da ganin koda burbushin da za'a bi diddiginsu ba......karka manta gidan nan nawa ne,kada kayi abinda zai sanya da kanka ka fahimci KAI DIN BA KOWAN KOWA BANE" Wani faffadan murmushi sama dana dazu ya kubce masa,ya sakeshi a nutse ba kuma tare daya waiwayo ba.

Ya yadda kalaman baki sune abu na farko dake fara fada maka WAYE WANE?. Ya aminta su din wasu maqullaine da a yanzu suka bude masa wata qatuwar qofa da zai sake zurfi a bincikensa

"Gida mallakin sultane ne.....ina tsaiwa daidai iyakokin da zasu amintar dashi ne shi kadai.......isata kuwa....." Ya fada yana waiwayowa a nutse.

"Lokaci yana tafe da zai baki amsarta......na isa? Ko akasin haka?" Ya fada yana tsaiwa daga nan gami da bata space,saidai bata iya cewa komai ba,wannan ya bashi daman juyawa yana ficewa,saidai duk da hakan bai hanashi jin furucinta na qarshe ba.

"Zan tabbatar da cewa na nunawa duniya kai din ba kowan kowa bane.....zan nunawa duniya baka isa a komai ba face zallar malami me cin takarda allo da tawwada".

A nutse ya zare Device din daga Kunennensa don ya fara jiyo karadin omari.

"Ina mamakin yadda yariman jimma yake iya dauke wadannan kalaman.....don Allah ko sau daya kayi abinda zatasan your not an ordinary man" .

Goshinsa kawai yake murzawa a hankali yana qoqarin calming kansa. Idan ya biyewa zancansu omari shirme zasuyi kawai a agadez,su kuma bata lokaci a banza cikin agadez din,su komawa Ethiopia a empty zero hands.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

____**Hannu ta miqa tana sake jawo takardar tana fidda wani huci daga bakinta zuciyarta tana jin kamar zata fasa qirjinta ta fito. A karon farko a rayuwarta ta d'an d'ani yadda dacin jayayya da qasqantar da isa take ga wanda yakejin ya isa yakai ta kowanne fanni. Idanunta ta maida saman dokokin tana sake bitarsu tun daga farko,tana so kuma ta dire kan sanya hannun sultane din da yayi iqirari akai.

_daga wannan daren,bayi da hadimai ba'a lamunce musu zirga zirga tsakanin sassa ba daga bayan sallar isha,har sai da rubutaccen izini_

_Dukkan masu ziyara zuwa cikin kowanne sashe zasu rubuta sunayensu asalinsu yare da qasarsu,da dalili na ziyarar kaman yadda tantancewa zata hau kan kowanne hadimi da bawa dake rayuwa cikin MASARAUTA daga gobe_

_an haramta kowanne ganawa da bayi a kebantattun dakuna ko gurare_

Kasa qarasa karantawa tayi,saboda tsananin bugu da qirjinta yakeyi. Tanajin kowacce doka qwaya daya tana kiran sunan ZAITUNA ne kai tsaye,saita zarce da idanunta kan sa hannun sultane. Sa hannu ne da tafi kowa sanin girma da qarfinsa. Sa hannu ne daya kasance na daban wanda muddin sultane yayi irinsa saman takarda to kowacce magana ce komai qarfinta ta zama TABBACIYAR da babu sauyi a cikinta!!!.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/22, 19:59] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 38*

"Yalwa!" Ta kira sunanta kai tsaye a yau din da kanta.

"Ki nemomin tamim yanzu.....ki gaya masa kada yazomin da tsohon labari,sabuwar magana nake son ji" . Umarnin daya qara yawan rawar jikin yalwa da son cikashi,wataqila wannan ya shafe hukuncin da take zaman jiran fuskanta kan aikenta na dazun.

★ "akwai boyayyu kuma nannadun al'amura masu girma da yawa cikin masarautar nan......haisam,akwai wani abu daban dake cikinta bayan abinda muke nema.....akwai wani abu na daban dake faruwa bayan bincikenmu......girman abinda ke cikin masarautar nan yafi qarfin princess akhnan kawai....yafi qarfin rikicin cikin aurenta kadai......inaji a jikina haisam.....matar nan tana hadarin gaske,me yasa ba zaka taimaki sultane ba?." Omari dake zaune suna fuskantar juna shida haisam ya furta damuwa zaune fal saman fuskarsa. Wani irin kallo haisam yayi masa yana qoqarin daidaita kansa tsakanin idanun omari din.

"Kasan me kake fada kuwa omari?" Ya masa tambayar calmly,saidai idanunsa na nuna girman abinda yake fadi din.

"I know haisam.....na sani" Ya fadi kai tsaye yana duban idanun haisam,yanason ya fahimci da gaske yana jin interest na fadada bincikensu da bin diddigin cikin gidan.

Kallon kallo ne ya wanzu a tsakaninsu na wasu sakanni kafin haisam ya zare idanunsa. Da gaske ya karanci tunanin omari,kuma da gaske yake fadin abinda yake fada din,ba wasa sam a ciki.

"I wasn't cross boarders to save the palace" Ya furta da wani irin accent dake nuna tasirin yaren oromo cikin harshensa,yayi maganar ne kuma yana dauke dubansa daga kan omari,yana maida dubansa ga cup din gabansa da omari ya zuba masa coffee.

Idanu sosai omari ya zubawa haisam din,a karon farko yana mamakin sauyawar dabi'ar haisam din. Baida kutsa kai kan sha'anin mutane.....amma yana damuwa kan mutumin da duk yaga zai cutu muddin yana da ikon taimaka masa. Me yasa a yau a yanzu yake kauda kai daga taimakawa akhnan da mahaifinta?.

"Amma......me yaci gaba da shigo da issue dinta cikin maganamu inde haka ne?" Omari ya jefa masa tambayar. Sau daya tak ya daga ido ya kalli omar,sannan ya dauki mug din coffee dinsa ya shanye,kana ya miqe a nutse yana zube hannayensa cikin aljihun trouser din jikinsa,ya taka a hankali zuwa bakin qarfen balcony din.

"Saboda tana kanannade da wadda nake zargi....dole a wasu lokutan maganan case dinta ya dinga ratsowa cikin aikinmu" Ya amsawa omari a nutse can qasan zuciyarsa kuma yanason canko dalilin da yasa omar ya masa wannan tambayar. Ya sani dukkansu ba wanda ke magana ko tambayar da bata da fa'ida ma'ana ko dalili......ko akwai wani dabi'a ko halayya ta daban da yake nunawa kan abinda ya shafi case din?. Bai iya gano komai ba,bayaso kuma ya waiwaya ya kalli omar kada ya dauka akwai wani abu daban da yake rayawa a ransa. Kaman yasan kuwa kallonshi omar din yake,kaman kuwa yasan neman reaction qwaya daya omari yake daga gareshi.

Ya jima yana raya wani abu a ransa game da haisam din. Bai taba masa wani dogon zance daya shafi akhnan ba.....amma ya dade da sanin wata dabi'a kebantacciya daga haisam din,dabi'ar da baya jin ko haisam din yasan yana da ita,dabi'ar da yasan itace SILA SANADI da saamee da MENELIK suka kasa samun matsugunni a zuciyarsa,duk kuwa da cewa suna da kowanne irin quality da ake buqata na zahiri daga gurin d'iya mace.

"Amma kasan sultane ya amince da kai?....."

".....wannan ne ma ya bani dalili na qauracewa iyakokinsa da shiga al'amuran da suka kebanci iyalinsa.......ina da kishi me yawa da nauyi,yadda bazan bari a kusanci iyalina ba daidai da d'ani ko taku guda ba.....hakanan bazan kusanci iyalin kowa da zarafinsu ba sai akan wanda gaskiya take buqatar tayi adalcinta a kansa" Ya qarashe maganar yana waiwayowa idanunsa cikin na omari.

Wani kallon kallon suka sake yiwa juna,sai kawai omari ya jinjina kansa a hankali sannan ya sauke idanunsa yana cewa.

"Nan da kwanaki uku maleek zai kawo maka ziyara,ba kuma iya gidanka kawai ba,har cikin masarauta yake sha'awar shigowa"

"Allah ya kaimu" Ya fadi kawai cikin nutsuwar rai. Dukkanin aminan nan bashi da haufi a kansu,sunsan boyayyen aikinsa da ko cikin ahalinsa ba kowa bane ya sani,tsananin amincin dake tsananinsu ya sanya sukasan kowanne doka da strategy na aikin,don haka bai shakkan haduwa da kowannensu a kowanne lokaci a kuma kowanne irin yanayi,bare maleek da abubuwansu da yawa yazo daya,saidai ta wani fannin sukance maleek ya fishi sauqin sabo da jama'a,duk da shi dinma SARAUTA na yawo a jininsa.

*MAMMINA*

Abinda takeji a ranta a lokacin wani irin yanayi ne da tun zamanin SAFEENA bata qara jin irinsa ba. Wani irin qanqanci takeji har a cikin jininta,wani irin tozarci da ya sanya takeji wani irin zafi saman fuskarta kaman an watsa mata borkono.

Kafin tamim ya iso tafisu ta rigashi isowa,tayi dukkan me yuwuwa ta kwantar da hankalin mammina amma hakan bai samu ba.

"Wai me kike tsoro game da malamin dake rayuwa qarqashin alfarmarku?" Kai ta jijjiga sosai tana gote da hannayenta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Ba malami bane gama gari......ba irin malamin da kika saba gani bane.....wannan idan na runtse idanuna ZAKI nake gani a gabana tafisu.....idan na kulle kunne na TSAWA nakeji tana fita a bakinsa maimakon magana irin ta kowanne dan adam.....shi ba irin kowa bane tafisu......tabbas akwai wani abu na daban a tare dashi". Shuru tafisun tayi,tana son gwargwaje magangun mammina cikin ma'aunin nazari da lissafinta,amma sai sallamar tamim ta yanke mata wannan hanzarin.

"Me ake ciki game da labarin Ethiopia?" Ta tambayeshi kai tsaye. Bai zauna ba,don bata bashi wannan damar ba yayi qasa da kansa ya soma magana cikin girmamawa.

"Sun gaya min,akwa alamu gwada biyu da suka gwada akwa wani shinge daya motsa daga muhallinsa.....alamu ne ba'a samu tabbaci ba"

"Su maida kai akan wannan alamun!.......su bani tabbaci a nan kusa!!" Ta furta atsawace tana jin wani abu yana motsawa daga qasan zuciyarta,tamkar an fusgi zuciyartata an kuma jijjigata.
Chapter 42 · 0% Book details