← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 101

Sashe 33

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kudade ne masu kauri ya sanya aka shirya masa su cikin qasa da awa daya kafin xama taron,ya fiddasu ne cikin asusunsa na rabon tallafi ga marayu da iyayen marayu da ake gudanarwa qarqashin kulawa haadeem cousin dinsa. Bai tsaya iya Ethiopia kadai ba,tallafi ne daya shafi kowacce qasa cikin qasashen africa......wannan karon ya sanya aka karkato dashi nijer din.

Yanaso ya fara iske abdii,amma kuma lokacin sallah ya riskeshi,sallar kuma tana cikin abu na farko da dukka kalar tsananin daya shiga baya wasa da lokacin ta,baya kuma bari ta kufce masa,don haka ya wuce masallaci kai tsaye kawai.

*MAMMINA*

Banda tarin izzar da takeji da babu abinda zai hanata sauka daga motar kafin isowar hadimanta,saidai duk da yadda hankalin ta ke son samun qarin bayanin sauyin data gani tun daga babbar katangar da zata sadaka da ainihin cikin ginin masarautar mamaki yake mamayarta.

"Me yake faruwa?.....ina kika ajiye wayarki?" Ta jefawa yalwa tambayar cikin dakewa ba tare data bari yalwar ta fahimci dan rudanin dake kai kawo saman fuskarta ba

"Taro muka shiga....."

"Wanne iri kenan?"

"Na wayar dakai.......sheikh haisam ya shirya shi.....zan miki bayanin komai.....muje daga ciki" Ta fada tana riqe mata handbag dinta da kyau,tabi kuma sahun hadimanta dake take mata baya a hankali har zuwa cikin sassan nata.

Dukkaninsu suna da iyakarsu,suna da iyakar da yalwa kadai ke iya qetareta,don haka suka ja tunda daga wannan iyakar,suka barta ita da yalwa suna wucewa ga parlor na gaba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Banason maimaita tambaya ta....." Mammina ta fada daidai sanda take tsaiwa tsakiyar parlor din ba tare data dubi yalwa ba.

"Taro ne aka shirya na awa daya kawai" Saita soma siffanta mata yadda komai ya gudana har zuwa tashinsu.

"Ina kyautata zaton yana neman suna ne wajen sultane......yana neman matsayi ne kawai a wajensa.......yanaso ya sallama masa ne dari bisa dari!"

"Tir da kalar tunani irin naki wasu lokutan da basu da wani amfani!!!" Mammina ta dakawa yalwa tsawa tana tsaidata cikin tsananin rudani.

"Allah ya huci zuciyarki" Yalwa ta fada tana yin qasa da kanta cikin fargaba da taraddadin shiga gona ko hurumin daba nata ba,wanda tasan hakan baida alaqa da komai sai sanya kanta a uku da bala'in da batasan wanne nau'i bane.

Wani irin rudadden yanayi ke yawo cikin kwanyarta,a wannan lokacin tafisu kadai take buqata,wadda ta tabbatar ita da ita ne kawai tunaninsu zai iya zuwa daya. Yadda yalwa ta gaya mata yadda komai ya faru ta aje qatuwar ayar tambaya akan komai.....saidai batasan akan ainihin meye take tuhumar ba.....meye kuma bata yarda dashi ba?......kawai tana jin akwai wani abu shiryayye.......akwai wani abu daba daidai ba har cikin ruhi da zuciyarta. Ba kasafai tafiya gasgata abubuwa ba koda abubuwan da suka kasance na gasken ne ba jabu ba......takan dauki lokaci tana sanya idanu da jarraba komai kafin ta miqa wuya da hannu ta karbeshi a yadda kowa yake kallonsa.

"Akwai wanda bai halasci taron ba cikin masu hidima a gidannan?"

"Kowa da kowa ne" Ta amsa mata a qasqance. Ta jijjiga da qarfi,tanason qulla zaren tunanin akan wacce manufa aka shirya hakan,saidai kuma ba abinda kwanyarta ke mata kai kawo akai sai irin hasashen yalwa dai sak.

"Yana neman yabo......yana neman gurbin zama......yanason ya siya soyayyar al'ummar gidan,ta kowacce fuska takara yakeyi da matsayinki". Duk da jerin gwanon wadannan tunanikan amma sai taji yaqi dacewa da abinda ke mata zirga zirga......ta gaza aminta da kalar wannan harsashen sam.

"Dashi aka gudanar da taron?" Ta sake tambayar yalwa.

"Shi yayi dukkan jawabai".

" Kota daqiqa daya baibar gurin ba?".

"Ban gani ba Allah ya taimakeki,dashi aka fara dashi aka kammala". Shuru ya sake ratsa gurin,kafin wata ajiyar zuciya ta subuce mata.

Tana jin bai kamata ta daga hankalinta akan malamin da tasan bai mallaki komai da zai iya challenge nata ba......bashi da wata power......baida wani iko na komai,face tarin litattafan da ta sanadin,ta albarkacinsu yake samu yake sha. A yanzun akwai abubuwa da yawa daya kamata ta girmama ta fadada sanya hankalinta akai. Saidai shi dinma.....akwai dalilai da yawa da suke sanyata take gaza dauke hankalinta a kanshi. Tana iya cewa shine mutum na farko banda IBRAHEEM da taji yana mata kwarjini irin haka,mutum na farko da dukka yanayinsa yake mata kama da wani BASARAKE da IZZA ke kewayewa cikin jininsa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/16, 17:28] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 30*

A kansa ta fara ganin mutumin da tana zaune saman kujera shima yana zaune. A kansa ta fara ganin mutumin dake iya duban qwayar idanunta yayi magana da ita a tsanake. A kansa ta fara ganin mutumin da sam batayi masa wani kwarjini ba ko daya......tarin jaran gwanon wadannan abubuwa suke sanya mata wani yanayi na daban a kansa.

Bawai a kansa malamai suka saba baquntar gidan ba,amma kowa yana rayuwa ne a qarqashin ikonta,gwargwadon yadda takeso ya rayu bisa tasarrufinta.

"Ki nema tamim duk inda yake kice ina buqatar ganinsa a yanzu".

"In sha Allahu.....ki huta lafiya,da fatan za'a gafarceni" Yalwa ta fada ta yunqura ta miqe tana ficewa.

Da idanu tabi yalwa din har sanda ta bacewa ganinta. Ta sauke hannayenta data rungume qirjinta dashi tana jan siririn tsaki. Ta tsani yadda takejin wani fargaba da razani suna ratsata......ba halinta bane batason kuma dabi'ar ta soma keta jininta. Tana da tarin abubuwa da takeso ta aiwatar,wadanda suke buqatar JARUMTA da RASHIN TSORO,abubuwa masu yawan da raguwar zuciya ba zata aikatasu ba.

Tsam ta miqe ta isa ga freezer din dake ajiye tana aikinta,ta bude da kanta ta zaro ruwa me sanyi sosai. Tana neman abinda zai sanya kanta ya huce......tana neman abinda zai sanyaya mata tunaninta ko kwanyarta zata dawo aiki da kyau.

Tana dora gorar saman freezer din sanarwar isowar tamim ya marabceta.

"Zan fito yanzu......bulama ya jirayi tafiyarsa tukunna" Ta fada tana komawa mazauninta na dazu.

Alkyabbar data shigo da ita ta sake maidawa,ta kuma maida yanayinta cikin izzarnan da bata yarda ta gushe daga gareta,ta fara saukowa cikin takun isa da nutsuwar da bata jin takai mata har cikin zuciya.

Har qasa yakai gwiwoyinsa kamar yadda ya saba,bai kuma gyara ba har sai data samu guri ta zauna.

"Ya ake cikin cikin qasar can?" Ta tambayeshi a izzance. Zamansa ya gyara sosai kanshi a qasa.

"Na sanya dukkanin wasu matakai da zasu zurfafa bincike,kuma sun dauki adadin wasu kwanaki akan zasu bani cikakken bayanin dana buqata.....kwanakin ba zasu haura goma sha hudu ba......"

"Suyi qoqari kada su dara sama da haka.....ko nawa suke buqata za'a biyasu......bayanai kadai nake buqata,sautin motsin kowanne me rai.....kowanne dan adam da ya shiga cikin da'irar buqatunmu......ban dauke kowa ba,yaro ko babba,mace ko namiji.....shugaba da mabiyi!"

"Yadda kikeso hakan za'ayi Allah ya qara miki nisan kwana" Tamim ya furta da yaren oromo da yakanyi amfani dashi kadai idan suka kebe irin haka......a muhallin daya tabbatar ba wani mahaluqi da zai iya jinsu.

"Wanne sakaci ke shirin faruwa cikin gidannan qarqashin jagorancinka!" Mammina tayi magana a gaba ta biyu cike da kausasawa me yawan gaske.

Qasa yayi sosai da kansa cikin neman afuwa daya sabawa kanshi kafin yakai ga jin wanne kalar laifi gareshi?.

"Akwai dama wani me zartarwa da tsara wani abu cikin gidannan ba tare dana sani ba?.....ba kuma tare dana sahale ba?,har kuma ku mara masa baya?" Tayi tambayar tana jin wani sabon bacin ran yana motsa mata sama dan dazu.

"Tuba muke giwa.....tuba muke uwarmu maganin kuka mu......taron yazo ne a bazata......lokacin da kika fita a gidan,ba damar neman izini ko sanarmiki......sannan duban matsayinsa a gurin sultane daya sahale masa aiwatar da komai,sultane ya shaida mana umarninsa daidai yake da nashi,haka girmamashi daidai yake daka girmamashi.....shi din d'a ne a gurinsa halak malak......"

"Ya isheni haka tamim!" Ta fada tana daga masa hannu.

"Kuskure na farko da zaku fara yi kenan,ku yadda ku daidaita matsayina da nashi......saidai nan gaba kadan zan cire masa wannan girman daka zuciyar dukkan wanda yake ganinsa da girman!" Ta fadi cikin cin alwashi. Wannan alwashin nata ne,ba wani daya isa yayi mata shiga hanci da qudundune ta qyaleshi!.....ko wayeshi!.

"Kada ka yarda irin haka ta sake maimaituwa......duk qanqantar zartarwa ina buqatar ta fara wucewa ta gaba na"

"An gama"

"Akwai wani abu ne daya haifar da rashin aminci ko wani motsi da ba'a amince masa ba?". Shuru tamim yayi,kafin ya girgiza kai a hankali.

"Banga komai ba......saidai wannan kwarjinin nasa daya cika gurin gaba......"

"Tamim.......akwai wani me kwarjini ne sama da nawa?"

"Babu" Ya amsa mata cikin qanqan da murya

"Yaushe idanunka suka fara ganin hakan?"

"Ayimin aikin gafara" Ya fada yana rusunawa,abinda ya haifar da shuru kenan.

"Zaka iya wucewa,ka tuntubi bulama ko akwai wani sabuwar alama ko sabuwar masaniya?". Ta fadi tana jin ranta yayi jagulewar da bazata iya ganin bulama bama.

"An gama Allah ya baki nasara" Ya fada yana miqewa,ya sake kai gaisuwar ban girma sannan ya juya yana fita.

Iska ta fesar,tana son ta riski akhnan don auna gwargwadon matsayar tunaninta,tanason kuma ta samu layin tafisu,don tana son shirya komai na auren akhnan ta fanni biyu. Bangaren akhnan din da almaz da takeso kowanne motsi ya tafi da babban motsin da zai ajiye alamun GIRMA cikin dukiyar aure shigarsa da cikar kamalar da zata masa jagorancin samun KARBUWA a zukatan kowa da kowa.

*MORSA SAFIYYA*

A nutse ta amsa sallamar nanny tana ajiye carbin dake hannunta a gefanta saman lallausan kujerar da take zaune a kai.
Chapter 33 · 0% Book details