← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 101

Sashe 83

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na nesanta kaina da ita ne saboda banason ta saba dani......nayi hakanne saboda banaso ya zame mata wani ciwo a zuciyarta.....saboda ina ban hangi ta inda zata samu yadda take so ba daga gareni,ban shirya ba nanay......ina da abubuwa da yawa a gabana" Ya fadi da dukka gaskiyarsa da fatan nanay ta fahimceshi.

Shuru ya ratsa tsakani kafin nanay ta saki wani murmushi me sauti kadan.

"Sai yaushe?.....muhammad sai yaushe?,ko kasan kwanaki kadan suka rage aje nemawa hussam aure?ana kammala bikin rumaisa?" Maganan yadan bashi mamaki,amma yasan hussam,rawar kai plus farinjinin 'yammata.

"Hussam dai?" Ya maimaita da dan mamaki. Murmushi nanay ta saki.

"Kowanne burina ya cika haisam banda abu biyu,ganawa da 'yan uwana da kuma ganin surukai da jikokina.....ina buqatar ganinku dukka da aure" Bai iya cewa nanay komai ba,don anzo bangaren da yakeji bashi da wani shiri akai,kuma shidin ba wani gwani bane ta wannan maganar musamman da nanay din da kunya da nauyi irin na tsakanin uwa da d'a yake ratsawa a tsakaninsu.

"Kasan saamee tana kwance ana qara mata ruwa?.....ko tsananin damuwa ce a kanka ta jawo mata haka?" Maganar ta bashi mamaki sosai,ya danyi ciki ciki da idanunsa yana sauraren nanay. Koda bata ganinsa tasan yanayinsa,ta gyada kanta a hankali.

"A shawarce.....me zai hana ka ceto saamee koda ta hanyar bata kulawa muhammad?,wataqila zuciyarta ta samu sassauci?". Wani shurunne ya sake ratsawa a tsakaninsu,a nutse ya motsa labbansa masu kyannan.

"Indai hakan kikeso nanay sai ayi" Ya fadi a nutse yana jin wani nauyi ya sake hawa kansa.

Idanu Nanay ta lumshe,murmushi mara sauti yana qwace mata,alfahari da samun yaro irin haisam din yana sake shigarta.

"Allah yayi maka albarka.....Allah ya shiga dukkan al'amuranka,yadda kake qoqarin ceto damuwar wasu Allah ya ceto damuwarka"

"Ameen Ameen" Yake amsawa da ita yana ware tafukan hannayensa. Addu'ar nanay wani abu ne da baya wasa dashi komai gajatarta

"Zan sanya noora ko Aanani su dinga sanar maka komai a yanayin da ake ciki" Da wanna sukayi sallama da nanay din,ya zare wayar yana ajeta gefe nannauyan ajiyar zuciya tana kubce masa.

"Ya ake ciki man". Maleek ya fada yana daukan gorar ruwan dake gaban haisam din ya fara zubawa da kansa a cup. Kai ya girgiza a hankali yana nutsa yatsun hannunsa cikin sumarsa wadda ya yafa amama saman kansa. Iska ya sake furzarwa daga bakinsa,saidai ba wanda ya samu daman cewa komai ta bayyana.

Falaak ce,dauke da kyakkyawan kwandon data cikashi da fresh 'ya'yan itatuwa,irin wadanda tassn akhnan na matuqar so. Kai tsaye daga lambunsu ta fito,ta kuma debosu da zummar zuwa ta kai kitchen su gyara ta wucewa da Akhnan din,dukka tanayin haka ne don cika alqawarinta data yiwa morsa safiyya.

Gefe daya wani sawai takejin qirjinta,nauyi me girma ya sauka ya kuma ragu daga zuciyarta. Farincikin kawai data sanya morsa safiyya ya isheta,tana jin wani dadi da yadda abinda tayi ya faranta ran morsa din.

A hankali idanunsa ya sauka a kanta sanda yake tsakiyar shan ruwan,daga omar har haisam da suke magana a tsakaninsu ba wanda ya lura da ita,sai qarar tarin qwarewar maleek. Haisam ne ya fara ajiye dubansa a saitinta sanda take wucewa ba tare data ankara dasu ba,sai kawai ya janye sannun da yake niyyar yiwa maleek din ya jefeshi da harara.

"Saika tashi ka bita ko?" Kamar baisan gatse ba,kamar bai fahimci gatse haisam din ya masa ba,ya kurbe ragowar ruwan daya tsaida masa tarin,ya ajiye cup din ya miqe da kuzarinnan nasa ya soma takawa yana bin bayanta.

Siririn tsaki haisam yaja......wato maleek zafin kai kawai yakeson qara masa,don haka ya miqe a nutse ya dauki wayarsa kadai yana juyawa zuwa hanyar da zata sadashi da sassansa,sai suka bar omar a tsakiya a zaune ba tare da yasan shi wacce tashar ya kama ba,qarshe ya zabi satar kallonsu maleek,don ta nan bangaren yasan zaifi samun labari me kyau da armashi.

Saura kadan tayi missing numfashinta sanda taji sallama a bayanta da wata irin nutsatsiyar murya. Ta tsaya cak ba tare data juya ba,muryar dai bata mata kama da muryar daya daga cikin hadiman gidan ba,to waye?. Sai maleek ya zagayo gabanta yana bayyana kamar me jiran takai ga tambayar kanta da kanta din.

Kai tsaye idanunsu suka gauraya guri daya,sai taja da baya kadan tana jin wani kwarjini tattare dashi. Murmushin dake fita saman fuskarsa ya daki zuciyarta da wani irin yanayi me nauyin gaske,tana jin kamar gurbi da muhallin loneliness da takeji a zuciyarta yana cikewa.

"Kawo na tayaki mana kona samu albarkacin princess?" Yayi maganan yana dage mata dukka girarta biyun. Kasa musantawa tayi,duk da batasan wayeshi ba,abu daya dake bata mamaki shine kwarjini da takejin yana mata masu cika idanu,shige wadanda take gani tattare da sheikh haisam,sai kawai ta miqa masa kwandon,yarima maleek din sai gashi da riqon kwando yana kuma jera kafada da ita a nutse suna takawa zuwa ciki ba tare da kowa yace da danuwansa komai ba.

*HAISAM*

A nutse yaji an kirashi da sunan da sukafi kiransa cikin masarautar na SHEIKH MUHAMMAD. Sai dakata yana juyowa a nutsensa. Me wada ne yake isowa gurin,cikin girmamawa ya rusuna yana fadin

"Barka da wannan lokaci" Murmushi kadan haisam din yayi yana bawa mewada din hannu,amma sai ya noqe. Wani girma suke bashi,wanda shikuma koda a jimma ba kasafai ya fiya son irin wannan abun ba.

"Musabaha a musulunci abune me matuqar muhimmanci,kankare zunubai da sadar da soyayya tsakanin bayi,assalamu alaikum" Ya qarasa fada yana sake bawa mewada hannu.

Cikin jin nauyi,cikin jin girman haisam din yana kai masa ko ina ya bashi hannu suka gaisa. Me wada ya zare hannun bayan sun kammala gaisawar yana girmama zatin Allah,da yadda ya sanya wasu halittunsa tun a duniya suka banbamta da wasu,wani irin laushi da qamshi tafin hannuwansa kawai keyi.

"Giwa ce tace a sanar maka tana son ganinka". Dubansa sosai haisam yayi,aiken yana dan saukar masa da mamaki qasan ranshi,amma sai ya gyara tsaiwarsa yana duban mewada.

"Ka shaida mata ka sanarmin,zan kuma amsa kiranta daga yanzu zuwa kowanne lokaci" Kai mewada ya jinjina a hankali. Qarfin halinsa,jarumtarsa da yadda yake iya aikewa giwa saqo kai tsaye game da abinda yake ranshi kuma ra'ayinsa kenan yana burgeshi qwarai.

"Zan shaida mata,na barka lafiya" Ya fada yana miqewa sosai ya fara takawa yana barin gurin.

Hannunsa ya goye a bayansa,sannu a hankali cikin nutsuwa yaci gaba da takawa yana nufar sassansa. Tunaninsa yana zurfafa,yana kuma laluben meye dalilin kiran da mammina din tayi masa?.

Daidai sanda zai gifta da qofofin da suka raba balcony dinta da nasa wadda zata kaishi kai tsaye zuwa sassan kowannensu. A hankali Idanunsa suka sauka akan sashen nata,sai ya zare idonsa dakai yana wucewa gaba.

Wani bangare na rayuwarta ya soma qoqarin dawo masa fes a kansa. HADARI ne sosai take fuskanta.....hadarin da yake kyautata zaton ya kamata ace hankalinta yakai kai.....amma me ya hanata fahimtar wasu abubuwan?......me ya hanata ta gane akwai QALUBALE?.....akwai GIBI a rayuwarta?. Ta sanya girman kai da izza gaba da komai nata?,bayan akwai tarin yaran SARAUTA da basu kai kansu inda takai kanta ba?.

Samun kansa yayi da jan siririn tsaki,ya dauki tunanin ya ajiyeshi gefe daya,saboda yana ji a ransa akwai wani aiki da yafi wannan muhimmanci da ya kamata ya maida hankalinsa akai.

*MAMMINA*

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Yatsunta kawai take murzawa guri daya sanda mewada yake gaya mata martanin sheikh muhamma haisam. Karo na biyu.....karo na biyu kenan yana fito na fito da martabarta. Karo na biyu kenan yana qalubalantar girman matsayinta naqin amsa kiranta a sanda ta buqaci haka. Qoqarin tauna fushinta da dukkan bacin ranta takeyi ta kuma hadiyesu kada ta furtasu ko ta bayyanasu gaban mewada dake matuqar girmamata da biyayya ga dukka umarninta.

"Zaka iya tafiya" Ta fadi a taqaice. Godiya yayi mata ya miqe yana barin gurin. Wani irin iska me zafi ta furzar daga bakinta,ta bude idanunta sosai sannan ta maidasu ta lumshe ta sake budesu,tana gayawa kanta ne yanzu ba lokaci bane na fushi,yanzu ba lokaci bane na bayyana zafinta ba,lokaci ne na kwantar da kai,lokaci ne na karbar duk wani abu da malamin zaiyi,har zuwa sanda haqarta zata cimma ruwa,a sannan ne zata banbance masa WACECE ZAITUNA?....WACECE GIWAR AGADEZ?.

"Farisa!" Ta kirayi daya daga cikin hadimanta dake can qofa tana jiran umarninta. Da gaggawa ta iso gabanta tana zubewa.

"Zan shiga naga akhnan,bana buqatar iso,bana kuma buqatar a gaya mata zuwa na".

" Hakan za'ayi Allah ya baki yawan rai" Ta fadi kanta a qasa sannan ta miqe itama ta fita.

Kwana da kwanaki tayi bata sanya akhnan din a idanunta ba,ba kuma wai don ta shirya faruwar hakan ba,sai don abubuwan da suka sha mata kai take qoqarin ganin komai ya tafi a tsari. Shirye shirye taketa yi,shiri kota kwana,maganan motsuwar daya daga cikin tarakuna Ethiopia ya tsaye mata a rai,shine kuma abu na farko da take kwana take kuma tashi dashi,sannan da kanta take bibiyar samun tabbacin abun,ta zare wakilci tana ganin kaman bazai mata ba.

Abinda yafi sanya mata wata fargaba shine......ganin yadda aka kasa samun cikakken bayani kai tsaye cikin sauqi kan da gaske akwai wanda yayi tafiya zuwa agadez?. Abinda yake sake luguiguita mata zuciya kenan.....yake sanya mata shakka da wasi wasin ANYA ba wani gagarumin abu bane yake shirin tunkarota?.

*AKHNAN*

Ba zata sake bari wani abu ya taba IKONTA ba.....ba zata sake bari wani abu ya girgiza duniyarta ba......ba kuma zata sake bawa kowa dama ya bude qofar rayuwarta ba.....koda wayeshi.....komai kusancin dake tsakaninsu.
Chapter 83 · 0% Book details