← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 101

Sashe 51

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusancinta da sultane daya karbe......haduwar jikinsu har sau uku duk da har yanzu bata tsakanin yaqini da kokwanto akan shine mutumin hippodrome......shine mutum na farko.....namiji na farko a duniyarta daya taba taba jikinta. Tsaki taja dan siriri tana jin hakan yana mata wani irin zafi,ba namijin daya taba TSALLAKA layikan data shata rayuwarta saishi......a karo na farko ya tsallake mata iyakokinta masu tarin yawa,har yana iya ji da samun confidence ya tsaya a gabanta yana gaya mata magana mai cike da tsatstsauran umarni.

Abinda ya faru kwanaki hudu da suka wuce ya dawo mata. Me yasa saishi kadai?,me yasa saishi kadai ne zai dinga kubutar da ita daga hatsari?. Ko hakanne ya sanya yake ganin kansa a wani abu?,har yake da confidence din challenging nata?.

Aah.....ko a yanzu yanayinsa da abinda take gani a idanun nan masu wani irin haske da kwarjini,tana jin confidence din da yake dashi ba na iya kusanci da muqamin da sultane ya bashi kawai bane......akwai wata jarumta da qarfin hali tattare dashi. Wani irin taku yakeyi da a MASAURAUTA a kuma SARAUCE yake kama da takun QASAITA irin takun isashen basaraken da baya shakkar ko tsoron tunkarar komai.....baya buqatar komai daga kowa.......irin takun da sai me ilimi cikin sarauta yake iya fahimtarsa.

"Me ya hadashi da izza bayan shi din qasqantaccen malami ne kawai?" Tambayar ta sake bijiro mata,wanda ita kanta batasan sau nawa ta yiwa kanta tambayar ba.

Siririn tsakin da yafi na dazu ta kuma saki tana kuma tuhumar kanta kan lissafen lissafen data shiga yi marasa tushe ballantana makama. Ba lokaci bane na noticing dinsa yanzu......me yasa yake bayyana a duk sanda ranta yake a bace?,bayyanarsa me yasa take qara tunzura fushinta?

"Na tsaneshi" Ta gayawa kanta da kanta da wani dan qaramin sauti tana jin gargadin da zuciyarta ke mata na dauke dubanta daga kansa.

Fitar sautin sai ya zamana kamar saukar wani yanayi ne saman gangar jikinsa. Yana iya jin baqon kallo a jikinsa koda bai san ana kallon nasa ba,wani yanayi da aka haifeshi dashi,ya kuma sake masa tasiri sabda yanayin aikin intelligent security da ya zame masa jinin jikinsa.

Ya sani cewa cikin lissafinsa a yanzun akwai boyayyun idanuwa masu yawan gaske dake bibiye da kowanne motsi da kuma takunsa. Yana da wani irin zurfin lissafin da yakan iya auna komai da zai iya kasancewa a lokaci na gaba,don haka cikin qwarewa ya motsa idanunsa yana dagasu a hankali zuwa sashen da yafijin tasirin kallon.

Tsam tayi da ranta bugun zuciyarta yana qaruwa lokacin da taga kaman yanayin tafiyarsa ya canza,duk da a nutse dama can yake takawar amma yanzun ya sake zama low.....zuciyarta ta gaya mata yana dab da daga idanunsa zuwa inda take tsaye,sai tayi hanzarin zare idanunta daga kansa tana gayawa kanta babbar faduwa ce da asara ya sameta tana kallonsa.....ba izzarta bace wannan.....ba martabarta bace,ba kuma darajarta bace. Zaya dauka wani abun dabanne.....wataqila ya dauka yana burgeta ne,bayan a duniya ta bangaren maza shine namiji na farko da takejin taqi jininsa sama da kowa KODA KUWA ALMAZ dake dab da cakuda rayuwarsa da tata.

Saidai kuma inaaaa,tayi wata kyakkyawar makara,da wani irin zafin nama irin na 'yan mazan da suke da gogewa ta fannin bincike ya sarqafe idanunsa cikin nata. Taji wani irin shocked,taji kuma wata irin faduwa da kunya gami da nauyin yadda ya kamata din. Wani bacin rai ya sauko mata sanda taga ya zare idonsa daga nata cikin kallon daya mata da duka duka bai wuce second biyar ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/28, 19:47] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 46*
_________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________

Da baya da baya ta koma tana sake sakin tsaki mai qarfin gaske. Don me yasa?,ita ya kamata ta fara dauke idanunta a kansa daga kallon farko don ta tabbatar masa da qarfin izzarta........me yasa ya rigata dauke idonsa?,me yasa ta bari har ya ganta tana kallonsa?.

"Sufa irin mutanen nan qarfin kurwa garesu......har yanzu na kasa gano siffar malunta ko daya tattare dashi idan ka dauke tarin nutsuwa kwarjini da kamalarsa.....wannnanzaifi kyau da GIDAN SARAUTA BA GIDAN MALUNTA BA". a mamakance ta bude idanunta sanda aisa dake tsaye jikin qarfen balcony din. Batasan sanda aisa din ta isa gurin ba,uwa uba ma sam ta manta dasu.....mamakinta shine na dogon sharhin aisa din na yau wadda ba kasafai ta fiya magana akan mutumin ba.

"Ashe bani kadai nake ganin hakan ba?.......na dade banga namiji irinsa ba......akwai maza ne hurul'eeni a duniya ne?" Shehnaz ta fada tana duban aisa. Dole aisa ta saki dariya sosai ganin yadda shehnaz tayi maganar da dukka iyakacin gaskiyarta.

"Wataqila an fara kawo mana sample daga kansa". A nutse ta miqe ta fara takawa tana ficewa daga gurin,tasan muddin taci gaba da zama zasu sake bata ranta ne akan mutumin da bata qaunar zancansa kwata kwata.

★Duk da ya kasance wani irin salon kalar aure da amaryar bata buqaci gudanar da kowanne shagali a bikin nata ba,amma hakan bai hana sauyawar masarautar ba da yanayin da zai tabbatar maka akwai wani gagarumin abun farinciki da zai faru cikin masarautar kamar na aurar da d'iya me daraja ta daya a yankin agadez dama nijer gaba daya.

A kowacce rana tun daga yammaci har zuwa lokacin da dokar taqaita zirga zirga zata fara aiki qananun wasanni da kide kiden gargajiya mammina ta zube akeyi. Kamar irinsu kidan qwarya wanda ake gaurayeshi da salon waqoqo da tsaffin wasannin al'adu irin na asalin buzaye.

Maroqa da makada musamman mata sai suka samu gurin yasar da zango,kusan wuni mammina keyi tana fidda kyaututtuka masu nauyi ga wanda Allah ya tsaga da rabonsa,kaman yadda zai wahala ka shigo gidan da qoqon barar nema daga taskar GIWA a wannan lokacin baka samu abinda kake nema ba.

Zirga zirgar hadimai ta yaiwaita sosai saboda shirye shiryen tarbar baqin da zasu iso don daurin aure. Abinciccika na alfarma,sutturu masu daraja da tsada take fiddawa kawai anata rabo zuwa ga bayi da hadimai da salon irin kyakkyawar shigar da takeso kowa yayi.

Zukata da dama sun sake nutsuwa da aminta da salon soyayyar da mammina ke gwadawa akhnan. Ko iya fuskarta kadai ka kalla zakasan tana cikin matsanancin farincikin aurar da gudar diyarta a iya hange da tsinkayensu. Yadda take narkar da dukiyarta wajen komai.....kyauta ta bajinta maroqan cikin fada kakarsu ta yanke saqa a cikin kwanakin. Kwana bakwai dukka ba wanda aka daga qafa a cikinsu,har zuwa yanzu da kwanakin daurin auren suka rage biyu tal!.

Ta kowanne fanni,ta kuma kowacce fuska tayi ruwa tayi tsaki,ta hana family din DIOARY HAMMANI tabuka komai akan diyar da take halalinsu ce......tsatsonsu ce. Kakannin da suka kasance su suka haifi SAFEENA amma a dole ta maidasu wash baqi ga rayuwa rai da duniyar akhnan. Bata kallonsu a matsayin wasu shaqiqai nata......ballantana kuma akai ga d'iyoyin qannen mahaifiyarta wato cousins dinta masu tarin yawa.

Duk da idan qaddara ta qaddara zuwansu gurin morsa safiyya da zummar gaisheta,hanya kuma tayi sanadin da suka hadu,tana ganin wasu alamu ko kamanni na jini tattare dasu wanda yake shige da nata.

Rashin wannan sabon,rashin wannan jituwar,rashin wannan shaquwar ya sanya ko a yanzun ba wata cousin dinta tattare da ita idan ka cire falaaq....aisa da shehnaz.

Sai HAIRAAN data iso qasar da yaranta anwaar da Aaaron,wanda wannan karon harda me gidanta daya kasance cikakken buzu,cousin dinta NAADIR. Zata dauki wata biyu aqalla cikin agadez,don ta kwana biyu basu zo ba,don haka da kayanta da yawa ta iso ta kuma fara sauka a masarauta har sai bayan kammala biki kafin ta wuce gidanta dake daura da titin gidan gwamnati.

★★Zaune take kawai saman tattausar kujerar data kasance daga cikin kujerun hutawa na cikin kebantaccen dakin gyaran jikinta. Sanye take cikin wata baqar gown wadda ta zauna a jikinta sosai,ta kuma fidda kyawunta me sanyinnan da wani qarin fayau da fuskarta tayi saboda gyaran gashin da akayi mata jiya daya bashi daman sauka gadon bayanta ya kwanta da wani irin glowing gami da sulbi kamar na 'yar tsana. Uwa uba kuma wani irin sarewa takeji,tana rasa inner peace daga kowanne bangare na zuciyarta.

Ko a yanzun data ware tafukan hannayenta tana kalla,wadanda sukasha zanen jan lalle da yake da wani irin maroon me daukan hankali saman jar fatarta dinnan dake samun tsananin kulawa da tattali......wani irin banbarakwai takejin lamarin idan ta tuna wai jibi zata zama matar aure?.

Akwai wani qunci da takura da takeji sosai cikin zuciyarta,saidai kuma ta laluba zuciyarta kaf bataji tsanar almaz ba saidai wani irin haushinsa dake danqare da ruhinta. Qila bata jin tsanar nasa ne ta yadda bai sake matsa mata da zuwa gurinta ko nemanta ta waya ba.....amma ta tabbatar sai ta sanya almaz ya tsani ganinta a gaban idanunsa,tsana ta har abada,ta tabbatar wannan ne kadai abinda zai iya bata peace da kuma kalar rayuwar da takeso.
Chapter 51 · 0% Book details