← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 101

Sashe 70

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta daga kanta zuwa ga morsa safiyya,zuciyarta na tafasa tana amsar duk wata magana data fita a bakinta tana farfasata,ba abinda zuciyarta ke gaya mata illa mammina take toxartawa da kalamanta. A qasan ranta karon farko tunda ta zauna a gurin tana jin wani zafin mammina ne a ranta akan zaben data mata,tana jin a wannan karon tana da tarin tambayoyin da zata yiwa mammina akan mijin data zaba mata......amma batasan me yasa takejin zafi da baqar magana ko baqar kalma guda daya da aka gaya mata ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Ta daga kai ne da niyyar tsare morsa safiyya da kallon da zai sanya ta fahimci ita din ba kowa bace da zata tasata a gaba da wannan tambayar,ba huruminta bane wannan bata da wannan ikon,amma kuma a yau a karon farko kallon dake cikin idanun morsa safiyya din wasu iri ne......wani kallo ne na daban daya sanyata dole ta juyar da fuskarta gefe tana jin wani abu me kama da tsananin nauyi yana sauka a idanunta da zuciyarta,tana kuma jin girman tambayar da nauyinta.

Siririn numfashi kawai morsa safiyya ta sauke,koda akwai rashin kunya da izza a idanun akhnan,amma ta gama samun amsar ba abinda ya hadata da almaz.

"Alhamdulillah" Ta furta a hankali tana miqewa. Hamdalar ta sake jawo hankalin akhnan din,me take nufi matar?,tana murna kenan da abinda ya sameta?. Me yasa wai ba zata canza ba?,me yasa ma take kiran kanta a matsayin qanwar mahaifiyarta?,bayan tana maraba da duk wani bala'i da zai sameta?.

Har cikin zuciyarta takejin wata nutsuwa tana saukar mata,duk wani tashin hankalinta akan auren yana sake gushewa,tana sake gasgata girman ubangiji da buwayarsa,komai zaiyi akwai hikimarsa a ciki amma ga ma'abota hankali.

*MAMMINA*

Sai data koma sassanta ta sauya shigar jikinta sannan ta nufi sassan akhnan. Sassan da tana sanya qafarta zata shiga morsa safiyya na fitowa da tata,saita samu kanta da wani irin faduwar gaba.

Bin juna sukayi da kallon kallo,zuciyar mammina cike da fargaba da shakku gami da tarin tambayoyin me yakai.morsa safiyya din sashen akhnan haka da wurwuri daga faruwar abun? Kada Allah ya bawa akhnan damar furta komai ga morsa safiyya din,duk da tana da yaqini,tasan abune me wahalar gaske wata magana ta shaquwa ko fahimtar juna ta shiga tsakaninsu. Ta dade da kashe wannan feeling din a tsakaninsu,ta dade da cusawa akhnan ra'ayi da hali na tsananin qyamar morsa safiyya da kuma sanyata a sahun farko na maqiyanta. To amma a yanzu bata da tabbas akan kowa da komai,har saita saita komai yadda takeso yaci gaba da kasancewa.

Sassanyan murmushi morsa safiyya ta saukewa mammina sannan a hankali ta dauke kanta tana fita a gurin cikin cikakkiyar nutsuwar nan tata data jima tana huda zuciyar mammina din..

Raga raga murmushin yayi da zuciyar mammina......ya sake ajiye wata qatuwar fargaba da kuma rashin tabbas a cikin zuciyarta,wannan ya qara mata qaimin sanya kai zuwa sassan akhnan da sassarfa.

Fitar morsa safiyya ta barta da wani irin tunani me zurfin gaske a kanta,tunanin da baiyi zurfi ba taji muryar mammina tana qwala mata kira da wannan muryar da kowanne lokaci take nuna zallar tashin hankali akan dukkan wani mummunan abu da zai sameta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/4, 19:51] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 62*

Idanunta ta lumshe kawai ba tare data waiwaya ba,idanunta ta lumshe kawai tana ci gaba da sauraron muryar mammina din maimakon ta tashi ta fada jikinta kamar yadda ta saba a dukkan wani abu da zai sameta.

Haka kawai yau bata jin saukar muryar saman zuciyarta,a yau din bata jin sautin da yanayin yana ratsa zuciyarta yadda ta saba jinsa.

Sak mammina tayi tana duban akhnan dake zaune kawai,ba wani alamun motsawa ko xuwa gareta kamar yadda ta saba a duk yanayi ko lokaci makamancin wannan.

Gabanta ya fadi,shakkarta da kokwantonta suka dadu,amma sai tayi saurin canza yanayinta da sake takowa gaban akhnan din da sassarfa tana fadin.

"Na shiga uku ni zaituna.......biftu,ya taba lafiyarki ne?" Ta qarasa maganan tana zubewa gaban akhnan,gami da sanya hannunta tana dudduba jikinta kamar me neman wani abu.

"Kiyimin magana mana biftu......na rantse da ubangiji dake busa mana numfashi bazan barshi ba".

" Zaki masa mene?,zaki iya goge abinda ya faru ne?,ko don bai bar tabo a jikina ba hakan yana nufin tabon dake zuciyata ma zai goge ne ko zai warke?,har abada" Akhnan ta amsa mata da wata irin dakakkiyar murya. Sosai mamaki ya tsarga a zuciyar mammina.......wanne irin magana akhnan din takeyi haka?,me takeson fadi?,anya safiyya batayi amfani da wata hanyar ba ta soma gotarwa da akhnan tunani?.

"Kuskurenki ne tun farko.....kuskurenki ne mammina.....kinyimin alqawarin zaki fiddani......amma kuma sai kika sake dilmiya ni cikin wata sabuwar matsalar.....mafi munin matsalar ma da gwara bijirewa maganan sultane da umarninsa akan wannan KARYAMIN DARAJAR da kikayi" Tayi maganar karon farko hawaye na taruwa cikin idanunta,duk da batajin zata bari hawaye ko daya ya zuba daga idanunta wai don aurenta ya mutu,koda zatayi kuka ma,zatayi kuka ne kawai saboda tabuwar DARAJARTA da kuma MARTABARTA.

"Me kikasha akhnan?.....baki da hankali ne?.....ni kikr tuhuma da jefa rayuwarki a wani yanayi bayan dukkan sadaukarwar da nayi?" Ta fadi da wani mugun hargagi da bata taba mata irinsa ba.

Da wani irin kallo kawai takebin mammina,tsawarta tana sauka saman zuciyarta da wani irin yanayi,saboda wani abune baqo kuma sabo da bai taba faruwa tsakaninsu ba.

"Ba komai biftu,na gode na gode" Mammina ta furta tana qoqarin dauke hawayen daya soma zarto mata daga ramin idanunta.

Har Tsakiyar kanta takejin fitar hawayen,a tsahon shekarun rayuwarta ashirin da hudu bata taba ganin duk girman tsanani mammina ta fidda hawaye ko sau daya ba,sai yau?,kuma a kanta?.

BAKI KYAUTA BA taji sautin yana sauka saman zuciyarta. A hankali ta dauke kanta gefe,muryarta dauke da izzarnan dake sake tsananta tsanarta a zuciyar mammina tayi magana.

"Bazanyi magana dake ba MAMMINA.....ina roqonki ki tafi daga nan". Idanu ta zuba mata sosai,tana jin wani abu yana taso mata. Ita kadai tasan me takeji akan yarinyar.......ita kadai tasan adadin kaiwa bango da tayi.

Ba shekara daya ko biyu ba,ta jima tana sanyata hidimta mata bawai kai tsaye ba.......ta jima tana bata umarni masu tarin yawa,kafin ita ta samu daman maidata qasa ta koma karbar umarninta.

"Zan tafi......amma hakan bai yana nufin xan kasa yin abinda ya dace ba a matsayina na uwa.....ko yau she xanbar miki qofata a bude,duk sanda kika buqaceni ina nan ina jiranki" Maganar mammina ta qarshe kenan ta juya tana fita da wani irin yanayi dake nuna sanyin jikinta.

*MORSA SAFIYYA*

Wani irin shuru ne ya ratsa dakin,ba a abinda ke motsi banda bugun zukatansu dake cike da wani irin nauyi. A zaune suke suna fuskantar juna ita da hairaan,gwiwoyinsu suna gugar juna,hannuwan morsa safiyya din dukka cikin na hairaan data kama ta riqe sosai tana matsasu a hankali don samarwa da morsa safiyya nutsuwa,wadda bugun zuciyarta da numfashinta suke fita wani iri.

"Ki shaqi iska sosai momma......ki fitar ta bakinki don Allah" Hairaan ta fadi cikin tashin hankali. Yanayin da take ganin morsa safiyya din a ciki yafi daga mata hankali fiye da labarin mutuwar auren akhnan din da take sanar mata a yanzu.

Murmushi kadan morsa safiyya ta saki cike da wannan qarfin halin nata,idanunta akan hairaan.

"Kina tunanin na rude da yawa ko zan rasa hayyacina?...." Saita girgiza kai.

"Ni da naga mutuwar safeena tsakanin cinyoyina hairaan,naga mutuwar mahaifinki,bacewar ahmad a sanda nafi tsananin buqatarsa,bana tunanin akwai wani abu da yayi saura wanda zai bugani sama da buguwar da nayi a wancan lokacin. Tabbas inajin radadi,inajin tsananin baqinciki da kalar rayuwar da aka shiryawa akhnan take kuma yinta,wannan rayuwar a yanzu ba qaddararta bace.....rubuta mata ita akayi,a wannan karon kuma sai inda qarfina ya qare,koda zan rasa numfashina.....koda zata batar dani kamar yadda tayi mana a faro a Ethiopia. Barazanarta tazo qarshe hairaan.....ku shirya RASANI daga yanxu zuwa kowanne lokaci.....na yarda da amince zan narkar da rayuwata saboda safeena,saboda biftu ". Sosai zuciyar hairaan ta karye,wani irin abu takeji cikin jikinta yana ratsata da yafi girman tashin hankali.

"Ki daina fadar haka momma.... Muna tare dake......tare zamu kawo sauyi wa rayuwar akhnan.....ba kuma tare da komai ya sameki ba.....gyara za'ayi kawai,ba batu ne na rasa rayuka ko salwantar wani abuba" Wani murmushi momma ta saki tana duban hairaan din.

"Hairaan.....kece aminiya guda daya da nake magana da sirri dake.....kinsan komai ba abinda yake boye gaba gareki,amma har yanzu bakisan girman SHARRI da KAIDIN MAMMINA BA......bakisan wace zaituna ba....sannan bakisan wace zeenatu ba.....a kaf tarihinta ni kadaice na tsaye mata a gaba ta kasa bi ta kaina......nasan Allah ne yayimin da girman addu'a. Har yanzu tun bayan shekaru talatin da suka shude baya ban qara kwanciya nayi bacci ba irin na kowa da kowa hairaan,bacci na gaske dama bacci na ma'ana......inda ace nayi hakan da ban haifeki ba,da ban haifi falaak ba,koda tsananin rabo ya sanya na haifeku da a yanzu ba maganata akeyi a nan ba......ba komai falaak zata iya daukewa ba,shi yasa na aiketa kitchen ta kawo madara......amma ke din mun saba binnewa da rufewa dake....."

".....za kuma muci gaba tare momma.......wanne mataki ne kike ganin zai zama na farko don tseratar da rayuwar biftu".

Shuru kadan morsa safiyya tayi,wani abune daya jima yana mata yawo cikin kanta,wani al'amari ne da takejin kamar ana tilasta mata.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Chapter 70 · 0% Book details