← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 101

Sashe 50

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Momma....." Falaak ta fadi a narke tana duban morsa safiyya. Da gaske tana buqatar morsa safiyya tasanmata qamshin nan,tana buqatar turare mai tsaiwa a rai kamar wannan,don tana jin dukka turarukanta suna dakushewa a duk sanda suka gauraya da sassanyan qamshin nan nasa da duk dare yake sanyata rungume pillow da kyau.

"Banason magana falaak,ki koma dashi,zamuje ki rakani,ki kaiwa yayarki a matsayin kyautarki ta farko ta aurenta" Morsa safiyya ta fadi tana laluben faffadan jilbab don yau bata buqatar wata shiga me nauyi da zata bayyana sarautarta ko wani abu makamancin hakan.

Fuska ta kyabe tana jin morsa safiyya ta bata mata duka tsarikanta.

"Mais momma....."

"Ki rufemin baki" Morsa safiyya ta buqata da yaren buzaye wanda ba kasafai ta fiya yiwa falaak din magana dashi ba,sai kawai tayi yadda morsa din ta buqata,ta juya ta fita tana jiran morsa din ta kammala shiryawa,saidai ta qudirta a ranta ko ta yaya saita samu turaren nan itama.

(Kaman yadda na gaya muku,kowanne turare da zan tallata muku kanku tsaye ku siya ba haufi,zamu dawo ku godemin,tasted and trusted).

*AKHNAN*

Hankali kwance take zaune cikin private balcony din nata dake bata daman hangen farfajiyar gidan kusan ta kowacce fuska. Da yammacin dake dauke da wani irin lullumi bayan ruwan saman da aka sha jiya,wanda a yau ya sanya garin y wani lumshe da wata irin iska me kyau da dadi data gauraya da yanayin la'asar

A yadda take zaunen zaka dauka nutsuwa ce a jikinta......saidai ba wata nutsuwa a tare da ita me yawa illa wannan miskilancin nata da izzar da suka gauraya suka bada launin nutsuwa a tare da ita.

Skirt ne a jikinta sai da bai qarasa idon sawunta ba,sai wata cross front shirt data haska fatarta ta kuma dace da slim body dinta dake da wani irin ajiyayyen shape da supplement ko table basu isa su baka irinsa ba. Qaramin baby hijab ta sanya saman kanta wanda ya bayyana alamun tudun tulin gashinta dake daure tsakiyar kan nata.

Qafafunta miqe suke saman ottoman,yayin data tattara hankalinta akan wayar hannunta tana danne dannenta. Ba wani digo ko alama na fara'a sam ko walwala a tattare da ita,kamar yadda ba wani abu daya sauya a tare da ita da zai sanyaka ka kirata da amarya,bayan gyaran data kasance ma'abociyarsa ce dama ita din tuntuni.

Daga gefanta a qasa saman wani lallausan kilishi dan madaidaici aisa ce shehnaz kaca kaca tsakiyar invitation card,iv din da ko sau daya ta daga ido ta kalleshi ma tana jin bata da lokacin yin hakan.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/28, 19:47] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 45*
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Iska aisa ta furzar tana ajiye card din hannun nata gami da dora idonta a kan akhnan din.

"Biftu" Ta kirata a dan tausashe tana jin wani iri a ranta.

"Ehnnnn" Kawai tace da aisa din ba tare data dago kanta ba.

"Ki duba yadda aka tsara events din mana". Kaman ba zatayi motsi kowanne iri ba kafin ta ajiye wayar hannun nata,sannan ta aza idonta akan aisa.

"Aisa......"

"Na'am" Ta amsa mata tana dubanta hadi da karantar kafiya da tabbacin ko me zai fito daga bakinta haka yake ba sauyawa.

"Bazanyi komai ba......ba abinda zanyi a auren nan,ku daina bata lokacinku bakinku da kudinku,za'a daura aure kaman yadda sultane yakeso nayi aure,amma ba wani abu da zai sanya na wahalar da jikina lokacina da kuma tunani na,daurin auren kawai nake jira na koma niamy kan harkokina". Ta sauke maganar a hankali sannan ta dauki wayarta taci gaba da danne dannenta.

Sosai aisa ta zuba mata ido tana tuna badaqalar da taje ta tarar me tarin yawa a sahel couture,wata irin badaqala data tabbatar a yanzu idan akhnan ta jita sai hankalinta yayi mugun tashi,ba zata ma iya gaya mata ba,don zata hada mata tashin hankali ne bayan wanda take ciki. Ta cika da mamakin yadda cikin watanni kadan komai ya dagule haka ba,tana tsaka da bin diddigin al'amarin,saidai ta kasa gano bakin zaren matsalar. Komai ya canza a kamfanin,mutane da dama babu su,an sallamesu an dauki wasu,wasu bayanan duka sun bace suma babu su.

Babban abinda yafi daga mata hankali shine,girman qarfin ikon da aka bawa wasu a cikin kamfanin,na sallama da daukar wanda suke ganin ya dace,gogayya suke da matsayinta dana shehnaz,suna qasa da nasu matsayinne kawai a yanzu a SUNA,saidai a power sun fisu.

Ba komai ta bari shehnaz ta sani ba,don ta fita juriyar abu da cinyeshi,da kuma nutsuwa wajen bibiyar al'amura,shi yasa ko tafiyarta ta wancan satin ta tafi ita daya,yace shehnaz din ta zauna ta kula da akhnan,don bai kyautu su barta haka ita kadai ba.

"Me yasa kike abu kaman bake kika zabi mijin aurenki ba?" Aisa ta jefa mata tambayar da ta sanya akhnan daga manyan idanunta ta zubesu kan aisa. Tambaya ce data sake tuna mata da yarjejeniyarta da mammina.......saidai tambayar da aisa din ta mata sai takejin kamar ta bude baki ta gayawa aisa EH ba ita ta zabeshi ba.......amma sam ba zata taba kwarewa mammina baya ba a sanda ta sadaukar da kanta don ganin nata farincikin.

"Ni na zabeshi.......amma bawai don hakan yana nufin ina sonshi ko ina son aure ba......na zabeshi ne don na amintar da sultane daga fushi dani" Ta qarasa maganan tana sauke qafafunta qasa,sannan ta miqe tsam tana takawa a nutse zuwa gaban balcony din.

"Zanyi abinda ban taba yi ba.....roqo,na roqeku kada ku sake tayarmin da zancan yin wani abu na aure" Ta qarashe maganar sanda ta tsaya gaban qarfen tana basu baya tana kuma fuskantar farfajiyar gidan da ba yawaitar zirga zirga da motsin jama'a sosai,hakan kuma tasan baya rasa nasaba da kawowar yammaci wanda zirga zirga takan ragu saboda kusantowar dokar hana yawon dare cikin masarautar.

Daidai lokacin da yake takowa shida maleek,sanye da kuwaiti slim fit thobe me sulbi saqar qasar kuwait. Dogon hannu ne da ita me wani irin zagayayyen abu a hannun da kuma wuyan jallabiyyar,royal blue data wani irin haskashi da wani irin yanayi daya fidda kyansa da kuma kyan fatarsa dake da wani irin yanayi lum lum. Sak balaren da ya tashi cikin yare da al'adun qasar larabawa,don hatta da amama(rawanin da larabawa kan nada saman kansu me kama da mayafi)sak irin nadin da wayayyun matasan larabawa keyi ne. Gefansa maleek ne,hira suke abinsu,da wannan nutsuwar da izzar sarauta a jikin kowannensu da bazai sanya kaji abinda suke fadi ba ba,magana ce a nutse duk da tana basu nishadi saboda qawataccen murmushin da yake fita saman fuskarsu gaba daya. Baisan me ya sanya maleek yace zaya qara kwanakin da yayi niyyar yi masa ba,saidai koma meye hakan ya masa dadi,yana kuma kyautata zaton maleek din ya karanci yanayinsa a kwanakin ba yadda ya sanshi bane,kamar akwai wani kewa da emptiness a tare dashi,duk kuwa da cewa yana kewaye yana kuma rayuwa cikin mutane.

Daddadar iskar dake kadawa taja sosai tana fitar da ita daga qirjinta a hankali,yanayin dake qara rage mata damuwar da takejin ta mata qawanya a duk sanda zuciyarta ta tuna nata kwanaki biyar suka rage mata a daura igiyarta a hannun wani d'a namiji da sunan mijinta,duk da tana samun sassauci idan ta tuna ba abinda hakan zai sauya ko ya sanya cikin rayuwarta,iya yadda bai matsa da neman sake ganinta ko.wata magana ko qulla wani dangantaka na sabo tsakaninsu ba kawai yana rage mata zullumi fargaba da quncin da takeji.

Idonta ta zare daga kan flower da take kalla ta saukesu a hankali zuwa farfajiyar. Kai tsaye idonta ya sauka a kansa,yana kuma damqe da hannun maleek da yake gaya masa an samo wani littafi da haisam din ke nema shekara guda kenan,babu shi a Egypt babu shi a duk inda yake zaton za'a samu littafin wanda kudinsa ya kama million daya da rabi.

"Surprise" Maleek ya furta a hankali yana jin dadin yadda alamun farinciki suka bayyana akan fuskar haisam din.

Tattausan murmushin nan nasa ya saki,yana jin wani dadi a zuciyarsa. Allah ya jarabceshi da qaunar litattafan addini da kuma karatunsa fahimta da aiki dashi.

"You're a rock star" Murmushi shima maleek ya saki yana duban idanunsa.

"Zamanka a nan English yana qoqarin janye yaren oromo daga bakinka ba?". Kai ya girgiza a hankali,murmushin nasa yana sake fadada wanda hakan ya sake tsananta kyawunsa a bayyane.

"Ba wani yare sama da nawa.....na zabi yinsa ne for security purpose".

Wani abu ya tsarga cikin zuciyarta tana fatan janye idanunta a kanshi. The giant and calm sheikh din yana tafiya da wata irin nutsuwa da yanayin da bata taba ganinsa tattare da wani ba,duk da izzarta bata barinta kallon maza sam sam......wannan ya sanya take qoqarin janye idanunta a kansa,saidai ta gaza aiwatar da hakan.

Tanaso ta karanci meye bambancin da yake dashi da sauran mutane da takejin kwarjininsa yana dukanta har daga inda take tsaye yanzu haka?. Tanaso ta qwaqulo dalilin da ya sanya yake da wannan IZZAR da JIN KAI da wannan calmness din data fassarashi da GIRMAN KAI?.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Chapter 50 · 0% Book details