← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 101

Sashe 87

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan yace zai dorata bisa mizanin dacewa da cancanta.....ko daya bata isa ta tsaya a gurbin da nagartar dabi'un Menelik ba ballantana akai ga saamee. To amma baisan me ya sanya daga Menelik har saamee din suka kasa samun gurbin da ya kamata ace sun samu daga gareshi ba.

_"zuciyarka nason kayi yaqi wajen nema da samun soyayya ne.....bawai ka samu soyayya a bagas har zuwa inda kake a zaune ba"_ wasu daga cikin maganganun maleek suka dawo kanshi.

Kai ya girgiza a hankali,koda haka ne.....amma yana buqatar neman soyayyar a gurin da GIRMA da GIRMAMAWA suke aiki.....ba gurin da wasu dabi'u suke taka rawarsu ba da salon mummunar rawa da ba girmamawa sam a cikin ta.

*AKHNAN*

A daren batasan me takeji ba,tsakanin duniya da lahira batasan inane zaifi mata dadi da sauqin rayuwa ba. Saqon data samu na kaitsaye daga gurin SULTANE kan cewa kada ta kuskura ta fita daga masarauta shine abinda yafi komai gigitata. Batasan daga inda yaji batun ba,duk da kusan dukka hadiman sassanta sun sani cewa tana shirin komawa Niamey ne,to amma kuma ba wanda yake da access da sultane da har zai shaida masa hakan. Mammina bata sani ba,bata ma saurareta sunyi magana ba ballantana ta gaya mata,koda mammina din taji bata tunanin zata gayawa sultane wata magana a kanta da zata sanyata tunzura.

Morsa safiyya ce tazo ranta,idan ita keda alhakin gaya masa ya akayi tasan da tafiyar?. Wadannan tunani da bacin ran daya hade mata guri daya ya sanya takejin zuciyarta da kanta kamar zai fashe.

Ta yiwa sultane abinda takeso a tunanin ta,ta daura aure,auren kuma baije ko ina ba.......wanda hakan tana kallonsa a matsayin nasu laifin. Tayi iya nata qoqarin na cika musu burinsu,don me yasa ita din ba za'a qyaleta ta koma rayuwarta ta baya ba?.

Ko meye ya faru BATA DA LAIFI ba ita keda alhakin faruwar komai ba. Ta nuna musu illar sanyo rayuwar wani d'a namiji cikin rayuwarta,amma sun gaza fahimta,in da ace sun barta da tsarin ta,tunanin ta dama rayuwarta,da tuni yanzu wannan abun daya faru da ita bai faru ba.

Ganin kamar kwanyarta zata buga ya sanyata zura baby hijab baqi saman kanta bayan ta daure gashinta a tsakiyar kanta,wannan ya bawa wannan fuskar me dauke da wani irin kwantaccen kyau daman fitowa das tsakiyar fuskar hijab din,fuskar data wani fada,tayi fayau da ita,ta sanya flip flops baqaqe a qafarta,ta sauko daga saman gadon tana nufar qofar balcony dinta.

A jikinsa yaji an bude qofar,abinda ya sanyashi daga manyan idanunsa a hankali yana maidasu qofar data raba nata balcony din da bedroom dinta.

Kyakkyawar farar fuskarta ta bayyana tsakiyar baqin hijabin saqar qasar Malaysia. Kan qafafunta ya maida dubansa,tana takowa zuwa tsakiyar balcony din da wannan takun nata. Wani irin taku daya fita daban,yana gauraye da tashen quruciya gata izza da kuma mulki. Mamaki kadan ya kamashi,yadda take tafiya da raina ciki jama'a,haka still takunta dai yake a sanda ta kebe ita daya cikin duhun dare CHARACTER ce kenan,ba izza bace.....ba kuma wani salo bane na jin kai.

A nutse ya dinga tafiya da idanunsa jikin cotton sleep wear din jikinta fari qal. Kaman wani character dinta ne yawan amfani da abubuwa masu hasken kala da dare irin haka. Tsaf idanunsa suka tsaya saman baby face dinta,almond eyes dinta sun qara girma kadan,abinda ya sanya blue eyes dinta fita sosai. Idanunsa ya lumshe a hankali yana qoqarin janye kallonsa daga kan fuskarta,saidai kuma maimakon hakan ta faru,sai idanun nasa suka sauka kan dan qaramin bakinta dake dauke da wani nau'in siraran lips marasa kauri. A tsuke bakinta yake guri guda,abinda ya sanyashi tunawa sa noorah..

Hanya guda daya da kake gane ran noorah ya baci,zata tsuke lips dinta ne,sannan ta samu guri kawai ta zauna tana tara ruwan hawaye. A yanzun koda bai san mood dinta ba,amma tsaf ya karanci itama irin noorah dince. Akwai alamun bacin rai sosai tattare da ita,kamannin safeena kuma suna bayyana sosai saman fuskarta. Takun data qara yi tana zama saman ottoman ya sanyashi zare idanunsa da wani mugun qarfi yana jin zuciyarsa tana wani irin bugawa. Zaman da tayi ya fidda shatin cinyoyinta ya kuma fidda shape din cinyoyin sosai,abinda ya sanya shape dinta ya bayyana. Ya sauke idanunsa a nutse yana qoqarin saita tunaninsa gami da tuhumar kansa daya gaza kame ganinsa kamar yadda musulunci ya tanada.

Wayarsa tayi burari,sasaanyan ringing din maras hanayaniya daya saci kunnuwan akhnan,ya sanya hannu ya fidda wayartasa yana duban me kiran,daidai sanda ita kuma take aje dubanta a kansa.

Wani abu ya matse mata qirjinta. Me yasa duk sanda take cikin yanayi irin wannan.....yanayin baqinciki da bacin rai shi kuma a sannan yake bayyana a gabanta?. Me yasa sai sanda ranta yake a bace sannan take ganinsa?,wannan alama ce bame kyau ba.....alama ce dake nuni da rashin alkhairin dake tattare dashi.

Kiran bobbo muhammad dawud ne,baya jin zai iya daga kiran bobbo din a yau,yana buqatar nutsuwa,yana buqatar dogon nazari,yana buqatar ya yanke hukuncin daya gamsu dashi,hukuncin da bazai taba rayuwarsa ko aikinsa ba. Zai iya aminta yayima sultane kowanne irin taimako.....zai iya aminta ya soma dora sultane akan hanyar da zata masa jagora ya fahimci tarin baragurbin daya bawa muhalli cikin gidansa......amma ba lallai bane ya sanya kansa a matsala ba. Don haka ya maida wayarsa a aljihu,ya juya kuma a nutse yana komawa ciki abunsa ba tare daya yarda ya kalli koda sashen da take zaune ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Wani mugun tsaki taja,a jikinta takejin yasan ta shigo gurin,a jikinta takejin yasan tana gurin,tsabar izza ce kawai......da zallar rainin wayo. Yadda yake bagarar da dubanta idan tana guri wani abune da yake mata ciwo gami da bata haushi,mutum ce da batason kallo.....amma batasan me yasa abinda yakeyi idan ya ganta din yake qona ranta ba,duk da haka tafiso,bata qaunar ta daga idanu ta samu idanun namiji qur a kanta,amma nasa kauda idanun haushi yake bata,tana ji a ranta yana yin hakanne kawai don ya nunawa duniya itadin tozartacciya ce.....yana yine kawai don ya iyakance matsayinta da isarta,tunda ta sani,duk yadda takai gason a dinga qauracewa hada idanu da ita wannan abun yana yiwa maza da yawa wahala. Tana da wani irin kyau me sanyi da fusgar hankali qwarai.

Idanunta ta maida ta lumshe,tana shaqar wannan qamshin nasa. Duk yadda take avoiding qamshin,duk yadda ta jima tana gayawa kanta da koyawa ruhinta yadda zai qyamaci qamshin amma abun yaci tura,sannu a hankali saita tsinci kanta ba wani scent dake mata dadin shaqa irinsa,idan kuma ta jishin sai taji dukka sauran turarukanta basuyi mata ba.

Qarar shigowar saqo wayarta ya sanyata bude idanu. Daga fareeda ce daya daga cikin ma'aikatanta take shaida mata cewa sun samo kamfanin dake fidda wannan turaren,kuma sun tura musu saqon buqatar irin qamshin,da kuma fadin dukka adadin da suke buqata daga garesu,saidai branch dinsu na asali yana Ethiopia,akwai kuma biki bude sabon babban branch a dubai da india. Saqon ya mata dadi,musamman daya iso a daidai sanda ya dace,ta maida fareeda amsa,tana shirin ajiye wayar saqon aisa ya fado cikin harshen faransanci kamar yadda suka saba

_"Komai yana sake dagulewa a sahel couture,zuwa kowanne lokaci komai yana dab da durqushewa akhnan,bansan ya zamu shawo kan matsalar ba,kin kuma sake dage dawowarki bisa umarnin sultane,zanyi dukkan iyawata,amma nan da kwana goma dole na dawo agadez Festival de l’Aïr saura 'yan kwanaki"_. Ajiyar zuciya ta sauke,hankalinta a yanzu dukka ya tattara kan sahel couture,warning signs da aisa da shehnaz suke bata akan company din yayi yawa,batasan me yake faruwa har haka ba,batasan wanne irin matsala ce haka take ta qwaqular kamfanin ba.

_"Ina bakin qoqarina aisa,komai zai daidaita in sha Allah"_ abinda ta maidawa aisa kenan,don batasan wanne bayani zata mata ba. Sultane ya kamata ya fara fahimtar matsalar,shi ya kamata ya fara fahimtar akwai buqatar komawarta kan dukiyarka,kan kamfanin ta,amma a yanzun ko giyar wake tasha ta sani ba ita ba tunkarar sultane da kowacce magana. Qasan ranta taji zuciyarta tana baci,inda ta iya zagi ko mummunar magana ko fata,tabbas data aikesu ga duk wadanda suka shiga cikin wannan qaunar da soyayyar da fahimtar junan dake tsakaninta da mahaifinta na tsahon shekarun da tayi a raye,tu daga sanda aka haifeta zuwa yanzu.

Calendar ta shiga sanda ta tuna da Festival de l’Aïr. Wani bikin al'ada guda daya da cikin bukukuwan al'adunsu na buzaye da take matuqar so take kuma ji dashi. Biki ne da bata taba bari ya wuceta ba,saboda yadda yake bata nishadi sosai,yake kuma bata daman yin rayuwa cikin qawaye,rayuwa me 'yanci dake mantar da ita wacece ita. Amma wannan yanayin da aka jefata a ciki ya sanya ta manta da lissafin kwanaki?. Kai ta juya a hankali,koda sultane ma ya bata daman komawa Niamey,zataje ta dawo,don ba abinda zai sanya ta bari tayi missing wannan festival din.

★★★A makare ya tashi washegari,wannan ya sanya bashi ya zauna breakfast ba sai kusan sha biyu na rana. Breakfast dinsa ba wani me zafi bane tunda yazo agadez,sam ya kasa sabawa da salon tsarin abincinsu,komai baqo ne a harshensa,ya riga ya saba da abinci irin na qabilae oromo. A abu daya nasu yake sakin jiki sosai yasha shine shayinsu da yake dan kamanceceniya da al'adun qabilar oromo.

Nutsuwa ta kama komai nasa,don haka a komai nasa sai kaga nutsuwar ta bayyana kanta da da kanta. Kamar yanzu da yake zaune yana breakfast din,kansa da jikinsa dukka sun masa nauyi saboda rashin samun isashen bacci a daren jiya.

Daya daga cikin hadiman sassansa ne ya shigo,ya kuma zube kaman yadda al'adarsu ta sabar musu. Ba kasafai yake hanasu ba duk da bayaso,yana kiyayewa a komai kada yayi abinda ya saba da al'adarsu da har zai sanya a fahimci wani baqon abu tattare dashi ko yabar zargi kokwanto ko ayar tambaya a kansa.

"Giwa ce take sake sanarmaka da buqatar ganinka da gaggawa"

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
Chapter 87 · 0% Book details