← Book details Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 101

Sashe 93

Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunsa ya daga a hankali ya zubesu akan omar dake zaune a gabansa yana dubansa. A iya tsahon rayuwar aikinsu omar din bai taba jin wani aiki daya masa nauyi akai.....aiki me wahala.....aiki dake cike da mugun mummunan qulli ba irin wannan.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Shekara talatin ta binne komai?". Idanunsa haisam ya lumshe sannan ya budesu,a zahiri murmushi ne qasan zuciyarsa,amma kuma ya kasance salon murmushin nan nasa dake cakude da miskilanci,don haka ba kowa ke fahimta ba. Ya sani......aiki ne me girman gaske a gabansa......amma baisan me yasa wasan yake masa dadi ba. Komai idan ya tabo ta kowanne bangare sai ya dinga ganin qofa ce me girma take bude masa.

"Shekara talatin bata birne gaskiya ba......tadai lullubeta ne kawai".

"Amma ta wanna fuskar haisam ka fahimta.....komai ya qare fa,ba sauran wani abu da bazai bada haske" Kansa ya girgiza a nutse

"Komai bai qare ba omar......hasalima komai yana sake saitamu ne akan hanya,yana qara nuna mana hanya ne kawai"

"Nuna mana hanya?" Yayi tambayar yana duban haisam cikin mamaki,ta ina ya hango hanyar?.

"Sosai.....ka fadamin.....waye yake da iko ko qarfin gwiwar shiga dakin haihuwa ba tare da barin sunansa ba?" Shuru kada omar yayi kafin ya amsa.

"Only someone above the hospital administration"

"Good" Ya fadi yana gyada kansa da lumsassun idanunsa.

"Waye kuma zai sace yaro ba tare da ya kasheshi ba?"

"Wanda yake buqatar yaron a raye"

"Exactly" Haisam ya sake amsawa omar da wani low tune.

"Amma koda hakan gaskiya ne.....there's no way to prove it now"

"I'm not looking for proofs.....I'm looking for pressure" Ya amsa masa calmly da wani accent cikin English dinsa me wani irin dadi saboda saboda da oromian language da yayi.

"Pressure on whom?" Wannan karon dole wannan sassanyan murmushi ya subuce,kyawawan labbansa suka motsa kadan.

"On the person who has spent thirty years protecting silence"

"Mammina?" Kai tsaye omar yayi tambayar yana duban haisam"

"May be.....amma ka sanya idanu.....mutanen dake dauke da tsaffin sirrika suna da saurin nuna kansu fiye ma da masu laifi a wadansu lokutan". Komai omar ya gama fahimta.....ya gama gane kuma inda haisam ya sanya gaba. Shuru kawai maleek yayi dake zaune a gefe sannan ya saki qaramar ajiyar zuciya. Iya zaman da yayi da aminan nasa a wannan dan taqin ya bashi tabbaci cewa aikinsu sai CIKAKKEN NAMIJI JARUMI daya amsa sunansa. Ya fahimci abubuwa masu yawa,yarukan da baka isa ka iyashi ba idan kai din ba mallakin intelligence agency bane......da gaske aikin na masu INTELLIGENT ne.

" Aure zanyi" Haisam ya saki maganar hankali kwance sanda ya jawo system dinsa da zummar turawa bobbo wasu bayanai

*_Ayimin afuwa,yau dai baqi nayi,ban samu daman rubuta abun arziqi ba,ina fata za'ayimin uzuri,naso yau muzo gurin😂,don nasan abinda duk muke jira kenan harda nima😂_

_na gode sosai,na gode da qaunarku da jumurin bibiyata_🙏🏽

SON SO🥰🥰🙏🏽

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/13, 12:26] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 82*

Dif wuta ta daukewa omari da maleek,kada ma omar yaji labari shida yafi kasancewa da haisam tsahon lokaci sama da kowa.

Yadda sukayi shuru haka yaci gaba da matsa system dinsa hankali kwance,ya basu isashen lokaci da zasuyi mamakinsu su gama,saboda ya sani mamaki dole ne......basu kadai bama,koma waye yazo da wannan maganar tsakaninsa dashi mamakin shine abu na farko da zai fara yi.

Sunsan halinsa dukkaninsu,tunda har yayi shuru bazai sake cewa dakowa komai ba,sai idan kai ka buqaci qarin bayanin.

"Wai.....da gaske kake ko wasa?" Omar ya fadi ba tare da samun yaqini cikin maganarsa ba,saboda kuwa yafi kowa sanin halin haisam din,baya fadin magana sau biyu......baya qarya koda kuwa da wasa ne......sai wasan ma da baya cikin tsarin yanayin dabi'ar halittarsa gaba daya.

"Aure zanyi omar,da gaske nake" Ya sake maimaitawa very calm,abinda ya sake tsumasu da gaske,ya sake kuma tabbatar musu abinda yake fadi din da gaske yake. Tashi maleek yayi daga relaxing din da yayi cikin kujera,ya zauna sosai yana duban idanun haisam dake saman system abinsa hankali kwance. A hankali dariya ya kubcewa omar,don hankalinsa ya gaza gasgata abinda kunnuwasa suka ji masa,duk da baida yaqinin ba gaskiya haisam yake fadi ba. Bai motsa ba bai kalli omar ba,ya barshi yayi dariyarsa yadda yakeso.

Sosai maleek ya tsareshi da idanu,yana karantar gaskiyar dake sama fuskarsa. Sai ya motsa labbansa a hankali.

"Haisam......aure fa?,a daidai wannan lokacin?" Sai a sannan ya dauke dubansa daga kan system din ya zubesu a fuskar maleek. Ya karanci maleek ya soma gasgata maganarsa shi yasa yaga yana da lokacin sake fahimtar dashi.

"Yes.....aure maleek,nan da juma'a in sha Allah.....kwana uku kacal masu zuwa" Idanu suka waro gaba dayansu,omar yana jin kamar wata dabi'a da basusan haisam da ita bane yake qoqarin fara kwatantawa. Suman wucin gadi sukayi,kafin maleek ya qara aro qarfin hali

"Amma haisam wanne irin cin amana ne wannan?......ba sign ba signal......ba alamar komai?". Ya fada yana jin nauyi da girman al'amarin. Bai ce masa komai ba......har zuwa sanda omar yayi nasa qoqarin.

"Wacece wannan a kwana uku kawai haisam?......kwana uku fa?,ko saamee ce?"

"Akhnan ce" Yayi maganar sanda ya zubewa omar dukkanin manyan fararen idanun nan nasa dake da wani irin kwarjini me narka zuciya.

Zabura omar yayi ya miqe tsaye,fuskarsa da wani irin mixed emotion,mamaki......kokwanto.....farinciki da kuma zallar rudewa.

"Akhnan.....akhnan Muhammad hammud?......dama kuna soyayya haisam baka taba bari na fahimci komai ba?" Omar yayi tambayar wadda maleek ma shi sam a wannan karon ya kasa tambaya. Idanunsa ya janye daga kan omar,sai kawai ya fara tattare kayansa da xummar barin gurin,bayajin zai iya zama ya amsa tarin tambayoyin daya fuskanci sun shirya yinsu a kansa d'aya bayan d'aya.

Caraf maleek ya riqe hannunsa gam,sanin halinsa sarai zai iya barinsu cikin rudaninsu. Ba kowanne lokaci yake zama yayi dogon bayani ba.

"Bakka eessayyuu deemuu hin dandeessu (ba zakaje ko ina ba).......akhnan dai kake magana akai kaman yadda omar ya fada?,nima inaso na sani" Maleek ya fadi shima yana tsareshi da idanunsa.

"Eh.....itace" Ya amsawa maleek kai tsaye yana duban cikin idanunsa kamar yadda shima yake duban nasa. Sake masa hannu maleek yayi yana sakin wata dariya shida omar me cike da nishadi,yasan kwanan zancan......yasan kuma me zai faru,idan ma ya tafi a yanzu be tsira ba,tunda suka fara wannan dariyar,sai kawai ya koma ya zauna salin alin,yayi relax sosai cikin lallausar sofa din yana qare musu kallo.

Tsam maleek ya miqe,ya soma takawa yana nufar briefcase dinsa yana fiddo system dinsa.

"Wannan labarin bazai cika ba,bazai kammala ba sai dasu khadeem a kusa......nikam bazanyi wannan cin amanar ba,ayi wannan sha'anin babu su?" Ya qarasa fada yana daidaita system din nasa gami da qoqarin kiran kowa a cikinsu. Idanu kawai ya lumshe,gwara ya barsu suyi iyayinsu,ba lallai su fahimci komai ba......ba kuma lallai yayi musu bayanin komai da komai ba.

Bayaso su kalli lamarin da wani idanu daban,shuru shi yafi dacewa ya zama amsa......koda kuwa hakan yana nufin zasu amince da cewar SHI YA ZABOTA.....shi yake sonta.

Wani irin aminci ne a tsakaninsa da zai wahala wani yaga kiran wani ya share,don haka cikin qaramin mintuna ya hadasu gaba daya,sai gasu sun cika su bakwai cif harda haisam da omar da maleek din dake guri daya a gari daya.

"Me yake faruwa da mr lowering gaze?". Naseeb dake zaune ciki parlor din gidansa yana shan fruit da alamu ke nuna matarsa ce a gefe tana yankawa tana miqa masa ya fadi,ganin har suka gama zama online dukkaninsu haisam bai motsa ba bai kuma ce komai ba.

Murmushi da yafi kama da dariya maleek yayi,irin wanda sunsan ba dabi'arsa bace. A cikinsu dukka shida haisam dinne keda wannan jinin sarautar a jikinsu,so izza wani lokacin zuwa musu kawai takeyi. Dariyar maleek taja hankalin kowa,don Omar gabadaya ya kurumce,bayajin yana da bakin bayani,yayin da ta wani gefe kuma zuciyarsa ta kasa gasgatawa da kuma yarda da inganci da sahihancin auren.

"Lowering gaze ya qare daga yau......mr man aure zaiyi,nan da kwanaki uku masu zuwa kawai". Dariya suka sanya gaba daya,kowa da irin abinda zai fada,abinda ya sanya haisam zama sosai yana ware idanunsa da suka dan sauya launi a kan screen din,wannan ya basu daman ganinsa sosai,sai kuma kowa ya fara komawa nutsuwarsa. Shuru ya ratsa ko ina,ya bude baki da nutsuwar nan da suka sanshi da ita.

"Da gaske maleek yake gaya muku.....ruwanku ku yarda.....ruwanku kuci gaba da duban abun ta fuskar wasa" Yana kaiwa nan ya sake relaxing abinsa,saidai kunnuwansa suna tare dasu,duk da qasa qasa yake kallon screen din da salon kallon da zaka dauka bacci yakeyi. Maganan ta saukarwa kowa a bazata.

"Haisam dinnan da baya iya kallon mace sai biyu?......guys a duba maganan nan fa?" Amjad ya furta sounding so amazing.

"I'm serious" Ya fada da wata murya kaman mejin bacci,yanayin dake nuna musu ya gundura da yadda suketa avoiding labarin.

"Wacce jarumar?.....wacce kuma me tsananin sa'ar ce?" Mutallab ya tambaya cikin son jin wadda tayi nasarar.

"Akhnan" Omar ya amsa wannan karon kai tsaye yana tallabe da kumatunsa,irin mamaki ya masa kisan mummuqe.

Yadda suka kama sunan kusan lokaci daya ya sanya haisam sake girman idanunsa yana jifan omar da kallo. Da alama akwai wani labari nata da suke dashi?. Tambayar data girmi tambaya a wajen haisam saidai qarin tabbaci,don kowa maganan naseeb ta tabbatar masa da haka.

"Akhnan?......the princess of agadez?.....stubborn and silly girl?" Naseeb ya jero gaba daya. Maganan ya sakashi qarasa bude idanunsa gaba daya ya azashi kan omar. Omar din da yaqi yadda ya kalleshi.

Komai kenan da yake fadi akan yarinyar akan kunnen omar ne?,komai omar yana hankalce dashi kenan?,komai omar ya labartawa su khadeem.
Chapter 93 · 0% Book details