Sashe 66
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SAKI UKU?,CIKIN KWANA UKU KACAL?,taji wani sashe na zuciyarsa yana jaddada tambayarsa a gareta,tambayar da batasan ita dince ko zuciyartata bane zasu baiwa kanta da kanta amsa ba.
Wanne irin aure mammina tayi mata?,ta samu kanta da tambayar kanta.
"D wanne idanu zata kalli duniya?,da wanne idanu zata kalli al'ummar masarautarta?,da kuma wanne idanu ne IZZARTA zataci gaba da tabbata?" Ta yiwa kanta Tambayar. Saita dinga jin kamar kowa ya tattaru a gurin yana kallonya,hadiman da dukkaninsu qasa sauke kalla saboda girmamawa a gareta saita dinga jin kamar satar kallonta suke,kamar dariya suke mata,don haka ta daga qafafunta da sassarfa ta fara barin gurin.
Birra ce kawai yake da qwarin gwiwar binta,ta daga qafa da sauri tabi bayanta hankalinta a matuqar tashe. Yanayin yadda akhnan din ke tafiya da wata irin sassarfa ya sake daga hankalin birra,don wani yanayi ne da bata taba ganin akhnan din a cikinsa ba.
Ba birra kawai ba,yanayin tafiyar akhnan din saiya zama abun kallo cikin masarautar. Duk inda zata jefa qefarta duk da tarin dokar taqaita kallo dake wuyan duk wani d'an masarautar,amma a yau sai kowa ke binta da kallo saboda ganin canji a yanayin tafiyarta,uwa uba kuma birra da suke gani biye da ita,abinda yabar ayar tambaya a zukatan mutane,suka kuma shiga neman ba'asin wannan sauyin tafiya tata.
*MAMMINA*
A nutse take karbar labarin yadda abubuwa ke tafiya na kasuwancinta dake qasar habasha,wanda ba wanda yasan itace mamallakiyar abubuwa masu yawa da kamfanoni na qasar. Adadin ribar data samu a wannan shekarar kawai take saurarar lissafinta,daidai sanda taga shigowar yalwa da wani irin yanayi da ya sanyata datse kiran ba tare data shirya hakan ba.
"Al'amari ya lalace Allah ya baki yawan rai.......komai ya dagule ranki ya dade". Haka kawai mammina din taji wani matsanancin faduwar gaba ya saukar mata. Ta sani muddin tanason labarin abinda ke wakana cikin gidan,ba qarya ba gauraye a ciki to yalwa take sanyawa akan komai,kuma a yanzun tasan kalan aikin data tura yalwa din tayi mata.
Ta sanya idanu akan dukkan wani abu daya gudana tsakanin almaz da akhnan. Ta tabbatar ta gama sallamar almaz da dukkan wani leakage da zai sake dasa kansa da shiga gami da bude qofar zuciyar akhnan komai qanqantarta. Ita tasan akhnan,tasan dukkan wani zabi nata,tasan meye abinda yafi komai burgeta,tasan kuma hanyoyin da zasu yiwa namiji sauqi wajen kama zuciyarta. Tunda ta shiga shekarun 'yammatanci.....shekarun da sarauta suka fara mata yawo cikin jini.....izza kuma ta soma mamayar zuciyarta,kalar izzar da mammina ta tabbatar ta mata mugun kamu,tun a sannna ta cika wani sashe na kwanyarta da karantar kalar zabinta cikin MAZA. Ta tattara komai kuma ta bawa almaz,ta tattare komai ta karanta masa,saidai yalwa ta gaya mata,bataga alamun shi din me sha'awe sha'awe bane game da harkar mata,amma tayi challenge na yalwa din
"Wani lokaci kina da gajeriyar kwanya me cike da gajeran tunani.....karki mata cikin gidan da zina ta zama ado ga kowanne d'a namiji ya taso,ta yaya halittar 'ya'ya mata zata gaza burgeshi?. Abu daya na sani biftu tana da kwarjini,tana kuma yiwa maza da yawa kwarjini,zata yuwu abinda ya sanya bai gama iya dorata a hanya ba kenan".
"Yalwa.....kina mantawa da cewa daurin talala nayi miki?"
"Na sani Allah ya taimakeki" Yalwa din ta fada tana jin numfashinta yana mata nauyi. Wani irin tsoro ne yake kama yalwa din idan ta tuna abinda ya sanyata shigowa gaban mammina.
"Meke tafe dake?" Ta tambayeta tana komawa gami da zama saman sofa tana sake hade girarta sosai.
"Saqon yayimin nauyi......yanayin ya girmi abinda bakina zai iya fada.....idan kuma kin matsa zan fada din,amma saidai kiyimin aikin gafara" Bayanan yalwa ba abinda suke qara mata face adadin bugun zuciyarta,haka kawai takejin zuciyarta na wani tsinkewa,amma duk da haka ta tattara izzarta da dakiyarta guri daya.
"Ci gaba da wannan banzan dogon sharhin naki shine abinda zaifi baki matsala sama da komai" Mammins ta fadi tana sake tsuke fuskarta.
"Kiyimin rai....kiyimin afuwa.....almaz ya saki akhnan saki uku" Yalwa ta fada muryarta tana rawa,don tana hangen girman abinda zai iya biyo baya.
Cak komai na mammina ya dakata daga aiki,wata irin tsawa ta sauka saman kanta. Duban yalwa kawai takeyi kamar itace almaz din,tsahon wasu sakanni sannan ta iya buda bakinta tana jin wani irin razani yana ratsa rayuwarta.
"Sake maimaitawa yalwa......amma ki tabbatar bakinki yasan abinda yake fadi,don wannan maganar ta tabbata qarya ce,ki tabbatar da cewa hukuncin kisa ne kawai zaiyi daidai da laifinki"
"Ina me miki rantsuwa da girman zatin Allah almaz ya saki sarauniya biftu saki har uku".
Sam batasan ta miqe tsaye zumbur ba,sam batasan ta dora hannuwanta dukka biyu saman kanta ba,tana shirin rusa gigitaccen ihu saita tuna da yalwa a gurin,don haka saita sulale kawai,sai gata zaune a dandaryar qasa ta zauna sosai,abinda ya sake gigita yalwa kenan ta sake durqushewa sosai,ganin me bada umarnin a zauna a qasa yau shine a qasa.
A zaune take amma jiri takeji,sai takejin bata da wani sauran hikima,kwanyarta ta daina aiki gaba daya,da wata irin hautsinanniyar muryar tace da yalwa.
"Kiramin tafisu.yanzu yanzu" Jikin yalwa na rawa ta dauki wayar da mammina kan bada umarni a kira mata wani ta fara kiran tafisun,duka duka kuma kira biyu tak ta daga.
A taqaice ta sanya yalwa isarwa da tafisu saqon,saqon da yayi masifar girgixa tafisun
"Dabarar farko da zaa fara amfani da ita kafin na iso.......yalwa ta kama bakinta,kada wani a waje yasan da maganar sakin,zamu gyara komai kamar komai din bai faru ba.
" Tafisu mun kusa mu talatin sanda yay furucin,bansa wa zaa hana magana ba,hasalima wasu da suke gurin ba zan ko shaida fuskokinsu ballantana a hana maganar fita ga sauran mutane". Yalwa ta fadi da dukkan tabbacinta da yaqini. Ta sani,a iya adadin gutsiri tsoma irin na gidan sarauta,a iya adadin cece kuce da qananun maganganu irin na hadimai,koda gaban mutum guda ne hakan ya faru ba shakka zai wahala a dakatar da yaduwar maganar,ballantana gaban mutanen da batasan adadinsu ba.
Dubanta kawai mammina takeyi,tana jin wani tashin hankali yana ratsata,tashin hankalin da ba zata tuna lokaci makamancin wannan da taji irinsa ko shigensa ba.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tana jin wacce irin cuta ce wannan almaz yayi mata?,wanne irin asararre kuma fallasassen yaro ne irin wannan?. Tana ji a ranta da zuciyarta,ya ruguza dukkan wani aiki nata,ya ruguza dukkan wata wahala tata ta shekara da shekaru. Doguwar tafiyar dake qunshe da dubban watanni......take qunshe da miliyoyin kwanaki,take qunshe da biliyoyin kwanaki?.....a yau cikin mintuna qalilan ya bata komai?. Nasarar kwana uku kacal?,kwana uku fa kawai nasararta ta kasance.
"Tafisu......nasarar kwana uku kawai zanci a iya shekarun dana nata ina jiran wannan ranar?" Ta tambayi tafisu da har yanzu take riqe da wayar,nata kan itama yana kullewa ba tare da tasan ainihin abinyi ba.
"Kiyi haquri,xamu shawo bakin zaren matsalar.....komai zai koma daidai" Ta fadi cikin salon kwantar da hankali.
"Ki sameni gidan yanzu" Kawai mammina ta fadi tana kashe wayar. Dubanta ta mayar ga yalwa.
"Inason zuwa na samu tamim da almaz kafin maganar ta fara yaduwa,inaso na gani ko akwai hanyar gyara". Ta fada tana jin komai ya jagule mata,wayo kuma da dabararta sunata narkewa gami da sulalewa suna bin ruwa.
*HAISAM*
A iyaka awannin yana zaune ne kawai yana monitoring dukkan wasu cameras daya saka aka maqala masa cikin dabara tsakanin d'akunan ajiyar sultane,morsa safiyya.....da kuma mammina.
Cikin awanni ya sake yaqini da samun tabbacin lallai akwai abubuwa masu tarin yawa a daidai gurin,akwai abubuwa masu nauyin da aka lullube cikin dakin ajiyar.
Numfashi ya zuqa a hankali yana fesarwa,ya maida bayansa ga lallausar kujerar da yake jingine a kanta. Idanunsa ya maida ya lumshe,sai maganganun nanay suka fara dawo masa a hankali. Fuskar safeena ta soma gilmawa cikin duhun idanunsa,kafin a hankali ta juye zuwa fuskar akhnan. Wannan fuskar da bai taba ganin gilmawar dariya ta cikinta ba,sabanin ta safeena da a kowanne hoto fuskarta dauke take da murmushi. Wannan fuskar dake cike da wata irin izza tsiwa da rashin sassauci. Da dukka qarfinsa ya sanya yana ture tunaninta gefe guda,amma sai wani sashe na zuciyarsa ya turashi zuwa wani tunanin na daban.
ALAQARSU da nanay dinsa......alaqar safeena safiyya da nanay dinsa......ita din wani tsatso ne daga jinin da NANAY dinsa ke matuqar so......
"Jininsa ce,yar uwarsa ce" Maganan ya harba cikin kansa,nanay na yiwa mahaifiyarta wani irin qauna,hakan na nufin KULAWA da dukka abinda zai cutar da ita zai zamana kamar kyautatawa ne kai tsaye zuwa ga safeena da bata raye?. Farantawa safeena kuma yana daidai da farantawa nanay dinsa?.
Idanunsa ya bude a hankali sanda sunan ALMAZ ya harba cikin kansa. Barinta tayi tarayya da almaz din a matsayin miji ya zama tamkar CIN AMANAR amincin da sultane ya bashi......wannan ya sanya a wannan daren yake jin bazai daga qafa ba har dai yakai ga ma'ajiyar mammina......inda yake da tabbacin a can din zai samu HUJJA ta qarshe......HUJJAR da zata bashi damar fita da mammina hankali kwance zuwa Ethiopia.....hujjar da zata sanyashi dakatar da duk wata alaqa tsakanin akhnan da almaz don ceto rayuwarta.
A hankali tunaninsa ya soma shawagi cikin tarin tarakunan da yake hangen yarinyar dumu dumu a tsakaninsu. Daya bayan daya ya dinga dauko dukkan wani hasashe yana hadawa da dan uwansa. Cikin dukkan wani jini da zai buga zuwa sassn jikinsa yake jin qarfin tabbacin MAMMINA HATSARI CE. ita kadai ta sarqa abubuwa masu yawa?,ita kadai ta qulla tarin abubuwan da hankalin me hankali bazaikai kai ba?,ita kadai ta zama sanadi ta bangarorin da zaka dauka basu da wani alaqa da junansu?.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/3, 20:17] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 59*